Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 3/1 p. 29-p. 31
  • Darussa Daga Littafin Esther

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Darussa Daga Littafin Esther
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • DOLE NE SARAUNIYAR TA SHIGA TSAKANI
  • (Esther 1:1–5:14)
  • JUYI BAYAN JUYI
  • (Esther 6:1–10:3)
  • Jehobah Zai yi Tanadin “Gudunmuwa da Ceto”
  • Ta Nuna Hikima da Gaba Gaɗi da Kuma Sadaukarwa
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Ta Kāre Bayin Allah
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Mordekai Da Esther
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Esther Ta Ceci Mutanenta
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 3/1 p. 29-p. 31

Maganar Jehobah Rayayyiya Ce

Darussa Daga Littafin Esther

KAMAR dai ba za a sami cikas wajen tafiyar da wannan shirin ba. Shirin yi wa Yahudawa kisan kiyashi. A rana guda da aka ƙayyade, ana shirin hallaka dukan Yahudawan da suke zaune a daular, da ta haɗe daga Indiya zuwa Habasha. Wannan shi ne tunanin da wanda ya yi ƙullin yake yi. Amma ya mance da wani abu mai muhimmanci. Wato, Allah wanda ke sama zai iya ceton zaɓaɓɓun mutanensa daga kowane irin yanayi mai wuya. An rubuta labarin wannan ceto cikin littafin Esther na Littafi Mai Tsarki.

Wani tsoho Bayahude ne mai suna Mordekai ya rubuta shi, littafin na ɗauke ne da labarin sarautar shekara 18 na Sarkin Farisa, Ahasuerus, ko kuwa Xerxes na 1. Wannan labarin mai ban mamaki ya nuna yadda Jehobah ya ceci mutanensa daga ƙullin maƙiyansu, ko da yake bayinsa sun yaɗu a ko’ina a cikin daular. A yau, sanin wannan yana ƙarfafa bangaskiyar mutanen Jehobah waɗanda suke bauta masa a ƙasashe 235. Bugu da ƙari, mutanen da aka ambata a cikin littafin Esther sun kafa mana misalan da ya kamata mu bi da kuma waɗanda da za mu ƙi. Hakika, “maganar Allah mai-rai ce, mai-aikatawa.”—Ibraniyawa 4:12.

DOLE NE SARAUNIYAR TA SHIGA TSAKANI

(Esther 1:1–5:14)

A shekara ta uku ta sarautarsa (493 B.C.E.), Sarki Ahasuerus ya yi babban biki na sarauta. Sarauniya Vashti gwanar kyau, ta gamu da fushin sarkin kuma aka cizge ta daga maƙaminta. A cikin dukan kyawawan ’yan matan da suke ƙasar, aka zaɓi Bayahudiya Hadassa ta zama sarauniya. Bisa umurnin da Mordekai ɗan kawunta ya ba ta, Hadassa ta ɓoye sunanta na Yahudanci ta yi amfani da sunanta na Farisanci, wato Esther.

Da shigewar lokaci, aka ɗaukaka Haman mai fahariya zuwa matsayin firayim minista. Haman ya fusata domin Mordekai ya ƙi ‘ya rusuna ya yi masa mubaya’a,’ hakan ya sa ya yi ƙulle-ƙulle don ya halaka dukan Yahudawan da suke cikin Daular Farisa. (Esther 3:2) Haman ya rinjayi Ahasuerus ya amince da wannan ƙullin kuma ya sa sarkin ya ba da umurni don a yi wannan kisan kiyashi. Hakan ya sa Mordekai “ya sa tsummoki da toka.” (Esther 4:1) Dole ne Esther ta shiga tsakani. Ta gayyaci sarki da firayim ministansa zuwa wani biki na musamman. Sa’ad da suka hallara, Esther ta roƙe su su sake zuwa domin wani bikin kuma da za a yi washegari. Hakan ya sa Haman farin ciki. Duk da haka, Haman yana baƙin ciki domin Mordekai ya ƙi ya daraja shi. Haman ya ƙulla yadda zai kashe Mordekai kafin bikin na washegari.

Tambayoyin Nassi da aka Amsa:

1:3-5—An yi bikin ne har tsawon kwanaki 180? Surar ba ta ce bikin ya ɗauki tsawon kwanaki da yawa haka ba, amma ta ce sarkin ya nuna wa shugabanni dukiyarsa da kuma wadatar mulkinsa mai daraja har kwanaki 180. Wataƙila sarkin ya yi amfani da wannan biki ne domin ya nuna ɗaukakar mulkinsa don ya burge shugabanni ya kuma tabbatar musu cewa zai iya cim ma shirinsa. Idan haka ne, sura ta 3 da ta 5 wataƙila suna nuni ne ga biki na kwana 7 da aka yi bayan taron na kwana 180.

1:8—A wace hanya ce ‘ba a yarda kowa ya tilasta wa wani ba domin shan bisa ga shari’a’? A wannan bikin, Sarki Ahasuerus ya yi watsi da al’adar Farisawa na ƙarfafa juna su sha barasa daidai kima a irin wannan taron. Wata majiya ta ce: “Idan sun ga dama suna iya sha su yi tatil ko kuwa su sha ɗan kaɗan.”

1:10-12—Me ya sa Sarauniya Vashti ta riƙa ƙin zuwa wajen sarki? Wasu manazarta sun ce wataƙila sarauniyar ta ƙi yin biyayya ne domin ba ta son ta zubar da mutuncinta a gaban bakin sarki da suke cikin maye. Ko kuwa wataƙila wannan kyakkyawar sarauniyar ba ta da ladabi ne. Ko da yake Littafi Mai Tsarki bai ambata dalilinta ba, mutane masu hikima na zamanin sun ga ya kamata a ɗauki mataki a kan rashin biyayyar da ta yi, kuma irin wannan halin marar kyau da Vashti ta nuna zai iya shafan dukan matan daular Farisa.

2:14-17—Esther ta yi lalata da sarkin ne? A’a. Tarihin ya ce, da safe ana maida matan da aka kai gaban sarki gida na biyu a ƙarƙashin kulawar bāban sarki, “wanda ke lura da ƙwaraƙwarai.” Da haka, matan da sarkin ya kwana da su sun zama ƙwaraƙwaransa. Bayan da Esther ta ga sarki ba a kai ta gidan ƙwaraƙwarai ba. Sa’ad da aka kawo Esther gaban Ahasuerus, “sarki kuwa ya ƙaunaci Esther gaba da dukan matan, ta kuwa sami tagomashi da alheri a wurinsa gaba da dukan yan budurwai.” (Esther 2:17) Ta yaya ta ‘sami tagomashi da alherin’ Ahasuerus? Kamar yadda ta sami tagomashi a wurin dukan mutanen da suka ganta. “Budurwan kuwa ta gamshe [Hegai], ta kuwa sami alheri a gareshi.” (Esther 2:8, 9) Hegai ya yi mata tagomashi ne domin abin da ya gani, wato kyaunta da kuma halayenta na kirki. Hakika, “Esther kuwa ta sami tagomashi a wurin dukan waɗanda suka gan ta.” (Esther 2:15) Hakazalika, abin da sarkin ya gani a Esther da ya burge shi, shi ya sa ya ƙaunace ta.

3:2; 5:9—Me ya Mordekai ya ƙi ya rusuna wa Haman? Ba laifi ba ne Isra’ilawa su nuna bangirma ga wani mai matsayi ta wajen rusuna masa. Amma, game da Haman kuwa, batun ya fi na girmamawa. Haman Ba-agagi ne, wataƙila Ba’amalike, kuma Jehobah ya ce zai halaka Amalekiyawa. (Kubawar Shari’a 25:19) Ga Mordekai kuwa, rusuna wa Haman batu ne na rashin aminci ga Jehobah. Ya ƙi yin haka gaba ɗaya, kuma ya faɗi cewa shi Bayahude ne.—Esther 3:3, 4.

Darussa Dominmu:

2:10, 20; 4:12-16. Esther ta bi ja-gora da kuma shawarar ƙwararren mai bauta wa Jehobah. Hikima ce mu ‘yi biyayya da waɗanda ke shugabannanmu, mu sarayadda kanmu garesu.’—Ibraniyawa 13:17.

2:11; 4:5. Ya kamata ka da ‘mu lura da namu abu kaɗai, amma kowane a cikinmu yana lura da na waɗansu kuma.’—Filibbiyawa 2:4.

2:15. Esther ta nuna filako da kuma kamun kai domin ba ta nemi ƙarin kayan kwalliya ko kuwa tufafi mafi kyau fiye da waɗanda Hegai ya ba ta. “Ɓoyayyen mutum na zuciya, cikin tufafi waɗanda ba su lalacewa, na ruhu mai-ladabi mai-lafiya” ne ya sa Esther ta sami tagomashi a gaban sarki.—1 Bitrus 3:4.

2:21-23. Esther da Mordekai misalai ne masu kyau na “biyayya da ikon masu-mulki.”—Romawa 13:1.

3:4. A wasu yanayi, zai iya kasancewa hikima mu ɓoye inda muka fito kamar yadda Esther ta yi. Amma, sa’ad da ya zo ga ɗaukan mataki a kan batu mai muhimmanci, kamar ikon mallakar Jehobah da kuma amincinmu, bai kamata mu ji tsoron bayyana cewa mu Shaidun Jehobah ba ne.

4:3. Sa’ad da muka fuskanci jaraba, ya kamata mu yi addu’a ga Jehobah domin mu sami ƙarfi da hikima.

4:6-8. Mordekai ya nemi shari’a ta warware haɗarin da ƙullin Haman ya jawo.—Filibbiyawa 1:7.

4:14. Abin koyi ne dogarar da Mordekai ya yi da Jehobah.

4:16. Domin ta dangana ƙwarai ga Jehobah, cikin aminci da gaba gaɗi Esther ta fuskanci yanayin da zai iya kai wa ga mutuwarta. Yana da muhimmanci mu koyi dogara ga Jehobah ba ga kanmu ba.

5:6-8. Domin ta sami tagomashin Ahasuerus, Esther ta gayyace shi zuwa biki na biyu. Ta aikata da hikima, mu ma ya kamata mu yi haka.—Misalai 14:15.

JUYI BAYAN JUYI

(Esther 6:1–10:3)

Yayin da al’amuran suka bayyana, sai reshe ya juye da mujiya. Aka rataye Haman akan gungumen da ya yi don ya rataye Mordekai, kuma wanda ake son a rataye ya zama firayim minista. Ƙullin da aka yi wa Yahudawa na kisan kiyashi fa? Shi ma zai juya.

Esther mai aminci ta sake yin magana. Ta sadaukar da ranta ta wajen bayyana a gaban sarki don ta roƙe shi ya hana abin da Haman ya ƙulla. Ahasuerus ya san matakin da ya kamata ya ɗauka. Saboda haka, sa’ad da lokaci ya kai na kisan, maimakon a kashe Yahudawa, sai aka kashe waɗanda suke son su yi musu illa. Mordekai ya ba da umurni cewa a riƙa yin Bikin Purim kowace shekara don tunawa da wannan babban ceto. Da yake shi ne wazarin Sarki Ahasuerus, Mordekai “yana aikin alheri ga al’ummatasa, yana maganar salama ga zuriyassa duka.”—Esther 10:3.

Tambayoyin Nassi da aka Amsa:

7:4—Ta yaya ne halakar Yahudawa za ta jawo ‘hasara ga sarki’? Ta wajen yin bayani cikin dabara game da sayar da Yahudawa a matsayin bayi, Esther ta nanata cewa sarkin zai yi hasara idan aka halakasu. Azurfa 10,000 da Haman ya yi alkawarin zai bayar a ajiye cikin ma’ajin sarki ba su kai yawan kuɗin da za a samu ba, da a ce Haman ya yi ƙulli ne a sayar da Yahudawa a matsayin bayi. Da an cika ƙullin da Haman ya yi, da hakan ya kai ga mutuwar sarauniya.

7:8—Me ya sa bābannin sarki suka rufe wa Haman fuska? Wataƙila wannan na nufin abin kunya ko kuwa hukunci da ke tafe. Wata majiya ta ce, “a zamanin dā, ana rufe fuskar waɗanda ake son a kashe.”

8:17—Ta yaya ne “mutanen ƙasa iri iri suka zama Yahudawa”? Yawancin Farisawa sun zama Yahudawa shigaggu ne, domin suna tunanin cewa umurnin sarki na nuna tagomashin Allah bisa Yahudawa. Wannan mizanin na aiki a yau wajen cika annabcin da ke cikin littafin Zechariah. Ya ce: “Mutum goma daga cikin dukan harsunan al’ummai za su kama ƙafar wanda shi ke Ba-yahudi, su ce, Za mu tafi tare da ku, gama mun ji labari Allah yana tare da ku.”—Zechariah 8:23.

9:10, 15, 16—Ko da yake dokar ta umurce su su kwashi ganima, me ya sa Yahudawa suka ƙi yin haka? Babu shakka, ƙin da suka yi ya nuna cewa manufarsu ita ce su kāre kansu, ba wai su azurta kansu ba.

Darussa Dominmu:

6:6-10. “A bayan girman kai sai halaka, faɗuwa kuma tana biye da tada hanci.”—Misalai 16:18.

7:3, 4. Muna bayyana kanmu cewa mu Shaidun Jehobah ne, ko da hakan zai jawo tsanantawa?

8:3-6. Za mu iya kuma ya kamata mu roƙi gwamnati da kuma kotun shari’a don kāriya daga maƙiya.

8:5. Cikin dabara Esther ba ta ambata cewa sarkin yana da hannu a cikin umurnin da aka yi na hallaka mutanenta ba. Hakazalika, muna bukatar mu nuna basira sa’ad da muke yi wa manyan ma’aikatan gwamnati wa’azi.

9:22. Ka da mu manta da mabukata da ke tsakaninmu.—Galatiyawa 2:10.

Jehobah Zai yi Tanadin “Gudunmuwa da Ceto”

Mordekai ya nuna cewa manufar Allah ne Esther ta zama sarauniya. Sa’ad da aka yi musu barazana, Yahudawa sun yi azumi kuma sun yi addu’a don taimako. Sarauniyar ta bayyana a gaban sarki ko da yake ba a gayyace ta ba, kuma ta sami tagomashi a wurinsa. A daren, sarkin ya kasa yin barci. Hakika, littafin Esther na ɗauke ne da yadda Jehobah ya juya al’amura domin amfanin mutanensa.

Wannan labari mai daɗi na Esther yana ƙarfafa mu da muke zaune a “kwanakin ƙarshe.” (Daniel 12:4) A “kwanakin ƙarshe,” Gog na Magog, wato Shaiɗan Iblis zai kai wa mutanen Jehobah farmaki. Kuma manufarsa shi ne ya kawo ƙarshen masu bauta ta gaskiya. Amma, kamar a zamanin Esther, Jehobah zai yi tanadin “gudunmuwa da ceto” ga masu bauta masa.—Ezekiel 38:16-23; Esther 4:14.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba