Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 6/1 pp. 14-18
  • Farin Cikin Tafiya Cikin Aminci

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Farin Cikin Tafiya Cikin Aminci
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Albarkar da ke Kyautata Rayuwarmu a Yanzu
  • “Ba Ya Kan Haɗa Ta Da Baƙinciki Ba”
  • Albarkar Jehovah Takan Kawo Mana Wadata
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ka Yi Tafiya Cikin Aminci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Matasa Da Suke Faranta Wa Jehovah Zuciya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • ‘Zai Kusace Ka’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 6/1 pp. 14-18

Farin Cikin Tafiya Cikin Aminci

“Albarkar Ubangiji ta kan kawo wadata, ba ya kan haɗa ta da baƙinciki ba.”—MISALAI 10:22.

1, 2. Me ya sa ya kamata mu kiyaye shaƙuwa ƙwarai da abubuwa da ke tafe?

WANI mai ussan ilimi a ƙasar Amirka ya ce: “Yawan tunanin abubuwa da suke zuwa a nan gaba . . . yakan hana mu mu more abubuwa na yanzu.” Wannan gaskiya ne game da yaran da suke yawan tunanin zama manya sai su mance da amfanin yarantakarsu har sai sun wuce wannan lokaci.

2 Wani lokaci masu bauta wa Jehobah ma suna yin irin wannan tunanin. Ka yi la’akari da abin da zai iya faruwa. Muna ɗokin Jehobah ya cika alkawarinsa na maida duniya ta zama aljanna. Muna jiran rayuwa marar ciwo, tsufa, azaba, da kuma wahala. Ko da yake yana da kyau mu sa rai a waɗannan abubuwa, amma me zai faru idan muka shaƙu da albarka ta zahiri da ke tafe, muka mance da albarka ta ruhaniya da muke mora yanzu? Wannan zai zama abin kunya! Za mu iya yin sanyin gwiwa fiye da yadda muke tsammani kuma mu yi ‘ciwon zuciya saboda muradin da ba a biya ba.’ (Misalai 13:12) Matsaloli da wahaloli za su iya sa mu yi baƙin ciki kuma mu ji tausayin kanmu. Maimakon mu jimre wa matsaloli, za mu iya fara gunaguni. Za mu iya guje wa irin waɗannan abubuwa idan mu ka yi bimbini bisa albarkar da muke samu yanzu.

3. Za mu maida hankalinmu ga menene a cikin wannan talifin?

3 Misalai 10:22 ta ce: “Albarkar Ubangiji ta kan kawo wadata, ba ya kan haɗa ta da baƙinciki ba.” Abin farin ciki ne idan muka ga bayin Jehobah na zamani suna ci gaba a ruhaniya. Bari mu yi la’akari da wasu fasalolin ni’imarmu ta ruhaniya da kuma yadda za su shafe mu. Yin tunani game da yadda Jehobah ya albarkaci mutanensa masu ‘adalci wanda suke tafiya cikin kamalassa’ zai ƙarfafa ƙudurinmu na ci gaba da bauta wa Ubanmu na samaniya da farin ciki.—Misalai 20:7.

Albarkar da ke Kyautata Rayuwarmu a Yanzu

4, 5. Wace koyarwar Littafi Mai Tsarki ce take da muhimmanci a gare ka, kuma me ya sa?

4 Cikakken sani na koyarwar Littafi Mai Tsarki. Addinan Kiristendom gabaki ɗaya suna cewa sun gaskata da Littafi Mai Tsarki. Duk da haka, sun kasa yarda da abin da yake koyarwa. Har waɗanda suke cikin addini ɗaya ma suna da ra’ayoyin da suka bambanta game da yadda suka fahimci abubuwan da Nassosi suke koyarwa. Yanayinsu ya bambanta da na bayin Jehobah! Ko daga wace ƙasa muka fito, al’ada, da kuma yare, muna bauta wa Allah da muka sani da sunansa. Saboda shi ba Allah uku ba ne. (Kubawar Shari’a; 6:4 Zabura 83:18; Markus 12:29) Mun kuma sani cewa an kusa sulhunta muhimmin batun nan na ikon Allah na mallakan dukan sararin samaniya, kuma mun sani cewa idan har muka riƙe amincinmu gare shi, wannan batun ya shafe mu. Mun san gaskiya game da matattu kuma an ’yantar da mu daga tsoron Allahn da ake cewa zai ƙona mutane a cikin wutar jahannama ko kuwa ya aika su gidan azaba.—Mai-Wa’azi 9:5, 10.

5 Bugu da ƙari, abin farin ciki ne sanin cewa ba ma cikin waɗanda suke koyar da ra’ayin bayyanau! Maimakon haka, mu halittun Allah ne, waɗanda aka yi mu a surarsa. (Farawa 1:26; Malachi 2:10) Mai Zabura ya rera waƙa ga Allahnsa ya ce: “Zan yi godiya gareka; gama ƙirata abin ban tsoro ne, abin al’ajabi ne kuwa: ayyukanka suna da ban al’ajabi; wannan ma raina ya sani sarai.”—Zabura 139:14.

6, 7. Waɗanne gyare-gyare ne a rayuwarka ko kuma a rayuwar waɗansu ka ga ya zama da albarka?

6 Ka guje wa halaye marasa kyau. Kullayaumi ana gargaɗi ta hanyar watsa labarai, a kan matsalolin shan taba, maye, da kuma lalata. Amma yawaci ba sa bin waɗannan umurni. Mai zai faru idan mutum sahihi ya fahimci cewa Allah na gaskiya ya hana waɗannan abubuwa kuma ba ya jin daɗin waɗanda suke yin haka? Hakika, mutumin yakan daina irin waɗannan halaye! (Ishaya 63:10; 1 Korinthiyawa 6:9, 10; 2 Korinthiyawa 7:1; Afisawa 4:30) Ya yi haka ne musamman don ya faranta wa Allah rai, ya kuma sami ƙarin albarka tare da lafiyar jiki da kuma kwanciyar rai.

7 Barin halaye marasa kyau yana da wuya ga waɗansu. Duk da haka, kowane shekara mutane dubbai suna yin haka. Sun keɓe kansu ga Jehobah sun kuma yi baftisma, domin su nuna cewa sun rabu da ayyukan da Allah baya so. Wannan yana ƙarfafa kowannenmu! Yana ƙarfafa ƙudurinmu na ƙin bauta wa zunubi da kuma nuna halaye marasa kyau.

8. Waɗanne shawarwari na Littafi Mai Tsarki ne ke kawo farin ciki ga iyali?

8 Farin ciki na rayuwar iyali. A ƙasashe da yawa rayuwar iyali tana sukukucewa. Aure-aure da yawa sukan ƙare a kisan aure, suna barin ’ya’ya a cikin baƙin ciki. A wasu ƙasashen Turai, iyalan gwauraye sun kai kusan kashi 20 na dukan iyalai. Ta yaya ne Jehobah ya taimake mu mu bi hanyar aminci a cikin wannan irin hali? Don Allah ka karanta Afisawa 5:22–6:4, sannan ka lura da shawarar da kalmar Allah ta ba magidanta, matan aure, da kuma ’ya’yansu. Yin amfani da wannan shawarar da kuma wanda ke cikin Nassosi zai ƙarfafa aure, ya taimaki iyaye wajen renon ’ya’ya, da kuma kawo farin ciki a rayuwar iyali. Wannan ba abin farin ciki ba ne?

9, 10. Ta yaya ne fahimtarmu game da rayuwa ta nan gaba ta bambanta da na mutanen duniya?

9 Tabbacin cewa matsalolin duniya za su ƙare. Duk da ƙwarewar ’yan kimiyya da fasaha da kuma ƙoƙarin wasu shugabanni, matsaloli masu tsanani a zamanin nan ba su ragu ba. Wanda ya kafa World Economic forum, mai suna Klaus Schwab ya lura cewa “Ƙalubale da a ke fuskanta a duniya ya ci gaba da ƙaruwa amma lokacin da za a yi gyara kuwa sai raguwa yake yi.” Ya kuma yi magana a kan “matsalolin da ƙasashe ke fuskanta kamar su ta’addanci, lalacewar mahalli, da kuma matsalar kuɗi.” Schwab ya kammala da cewa: “Fiye da dā, duniya yanzu tana fuskantar matsaloli da ke bukatar ɗaukan mataki.” Sa’ad da ƙarni na 21 ya ci gaba, begen mutane sai ƙara lalacewa yake yi.

10 Abin farin ciki ne ka sani cewa Jehobah ya yi tanadin wani tsari da zai gyara matsalolin da mutane ke fuskanta wato, ta wurin Mulkin Almasihu! Ta wurin Mulkin Almasihu, Allah na gaskiya zai “sa yaƙoƙi su ƙare” ya kuma kawo “salama mai-yawa.” (Zabura 46:9; 72:7) Shafaffen Sarki Yesu Kristi, “za ya ceci fakiri, matalauci, mai-mayata daga zalunci da ƙwace.” (Zabura 72:12-14) A lokacin sarautar Mulkinsa, ba za a yi rashin abinci ba. (Zabura 72:16) Jehobah “za ya share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin zuciya, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.” (Ru’ya ta Yohanna 21:4) An riga an kafa Mulki a sama da zai ɗauki matakin gyara dukan wani irin matsala a duniya.—Daniel 2:44; Ru’ya ta Yohanna 11:15.

11, 12. (a) Neman jin daɗin rayuwa yakan kawo farin ciki na har abada kuwa? Ka yi bayani. (b) Menene ke kawo farin ciki na gaskiya?

11 Sani da ke kawo farin ciki na gaskiya. Menene ke kawo farin ciki na gaskiya? Wani masanin mutumtaka ya ce farin ciki yana da fasaloli uku, wato jin daɗi, aikace-aikace (na wurin aiki da na iyali), kuma manufar (aiki da ke cika makasudin waɗansu). A cikin ukun, ya lissafa jin daɗi a ƙarshe kuma ya lura cewa: “Wannan abu ne mai muhimmanci sosai saboda mutane da yawa suna daidaita rayuwarsu da neman jin daɗi.” Menene ra’ayin Littafi Mai Tsarki game da irin wannan rayuwa?

12 Sarki Sulemanu na zamanin Isra’ila ta dā ya ce: “Na ce ma raina, bari dai, in gwada ka da jin daɗi; sai ka ji daɗin nishatsi fa; amma wannan kuma banza ne. Na ce da dariya, Hauka ne; na ce ma jin daɗi, Mi ya daɗa?” (Mai-Wa’azi 2:1, 2) Bisa ga Nassi, ko wane irin farin ciki ne jin daɗi ke kawowa, ba mai daɗe wa ba ne. Aiki kuma fa? Akwai aiki na musamman da ya kamata mu yi, wato wa’azi na Mulki da kuma almajirantarwa. (Matta 24:14; 28:19, 20) Ta wurin shelar saƙo na ceto kamar yadda aka bayyana a cikin Littafi Mai Tsarki, muna kasancewa a aikin da zai cece mu tare da masu jin mu. (1 Timothawus 4:16) Saboda “mu abokan aiki na Allah ne,” mun shaida cewa “bayarwa ta fi karɓa albarka.” (1 Korinthiyawa 3:9; Ayukan Manzanni 20:35) Wannan aiki yana ƙara wa rayuwarmu ma’ana kuma yana mayar da magana ga wanda ya ke zargin Mahalicci, wato Shaiɗan Iblis. (Misalai 27:11) Hakika, Jehobah ya nuna mana cewa yi masa ibada zai sa mu sami farin ciki na gaskiya har abada.—1 Timothawus 4:8.

13. (a) Ta yaya Makarantar Hidima ta Allah albarka ce da ke bukatar mu yi farin ciki? (b) Ta yaya ne ka amfana daga Makarantar Hidima ta Allah?

13 Tsarin koyarwa na musamman. Gehard dattijo ne a ikilisiyar Shaidun Jehobah. Ya tuna lokacin da yake ƙuruciyarsa, ya ce: “Sa’ad da nake yaro, ina da matsalar yin magana. A lokacin da nake cikin matsi, sai in kasa magana. Sai in ji na kasa, wannan kuwa sai ya sa ni baƙin ciki. Iyayena suka shirya a koya mini yin magana amma duk wannan bai yi nasara ba. Wannan matsala ta, ba ta jiki ba ne amma ta hankali ne. Amma akwai wani tanadi daga Jehobah wato, Makarantar Hidima ta Allah. Shiga wannan makarantar ta ƙarfafa ni. Na yi iyaka ƙoƙarina in yi amfani da abin da nake koya. Na kuma ci nasara! Na iya magana ba tare da damuwa ba, na kuma zama mai gaba gaɗi a hidima. Yanzu ina ba da jawabai. Ina godiya ga Jehobah da ya ba ni sabuwar rayuwa ta wannan makaranta.” Ba abin farin ciki ba ne yadda Jehobah yake koyar da mu don yin aikinsa?

14, 15. A lokacin wahala, wane taimako ne ake samu? Ka ba da misali.

14 Dangantaka da Jehobah da kuma taimako daga ’yan’uwantaka na dukan duniya. Katrin, da ke zama a ƙasar Jamus ta damu sosai sa’ad da ta ji labarin girgizar ƙasa mai tsanani da kuma raƙumin ruwa mai girma a ƙasar Asiya ta kudu maso gabas. Bala’in ya faru ne sa’ad da ’yarta take ziyara a ƙasar Thailand. Fiye da awoyi 32 wannan matar ba ta san ko ɗiyar ta tana nan da rai ba ko tana cikin waɗanda suka ji rauni ko kuma waɗanda suka mutu da ake tarawa kusan ko wane awa. Katrin ta yi farin ciki da ta sami tabbacin cewa ’yarta tana da rai!

15 Menene ya taimaki Katrin a lokacin wannan ɗawainiya? Ta ce: “Na daɗe ina addu’a ga Allah. Na lura yadda addu’ar ta ci gaba da ƙarfafa ni da kuma ba ni kwanciyar hankali. Bugu da ƙari, ’yan’uwa na ruhaniya sun ziyarce ni kuma sun ƙarfafa ni.” (Filibbiyawa 4:6, 7) Da ba don addu’a da ta ɗin ga yi sa’ad da take cikin damuwa, da kuma taimakon ’yan’uwa na ruhaniya ba, da ta shiga cikin wani mummunan hali! Dangantakarmu da Jehobah da kuma ɗansa tare da cuɗanyarmu da ’yan’uwa Kiristoci, albarka ne da bai kamata a yi wasa da shi ba!

16. Ka yi bayanin labarin da ya nuna muhimmancin begen tashin matattu.

16 Begen sake ganin ƙaunatattu da suka mutu. (Yohanna 5:28, 29) Matthias wani Mashaidin Jehobah ne tun yana matashi. Don rashin sanin muhimmancinsa, ya rabu da ikilisiyar Kirista sa’ad da yake saurayi. Ya ce: “Ban taɓa taɗi sosai da mahaifi na ba. Shekaru da suka wuce, mun yi jayayya sosai. Duk da haka, mahaifi na yana so in sami rayuwa mai kyau. Yana so na sosai, amma a lokacin nan ban fahimci haka ba. A shekara ta 1996, sa’ad da nake zaune a gefen gadonsa, ina riƙe da hannunsa ina kuka mai zafi, na ba shi haƙuri game da abubuwan da na yi kuma na gaya masa cewa ina ƙaunarsa sosai. Amma ba ya ji na kuma. Bayan da ya yi ciwo na kwanaki kaɗan, sai ya rasu. Idan har na sadu da mahaifi na a ranar tashin matattu, za mu sasanta. Zai yi farin ciki idan ya ji cewa yanzu na zama dattijo, kuma ni da matata mun zama majagaba.” Begen tashin matattu abin farin ciki ne garemu!

“Ba Ya Kan Haɗa Ta Da Baƙinciki Ba”

17. Menene yin bimbini game da albarkar Jehobah zai taimake mu yi?

17 Game da Ubansa na samaniya, Yesu Kristi ya ce: “Ya kan sa ranarsa ta fito ma miyagu da nagargaru, ya kan aiko da ruwa bisa masu-adalci da marasa-adalci.” (Matta 5:45) Idan har Jehobah yana taimakon marasa adalci da masu mugunta, me zai hana shi taimakawa waɗanda suke tafiya cikin aminci! Zabura 84:11 ta ce: “Ubangiji za ya bada alheri da daraja: Babu wani abu mai-kyau da za ya hana ma masu-tafiya sosai.” Idan muka yi bimbini a kan yadda ya kula da waɗanda suke ƙaunarsa, zai sa mu yi farin ciki kuma mu nuna godiya!

18. (a) Ta yaya za a iya cewa Jehobah ba ya haɗa albarkarsa tare da baƙin ciki? (b) Me ya sa amintattun Jehobah suke fuskantar azaba?

18 “Albarkar Ubangiji” ita ce take kawo ci gaba a ruhaniya ga mutanensa. Kuma an tabbatar mana cewa “ba ya kan haɗa ta da baƙin ciki ba.” (Misalai 10:22) Me ya sa jarabobbi da kuma gwaji sukan shafi amintattun Allah, su bar su da azaba da kuma wahala? Muna fuskantar wahaloli da kuma ɓacin rai saboda dalilai uku. (1) Saboda halin zunubi da muke da shi. (Farawa 6:5; 8:21 Yaƙub 1:14, 15) (2) Shaiɗan da aljanunsa. (Afisawa 6:11, 12) (3) Mugun zamani. (Yohanna 15:19) Ko da yake Jehobah ya ƙyale mugayen abubuwa su faru mana, amma ba shi ba ne yake sa su faru. Hakika, “Kowacce kyakkyawar baiwa, da kowacce cikakkiyar kyauta, daga Sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki.” (Yaƙub 1:17) Albarkar Jehobah ba ta kawo baƙin ciki.

19. Menene ke jiran waɗanda suka ci gaba da tafiya cikin aminci?

19 Idan muna so mu ci gaba a ruhaniya sai mu kusaci Allah. Sa’ad da muka yi kusa da shi, ‘muna ajiye wa kanmu tushe mai kyau domin lokaci mai zuwa, da za mu ruski rai wanda shi ke hakikanin rai’ wato rai madawwami. (1 Timothawus 6:12, 17-19) A sabuwar duniya ta Allah da za ta zo, arzikinmu na ruhaniya za ta kasance tare da albarka ta zahiri. Dukan waɗanda suka ci gaba da ‘sauraran muryar Ubangiji Allahnsu’ za su sami rai wanda yake na hakika. (Kubawar Shari’a 28:2) Da ƙudiri mai ƙarfi, bari mu ci gaba da tafiya cikin aminci.

Menene Ka Koya?

• Me ya sa babu kyau ka riƙa tunani sosai a kan abubuwa da ke tafe a nan gaba?

• Wace albarka ce muke morewa yanzu?

• Me ya sa bayin Jehobah amintattu suke shan azaba?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba