Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 7/1 pp. 8-12
  • “Ina Ƙaunar Shari’arka Ba Misali!”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ina Ƙaunar Shari’arka Ba Misali!”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Biyan Bukatunmu na Ruhaniya
  • Dokar Allah Game da Kala
  • Ka Kāre Kanka Daga Ƙyashi
  • Dokar ‘Jehobah Cikakkiya Ce’
    Ka Kusaci Jehobah
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 7/1 pp. 8-12

“Ina Ƙaunar Shari’arka Ba Misali!”

“Ina ƙaunar shari’arka ba misali! Abin tunawa ne a gareni dukan yini.”—ZABURA 119:97.

1, 2. (a) Wane yanayi ne marubucin Zabura 119 da aka hura ya fuskanta? (b) Yaya ya aikata, kuma me ya sa?

MARUBUCIN Zabura 119 ya fuskanci gwaji mai tsanani. Abokan gaba masu girman kai da suka raina dokar Allah sun yi masa ba’a kuma sun tsegunta shi. ’Ya’yan sarki suka yi shawara a kansa kuma suka tsananta masa. Miyagu sun kewaye shi, suna barazana za su kashe shi. Dukan waɗannan sun sa ya “narke saboda nauwa.” (Zabura 119:9, 23, 28, 51, 61, 69, 85, 87, 161) Duk da wannan gwaji, mai zabura ya rera waƙa yana cewa: “Ina ƙaunar shari’arka ba misali! Abin tunawa ne a gareni dukan yini.”—Zabura 119:97.

2 Kana iya tambaya, “Ta yaya dokar Allah ta yi wa mai zabura ta’aziyya?” Ya tabbata cewa Jehobah ya damu da shi, kuma hakan ya kiyaye shi. Amfanin bin dokar Allah ne ya sa mai zabura farin ciki, duk da wahala da ya fuskanta daga magabtansa. Ya fahimci cewa Jehobah ya yi masa kirki. Ƙari ga haka, bin dokar Allah ya sa mai zabura ya sami hikima fiye da abokan gabansa kuma hakan ya cece sa. Yin biyayya da dokar ya ba shi kwanciyar rai da lamiri mai tsabta.—Zabura 119:1, 9, 65, 93, 98, 165.

3. Me ya sa yake da wuya Kiristoci su yi rayuwa bisa mizanan Allah a yau?

3 Wasu ma cikin bayin Allah a yau suna fuskantar gwaji mai tsanani na bangaskiyarsu. Wataƙila ba za mu fuskanci haɗari kamar na mai zabura ba, amma muna raye ne a “miyagun zamanu.” Mutane da yawa da muke saduwa da su kowace rana ba sa son mizanai na ruhaniya, suna biɗan makasudai na kansu da abin duniya, suna da halin girman kai da rashin ladabi. (2 Timothawus 3:1-5) Matasa Kiristoci suna fuskantar gwaji don mizanan ɗabi’arsu a kai a kai. A irin wannan yanayin, zai kasance da wuya mu ci gaba da ƙaunar Jehobah da kuma yin abin da ke daidai. Ta yaya za mu kāre kanmu?

4. Ta yaya mai zabura ya nuna godiya ga dokar Allah, ya kamata Kiristoci su yi hakan ne?

4 Abin da ya taimaki mai zabura ya jimre matsi da ya fuskanta shi ne cewa ya ba da lokaci sosai wajen nazarin dokar Allah. Wannan ya sa ya ƙaunaci dokar Allah. Hakika, kusan kowace aya a Zabura 119 ta ambaci wani fasali na dokar Jehobah.a Kiristoci a yau ba sa bin Dokar Musa da Allah ya ba al’ummar Isra’ila ta dā. (Kolossiyawa 2:14) Amma, har ila ƙa’idodi da aka furta a wannan Dokar na da amfani. Waɗannan ƙa’idodin ne suka yi wa mai zabura ta’aziyya, hakanan ma za su yi wa bayin Allah ta’aziyya da suke fama da matsalolin rayuwar zamani.

5. Wane ɓangare ne na doka za mu bincika?

5 Bari mu ga yadda fanni uku kawai na Dokar Musa zai ƙarfafa mu: tsarin Asabarci, tanadin yin kala, da umurni game da ƙyashi. A kowane fanni za mu ga cewa fahimtar ƙa’idodi da ya sa aka yi waɗannan dokoki suna da muhimmanci idan za mu jimre wa matsi na zamaninmu.

Biyan Bukatunmu na Ruhaniya

6. Wace bukata ce mai muhimmanci mutane suke da ita?

6 An halicci ’yan adam da bukatu da yawa. Alal misali, abinci, abin sha, wurin kwanciya suna da muhimmanci idan mutum zai sami lafiyar jiki. Duk da haka, ya kamata mutane su biya bukatunsu na “ruhu.” Ba za su yi farin ciki ba idan ba su yi hakan ba. (Matta 5:3) Jehobah ya ɗauki biyan wannan bukata da muhimmanci, shi ya sa ya umurci mutanensa su daina ayyukansu na kullum na mako guda domin su mai da hankali ga al’amura ta ruhaniya.

7, 8. (a) Ta yaya Allah ya bambanta tsakanin Asabarci da sauran kwanaki? (b) Menene manufar Asabarcin?

7 Tsarin Asabarci ya nanata muhimmancin biɗan abubuwa na ruhaniya. Lokacin da aka yi tanadin manna a cikin jeji ne kalmar ‘asarbaci’ ya bayyana da farko a cikin Littafi Mai Tsarki. An gaya wa Isra’ilawa su tara wannan gurasa na mu’ujiza kwanaki shida. A rana ta shida, za su tara “abinci na kwana biyu,” domin a rana ta bakwai ba za a ba su abinci ba. Rana ta bakwai za ta zama “assabbat mai-tsarki ne ga Ubangiji,” a ranar ya kamata kowane mutum ya zauna a gidansa. (Fitowa 16:13-30) Wata doka cikin Dokoki Goma ta ce kada a yi aiki a ranar Assabaci. Rana mai tsarki ce. Za a kashe wanda bai bi dokar ba.—Fitowa 20:8-11; Litafin Lissafi 15:32-36.

8 Dokar Assabaci ta nuna cewa Jehobah ya damu da lafiyar mutanensa ta zahiri da kuma ta ruhaniya. Yesu ya ce “aka yi ran assabaci domin mutum.” (Markus 2:27) Wannan ya sa Isra’ilawa su huta kuma ya ba su zarafi su matsa kusa ga Mahaliccinsu kuma su ƙaunace shi. (Kubawar Shari’a 5:12) An keɓe ranar don ayyuka na ruhaniya kawai. Ayyukan sun haɗa da bauta ta iyali, addu’a, da kuma yin bimbini a kan Dokar Allah. An tsara wannan don kada Isra’ilawa su yi amfani da dukan lokacinsu da kuzari wajen biɗan abin duniya. Assabaci ya tuna musu cewa dangantakarsu da Jehobah ne ya fi muhimmanci a rayuwarsu. Yesu ya maimaita wannan ƙa’ida sa’ad da ya ce: “An rubuta, ba da abinci kaɗai ba mutum za ya rayu, amma da kowace magana da ke fitowa daga bakin Allah.”—Matta 4:4.

9. Wane darasi ne tsarin Asabarci ya koya wa Kiristoci?

9 Ba a bukatar mutanen Allah a yau su kiyaye assabaci na zahiri na kwana ɗaya, amma tsarin Assabaci ba tarihi ba ne kawai. (Kolossiyawa 2:16) Tunasarwa ne cewa ya kamata mu ma mu sa ayyuka ta ruhaniya farko a rayuwarmu. Bai kamata shagala cikin abin duniya ko kuma ayyukan nishaɗi su sha kan abubuwa na ruhaniya ba. (Ibraniyawa 4:9, 10) Muna iya tambayar kanmu: Menene abu na farko a rayuwata? Ina sa yin nazari, addu’a, halartan taro, da yin wa’azin Mulki, farko a rayuwata kuwa? Ko kuwa wasu ayyuka sun sha kan irin waɗannan ayyuka?” Idan mun sa abubuwa ta ruhaniya farko a rayuwarmu, Jehobah ya tabbatar mana cewa ba za mu rasa abubuwa na biyan bukatar rayuwa ba.—Matta 6:24-33.

10. Ta yaya za mu amfana daga keɓe lokaci domin abubuwa na ruhaniya? Ka kwatanta.

10 Lokaci da muka ba da wajen nazarin Littafi Mai Tsarki da littattafansa, da kuma yin bimbini game da saƙonsu, zai taimake mu mu matsa kusa da Jehobah. (Yaƙub 4:8) Susan da kusan shekara 40 da ta shige ta soma keɓe lokaci don nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai ta ce, da farko ba ta ji daɗi yin karatun ba. Yana da wuya. Amma da ta ci gaba da karatun, sai ta fara jin daɗinsa. Yanzu ba ta farin ciki idan don wani dalili ba ta yi nazari ba. Ta ce “nazari ya taimake ni na ɗauki Jehobah kamar Ubana. Na dogara a gare shi, kuma na yi masa magana cikin addu’a. Abin ban al’ajabi ne mu ga yadda Jehobah yake ƙaunar bayinsa, yadda yake kula da ni, da kuma yadda ya taimake ni.” Mu ma za mu yi farin ciki sosai wajen mai da hankali ga bukatunmu ta ruhaniya a kai a kai!

Dokar Allah Game da Kala

11. Ta yaya tsarin kala yake aiki?

11 Fanni na biyu na Dokar Musa da ya nuna cewa Allah ya damu da lafiyar mutanensa shi ne damar yin kala. Jehobah ya ba da umurni cewa sa’ad da manomi Ba’isra’ile ya girbe kayan gonarsa, ya bar mabukaci ya tara abin da masu girbi suka rage. Manoma ba za su girbe kan iyakar gonakinsu gabaki ɗaya ba, ba za su tattara ’ya’yan inabinsu da suka kakkaɓe ba. Idan sun manta da wani dami a gona, ba za su koma su ɗauka ba. Wannan shiri ne mai kyau domin matalauta, baƙi, marayu, da kuma gwauraye. Hakika, yin kala na bukatar su yi aiki tuƙuru amma ta yin hakan ba za su yi roƙo ba.—Leviticus 19:9, 10; Kubawar Shari’a 24:19-22; Zabura 37:25.

12. Wane zarafi ne tsarin kala ya bai wa manoma?

12 Doka game da kala ba ta faɗi ainihin yawan amfanin gona da manoma za su bar wa mabukata ba. Su za su tsai da shawarar yawan abin da za su bari a gonakinsu ba za su girbe ba, ko kaɗan ko mai yawa. Ta yin hakan, tsarin kala ya koya musu karimci. Ya ba manoma zarafin nuna godiyarsu ga mai kawo lokacin kaka, tun da yake “wanda ya nuna jinƙai ga masu-mayata yana girmama [Mahaliccinsa].” (Misalai 14:31) Boaz ya yi hakan. Ya tabbata cewa Ruth gwauruwa da take kala a gonarsa ta ɗebi isashen hatsi. Jehobah ya albarkaci Boaz don karimcinsa.—Ruth 2:15, 16; 4:21, 22; Misalai 19:17.

13. Mecece doka ta dā game da kala ta koya mana?

13 Ƙa’ida da ke bisa dokar kala bai canja ba. Jehobah na bukatar bayinsa su zama masu karimci, musamman ga mabukata. Idan muka nuna karimci sosai, za mu sami albarka sosai. Yesu ya ce: “Ku bayar, za a ba ku, mudu mai-kyau, danƙararre, girgizajje, mai-zuba, za su bayar cikin ƙirjinku. Gama da mudun da ku ke aunawa, da shi za a auna muku.”—Luka 6:38.

14, 15. Ta yaya za mu nuna karimci, kuma wane amfani za mu samu duk da waɗanda muka taimaka?

14 Manzo Bulus ya yi mana gargaɗi mu “bari mu aika nagarta zuwa ga dukan mutane, tun ba waɗanda su ke cikin iyalin imani.” (Galatiyawa 6:10) Saboda haka, muna bukatar mu taimaki ’yan’uwa Kiristoci su sami taimako na ruhaniya sa’ad da suke fuskantar gwajin bangaskiyarsu. Suna bukatar taimako na zahiri ne, alal misali, wajen zuwa Majami’ar Mulki ko kuma yin cefane? Kuna da tsofaffi, marasa lafiya ko kuma waɗanda ba sa fita a ikilisiyarku da za su yi farin ciki idan aka ziyarce su ko kuma aka taimaka musu? Idan muka yi ƙoƙari mu san waɗannan bukatu, Jehobah zai iya amfani da mu ya amsa addu’ar mabukaci. Ko da yake kula da juna wajibi ne ga Kirista, mai ba da taimakon ma yana amfana. Nuna tabbataciyar ƙauna ga ’yan’uwa masu bi abin farin ciki ne kuma yana ba da gamsuwa ta ƙwarai da ke sa mu sami amincewar Jehobah.—Misalai 15:29.

15 Wata hanya mai muhimmanci da Kiristoci suke nuna rashin sonkai ita ce ta yin amfani da lokacinsu da kuzarinsu su yi magana game da ƙudurin Allah. (Matta 28:19, 20) Kowane mutum da ya taimaki wani har ya keɓe ransa ga Jehobah zai fahimci gaskiyar kalmomin Yesu: “Bayarwa ta fi karɓa albarka.”—Ayukan Manzanni 20:35.

Ka Kāre Kanka Daga Ƙyashi

16, 17. Menene doka ta goma ta hana, kuma me ya sa?

16 Fanni na uku na Dokar Allah ga Isra’ila da za mu bincika shi ne doka ta goma, da ta hana ƙyashi. Dokar ta ce: “Ba za ka yi ƙyashin gidan makusancinka ba, ba za ka yi ƙyashin matar makusancinka ba, ko bawansa, ko baiwassa, ko sansa, ko jākinsa, ko kowane abin da ke na makusancinka.” (Fitowa 20:17) Ba ɗan adam da zai iya sa a bi wannan dokar, tun da ba wanda zai iya sanin zuciya. Amma, wannan umurnin ya ɗaukaka Dokar fiye da tsarin doka na ’yan adam. Ya sa kowane Ba’isra’ile ya san cewa zai ba da lissafi kai tsaye ga Jehobah, wanda yake sanin zuciya. (1 Samuila 16:7) Ban da haka, wannan dokar ta nuna ainihin dalili da ya sa ake ayyukan lalata.—Yaƙub 1:14.

17 Doka game da ƙyashi ta ƙarfafa mutanen Allah su kauce wa son abin duniya, haɗama, da gunaguni game da yanayin rayuwarsu. Ya kuma tsare su daga jarabar sata ko lalata. Da akwai waɗanda suke da abin duniya da muke so ko kuma waɗanda a wasu fanni kamar sun yi nasara a rayuwa fiye da mu. Idan ba mu kame kanmu daga irin wannan tunanin ba, ba za mu yi farin ciki ba kuma za mu yi ƙishin wasu. Littafi Mai Tsarki ya kira ƙyashi nuna “sangartacen hankali.” Zai fi kyau idan mu ba masu ƙyashi ba ne.—Romawa 1:28-30.

18. Wane hali ne ya yaɗu a duniya, kuma wane mummunan sakamako yake jawowa?

18 Hali da ke yaɗuwa a duniya a yau na ƙarfafa abin duniya da yin gasa. Ta wurin talla, masu kasuwanci suna sa mutane su so sababbin kaya kuma sau da yawa suna nuna cewa ba za mu yi farin ciki ba idan ba mu saye su ba. Irin wannan halin ne Dokar Jehobah ta hana. Wani hali kuma da dokar Allah ta haramta shi ne son tara dukiya da samun abin duniya don dole. Manzo Bulus ya yi gargaɗi cewa: “Waɗanda suna so su zama mawadata su kan fāɗa cikin jaraba da tarko da sha’awoyi dayawa na wauta da ɓarna, irin da kan dulmaya mutane cikin hallaka da lalacewa. Gama son kuɗi asalin kowace irin mugunta ne: waɗansu kuwa garin begen samu sun ratse daga imani, sun huda kansu da baƙinciki mai-yawa.”—1 Timothawus 6:9, 10.

19, 20. (a) Waɗanne abubuwa ne suke da amfani ga mai ƙaunar dokar Jehobah? (b) Wane batu ne za a tattauna a talifi na gaba?

19 Waɗanda suke ƙaunar Allah sun fahimci haɗari da ke cikin kasancewa da halin son abin duniya kuma suna kāre kansu. Alal misali, mai zabura ya yi addu’a ga Jehobah: “Ka nufi zuciyata zuwa wajen shaidunka, ba wajen ƙyashi ba. A gareni shari’ar bakinka ta fi dubban zinariya da azurfa.” (Zabura 119:36, 72) Gaskata gaskiyar waɗannan kalmomi zai taimake mu mu kauce wa tarkon son abin duniya, haɗama, da kuma rashin gamsuwa da yanayinmu na rayuwa. “Ibada” za ta sa mu sami riba mai yawa ba tara dukiya ba.—1 Timothawus 6:6.

20 Ƙa’idodi da ke bisa Doka da Jehobah ya ba al’ummar Isra’ila ta dā suna da amfani a zamaninmu mai wuya kamar yadda suke sa’ad da Jehobah ya ba Musa wannan Dokar. Idan mun ci gaba da yin amfani da waɗannan ƙa’idodi a rayuwarmu, za mu ƙara fahimtarsu, za mu ƙara son su, kuma za mu fi yin farin ciki. Dokar na da misalai masu yawa dominmu, an nuna amfanin waɗannan darussan a rayuwar mutane da ke cikin Littafi Mai Tsarki da kuma abin da ya faru da su. Za a bincika wasu cikin talifi na gaba.

[Hasiya]

a Ayoyi 4 ne kawai cikin ayoyi 176 na wannan zabura ba su ambaci umurnin, shari’u, dokoki, farillai, tunasarwa, kalmomi, tafarki, da kuma magana na Jehobah ba.

Ta Yaya Za Ka Amsa?

• Me ya sa marubucin Zabura 119 ya ƙaunaci dokar Jehobah?

• Menene Kiristoci za su koya daga tsarin Assabaci?

• Wane amfani na dindindin ne dokar Allah game da kala take da shi?

• Ta yaya doka game da ƙyashi ya kāre mu?

[Hoto a shafi na 9]

Menene dokar Assabaci ta nanata?

[Hoto a shafi na 11]

Menene doka a kan kala ta koya mana?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba