Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 11/1 p. 26-p. 28 par. 18
  • Darussa Daga Littafin Misalai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Darussa Daga Littafin Misalai
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ‘KA SAMI HIKIMA KUMA KA KAMA KOYARWA DA KYAU’
  • (Misalai 1:1–9:18)
  • MISALAI DA ZA SU YI MANA JA-GORA
  • (Misalai 10:1–29:27)
  • ‘JAWABI MAI MUHIMMANCI’
  • (Misalai 30:1–31:31)
  • Hikima Tana Kira da Babban Murya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • “Hikima Mai-Fitowa Daga Bisa” Tana Aiki Kuwa A Rayuwarka?
    Ka Kusaci Jehobah
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 11/1 p. 26-p. 28 par. 18

Maganar Jehobah Rayayya Ce

Darussa Daga Littafin Misalai

SARKI SULEMANU na zamanin Isra’ila ta dā ya yi “karin magana guda talata.” (1 Sarakuna 4:32) Muna da hanyar samun wannan furcinsa masu hikima kuwa? Hakika, muna da ita. Littafin Misalai da aka kammala rubutawa a kusan shekara ta 717 K.Z., ya ƙunshi karin magana masu yawa da Sulemanu ya yi. Agur ɗan Jakeh da sarki Lemuel ne suka rubuta surori biyu na ƙarshe. Duk da haka, wasu sun gaskata cewa Lemuel wani suna ne na Sulemanu.

Hurarrun magana da suke cikin littafin Misalai suna da muhimmanci guda biyu, wato “domin a san hikima da koyarwa.” (Misalai 1:2) Waɗannan kalmomin za su taimake mu mu sami hikima, wadda za ta sa mu fahimci abubuwa dalla-dalla kuma mu yi amfani da abin da muka fahimta wajen warware matsaloli. Yin hakan, zai sa mu koyi tarbiyya. Idan muka mai da hankali ga waɗannan misalai kuma muka yi amfani da shawarar da yake ɗauke da ita, zai shafi zuciyarmu, kuma zai kawo mana farin ciki, wanda zai sa mu yi nasara.—Ibraniyawa 4:12.

‘KA SAMI HIKIMA KUMA KA KAMA KOYARWA DA KYAU’

(Misalai 1:1–9:18)

Sulemanu ya ce: “Hikima tana yin shela a waje.” (Misalai 1:20) Me ya sa ya kamata mu saurare ta? Misalai sura biyu ta bayyana albarka masu yawa da za mu samu idan muka sami hikima. Sura ta uku ta bayyana yadda za mu nemi dangantaka da Jehobah. Sulemanu ya ce: “Hikima ita ce musamman: sami hikima fa: i, tare da dukan abin da ka rigaya ka samu, ka sami fahimi. Ka kama koyarwa da kyau: kada ka sake ta.”—Misalai 4:7, 13.

Menene zai taimake mu mu ƙi halayen lalata na duniya? Misalai sura ta biyar ta amsa: Ka tsare hankalinka, kuma ka fahimci yadda duniya take rinjayar mutane. Ka yi la’akari da mugun sakamako na yin lalata. Sura da ke gaba ta ba da gargaɗi bisa ayyuka da kuma halayen da za su lalata dangantakarmu da Jehobah. Sura ta bakwai ta ba da bayani mai amfani bisa yadda mutum mai lalata yake aikata abubuwa. A sura ta takwas, an bayyana muhimmancin hikima a hanyar da ta dace. Sura ta tara kammala ce mai motsawa ga surori da aka tattauna kuma an bayyana ta ne yadda za ta motsa mu mu nemi hikima.

Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:

1:7; 9:10—Ta yaya ne tsoron Allah shi ne “mafarin ilimi” da kuma “mafarin hikima?” Idan mutum ba shi da tsoron Allah, ba zai kasance da ilimi ba, saboda Allah ne Mahaliccin dukan abubuwa da kuma Mawallafin Nassosi. (Romawa 1:20; 2 Timothawus 3:16, 17) Jehobah ne Tushen ilimi na gaskiya. Hakika, mafarin ilimi shi ne tsoron Jehobah. Tsoron Allah shi ne mafarin hikima, saboda sai an sami ilimi ake samun hikima. Bugu da ƙari, wanda ba shi da tsoron Jehobah ba zai iya amfani da ilimi da yake da shi ya ɗaukaka Mahaliccin ba.

5:3—Me ya sa ake kiran karuwa “baƙuwa”? Misalai 2:16,17 sun kwatanta matar da ta “manta da wa’adin Allahnta” da “baƙuwa.” Duk wanda ya bauta wa allolin ƙarya kuma ya ko ta mance da Dokar Allah, har da karuwa, ana ce da su baƙuwa.—Irmiya 2:25; 3:13.

7:1, 2—Menene wannan furcin “zantattukana” da kuma “dokokina” suka ƙunsa? Ƙari ga koyarwa da ke cikin Littafi Mai Tsarki, wannan furcin ya shafi doka da iyaye suka kafa domin amfanin iyalinsu. Dole ne ’ya’ya su yi biyayya ga koyarwa da ke cikin Littafi Mai Tsarki da kuma koyarwa na cikin Nassi da iyayensu suke koya masu.

8:30—Wanene “gwanin mai-aiki”? Mutumin da aka kira hikima ne ya kira kansa gwanin mai aiki. Irin wannan hikima ba rubutu ba ne da ake yi domin a rinjayi ra’ayin mai karatu don a bayyana abin da hikima ta ƙunsa, amma wannan hikima tana nufin Ɗan̄ Allah Yesu Kristi ne kafin ya zama ɗan adam. Kafin a haife shi a kamanin mutum a duniya, ‘Ubangiji ya yi shi tun farkon hanyassa.’ (Misalai 8:22) A matsayin “gwanin mai-aiki,” Yesu ya yi aiki sosai tare da Ubansa a lokacin halittar dukan abubuwa.—Kolossiyawa 1:15-17.

9:17—Menene “ruwaye na sata,” kuma me ya sa suke da “zaƙi”? Tun da yake Littafi Mai Tsarki ya kwatanta yin jima’i tsakanin mata da miji da shan ruwa mai kashe kishi daga rijiya, ruwaye na sata suna nufin yin jima’i na lalata a ɓoye. (Misalai 5:15-17) Yin irin wannan lalata ba tare da ya fallasa ba shi ne ke sa irin wannan ruwaye zaƙi.

Darussa Dominmu:

1:10-14. Mu kauce wa mugun hanyoyin da masu zunubi suke bi, don kada su rinjaye mu da alkawarin cewa za su ba mu arziki.

3:3. Mu ɗauki alheri da gaskiya da muhimmanci, kuma mu nuna muna da waɗannan halayen kamar yadda za mu yi idan mun saka abin wuya mai tsada. Ya kamata mu saka waɗannan halaye a zukatanmu, su zama halinmu ko da yaushe.

4:18. Ilimin Nassi mai ci gaba ne. Domin mu ci gaba a cikin gaskiya, dole ne mu ci gaba da nuna halin tawali’u.

5:8. Mu kauce wa abubuwa da za su kai mu ga yin lalata, ko ta wurin sauraron kiɗe-kiɗe, zuwa nishaɗi, bincike cikin Intane, ko kuma karatun littattafai da jaridu.

5:21. Mai ƙaunar Jehobah zai so ya yi musanyar dangantakarsa da Allah domin nishaɗi na ɗan lokaci? Ko kaɗan! Dalili mai girma da ya kamata mu tsabtace ɗabi’armu shi ne, idan muka fahimci cewa Jehobah yana ganinmu, kuma za mu bayyana abin da muka aikata.

6:1-5. Waɗannan ayoyi sun ba mu shawara mai kyau bisa ga ‘lamuni,’ ko kuma tsaya wa waɗanda suke so su ci bashi! Idan muka ga cewa matakin da muka ɗauka bai dace ba, ba tare da ɓata lokaci ba, mu ‘yi gudu zuwa wurin maƙwabcinmu’ mu roƙe shi kuma mu yi ƙoƙari mu daidaita abubuwa.

6:16-19. Waɗannan abubuwa guda bakwai na musamman sun ƙunshi kusan dukan abubuwan da ba su da kyau. Saboda haka ya kamata mu kauce daga yin su.

6:20-24. Yadda aka yi renon mutum bisa ga Nassi zai iya kāre shi daga yin lalata. Kada iyaye su yi sanyi wajen koya wa ’ya’yansu wannan tarbiyya.

7:4. Mu ƙaunaci hikima da kuma fahimi.

MISALAI DA ZA SU YI MANA JA-GORA

(Misalai 10:1–29:27)

Sauran misalan Sulemanu gajeru ne. An gabatar da su musamman domin kwatanci, saboda suna ɗauke da darussa game da hali da kuma maganar mutane.

Sura ta 10 zuwa ta 24 sun nanata muhimmancin tsoron Jehobah. “Mutanen Hezekiah sarkin Yahuda” ne suka kofi karin magana da suke sura ta 25 zuwa ta 29. (Misalai 25:1) Waɗannan karin magana sun koyar da dogara ga Jehobah da kuma wasu darussa masu muhimmanci.

Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:

10:6—Ta yaya ne “zilama tana rufe bakin miyagu”? Wannan zai yiwu ta wurin magana mai daɗi wadda za ta sa miyagu su ɓoye nufinsu na yi wa wasu lahani. Ko kuma saboda miyagu suna fuskantar hamayya daga wurin wasu shi ya sa suke rufe bakin su.

10:10—Ta yaya ne “mai-ƙibce da ido” yana sa ɓacin zuciya? “Mutumin wofi” ba ya “tafiya da gamtsin baki” kaɗai, amma yana ƙoƙarin ya nuna nufinsa sa’ad da ya yi magana da jikinsa, kamar “ƙifce da idanunsa.” (Misalai 6:12, 13) Irin wannan yaudara zai iya sa mutum cikin damuwa.

10:29—Menene “tafarkin Ubangiji”? Wannan yana nufin hanyar da Jehobah yake sha’ani da mutane ne, ba tafarkin rayuwa da ya kamata mu bi ba. Yadda Jehobah yake sha’ani da mutane yana nuna cewa zai kāre masu adalci amma zai halaka masu aikata mugunta.

11:31—Me ya sa za a sāka wa miyagu fiye da masu adalci? Wannan lada horo ne da kowannen su zai karɓa. Idan mai adalci ya yi kuskure, za a yi masa horo. Amma idan mugu ya yi zunubi na ganganci kuma ya ƙi ya sake rayuwansa, ya cancanta a yi masa horo mai tsanani.

12:23—Ta yaya ne mutum yakan “ɓoye saninsa”? Idan aka ce mutum ya ɓoye saninsa ba wai ana nufin kada ya nuna yana da ilimi ba ne. Amma, yana nufin mutum ya nuna iliminsa da hikima, ba tare da fahariya ba.

14:17—Ta yaya ne ‘mutum mai-tsiradda munanan dabaru ana ƙinsa’? Furcin Ibrananci da aka fassara “tsiradda munanan dabaru” yana iya nufin fahimi ko kuma mugun tunani. Hakika, dole ne a ƙi mutum mai tsiradda munanan dabaru. Haka nan kuma ana ƙin mutumin da ke da fahimi yana amfani da dabararsa domin ya nuna cewa shi “ba na duniya ba ne.”—Yohanna 15:19.

18:19—Ta yaya ne “ɗan’uwa wanda an ɓāta da shi ya fi birni mai-ƙarfi wuyan shiryawa”? Kamar birni mai ƙarfi da aka kai wa hari, wannan mutum zai ƙi gafartawa. Irin wannan tashin hankali da ke tsakaninsa da mai laifin zai yi tsanani kamar “gardunan kagara.”

Darussa Dominmu:

10:11-14. Domin kalamanmu su zama da ƙarfafa, ya kamata mu inganta zuciyarmu da sanin gaskiya, kuma ƙauna ta motsa zuciyarmu, mu kuma nuna hikima ta wurin abin da ke fitowa daga bakinmu.

10:19; 12:18; 13:3; 15:28; 17:28. Mu yi tunani kafin mu yi magana, kuma kada mu kasance masu maganganu.

11:1; 16:11; 20:10, 23. Jehobah yana son mu faɗi gaskiya idan muna kasuwanci.

11:4. Ba zai yi kyau ba idan muka yi watsi da nazarin Littafi Mai Tsarki na kanmu, muka daina zuwa taro, yin addu’a, da kuma zuwa wa’azi, saboda neman arziki.

13:4. Idan muna “fata” mu samu hakki a cikin ikilisiya ko kuma rai a sabuwar duniya, ya kamata mu yi ƙoƙari don mu cika farillanmu.

13:24; 29:15, 21. Uba mai ƙauna ba zai ƙyale ɗansa ba idan ya yi laifi. Amma, uba ko kuma uwa za su ɗauki matakin gyara kuskuren da ɗan ya yi kafin ya yi wuya.

14:10. Tun da yake mutane ba za su iya fahimtar irin yanayin da muke ciki ba, ba za su iya ba mu ta’aziyya da muke bukata ba. Saboda haka sai mu dogara ga Jehobah sa’ad da muke fuskantar wahaloli.

15:7. Kamar yadda manomi ba ya zuba irinsa a waje ɗaya, ba zai yi kyau mu bayyana wa wani dukan abubuwan da muka sani a lokaci ɗaya ba. Mutum mai hikima yana fito da abin da ya sani ne a lokacin da ya kamata.

15:15; 18:14. Kasancewa da halin kirki zai taimake mu mu sami farin ciki a lokacin da muke fuskantar yanayi mai wuya.

17:24. Kamar yadda idanu da zuciyar “wawa” suna rabuwa maimakon ya kula da abubuwa masu muhimmanci, ya kamata mu nemi fahimi don mu yi hikima.

23:6-8. Mu kauce wa nuna halin karɓan baƙi na riyya.

27:21. Yabo yana nuna irin halin da muke da shi. Za mu nuna muna da tawali’u idan muka bar yabo ya motsa mu mu nuna godiyarmu ga Jehobah kuma ya ƙarfafa mu mu ci gaba da bauta wa Allah. Za mu nuna rashin tawali’u idan muka bar yabo ya sa muka fara jin kamar mun fi kowa.

27:23-27. Ta wurin yin amfani da misalin makiyaya, Misalai ya bayyana muhimmancin yin rayuwa mai sauƙi ta wurin sa ƙwazo a aiki. Ya kamata su koya mana yadda za mu dogara ga Allah.a

28:5. Idan muka ‘biɗi Ubangiji’ ta wurin addu’a da kuma nazarin Kalmarsa, za mu iya fahimtar ‘dukan abubuwa’ da ya kamata mu yi don mu bauta masa yadda yake so.

‘JAWABI MAI MUHIMMANCI’

(Misalai 30:1–31:31)

Littafin Misalai ya kammala da ‘jawabai’ biyu. (Misalai 30:1; 31:1) Agur ya yi amfani da kwatanci masu sa tunani ya bayyana cewa masu ƙyashi ba za su taɓa gamsuwa ba, kuma ya bayyana cewa ba za a iya fahimtar yadda na miji yake rinjayar budurwa ba.b Ya kuma yi gargaɗi a kan girman kai da kuma fushi.

Jawabi mai muhimmanci da Lemuel ya samu daga wurin mahaifiyarsa yana ɗauke da tabbataciyar shawara game da yadda ya kamata a sha ruwan inabi ko barasa da kuma yin shari’a cikin adalci. Ya kammala kwatanta matar kirki da wannan furcin: “A ba ta daga cikin amfanin hannuwanta: bari kuma ayyukanta su yabe ta.”—Misalai 31:31.

Idan ka dogara ga Allah za ka iya samun hikima, horo, da kuma tsoron Allah. Hurarrun kalmomin Misalai suna koya mana darussa masu muhimmanci. Saboda haka, idan muka yi amfani da shawarar da suke ciki Misalai, za mu sami farin cikin “mutum wanda ya ke tsoron Ubangiji.”—Zabura 112:1.

[Hasiya]

a Ka dubi Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Agusta, 1991, shafi na 31 (Turanci).

b Ka dubi Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Yuli, 1992, shafi na 31 (Turanci).

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba