Kana Daraja Abubuwa Masu Tsarki Kamar Jehobah?
“Kuna lura a hankali . . . kada wani mai-fasikanci ya kasance, ko kuwa wani marar-ibada.”—IBRANIYAWA 12:15, 16.
1. Wane irin hali ne bayin Jehobah ba sa nunawa?
DUNIYA galibi ba ta damu da abubuwa masu tsarki ba. Edgar Morin wani ɗan faransa mai ilimin halayen zaman jama’a ya ce: “Duka tushen ɗabi’u, wato, Allah, yanayi, ƙasa, tarihi, da kuma tunani, ba su da muhimmanci kuma. . . . Saboda mutane suna zaɓan irin ɗabi’ar da suke so su bi.” Wannan daidai yake da “ruhun duniya,” ko kuma “ruhun da ke aikawa yanzu a cikin ’ya’yan kangara.” (1 Korinthiyawa 2:12; Afisawa 2:2) Waɗanda suka keɓe kansu ga Jehobah kuma suka miƙa kansu da son rai ga ikon mallakarsa ba sa nuna irin wannan halin. (Romawa 12:1, 2) Maimakon haka, bayin Jehobah sun fahimci muhimmancin tsarkakar bautarsu ga Jehobah. Waɗanne abubuwa ne ya kamata mu tsarkaka a rayuwarmu? A cikin wannan talifin za mu tattauna abubuwa biyar da ke da tsarki ga duka bayin Allah. Talifi na gaba kuma zai mai da hankali ne a kan tsarkakken wurin taronmun na Kirista. Amma, menene ainihin ma’anar kalmar nan “tsarki”?
2, 3. (a) Ta yaya ne Nassosi suka nanata tsarkakar Jehobah? (b) Me ya sa ya kamata mu tsarkake sunan Jehobah?
2 A cikin Ibrananci na Littafi Mai Tsarki, kalmar nan “tsarki” tana nufin warewa. A bauta, “tsarki” na nufin wani abin da ake tsarkakawa. Jehobah yana da tsarki sosai. Shi ya sa ake kiransa “Mai-tsarki.” (Misalai 9:10; 30:3) A Isra’ila ta dā, babban firist yakan sa rawani mai rubutun zinariya da ke ɗauke da waɗannan kalamai “MAI-TSARKI GA UBANGIJI.” (Fitowa 28:36, 37) A cikin Nassosi an faɗi cewa mala’iku kerub da seraphim sun kewaye kursiyin Jehobah suna cewa: “Mai-tsarki, Mai-tsarki, Mai-tsarki ne, Ubangiji.” (Ishaya 6:2, 3) Wannan maimaitawa yana nuna cewa Jehobah mai tsarki ne, yana da tsabta da kuma tsarkaka da babu kamarsa. Hakika, shi ne Tushen tsarkaka.
3 Sunan Jehobah mai tsarki ne. Mai zabura ya furta: “Bari su yi yabon sunanka mai-girma mai-ban razana: Mai-tsarki ne shi.” (Zabura 99:3) Yesu ya koya mana yadda za mu yi addu’a: “Ubanmu wanda ke cikin sama, A tsarkake sunanka.” (Matta 6:9) Maryamu, uwar Yesu a duniya, ta ce: “Raina yana girmama Ubangiji . . . mai-iko ya yi al’amura masu-girma gareni; sunansa kuwa mai-tsarki ne.” (Luka 1:46, 49) A matsayinmu na bayin Jehobah, muna tsarkaka sunansa kuma muna kauce wa yin abubuwan da za su jawo kunya ga sunansa mai tsarki. Bugu da ƙari, muna daraja abubuwa masu tsarki kamar yadda Jehobah ke daraja su.—Amos 5:14, 15.
Dalilin da Ya Sa Muke Daraja Yesu Sosai
4. Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya kira Yesu “Mai Tsarki”?
4 An halicci Yesu tsarkakke wanda shi ne “haifaffe kaɗai” na Jehobah Allah mai-tsarki. (Yohanna 1:14; Kolossiyawa 1:15; Ibraniyawa 1:1-3) Shi ya sa ake kiransa ‘Mai Tsarki na Allah.’ (Yohanna 6:69) Ya ci gaba da tsarkakarsa sa’ad da Allah ya mai da ransa daga sama zuwa duniya, domin Maryamu ta haifi Yesu ta ikon ruhu mai tsarki. Mala’ika ya ce mata: “Ruhu Mai-tsarki za ya auko miki, . . . abin nan da za a haifa, za a ce da shi mai-tsarki, Ɗan Allah.” (Luka 1:35) Sau biyu a addu’arsu ga Jehobah, Kiristocin da ke Urushalima sun kira Ɗan Allah “Yesu baranka mai tsarki.”—Ayukan Manzanni 4:27, 30.
5. Wane aiki ne mai tsarki Yesu ya yi a duniya, kuma me ya sa jininsa ke da daraja?
5 Yesu yana da aiki mai tsarki da zai yi a duniya. A ranar baftismarsa a shekara ta 29 K.Z., an naɗa Yesu ya zama Babban Firist ɗin haikali na ruhaniya mai girma na Jehobah. (Luka 3:21, 22; Ibraniyawa 7:26; 8:1, 2) Bugu da ƙari, zai yi mutuwar hadaya. Jininsa zai kawo fansa ta wurin da masu zunubi za su tsira. (Matta 20:28; Ibraniyawa 9:14) Shi ya sa muke “daraja” jinin Yesu.—1 Bitrus 1:19.
6. Wane hali ne ya kamata mu nuna ga Yesu Kristi, kuma me ya sa?
6 Don ya nuna cewa muna daraja Sarkinmu kuma Babban Firist, Yesu Kristi, manzo Bulus ya rubuta: “Domin wannan Allah kuma ya ba . . . [Ɗansa] mafificiyar ɗaukaka, ya ba shi suna wanda ke bisa kowane suna; domin cikin sunan Yesu kowacce gwiwa ta rusuna, ta cikin sama da ta kan duniya da ta ƙarƙashin duniya, kowane harshe kuma shi shaida Yesu Kristi Ubangiji ne, zuwa darajar Allah Uba.” (Filibbiyawa 2:9-11) Za mu nuna cewa mun amince da ra’ayin Jehobah game da abubuwa masu tsarki ta wajen yin biyayya ga Shugabanmu kuma Sarkinmu, Yesu Kristi, wanda shi ne Shugaban ikilisiyar Kirista.—Matta 23:10; Kolossiyawa 1:18.
7. Ta yaya muke nuna biyayyarmu ga Kristi?
7 Biyayyarmu ga Yesu Kristi ya ƙunshi yin biyayya ga mutanen da ya naɗa su shugabanci aikin da yake ja-gora. Ya kamata mu tsarkaka aikin shafaffu na Hukumar Mulki da kuma masu kula da suka naɗa a ofisoshin reshe, gundumomi, da’irori, da kuma ikilisiyoyi. Ya kamata mu yi biyayya mu kuma ba da kai ga wannan shirin sosai.—Ibraniyawa 13:7, 17.
Mutane Masu Tsarki
8, 9. (a) Ta yaya ne Isra’ilawa suka zama tsarkakkun mutane? (b) Ta yaya ne Jehobah ya kafa wa Isra’ila ƙa’idar kasancewa da tsarki?
8 Jehobah ya yi alkawari da Isra’ila. Wannan dangantakar tana nuna cewa sabuwar al’ummar tana da matsayi na musamman. Kuma an tsarkake su, ko kuwa an keɓe su. Jehobah da kansa ya ce masu: “Ku ma za ku zama tsarkaka a gareni: gama ni Ubangiji mai-tsarki ne, na kuma keɓe ku daga cikin al’ummai, domin ku zama nawa.”—Leviticus 19:2; 20:26.
9 Sa’ad da Jehobah ya kafa ƙasar Isra’ila, ya koya masu ƙa’idar kasancewa da tsarki. An ce kada su taɓa dutsen da aka ba da Dokoki Goma, domin yin haka zai jawo mutuwa. Shi ya sa suka ɗauki dutsen Sinai abu mai tsarki a wannan lokacin. (Fitowa 19:12, 23) Haka ma ya kamata su ɗauki Firistoci, da mazauni, da kuma abubuwan da ke cikinsa, da tsarki. (Fitowa 30:26-30) Wani masanin Littafi Mai Tsarki ya ce: “Umurni na aikin Kohatawa abubuwa ne mafi tsarki [Litafin Lissafi 4:4, 17-20] amma ga masu karatu na zamani, tsohon yayi ne. An daina kula da kuma mai da hankali ga abubuwa masu tsarki.” Amma, ba haka yake ga Kiristoci na gaskiya na ƙarni na farko da kuma na zamani ba.
Ikilisiyar Kirista
10, 11. Me ya sa za a iya cewa ikilisiyar Kirista ta shafaffun Kiristoci tana da tsarki, kuma ta yaya hakan ya shafi “waɗansu tumaki”?
10 Ikilisiyar Kirista ta shafaffun Kiristoci tana da tsarki a gaban Jehobah. (1 Korinthiyawa 1:2) Ana kwatanta duka shafaffun Kiristoci da suke duniya a kowane lokaci da haikali mai tsarki, duk da cewa ba sa cikin haikalin ruhaniya mai girma na Jehobah. Jehobah yana zaune a wannan haikali ta wajen ruhunsa mai tsarki. Manzo Bulus ya ce: “A cikin sa [Yesu Kristi] kuwa dukan gini, sassadadde ne, yana hawa yana zama haikali mai-tsarki cikin Ubangiji; a cikinsa kuwa an gina ku tare domin ku zama mazannin Allah cikin Ruhun.”—Afisawa 2:21, 22; 1 Bitrus 2:5, 9.
11 Bulus ya sake rubuta wa shafaffun Kiristoci, yana cewa: “Ba ku sani ba ku haikali ne na Allah, Ruhun Allah kuwa a cikinku ya ke zaune? . . . Haikalin Allah mai tsarki ne, watau ku ne.” (1 Korinthiyawa 3:16, 17) Ta wajen ruhunsa, Jehobah yana ‘zaune’ tare da shafaffunsa kuma yana ‘tafiya a cikinsu.’ (2 Korinthiyawa 6:16) Ya ci gaba da kula da ‘bawansa’ mai aminci. (Matta 24:45-47) “Waɗansu tumaki” suna daraja gatarsu na zama abokan rukunin “haikali.”—Yohanna 10:16; Matta 25:37-40.
Abubuwa Masu Tsarki a Rayuwarmu ta Kirista
12. Waɗanne abubuwa ne muke ɗauka da tsarki a rayuwarmu, kuma me ya sa?
12 Ba abin mamaki ba ne, ana ɗaukan abubuwan da suka shafi rayuwar shafaffun Kiristoci na ikilisiya ta Kirista da kuma abokansu da tsarki. Dangantakarmu da Jehobah abu ne mai tsarki. (1 Labarbaru 28:9; Zabura 36:7) Yana da daraja a garemu shi ya sa ba ma barin komi ko kuwa wani ya shiga tsakaninmu da Allahnmu, Jehobah. (2 Labarbaru 15:2; Yaƙub 4:7, 8) Addu’a tana da muhimmanci a wajen riƙe dangantakarmu da Jehobah. Annabi Daniel ya ɗauki addu’a da tsarki, shi ya sa ya ci gaba da al’adarsa ta yin addu’a ga Jehobah har ma ya kasadar da ransa. (Daniel 6:7-11) ‘Addu’o’in tsarkakku,’ ko kuma shafaffun Kiristoci, suna kama da turare da ake amfani da shi a wajen bauta ta haikali. (Ru’ya ta Yohanna 5:8; 8:3, 4; Leviticus 16:12, 13) Wannan alamar tana nanata tsarkakar addu’a. Wannan gata ce na yin magana da Mamallakin sararin samaniya! Babu shakka, muna ɗaukan addu’a abu mai tsarki a rayuwarmu.
13. Wane iko ne yake da tsarki, kuma ta yaya za mu bar shi ya yi aiki a rayuwarmu?
13 Ruhu mai tsarki shi ne ikon da shafaffun Kiristoci da kuma abokansu suke ɗauka da tsarki a rayuwarsu. Wannan ruhu ikon aiki ne na Jehobah, tun da yake yana aiki bisa ga nufin Allah ne, ya dace da aka ƙira shi “Ruhu Mai-tsarki,” ko kuma ‘tsarki na ruhu.’ (Yohanna 14:26; Romawa 1:4) Ta wajen ruhu mai tsarki, Jehobah ya yi tanadin ikon shelar bishara ga bayinsa da yake su Shaidunsa ne. (Ayukan Manzanni 1:8; 4:31) Jehobah yana ba da ruhunsa ga “waɗanda su ke biyayya gareshi,” da kuma waɗanda suka “yi tafiya bisa ga Ruhu,” ban da masu sha’awar jiki. (Ayukan Manzanni 5:32; Galatiyawa 5:16, 25; Romawa 8:5-8) Wannan iko mai ƙarfi yakan sa Kiristoci su nuna “ɗiyan Ruhu” wato, ayyuka masu kyau da kuma “tasarrufi mai-tsarki da ibada.” (Galatiyawa 5:22, 23; 2 Bitrus 3:11) Idan mun ɗauki ruhu mai tsarki abu mai muhimmanci, za mu kauce daga yin abubuwan da za su “ɓata zuciyar” ruhun, ko kuma mu hana shi aiki a rayuwarmu.—Afisawa 4:30.
14. Wane gata ne shafaffun Kiristoci suke ɗauka da tsarki, kuma ta yaya ne waɗansu tumaki suke saka hannu a wannan gatan?
14 Gata da muke da shi na shaida sunan Jehobah, Allah Mai Tsarki, da kuma zama Shaidunsa abu ne da ya kamata mu riƙe da tsarki. (Ishaya 43:10-12, 15) Jehobah ya sa shafaffun Kiristoci sun cancanta su zama “masu hidiman sabon alkawari.” (2 Korinthiyawa 3:5, 6) Saboda haka, an umurce su su yi wa’azin ‘bishara ta mulki’ kuma su “almajirtadda dukan al’ummai.” (Matta 24:14; 28:19, 20) Suna yin wannan aikin sosai, kuma miliyoyin mutane suna yin na’am da saƙonsu, a alamance suna cewa shafaffun Kiristoci: “Za mu tafi tare da ku, gama mun ji labari Allah yana tare da ku.” (Zechariah 8:23) Waɗannan suna yin hidima ta ruhaniya da farin ciki kamar ‘manoma’ da kuma ‘masu gyara gonakin anab’ na shafaffu ‘masu hidima na Allah.’ A haka, waɗansu tumaki suna taimakon shafaffun Kiristoci sosai a wajen cim ma hidimarsu a duka duniya.—Ishaya 61:5, 6.
15. Wane aiki ne manzo Bulus ya ɗauka da tsarki, kuma me ya sa muke da irin wannan ra’ayin?
15 Alal misali, manzo Bulus ya ɗauki hidimarsa na fage da tsarki. Ya ƙira kansa ‘mai-hidiman Kristi Yesu zuwa Al’ummai, yana hidimar bisharar Allah.’ (Romawa 15:16) Da yake rubuta wasiƙa zuwa ga Kiristoci a Koranti, Bulus ya kira hidimarsa “wadata.” (2 Korinthiyawa 4:1, 7) Ta hidimarmu, muna sa mutane su fahimci “kalmomin Allah.” (1 Bitrus 4:11) Saboda haka, ko mu shafaffu ne ko waɗansu tumaki, ya kamata mu ɗauki gatar shelar bishara da tsarki.
“Kāmala Tsarki Cikin Tsoron Allah”
16. Menene zai taimaka mana kada mu zama mutane “marar ibada”?
16 Manzo Bulus ya gargaɗi ’yan’uwansa Kiristoci cewa kada su zama mutane “marar-ibada.” Maimakon haka, ya umurce su su ‘nemi tsarkakewa,’ kuma su ‘lura a hankali kada wani . . . tushen ɗaci ya ciro har ya wahalshe su, masu-yawa kuma su ƙazantu ta wurin.’ (Ibraniyawa 12:14-16) Furcin nan “tushen ɗaci” yana nufin mutane kaɗan da suke cikin ikilisiyar Kirista da za su ga cewa abin da ake yi bai dace ba. Alal misali, wataƙila za su ƙi amincewa da ra’ayin Jehobah game da tsarkakar aure, ko ta tsabtar ɗabi’a. (1 Tassalunikawa 4:3-7; Ibraniyawa 13:4) Ko kuma za su kasance da “zantattukan banza na saɓo” daga masu ridda, waɗanda suka yi “kuskure wajen gaskiya.”—2 Timothawus 2:16-18.
17. Me ya sa shafaffun Kiristoci suke bukatar su yi iya ƙoƙarinsu su nuna ra’ayin Jehobah game da tsarki?
17 Ga ’yan’uwansa shafaffu, Bulus ya rubuta: “Ƙaunatattu, . . . bari mu tsarkake kanmu daga dukan ƙazamtar jiki da ta ruhu, muna kāmala tsarki cikin tsoron Allah.” (2 Korinthiyawa 7:1) Wannan furcin ya nuna cewa shafaffun Kiristoci, ‘masu-tarayya na kiran samaniya,’ suna bukatar su yi iya ƙoƙarinsu su nuna cewa suna daraja abubuwa masu tsarki a rayuwarsu kamar Jehobah. (Ibraniyawa 3:1) Hakazalika, manzo Bitrus ya gargaɗi ’yan’uwansa da aka shafa da ruhu ya ce: “Kamar ’ya’yan biyayya, ba za ku daidaita kanku bisa sha’awoyinku na dā a zamanin jahilcinku ba: amma yadda shi wanda ya kira ku mai-tsarki ne, ku kuma ku zama masu-tsarki cikin dukan tasarrufi.”—1 Bitrus 1:14, 15.
18, 19. (a) Ta yaya ne “taro mai-girma” suke nuna cewa suna da ra’ayin Jehobah na abubuwa masu tsarki? (b) Wane abu mai tsarki ne a rayuwarmu ta Kirista za a tattauna a talifi na gaba?
18 Menene ake bukata daga “taro mai-girma,” waɗanda za su tsira daga cikin “babban tsananin”? Dole ne su ma su daraja abubuwa masu tsarki kamar Jehobah. A littafin Ru’ya ta Yohanna, an kwatanta cewa suna yi wa Jehobah “bauta” a haikali na ruhaniya da ke farfajiyar duniya. Sun ba da gaskiya ga hadayar fansar Yesu, a alamance suna ‘wanke rigunansu, suka faranta su cikin jinin Ɗan rago.’ (Ru’ya ta Yohanna 7:9, 14, 15) Wannan ya ba su matsayi mai tsarki a wajen Jehobah kuma ya kamata su ‘tsarkake kansu daga dukan ƙazamtar jiki da ta ruhu, suna kāmala tsarki cikin tsoron Allah.’
19 Kasancewa a taro a kowane lokaci don bauta wa Jehobah da kuma yin nazarin Kalmarsa, su ne abubuwa masu muhimmanci a rayuwar shafaffun Kiristoci da abokansu. Jehobah yana ɗaukan taron mutanensa da tsarki. A talifi na gaba za a tattauna yadda da kuma dalilin da ya sa ya kamata mu kasance da ra’ayin Jehobah game da abubuwa masu tsarki a wannan hanyar mai muhimmanci.
Domin Bita
• Wane irin ra’ayi na duniya ne bayin Jehobah ba sa bi?
• Me ya sa Jehobah ne Tushen abubuwa masu tsarki?
• Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja abubuwa masu tsarki na Kristi?
• Waɗanne abubuwa ne ya kamata mu tsarkake a rayuwarmu?
[Hoto a shafi na 17]
A Isra’ila ta dā, ana ɗaukan Firistoci, da mazauni, da kuma abubuwan da ke cikinsa da tsarki
[Hoto a shafi na 18]
Shafaffun Kiristoci a duniya su ne haikali mai tsarki
[Hotuna a shafi na 19]
Addu’a da hidimarmu na fage gata ne masu tsarki