Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 12/1 pp. 8-11
  • Ka Yi Na’am Da Horon Jehobah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Na’am Da Horon Jehobah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Dalilin da Ya Sa Ake Yi wa Wasu Yankan Zumunci
  • Tuba na da Muhimmanci
  • Me Ya Sa Ya Kamata Mu Faɗi Zunubinmu?
  • Ka Gaskata ’Yan’uwanka Masu Aminci
  • Yadda Makiyaya Suke ba da Taimako
  • Ka Ci Gaba da Amincewa da Horon Allah
  • Me Ya Sa Yankan Zumunci Tsari Ne Mai Kyau?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Yadda Za A Nuna wa Mai Zunubi Kauna da Jinkai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Me Za Ka Yi Idan Ka Yi Zunubi Mai Tsanani?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Mu Bi Raꞌayin Jehobah Game da Wadanda Suka Yi Zunubi Mai Tsanani
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 12/1 pp. 8-11

Ka Yi Na’am Da Horon Jehobah

“Kada ka rena koyaswar Ubangiji.”—MISALAI 3:11.

1. Me ya sa ya kamata mu yi na’am da horon Allah?

SARKI SULEMANU na Isra’ila ta dā ya ba kowannenmu dalili mai kyau na yin na’am da horon Allah. “Ɗana kada ka rena koyaswar Ubangiji,” in ji Sulemanu, “kada ka yi kasala kuma da tsautawassa: Gama wanda Ubangiji ya ke ƙauna shi ya ke tsauta ma: Kamar yadda uba ya kan yi ma ɗan da ya ke jin daɗinsa.” (Misalai 3:11, 12) Hakika, Ubanka na samaniya yana yi maka horo domin yana ƙaunarka.

2. Menene ma’anar “horo,” kuma ta yaya za a iya horar da mutum?

2 “Horo” na nufin gyara, umurni, da koyarwa. “Kowane irin horo ana ganinsa ba abin faranta zuciya ba, amma abin ban ciwo ne a loton yi,” in ji manzo Bulus, “amma daga baya ya kan bada amfani mai-salama-watau na adalci ke nan-ga waɗanda sun wāsu ta wurinsa.” (Ibraniyawa 12:11) Karɓa da kuma yin na’am da horo daga Allah na iya taimaka maka ka biɗi tafarki na aminci wanda hakan zai jawo ka kusa da Allah mai tsarki, Jehobah. (Zabura 99:5) Ana iya samun gyara ta wurin ’yan’uwa masu bi, ta wurin abubuwan da aka koya a taron Kirista, da kuma nazarin da ka yi na Kalmar Allah da kuma littattafan “wakili mai-aminci.” (Luka 12:42-44) Abin farin ciki ne idan ka ji wuraren da kake bukatar yin gyara! Amma, wane irin horo ne za a iya yi idan aka yi mugun zunubi?

Dalilin da Ya Sa Ake Yi wa Wasu Yankan Zumunci

3. A wane lokaci ne ake yin yankan zumunci?

3 Bayin Allah suna yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma littattafai na Kirista. Ana tattauna mizanan Jehobah a taronsu, da manyan taro. Saboda haka, Kiristoci suna da dama mai kyau na sanin abin da Jehobah yake bukata a gare su. Ana yin yankan zumunci ne kawai idan wani a cikin ikilisiya ya ci gaba da yin mugun zunubi.

4, 5. Wane misali daga Nassi na yankan zumunci ne aka gabatar a nan, kuma me ya sa aka aririci ikilisiyar ta mai da mutumin?

4 Yi la’akari da wani misali daga Nassi na yankan zumunci. Ikilisiyar da ke Koranti ta ƙyale “irin fasikanci ma da ba a iske shi ko wurin Al’ummai, mutum [ya yi zina] da matar ubansa!” Bulus ya aririci Korinthiyawan su “bada wannan irin mutum ga Shaiɗan garin a hallaka jiki, domin ruhu shi tsira.” (1 Korinthiyawa 5:1-5) Idan aka yi yankan zumunci kuma aka miƙa mutumin ga Shaiɗan, da haka, mai zunubin ya zama sashen duniyar Iblis. (1 Yohanna 5:19) Korar da aka yi masa ya fitar da mugun tasiri daga ikilisiya kuma an kāre “ruhun,” Allah ko hali na musamman.—2 Timothawus 4:22; 1 Korinthiyawa 5:11-13.

5 Bayan wani ɗan lokaci, Bulus ya aririci Kiristocin da ke Koranti su maido da mai laifin. Me ya sa? Domin “kada Shaiɗan ya ci ribar kome,” in ji manzon. Mai zunubin ya riga ya tuba kuma ya tsabtace rayuwarsa. (2 Korinthiyawa 2:8-11) Idan Korinthiyawan suka ƙi maido da mutumin da ya tuba, Shaiɗan zai ribace su domin za su kasance mutane marar tausayi kuma marar gafartawa kamar yadda Iblis yake so. Sun “gafarta masa, [kuma sun] yi masa ta’aziya” wato, mutumin da ya tuba.—2 Korinthiyawa 2:5-7.

6. Menene yankan zumunci zai iya cim ma?

6 Menene aka cim ma idan aka yi yankan zumunci? Yana kawar da kunyar da aka jawo wa suna mai tsarki na Jehobah, kuma yana kāre suna mai kyau na mutanensa. (1 Bitrus 1:14-16) Cire mai zunubi daga cikin ikilisiya na ɗaukaka mizanan Allah kuma yana sa ikilisiyar ta kasance a tsabtace a ruhaniya. Kuma yana iya sa wanda ya yi zunubin ya dawo cikin hankalinsa.

Tuba na da Muhimmanci

7. Menene ya sami Dauda sa’ad da ya ƙi ya furta zunubansa?

7 Yawanci da suka yi mugun zunubi da suka tuba da gaske, ba a yi musu yankan zumunci daga ikilisiya ba. Hakika, yana yi wa wasu wuya su tuba da gaske. Yi la’akari da Sarki Dauda na Isra’ila, wanda ya rubuta Zabura ta 32. Wannan waƙar ta nuna cewa Dauda bai furta mugun zunubin da ya yi da Bath-sheba ba. Sakamakon shi ne, baƙin ciki saboda zunubin da ya yi ya sha ƙarfinsa, kamar yadda zafi ke janye ruwan da ke cikin itace. Dauda ya sha wuya a zahiri ya kuma damu, amma sa’ad da ya ‘faɗi laifofinsa, Ubangiji ya gafarta muguntar zunubinsa.’ (Zabura 32:3-5) Dauda ya rera waƙa: “Mai-albarka ne mutum wanda Ubangiji ba ya lissafta mugunta gareshi ba.” (Zabura 32:1, 2) Abu ne mai ban al’ajabi mu shaida tagomashin Allah!

8, 9. Ta yaya ake nuna tuba, kuma menene muhimmancinsa game da maido da wanda aka yi wa yankan zumunci?

8 Babu shakka, dole ne mai zunubi ya tuba idan yana son ya sami tagomashi. Amma, kunya ko kuwa tsoron cewa za a gane zunubin mutum ba shi ne tuba ba. “Tuba” na nufin “daina yin” zunubi domin an yi da na sani. Mutumin da ya tuba yana da “karyayyar zuciya,” kuma wataƙila yana son ya daidaita al’amuran.—Zabura 51:17; 2 Korinthiyawa 7:11.

9 Tuba abu ne mai muhimmanci da zai sa a maido mutum cikin ikilisiyar Kirista. Ba a maido mutumin da aka yi wa yankan zumunci zuwa cikin ikilisiya bayan ɗan ƙanƙanin lokaci. Kafin a maido shi, sai ya canza yanayin zuciyarsa sosai. Dole ne ya fahimci irin zunubin da ya yi, da kuma kunyar da ya jawo wa Jehobah da kuma ikilisiya. Dole ne mai zunubin ya tuba, ya roƙi gafara, ya kuma ba da kai ga umurnan Allah na adalci. Sa’ad da ya biɗi a mai da shi, dole ne ya nuna alamun cewa ya tuba kuma yana ‘ayyuka waɗanda sun cancanci tubarsa.’—Ayukan Manzanni 26:20.

Me Ya Sa Ya Kamata Mu Faɗi Zunubinmu?

10, 11. Me ya sa bai kamata mu ɓoye zunubi ba?

10 Wasu da suka yi zunubi suna iya tunani: ‘Idan na faɗi zunubin, wataƙila zan amsa wasu tambayoyi masu kunyatarwa kuma ana iya yi mini yankan zumunci. Amma idan na yi shiru, zan iya guje wa hakan kuma babu wanda zai taɓa sani a cikin ikilisiya.’ Mai yin irin wannan tunanin ya ƙi yin la’akari da wasu batutuwa masu muhimmanci. Menene waɗannan batutuwan?

11 Jehobah “Allah ne cike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinƙai da gaskiya; yana tsaron jinƙai domin dubbai, yana gafarta laifi da saɓo da zunubi.” Duk da haka, yana yi wa mutanensa horo “da shari’a.” (Fitowa 34:6, 7; Irmiya 30:11) Idan ka yi mugun zunubi, ta yaya za ka sami tagomashin Allah idan ka yi ƙoƙarin ɓoye zunubinka? Jehobah yana sane da zunubinka, kuma ba ya yin watsi da zunubin.—Misalai 15:3; Habakkuk 1:13.

12, 13. Menene zai iya faruwa idan aka ɓoye zunubi?

12 Idan ka yi mugun zunubi, furta zunubinka zai taimaka maka ka sake samun lamiri mai kyau. (1 Timothawus 1:18-20) Amma ƙin furta zunubi na iya lalata lamiri wanda hakan na iya kai ga ƙarin zunubi. Ka tuna cewa zunubin da ka yi ba ga wani mutum ko ikilisiya ba ne. Amma ga Allah. Mai zabura ya rera: “Ubangiji, kursiyinsa yana cikin sama; Idanunsa suna duban yan adam, maƙyaptansa suna gwada su. Ubangiji yana gwada mai-adalci [da] mai-mugunta.”—Zabura 11:4, 5.

13 Jehobah ba zai albarkaci duk wanda ya ɓoye mugun zunubinsa kuma ya kasance a cikin ikilisiyar Kirista mai tsabta ba. (Yaƙub 4:6) Saboda haka, idan ka riga ka yi zunubi kuma kana son ka yi abin da ya dace, kada ka ɓata lokaci ka je ka furta zunubinka. Idan ba haka ba, lamirinka zai dinga damunka, musamman sa’ad da ka karanta ko ka ji gargaɗi game da irin waɗannan abubuwan. Idan Jehobah ya janye ruhunsa daga gare ka fa, kamar yadda ya yi wa Sarki Saul? (1 Samuila 16:14) Idan Allah ya cire ruhunsa, kana iya faɗawa cikin zunubi mafi muni.

Ka Gaskata ’Yan’uwanka Masu Aminci

14. Me ya sa ya kamata wanda ya yi laifi zai bi shawarar da take Yaƙub 5:14, 15?

14 Saboda haka, menene ya kamata mai zunubi da ya tuba ya yi? “Shi kira dattiɓan ikilisiya su yi addu’a a bisansa, suna shafe shi da mai cikin sunan Ubangiji: addu’ar bangaskiya kuwa za ta ceci mai-ciwo, Ubangiji kuwa za ya tashe shi.” (Yaƙub 5:14, 15) Gaya wa dattawa ita ce hanya ɗaya da mutum zai “fito da yaya fa masu-isa tuba.” (Matta 3:8) Waɗannan mutane masu aminci da ƙauna za ‘su yi masa addu’a kuma su shafe shi da mai cikin sunan Jehobah.’ Kamar mai mai kyau, shawararsu ta Littafi Mai Tsarki za ta ƙarfafa duk wanda ya tuba.—Irmiya 8:22.

15, 16. Ta yaya ne Kiristoci dattawa suke bin misalin da Allah ya kafa kamar yadda aka rubuta a Ezekiel 34:15, 16?

15 Jehobah, Makiyayinmu, ya kafa misali mai kyau sa’ad da ya ’yantar da Yahudawa daga bauta a Babila a shekara ta 537 K.Z., da kuma sa’ad da ya ’yantar da Isra’ila ta ruhaniya daga “Babila Babba” a shekara ta 1919 A.Z.! (Ru’ya ta Yohanna 17:3-5; Galatiyawa 6:16) Da haka, ya cika alkawarinsa: “Ni da kaina zan yi kiwon tumakina, in kai su wurin kwanciya, . . . In nemi abin da ya ɓace, in dawo da abin da aka kora, abin da ya karye in yi masa ɗori, in ƙarfafa abin da ke da ciwo.”—Ezekiel 34:15, 16.

16 Jehobah yana ciyar da tumakinsa ta alama, yana kāre su, kuma yana neman waɗanda suka ɓace. Hakazalika, Kiristoci makiyaya suna tabbatar da cewa tumakin Allah suna cin abinci na ruhaniya sosai kuma suna samun kāriya. Dattawa suna neman tunkiya da ta bar ikilisiya. Kamar yadda Allah yake ‘ɗaure wanda ya karye,’ masu kula suna ‘ɗaure’ tumakin da ya ji rauni ta wurin kalaman wani ko kuwa ta ayyukansa. Kamar yadda Allah yake ‘ƙarfafa masu ciwo,’ dattawa suna taimaka wa waɗanda suke ciwo a ruhaniya, wataƙila domin sun yi zunubi.

Yadda Makiyaya Suke ba da Taimako

17. Me ya sa bai kamata mu ɓata lokaci ba wajen neman taimako na ruhaniya daga dattawa?

17 Dattawa suna bin wannan umurnin: “A yi jinƙai tare da tsoro.” (Yahuda 23) Ta wajen yin lalata, wasu Kiristoci sun yi mugun zunubi. Amma idan suka tuba da gaske, za su iya samun tagomashi da kuma ƙauna daga dattawan da suke son su taimaka musu a ruhaniya. Tare da shi kansa, Bulus ya ce game da waɗannan mazaje: “Ba sarauta mu ke yi bisa bangaskiyarku ba, amma mataimaka ne na farinzuciyarku.” (2 Korinthiyawa 1:24) Saboda haka, kada ka ɓata lokaci wajen neman taimakonsu na ruhaniya.

18. Ta yaya ne dattawa suke bi da Kirista da suka yi zunubi?

18 Idan ka yi mugun zunubi, me ya sa ya kamata ka amince da dattawa? Domin sune ainihin makiyayan tumakin Allah. (1 Bitrus 5:1-4) Babu makiyayi mai ƙauna da zai bugi tunkiyar da take kuka don ta ji wa kanta rauni. Sa’ad da dattawa suke bi da Kirista da ya yi zunubi, wannan batu ne na zunubi da maidowa ta ruhaniya idan zai yiwu, ba na laifi ko horo ba. (Yaƙub 5:13-20) Dattawa suna bukatar su yi shari’a cikin adalci kuma su “kewaye ma garke.” (Ayukan Manzanni 20:29, 30; Ishaya 32:1, 2) Kamar duka Kiristoci, dattawa suna bukatar su yi ‘aikin gaskiya, su nuna jinƙai, kuma su yi tafiya da tawali’u tare da Allahnsu.’ (Mikah 6:8) Irin waɗannan halayen suna da muhimmanci sa’ad da suke yanke shawarar da ta shafi rayuwa da kuma tsarkakkiyar hidima ta “tumakin makiyaya [ta Jehobah] kuma.”— Zabura 100:3.

19. Wane irin hali ne Kiristoci dattawa suke nuna wa wajen daidaita wani?

19 Ruhu mai tsarki ne ya naɗa Kiristoci makiyaya, kuma suna son ya yi musu ja-gora. Idan “an iske mutum a cikin kowane laifi,” wato, kamar an kama shi ba zato ba tsammani, maza da suka ƙware a ruhaniya sukan ƙoƙarta su ‘komo da irin wannan mutumin cikin ruhun tawali’u.’ (Galatiyawa 6:1; Ayukan Manzanni 20:28) Da tawali’u da kuma manne wa mizanai na Allah, dattawa suna ƙoƙartawa su daidaita tunaninsa, kamar yadda likita mai tausayi ke ɗaure karyayyar kafa a hankali, don kada zafin ya yi yawa kuma ya kula da matsalar. (Kolossiyawa 3:12) Tun da nuna tagomashi ya dangana ne a kan addu’a da Nassosi, shawarar da dattawan suka yanke za ta nuna ra’ayin Allah game da batun.—Matta 18:18.

20. A wane irin yanayi ne zai dace a sanar da ikilisiya cewa an tsauta wa mutum?

20 Idan mutane sun san zunubin ko kuwa za su sani a nan gaba, zai dace a sanar da ikilisiyar don a kāre sunanta. Za a iya yin sanarwa kuma, idan da wani dalilin da zai sa a sanar da ikilisiyar. A lokacin da wanda aka tsauta wa yake warkewa a ruhaniyance, za a iya kwatanta shi da wanda yake warkewa daga raunin da ya ɗan dakatar da shi daga yin aiki. A wannan lokacin, zai dace wanda ya tuban ya yi sauraro maimakon ya yi kalami a taro. Dattawan suna iya ce wani ya je ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi don ya ƙarfafa shi a inda ya raunana domin ya zama ‘sahihi cikin bangaskiya.’ (Titus 2:2) Ana yin duka wannan ne cikin ƙauna ba wai don a horar da wanda ya yi zunubin ba.

21. Ta yaya ne za a iya bi da wasu zunubai?

21 Dattawa suna iya ba da taimako a hanyoyi dabam dabam. Alal misali, a ce ɗan’uwa da ke da matsalar yin maye a dā yana shan barasa sosai sau ɗaya ko sau biyu sa’ad yake gida shi kaɗai. Ko kuwa wanda ya daina shan taba tun da daɗewa amma yana shan taba sau ɗaya ko sau biyu sa’ad da ya karaya. Ko da yake ya yi addu’a kuma ya gaskata cewa Allah ya yafe masa, ya kamata ya nemi taimako daga dattawa saboda kada irin wannan zunubin ya zama halinsa. Dattijo ɗaya ko biyu na iya tattauna batun. Amma, dattijon na iya sanar da shugaban ikilisiya, tun da ƙila akwai abubuwan da suka sa shi yin haka.

Ka Ci Gaba da Amincewa da Horon Allah

22, 23. Me ya sa ya kamata ka ci gaba da yin na’am da horon Allah?

22 Don samun amincewar Allah, ya kamata kowane Kirista ya mai da hankali ga horon Jehobah. (1 Timothawus 5:20) Saboda haka, ka yi amfani da gyaran da aka yi maka sa’ad da kake nazarin Nassosi da kuma littattafai na Kirista, ko kuwa sa’ad da aka ba da umurni a taro, da manyan taro na mutane Jehobah. Ka kasance a faɗake don yin nufin Jehobah. Da haka, horon Allah zai taimaka maka ka sami kāriya mai girma na ruhaniya da zai hana ka yin zunubi.

23 Amincewa da horon Allah zai taimaka maka ka kasance cikin ƙaunar Allah. Hakika, an fitar da wasu daga ikilisiyar Kirista, amma wannan ba zai same ka ba idan ka “kiyaye zuciyarka” kuma ‘ka yi tafiya kamar mai hikima.’ (Misalai 4:23; Afisawa 5:15) Idan an yi maka yankan zumunci, me ya sa ba za ka ɗauki matakin da zai sa a maido ka ba? Allah yana son duka waɗanda suka keɓe kansu a gare shi su bauta masa cikin aminci da “farinciki.” (Kubawar Shari’a 28:47) Za ka iya yin haka har abada idan ka ci gaba da yin na’am da horon Jehobah.—Zabura 100:2.

Yaya Za Ka Amsa?

• Me ya sa ake fitar da wasu daga ikilisiyar Kirista?

• Menene tuba na gaskiya ya ƙunsa?

• Me ya sa ya kamata a furta mugun zunubi?

• A waɗanne hanyoyi ne Kiristoci dattawa suke taimaka wa masu zunubi da suka tuba?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba