“ ’Ya’ya, Ku Yi Biyayya Da Waɗanda Suka Haife Ku”
“ ’Ya’ya, ku yi biyayya da waɗanda suka haife ku cikin Ubangiji: gama wannan daidai ne.”—AFISAWA 6:1.
1. Ta yaya ne biyayya zai iya kāre ka?
MUNA da rai yanzu wataƙila domin mun yi biyayya ne, amma waɗansu ba su da rai saboda rashin biyayya. Biyayya ga menene? Alal misali, gargaɗi daga jikinmu, “abin al’ajabi”. (Zabura 139:14) Idanunmu na ganin hadari kuma kunnuwanmu na jin ƙarar tsawa. Wannan ƙarar na sa gashin jikinmu ya tashi. Waɗanda suka san haɗarin da ke tattare da wannan za su san cewa waɗannan alamu gargaɗi ne na neman wurin ɓuya daga ruwa da ƙanƙara da kuma walƙiya da zai iya yin kisa.
2. Me ya sa yara suke bukatar gargaɗi, kuma me ya sa ya kamata su yi biyayya ga iyayensu?
2 Ku matasa kuna bukatar gargaɗi game da haɗarin da ke tafe, kuma iyayenku suna da hakkin yi muku gargaɗin. Za ka iya tuna an taɓa ce maka: “Kada ka taɓa murhu. Yana da zafi.” “Kada ka yi kusa da ruwa mai zurfi. Yana da haɗari.” “Ka duba hanya kafin ka tsallaka titi.” Abin baƙin ciki, yara sun ji rauni ko kuma sun mutu saboda rashin biyayya. Yin biyayya ga iyaye “daidai ne” kuma ya dace. Yana sa mutum hikima. (Misalai 8:33) Wata aya a cikin Littafi Mai Tsarki ta ce “abin yarda ne” ga Ubangijinmu Yesu Kristi. Hakika, Allah ya umurce ku ku yi wa iyayenku biyayya.—Kolossiyawa 3:20; 1 Korinthiyawa 8:6.
Sakamako na Dindindin na Biyayya
3. Menene “hakikanin rai” ga yawancinmu, kuma ta yaya ne yara za su more ta?
3 Biyayya ga iyaye za ta kiyaye ‘ranka yanzu,’ kuma yin biyayya zai sa ka mori rayuwa “mai-zuwa,” wanda kuma ake kira “hakikanin rai.” (1 Timothawus 4:8; 6:19) A gare mu, hakikanin rai rayuwa ce ta dindindin a sabuwar duniya ta Allah, wadda ya yi alkawarin zai ba waɗanda suka bi dokokinsa. A wata doka mai muhimmanci an ce: “Ka girmama ubanka da uwarka ita ce doka ta fari tare da wa’adi, domin ka sami alheri, ka yi tsawon rai kuma cikin ƙasan.” Idan ka yi biyayya ga iyayenka, za ka yi farin ciki. A nan gaba za ka sami kwanciyar rai, kuma wataƙila za ka more rayuwa har abada a aljanna ta duniya!—Afisawa 6:2, 3.
4. Ta yaya ne yara za su yi biyayya ga Allah kuma hakan ya amfane su?
4 Idan ka yi biyayya ga iyayenka, kana yin biyayya ne ga Allah saboda shi ne ya umurce ka ka yi masu biyayya. Kuma za ka amfana. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya ke koya maka zuwa amfaninka.” (Ishaya 48:17; 1 Yohanna 5:3) Ta yaya ne za ka amfana don yin biyayya? Zai sa mahaifinka da mahaifiyarka su yi farin ciki, kuma za su nuna farin cikinsu a hanyoyin da za su sa ka fi farin ciki a rayuwarka. (Misalai 23:22-25) Abu mafi muhimmanci shi ne, biyayyarka za ta faranta wa Allahnka na samaniya rai, kuma zai albarkace ka ta hanyoyi masu kyau! Bari mu ga yadda Jehobah ya kāre Yesu kuma ya albarkace shi, wanda ya ce game kansa: “Ina aika abin da ya gamshe shi.”—Yohanna 8:29.
Yesu Mai Aiki Ne Tuƙuru
5. Wane dalili ne ya sa ka gaskata cewa Yesu mai aiki tuƙuru ne?
5 Yesu ne ɗan fari na mahaifiyarsa, Maryamu. Mahaifinsa Yusufu kafinta ne. Yesu ma ya zama kafinta, ya koyi aikin daga wurin Yusufu. (Matta 13:55; Markus 6:3; Luka 1:26-31) Wane irin kafinta ne Yesu? Sa’ad da yake sama kafin Allah ya sa mahaifiyarsa ta ɗauki cikinsa ta wurin mu’ujiza, da yake shi ne hikima, ya ce: “Ina nan wurinsa, gwanin mai-aiki ne: kowace rana ni ne abin daularsa.” Allah ya amince da Yesu da yake shi mai aiki tuƙuru ne a sama. Kana tsammanin sa’ad da yake matashi a duniya ya yi ƙoƙari ya kasance mai aiki tuƙuru, wato ƙwararren kafinta?—Misalai 8:30 Kolossiyawa 1:15, 16.
6. (a) Me ya sa kake tsammanin cewa wataƙila sa’ad da Yesu yake matashi ya yi aiki a gida? (b) A waɗanne hanyoyi ne yara za su iya yin koyi da Yesu?
6 Babu shakka, sa’ad da Yesu yake yaro, wani lokaci yana yin wasa, kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ce yara sun yi a ƙarni na farko. (Zechariah 8:5; Matta 11:16, 17) Duk da haka, da yake shi ɗan fari ne a cikin iyali marasa dukiya, dole ne ya yi wasu aikace-aikace bayan aikin kafinta da Yusufu yake koya masa. Daga baya, Yesu ya zama mai bishara kuma ya ba da kansa ga hidima har ya hana wa kansa jin daɗin rayuwa. (Luka 9:58; Yohanna 5:17) Ka ga hanyoyin da za ka iya yin koyi da Yesu? Iyayenka suna gaya maka ka share ɗakinka ko kuma ka yi wasu aikace-aikace? Suna ƙarfafa ka ka bauta wa Allah ta wurin halartar taron Kirista da kuma gaya wa wasu imaninka? Ta yaya kake tsammanin cewa sa’ad da Yesu yake matashi ya ɗauki irin wannan umurni?
Ɗalibi Mai Kyau da kuma Malami na Littafi Mai Tsarki
7. (a) Da su wanene mai yiwuwa Yesu ya yi tafiya zuwa Idin Ƙetarewa? (b) Ina ne Yesu yake sa’ad da sauran suke komawa gida, kuma me ya sa yake wurin?
7 An umurci kowane namiji ya je ya bauta wa Jehobah a haikali a lokacin Idin Yahudawa na kwanaki uku. (Kubawar Shari’a 16:16) Sa’ad da Yesu yake ɗan shekara 12, mai yiwuwa dukan iyalansa sun tafi Urushalima saboda Idin Ƙetarewa. Har da ƙannen Yesu maza da mata. Waɗanda suke tafiya tare da iyalin su Yesu wataƙila sun haɗa da Salome, wadda mai yiwuwa ’yar’uwar Maryamu ce, tare da maigidanta Zebedee da kuma ’ya’yansu Yakubu da Yohanna, waɗanda daga baya suka zama manzannin Yesu.a (Matta 4:20, 21; 13:54-56; 27:56; Markus 15:40; Yohanna 19:25) Sa’ad da suke komawa gida, Yusufu da Maryamu suna zaton cewa Yesu yana tare da danginsu ne, shi ya sa da farko ba su lura ba cewa ba ya tare da su. Bayan kwanaki uku, Maryamu da Yusufu suka sami Yesu a cikin haikali, “yana zaune a tsakiyar malamai, yana jinsu, yana kuwa yi masu tantambaya.”—Luka 2:44-46.
8. Menene Yesu ya yi a haikali, kuma me ya sa mutanen suka yi mamaki?
8 Ta yaya ne Yesu yake “tantambayar” malaman? Ba wai yana tambaya don ya sani ko kuma don ya sami bayani ba ne. Kalmar Helenanci da aka yi amfani da ita a nan tana nufin tambaya da ake yi don bincike na shari’a wanda ya ƙunshi yin amfani da tambaya don a amsa tambaya. Hakika, sa’ad da yake yaro, Yesu ya kasance ɗalibin Littafi Mai Tsarki wanda ya ba malaman addinai mamaki! Littafi Mai Tsarki ya ce: “Dukan waɗanda suka ji shi suka yi mamaki da fahiminsa da magana da ya ke mayarwa.”—Luka 2:47.
9. Ta yaya za ka bi misalin Yesu a yin nazarin Littafi Mai Tsarki?
9 Me ya sa sa’ad da Yesu yake yaro ya ba ƙwararrun malamai mamaki da iliminsa na Littafi Mai Tsarki? Saboda yana da iyaye masu tsoron Allah waɗanda suka koya masa umurnin Allah tun yana jariri. (Fitowa 12:24-27; Kubawar Shari’a 6:6-9; Matta 1:18-20) Mun tabbata cewa Yusufu ya kai Yesu majami’a sa’ad da yake yaro don ya ji yadda ake karanta da kuma tattauna Nassosi. Kana da iyaye da suke yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kai kuma suna kai ka taron Kirista? Kana godiya don ƙoƙarin da suke yi, kamar yadda Yesu ya yi godiya ga iyayensa? Kana gaya wa waɗansu abubuwan da ka koya, kamar yadda Yesu ya yi?
Yesu Ya Yi Biyayya
10. (a) Me ya sa ya kamata iyayen Yesu su san inda za su same shi? (b) Wane misali ne mai kyau Yesu ya kafa wa yara?
10 Yaya kake tsammanin Maryamu da Yusufu suka ji sa’ad da suka sami Yesu a haikali bayan kwanaki uku? Babu shakka, sun yi farin ciki sosai. Yesu kuwa ya yi mamakin cewa iyayensa ba su san inda yake ba. Dukansu suna sane da haihuwar Yesu na mu’ujiza. Bugu da ƙari, ko da yake ba su fahimci batun dalla-dalla ba, amma ya kamata su san wani abu game da matsayinsa na mai ceto da kuma Sarki na Mulkin Allah a nan gaba. (Matta 1:21 Luka;1:32-35; 2:11) Shi ya sa Yesu ya tambaye su: “Ina abin da ya sa kuka neme ni? ba ku sani ba wajib ne a gareni ina cikin sha’anin Ubana?” Duk da haka, Yesu ya yi biyayya ya bi iyayensa suka koma gida a Nazarat. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ya ci gaba da biyayya da su.” Bugu da ƙari, “uwatasa kuma ta riƙe dukan al’amuran nan a cikin zuciyarta.”—Luka 2:48-51.
11. Wane darasi ne game da biyayya za ka iya koya daga wurin Yesu?
11 Kana gani yana da sauƙi ka yi koyi da Yesu, ka yi biyayya ga iyayenka koyaushe? Ko kuma kana ganin cewa ba su fahimci duniya ta zamani ba kuma ka san abubuwa fiye da su? Hakika, za ka iya sanin wasu abubuwa fiye da su kamar yin amfani da selula, kwamfuta, ko kuma na’ura ta zamani. Ka yi tunanin Yesu, wanda ya ba ƙwararrun malamai mamaki da “fahiminsa da magana.” Za ka yarda cewa idan aka kwatanta ka da shi, ba ka san kome ba. Duk da haka, Yesu ya yi biyayya ga iyayensa. Wannan ba ya nufin cewa ya yarda da dukan shawararsu ba. Amma, ‘ya ci gaba da yin biyayya da su’ har ya girma. Wane darassi ne kake ganin za ka iya koya daga misalinsa?—Kubawar Shari’a 5:16, 29.
Biyayya Ba Shi da Sauƙi
12. Ta yaya ne yin biyayya zai ceci ranka?
12 Biyayya ba ta da sauƙi, kamar yadda aka kwatanta a shekaru da suka wuce sa’ad da wasu yara mata biyu suke son su tsallaka babban titi maimakon su bi kan gadar da aka yi don masu tafiya. “Ka zo mu je John,” suka ce wa wani abokinsu sa’ad da yake bin gadar da aka yi don masu tafiya. “Ba za ka bi mu ba?” Sa’ad da yake shakka, ɗaya daga cikin yaran ta ce masa, “Kai wawa ne!” Da gabagaɗi John, ya ce, “Dole ne in saurari mamata.” Sa’ad da John yake tafiya a kan gadar, ya ji ƙarar mota da ya duba sai ya ga mota ce ta kaɗe yaran nan. Ɗaya daga cikin yaran ta mutu, ɗaya kuma ta ji rauni sosai har aka yanke mata kafa. Daga baya, uwar yaran, wadda ta gargaɗe su su bi gadar da aka yi don masu tafiya ta gaya wa mahaifiyar John cewa: “Da a ce sun yi biyayya kamar yadda yaron ki ya yi.”— Afisawa 6:1.
13. (a) Me ya sa ya kamata ka yi wa iyayenka biyayya? (b) Yaushe ne bai dace yaro ya yi abin da iyayensa suka ce ya yi ba?
13 Me ya sa Allah ya ce: “ ’Ya’ya, ku yi biyayya da waɗanda suka haife ku”? Idan ku ka yi biyayya da iyayenku, Allah ne ku ke yi masa biyayya. Ban da haka, iyayenku sun fi ku fahimi a rayuwa. Alal misali, shekaru biyar kafin hatsarin da aka ambata a baya ya faru, yaron abokiyar uwar John ya mutu a hatsarin mota sa’ad da yake son ya tsallake wannan babban titin! Hakika, yin biyayya ga iyaye ba koyaushe yake da sauƙi ba, amma Allah ya ce ka yi musu biyayya. A wani ɓangare kuma, idan iyayenka suka ce ka yi ƙarya, ko sata, ko kuma ka yi wani abu da Allah ba ya so, dole ne ka yi “biyayya ga Allah da mutane.” Shi ya sa bayan da Littafi Mai Tsarki ya ce “ku yi biyayya da waɗanda suka haife ku,” ya daɗa, a “cikin Ubangiji.” Wannan ya ƙunshi yin biyayya ga iyayenka a dukan abubuwa da suka yi daidai da dokokin Allah.—Ayukan Manzanni 5:29.
14. Me ya sa biyayya take da sauƙi ga kamiltaccen mutum, duk da haka me ya sa ya kamata ya koya?
14 Kana gani idan kai kamili ne wato “marar-ƙazamta,” kamar Yesu zai yi maka sauƙi ne ka yi biyayya ga iyayenka? (Ibraniyawa 7:26) Da a ce kai kamili ne, ba za ka yi tunanin yin abu marar kyau ba, kamar yadda ka ke yi yanzu. (Farawa 8:21; Zabura 51:5) Yesu ma ya koyi darassi game da biyayya. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ko da shi ke [Yesu] Ɗa ne, duk da wannan ya koya biyayya ta wurin wahalar da ya sha.” (Ibraniyawa 5:8) Ta yaya ne wahala ta koya wa Yesu yin biyayya, darassin da bai koya ba lokacin da yake sama?
15, 16. Ta yaya ne Yesu ya koyi yin biyayya?
15 Da taimakon Jehobah, Yusufu da Maryamu sun kāre Yesu daga mugunta sa’ad da yake yaro. (Matta 2:7-23) Daga baya, Allah ya cire mafificin kāriya daga wurin Yesu. Wahalar da Yesu ya sha ya yi tsanani sosai har Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu ya “miƙa addu’o’i da roƙe-roƙe tare da kuka mai-zafi da hawaye.” (Ibraniyawa 5:7) Yaushe ne hakan ya faru?
16 Wannan ya faru a ƙarshen rayuwar Yesu a duniya sa’ad da Shaiɗan ya yi ƙoƙari sosai ya karya amincinsa. Yesu ya damu sosai game da yadda mutuwarsa ta wulakanci za ta ɓata sunan Ubansa shi ya sa da ya “ƙara naciyar addu’a [a lambun Jathsaimani] jiɓinsa kuma ya zama kamar manyan ɗararasa na jini, sun fāɗuwa a ƙasa.” Bayan ɗan lokaci, mutuwarsa a kan gungumen azaba ta yi masa zafi sosai har Yesu ya yi “kuka mai-zafi da hawaye.” (Luka 22:42-44; Markus 15:34) Ya “koyi biyayya ta wurin wahalar da ya sha” da haka ya faranta zuciyar Ubansa. Yanzu da yake sama, Yesu ya san wahalar da muke sha yayin da muke ƙoƙarin mu yi biyayya.— Misalai 27:11; Ibraniyawa 2:18; 4:15.
Koyan Darassi na Biyayya
17. Ta yaya ya kamata mu ɗauki horo?
17 Idan mahaifinka da mahaifiyarka suka yi maka horo, yana nuna cewa suna son abin da zai amfane ka ne kuma suna ƙaunarka. Littafi Mai Tsarki ya yi tambaya: “Ina ɗan wanda ubansa ba ya yi masa horo ba?” Ba za ka yi da na sani ba idan iyayenka suka ƙi su nuna maka ƙauna wadda za ta sa su sami lokacin yi maka gyara? Haka nan ma, saboda Jehobah yana ƙaunarka, shi ya sa yake maka gyara. “Kowane irin horo ana ganinsa ba abin faranta zuciya ba, amma abin ban ciwo ne a loton yi: amma daga baya ya kan bada amfani mai-salama-watau na adalci ke nan-ga waɗanda sun wāsu ta wurinsa.”—Ibraniyawa 12:7-11.
18. (a) Menene horo cikin ƙauna yake nunawa? (b) Ta wace hanya ce mai kyau ka gani horo ya gyara mutane?
18 Wani Sarki a Isra’ila ta dā, wanda Yesu ya yi magana game da hikimarsa mai girma, ya yi magana game da gyara daga iyaye. Sulemanu ya rubuta, “Wanda ya sauƙaƙa bulalatasa yana ƙin ɗansa ke nan: Amma wanda ya ƙaunace shi ya kan fore shi da anniya.” Sulemanu ya ce mutumin da yake son gyara zai ceci ransa kuma daga mutuwa. (Misalai 13:24; 23:13, 14; Matta 12:42) Wata mata ta tuna cewa sa’ad da take yarinya idan ta yi abin da bai dace ba a taron Kirista, babanta zai yi alkawarin cewa idan suka koma gida zai yi mata horo. Yanzu tana farin ciki don horon nan da babanta ya yi mata cikin ƙauna da ya gyara rayuwarta.
19. Me ya sa ya kamata ka yi biyayya ga iyayenka?
19 Ka yi godiya idan kana da iyaye da suke ƙaunar ka sosai kuma suna ɗaukan lokaci su yi maka horo a cikin ƙauna. Ka yi musu biyayya, kamar yadda Yesu Kristi ya yi biyayya da iyayensa, Yusufu da Maryamu. Ka yi musu biyayya saboda musamman Ubanka na samaniya, Jehobah Allah, ya ce ka yi haka. Ta yin haka, za ka amfane kanka, kuma za “ka sami alheri, ka yi tsawon rai kuma cikin ƙasan.”—Afisawa 6:2, 3.
[Hasiya]
a Ka duba Insight on the Scriptures, Littafi na 2, shafi na 841, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
Ta Yaya Za Ka Amsa?
• Waɗanne amfani ne yara za su iya samu idan suka yi biyayyya ga iyayensu?
• Ta yaya ne Yesu ya nuna misalin yin biyayya ga iyaye sa’ad da yake yaro?
• Ta yaya ne Yesu ya koyi yin biyayya?
[Hoto a shafi na 18]
Yesu ɗan shekara sha biyu ya san Nassosi sosai
[Hoto a shafi na 20]
Ta yaya ne Yesu ya koyi biyayya daga wahalar da ya sha?