Yadda Za a Gane Bauta Ta Gaskiya
YAWANCIN addinai suna da’awar cewa abin da suke koyarwa ya fito ne daga Allah. Saboda haka, ya dace mu saurari kalaman Yohanna, manzon Yesu, wanda ya rubuta: “Masoya, kada ku bada gaskiya ga kowane ruhu, amma ku gwada ruhohi, ko na Allah ne: gama masu-ƙaryan annabci dayawa sun fita zuwa cikin duniya.” (1 Yohanna 4:1) Ta yaya za mu iya gwada wani abu mu gani ko ya fito ne daga Allah?
Duk abin da ya fito daga Allah yana nuna mutumtakarsa, musamman ƙauna, halinsa mafi muhimmanci. Alal misali, hancinmu, wanda ke sa mu ji daɗin ƙamshin tsimi, fure, ko kuma burodin da aka gasa, yana nuna ƙaunar Allah. Iya ganin rana, malam-buɗe-littafi, ko kuwa murmushin ɗan ƙaramin yaro, duk suna nuna ƙaunar da Allah ke mana. Haka yake kuma da iyawarmu na jin waƙa mai daɗi, kukan tsuntsaye, ko kuma muryar wanda muke ƙauna. Yadda aka halicce mu, duk da cewa mu ajizai ne, hakan na nuna ƙaunar Allah. Shi ya sa muke shaida gaskiyar kalaman Yesu a yawancin lokaci: “Bayarwa ta fi karɓa albarka.” (Ayukan Manzanni 20:35) Muna jin daɗin nuna ƙauna domin an halicce mu a “cikin surar Allah.” (Farawa 1:27) Ko da yake Jehobah yana da wasu halaye masu yawa, ƙauna ita ce mafifici a cikin dukansu.
Rubuce-rubucen da suka fito daga Allah ya kamata su nuna ƙaunarsa. Addinai na duniya suna da rubuce-rubuce masu yawa na dā. Ta yaya ne irin waɗannan rubuce-rubucen suka yi nasara wajen nuna ƙaunar Allah?
Gaskiyar ita ce, yawancin rubuce-rubuce na dā na addinai ba su yi wani cikakken bayani ba game da yadda Allah ya ƙaunace mu ko yadda za mu ƙaunaci Allah. Da haka, miliyoyin mutane ba sa samun amsa sa’ad da suka yi tambaya cewa, “Me ya sa muke ganin alamar ƙaunar Allah a halittu, amma wahala da mugunta na ci gaba da faruwa?” A wani ɓangaren kuma, Littafi Mai Tsarki ne kaɗai tsohon rubutu na addini da ya bayyana ƙaunar Allah sosai. Kuma ya koya mana yadda za mu nuna ƙauna.
Littafin da Ya Yi Magana Game da Ƙauna
Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki, ta bayyana cewa Jehobah ne “Allah kuwa na ƙauna.” (2 Korinthiyawa 13:11) Littafi Mai Tsarki ya kwatanta yadda ƙauna ta motsa Jehobah ya ba mutane na farko rayuwar da babu rashin lafiya da mutuwa. Amma yin tawaye ga ikon Allah ya jawo wa mutane wahala. (Kubawar Shari’a 32:4, 5; Romawa 5:12) Jehobah ya ɗauki mataki don ya maido da abin da aka ɓatar. Kalmar Allah ta ce: “Allah ya yi ƙaunar duniya har ya bada Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana bada gaskiya gareshi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.” (Yohanna 3:16) Nassosi Mai Tsarki ya ƙara bayyana ƙaunar Allah sa’ad da ya kwatanta yadda Allah ya yi tanadin gwamnati a ƙarƙashin ikon Yesu don kawo salama ga mutane masu biyayya.—Daniel 7:13, 14; 2 Bitrus 3:13.
Littafi Mai Tsarki ya ƙayyade hakkin mutum da waɗannan kalmomin: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka. Wannan ce babbar doka, ita ce kuwa ta fari. Wata kuma ta biyu mai-kamaninta ke nan, Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka. Ga waɗannan doka biyu dukan Attaurat da Annabawa su ke ratayawa.” (Matta 22:37-40) Littafi Mai Tsarki ya faɗi cewa, shi hurarre ne daga Allah. Tun da yake ya nuna halin Allah babu rufa-rufa, muna da tabbacin cewa ya zo ne daga “Allah kuwa na ƙauna.”—2 Timothawus 3:16.
Ta wajen yin amfani da wannan mizanin guda, za mu iya gane ko waɗanne littattafai na dā ne ainihi suka fito daga Allah. Ƙauna kuma tana nuna masu bauta ta gaskiya, domin suna yin koyi da Allah wajen nuna ƙauna.
Yadda Za a Gane Mutanen da Suke Ƙaunar Allah
Waɗanda suke ƙaunar Allah da gaske su fitattu ne, musamman yanzu da muke zaune a lokacin da Littafi Mai Tsarki yake ƙira “kwanaki na ƙarshe.” A kullum mutane suna ƙara zama “masu-son kansu, masu-son kuɗi, . . . ma-fiya son annishuwa da Allah.”—2 Timothawus 3:1-4.
Ta yaya za ka iya gane mutanen da ke ƙaunar Allah? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa.” (1 Yohanna 5:3) Ƙaunar Allah yana motsa mutane su daraja mizanan Littafi Mai Tsarki game da ɗabi’a. Alal misali, Kalmar Allah tana ɗauke da dokoki game da jima’i da aure. An amince da jima’i kawai ne a cikin aure, kuma aure abu ne na dindindin. (Matta 19:9; Ibraniyawa 13:4) Sa’ad da wata mata a Spain da ta yi nazarin tauhidi ta halarci taro a inda Shaidun Jehobah suke taruwa a kowane lokaci su yi nazarin dokokin Littafi Mai Tsarki game da ɗabi’a, ta ce: “Na bar taron a ƙarfafe, ba kawai domin jawaban Nassosin da suka ba ni haske ba ne, amma domin haɗin kai da ke tsakanin waɗannan mutanen, da kuma ɗabi’unsu masu kyau.”
Ƙari ga ƙaunar da suke yi wa Allah, ana gane Kiristoci na gaskiya ta yadda suke nuna wa maƙwabtansu ƙauna. Aikinsu mafi muhimmanci shi ne gaya wa mutane game da begen ’yan adam kaɗai, wato Mulkin Allah. (Matta 24:14) Ba abin da zai iya kawo wa maƙwabtansu amfani na dindindin fiye da taimaka musu su sami sani na Allah. (Yohanna 17:3) Kiristoci na gaskiya suna kuma nuna ƙaunarsu a wasu hanyoyin. Suna taimaka wa waɗanda suke shan wahala. Alal misali, sa’ad da girgizar ƙasa ta jawo bala’i a ƙasar Italiya, wata jaridar ƙasar ta ba da rahoto cewa Shaidun Jehobah “sun taimaka wa waɗanda suke wahala, ba tare da sun damu da irin addinin da suke bi ba.”
Ban da ƙaunar Allah da maƙwabta, Kiristoci na gaskiya suna ƙaunar juna. Yesu ya ce: “Sabuwar doka ni ke ba ku, ku yi ƙaunar juna; kamar yadda ni na ƙaunace ku, ku ma ku yi ƙaunar juna. Bisa ga wannan mutane duka za su fahimta ku ne almajiraina, idan kuna da ƙauna ga junanku.”—Yohanna 13:34, 35.
Ƙaunar da Kiristoci na gaskiya suke yi wa juna ya bambanta kuwa? Wata mai kula da gida mai suna Ema ta yi tunanin haka. Tana aiki ne a La Paz, a ƙasar Bolivia, inda bambance-bambance na ƙabila ke raba masu kuɗi daga talakawa. Ta ce: “A ranar da na soma halartar taron Shaidun Jehobah, na ga wani mutum da ya yi shiga mai kyau ya zauna yana tattaunawa da wata mata ’yar Indiya. Ban taɓa ganin haka ba. A wannan lokacin, na san cewa waɗannan su ne mutanen Allah.” Hakazalika, wata budurwa ’yar Brazil mai suna Miriam ta ce: “Ba na samun farin ciki, har ma a cikin iyalina. Amma, a tsakanin Shaidun Jehobah ne na soma ganin yadda ake nuna ƙauna.” A Amirka, wani mai kula da labarai na gidan talabijin ya rubuta: “Da a ce yawancin mutane suna irin rayuwar da mutanen addininku suke yi, da wannan ƙasar ba ta cikin irin halin da take yanzu. Ni ɗan jarida ne da na san cewa ƙungiyarku ta kafu ne a kan ƙauna da kuma bangaskiya mai ƙarfi a Mahalicci.”
Ka Biɗi Bauta Ta Gaskiya
Ƙauna ita ce alamar da ke bambanta bauta ta gaskiya. Yesu ya kwatanta samun bauta ta gaskiya da samun hanyar da ta dace da kuma yin tafiya a kanta. Ita kaɗai ce hanyar da ta nufi rai na madawwami. Yesu ya ce: “Ku shiga ta wurin ƙunƙuntar ƙofa: gama ƙofa da fāɗi ta ke, hanya kuwa da fāɗi, wadda ta nufa wajen hallaka, mutane dayawa fa suna shiga ta wurinta. Gama ƙofa ƙunƙunta ce, hanya kuwa matsatsiya, wadda ta nufa wajen rai, masu samunta fa kaɗan ne.” (Matta 7:13, 14) Rukuni guda ne kawai na Kiristoci na gaskiya yake bin Allah a kan hanyar bauta ta gaskiya. Saboda haka, ya kamata ka damu da irin addinin da ka zaɓa. Idan ka sami irin wannan hanyar kuma ka zaɓi yin tafiya a kanta, babu shakka, ka sami hanya mafi kyau a rayuwa, domin ita ce hanyar ƙauna.—Afisawa 4:1-4.
Ka yi tunanin irin farin cikin da za ka samu yayin da kake tafiya a kan hanyar bauta ta gaskiya! Kamar kana tafiya da Allah ne. Daga wurin Allah za ka iya koyon hikima da ƙauna domin ka more dangantaka mai kyau da mutane. Daga wurinsa za ka iya koyan manufar rayuwa, kuma za ka iya fahimtar alkawuran Allah kuma ka kasance da bege don nan gaba. Ba za ka taɓa yin nadamar biɗar bauta ta gaskiya ba.
[Hoto a shafi na 3]
A cikin duka rubuce-rubuce na dā, Littafi Mai Tsarki kaɗai ne ya bayyana ƙaunar Allah
[Hotuna a shafi na 5]
Ana gane Kiristoci na gaskiya domin suna nuna ƙauna