Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 4/1 pp. 26-30
  • Ka Yi Biyayya Cikin Tawali’u Ga Makiyaya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Biyayya Cikin Tawali’u Ga Makiyaya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Kyauta Daga Sammai ga Ikilisiya
  • Ka Yi Biyayya ka Bi Umurni
  • Dalilai Huɗu da ya sa za Mu Ba da Haɗin Kai
  • Nuna Biyayyarmu
  • Jehobah Yana Yi wa Waɗanda Suka ba da Haɗin kai da Son Rai Albarka
  • Ka Yi Biyayya ga Makiyayan da Jehobah Ya Naɗa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Makiyaya, Ku Yi Koyi da Makiyaya Mafi Girma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Kristi Yana Ja-gorar Ikilisiyarsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 4/1 pp. 26-30

Ka Yi Biyayya Cikin Tawali’u Ga Makiyaya

“Ku yi biyayya da waɗanda ke shugabannanku, ku sarayadda kanku garesu.”—IBRANIYAWA 13:17.

1, 2. Waɗanne nassosi ne suka nuna cewa Jehobah da Yesu Makiyaya ne masu ƙauna?

JEHOBAH ALLAH da Ɗansa Yesu Kristi makiyaya ne masu ƙauna. Ishaya ya annabta: “Duba, Ubangiji za ya zo kamar mai-iko, hannunsa za ya yi mulki: ga shi, ladansa yana tare da shi . . . Za ya yi kiwon garkensa kamar makiyayi, za ya tattara ’ya’yan tumaki a hannunsa, ya ɗauke su a cikin ƙirjinsa, a hankali kuma za ya bida masu-bada mama.”—Ishaya 40:10, 11.

2 Wannan annabci na maidowa ya samu cikawa ta farko a lokacin da Yahudawa da suka rage suka koma Yahuda a shekara ta 537 K.Z. (2 Labarbaru 36:22, 23) Ya sake cika sa’ad da Cyrus Babba Yesu Kristi ya ceci shafaffun da suka rage daga “Babila babba” a shekara ta 1919. (Ru’ya ta Yohanna 18:2; Ishaya 44:28) Shi ne “hannun” Jehobah na sarauta, da yake ya tattara tumaki kuma ya kula da su da kyau. Yesu ya ce: “Ni ne makiyayi mai-kyau; na san nawa, nawa kuma sun san ni,”—Yohanna 10:14.

3. Ta yaya ne Jehobah ya nuna yana kula da yadda ake bi da tumakinsa?

3 Annabci na Ishaya 40:10, 11 sun nanata yadda Jehobah yake kula da mutanensa cikin ƙauna. (Zabura 23:1-6) A lokacin da yake hidima a duniya, Yesu ya nuna ƙauna ga almajiransa da kuma mutane gabaki ɗaya. (Matta 11:28-30; Markus 6:34) Jehobah da Yesu sun ƙi jinin muguntan makiyaya ko kuma shugabannin Isra’ila da suka yasar da tumakinsu kuma suka cuce su. (Ezekiel 34:2-10; Matta 23:3, 4, 15) Jehobah ya yi alkawari: “Sai in ceci garkena, ba za su ƙara zaman ganima ba; tsakanin dabba da dabba kuma zan raba shari’a. In sa makiyayi ɗaya a kansu, shi yi kiwonsu, watau bawana Dauda; shi ne za ya yi kiwonsu, ya zama makiyayinsu.” (Ezekiel 34:22, 23) A wannan zamani na ƙarshe, Yesu Kristi, wato Dauda Babba shi ne “makiyayi ɗaya” wanda Jehobah ya naɗa bisa duka bayinsa a duniya duk da Kiristoci shafaffu na ruhu da “waɗansu tumaki.”—Yohanna 10:16.

Kyauta Daga Sammai ga Ikilisiya

4, 5. (a) Wace kyauta mai tamani ce Jehobah ya ba mutanensa na duniya? (b) Wace kyauta ce Yesu ya ba ikilisiyarsa?

4 Yesu Kristi da Jehobah sun ba da kyauta mai tamani ga ikilisiyar Kirista ta wajen ba bayinsa a duniya “makiyayi ɗaya.” An annabta kyautar Shugaba na sammai a Ishaya 55:4: “Ga shi, na sanya shi shaida ga al’ummai, shugaba da mai-mulki ga al’ummai.” An tattara Shafaffun Kiristoci da “taro mai-girma” daga kowace ƙasa, kabila, al’ummai, da kuma harsuna. (Ru’ya ta Yohanna 5:9, 10; 7:9) Sun zama ikilisiya ta duka duniya, “garke ɗaya,” a ƙarƙashin shugabancin “makiyayi ɗaya,” wato Yesu Kristi.

5 Yesu kuma ya ba ikilisiyarsa ta duniya kyauta mai tamani. Ya yi tanadin dattawa masu aminci waɗanda za su bi gurbin Jehobah da Yesu wajen kula da garken cikin ƙauna. Manzo Bulus ya yi magana game da wannan kyauta a wasiƙarsa zuwa ga Kiristoci a Afisa. Ya ce: “Sa’anda ya hau bisa, ya bida rundunar bayi cikin bauta, Ya bada kyautai ga mutane. Ya kuma bada waɗansu su zama manzanni; waɗansu, annabawa; waɗansu, masu-wa’azin bishara; waɗansu, makiyaya da masu-koyarwa; domin kamaltawar tsarkaka, domin aikin hidima, domin ginin jikin Kristi.”—Afisawa 4:8, 11, 12.

6. A cikin Ru’ya ta Yohanna 1:16, 20, ta yaya ne aka kwatanta dattawa shafaffu masu kula, kuma menene za a iya cewa game da dattawan da aka naɗa waɗanda suke cikin waɗansu tumaki?

6 Waɗannan ‘kyauta ga mutane’ sune masu kula ko kuma dattawa, waɗanda Jehobah da Ɗansa suka naɗa da taimakon ruhu mai tsarki, don su kula da tumakin cikin ƙauna. (Ayukan Manzanni 20:28, 29) Dā waɗannan maza masu kula shafaffun Kiristoci ne. A Ru’ya ta Yohanna 1:16, 20, an kwatanta rukunin dattawa da suke yin hidima a ikilisiyar shafaffu, kamar “taurari” ko kuma “mala’iku” waɗanda suke hannun dama na Kristi, wato a ƙarƙashin ikonsa. Duk da haka, a wannan zamani na ƙarshe, da adadin shafaffu masu kula suke ragewa a duniya, yawancin dattawa a ikilisiyar Kirista waɗansu tumaki ne. Tun da masu wakiltar Hukumar Mulki ne suke naɗa waɗannan da taimakon ruhu mai tsarki, ana iya cewa su ma suna hannun dama (ko kuma a ƙarƙashin ja-gorancin) Makiyayi Mai Kyau, Yesu Kristi. (Ishaya 61:5, 6) Ya kamata mu ba dattawa da suke ikilisiyoyinmu haɗin kai, tun da suna yin biyayya ga Kristi, wato Shugaban ikilisiya.—Kolossiyawa 1:18.

Ka Yi Biyayya ka Bi Umurni

7. Wane gargaɗi ne manzo Bulus ya yi game da halin da ya kamata mu nuna wa dattawa Kirista?

7 Makiyayanmu na samaniya Jehobah Allah da Yesu Kristi, suna bukatar mu yi biyayya kuma mu bi umurnin dattawan da suka ba hakkin kula da ikilisiya. (1 Bitrus 5:5) An huri manzo Bulus ya rubuta: “Ku tuna da shugabanninku na dā, waɗanda suka faɗa muku Maganar Allah. Ku dubi ƙarshensu, ku kuma yi koyi da bangaskiyarsu. Ku yi wa shugabanninku biyayya, ku bi umarnansu, don su ne masu kula da rayukanku, su ne kuma za su yi lissafin aikinsu, don su yi haka da farin ciki, ba da baƙin ciki ba, don in sun yi da baƙin ciki ba zai amfane ku ba.”—Ibraniyawa 13:7, 17; Littafi Mai Tsarki.

8. Menene Bulus ya ce mu ‘duba,’ kuma ta yaya ya kamata mu “yi biyayya”?

8 Ka lura cewa Bulus ya ce mu “dubi,” ko kuma mu yi la’akari da halayen dattawa masu aminci kuma mu bi irin wannan misalai na bangaskiya. Bugu da ƙari, ya shawarce mu mu yi biyayya kuma mu bi umurnin waɗannan maza da aka naɗa. Wani masanin Littafi Mai Tsarki, R. T France ya bayyana cewa, “a ainihin Helenanci, kalmar da aka fassara “yi biyayya” ba ita ba ce ainihin kalmar da ta dace ba, amma a zahiri tana nufin ‘rinjaya,’ wadda take nuna amincewa da shugabancinsu.” Muna yin biyayya ga dattawa saboda Kalmar Allah ta ce mu yi hakan kuma saboda mun tabbata cewa suna son abubuwa na Mulki da kuma ci gabanmu a ruhaniya. Za mu yi farin ciki idan muka bi shugabancinsu.

9. Ƙari ga yin biyayya, me ya sa ya kamata mu “bi umurni”?

9 Me ya kamata mu yi idan muna shakkar wata shawarar da dattawa suka tsai da game da wani batu? A nan ne ake bukatar yin biyayya. Yana da sauƙi mu yi biyayya idan muka amince da shawarar da aka tsai da, amma za mu nuna cewa muna yin biyayya da gaske idan muka bi umurni ko da ba mu amince da shawarar ba. Bitrus wanda ya zama manzo daga baya, ya nuna irin wannan biyayya.—Luka 5:4, 5.

Dalilai Huɗu da ya sa za Mu Ba da Haɗin Kai

10, 11. Ta wace hanya ce masu kula suka ‘faɗi maganar Allah’ ga ’yan’uwansu Kirista a ƙarni na farko da kuma a zamaninmu?

10 A Ibraniyawa 13:7, 17, da aka yi ƙaulinsa a baya, manzo Bulus ya ba da dalilai huɗu da ya sa ya kamata mu yi biyayya kuma mu bi umurnin dattawa Kirista. Na farko shi ne sun ‘faɗa mana maganar Allah.’ Ka tuna cewa Yesu ya ba ikilisiya ‘kyauta ga mutane’ domin “kamaltawar tsarkaka” ne. (Afisawa 4:11, 12) Ya gyara tunani da halayen Kiristoci na ƙarni na farko ta wurin dattawa masu aminci, waɗansunsu an hure su su rubuta wasiƙu zuwa ga ikilisiyoyi. Ya yi amfani da waɗannan masu kula da aka shafa da ruhu su ja-goranci Kiristoci na farko kuma su ƙarfafa su.—1 Korinthiyawa 16:15-18; 2 Timothawus 2:2; Titus 1:5.

11 A yau, Yesu yana yi mana ja-gora ta wurin “bawan nan mai-aminci, mai-hikima,” waɗanda suke wakiltar Hukumar Mulki da kuma dattawa da aka naɗa. (Matta 24:45) Saboda muna biyayya ga “babban Makiyayi,” Yesu Kristi, ya kamata mu bi shawarar Bulus: “Ku sansance waɗannan da ke hidima a wurinku, shugabannai ne a gareku cikin Ubangiji, suna kuma faronku.”—1 Bitrus 5:4; 1 Tassalunikawa 5:12; 1 Timothawus 5:17.

12. Ta yaya ne dattawa suke ‘kula da rayukanmu’?

12 Dalili na biyu da ya sa za mu ba da haɗin kai ga masu kula shi ne don su ne ‘masu kula da rayukanmu.’ Idan suka ga wani abu a halinmu da zai sa ruhaniyarmu a cikin haɗari, za su ba mu shawara nan da nan don mu gyara halinmu. (Galatiyawa 6:1) Kalmar Helenanci da aka fassara “kula” tana nufin “kasancewa a faɗake.” Wani masanin Littafi Mai Tsarki ya ce, “tana nufin makiyayi ya ci gaba da yin tsaro.” Domin suna yin tsaro na ruhaniya, a wani lokacin dattawa ba sa iya yin barci domin suna damuwa da lafiyarmu ta ruhaniya. Ya kamata mu ba da haɗin kai ga waɗannan dattawa masu ƙauna, waɗanda suke iyakar ƙoƙarinsu su yi koyi da yadda Yesu Kristi “babban makiyayin tumakin” yake kula da mutane.—Ibraniyawa 13:20.

13. Masu kula da Kiristoci za su ba da lissafi ga waye kuma ta yaya ne za su yi hakan?

13 Dalili na uku da ya sa ya kamata mu ba da haɗin kai ga dattawa shi ne suna tsaro sabili da rayukanmu domin “su ne kuma za su yi lissafin aikinsu.” Ya kamata masu kula su tuna cewa su dattawa ne, suna aiki a ƙarƙashin Makiyayi na samaniya, wato Jehobah Allah da kuma Yesu Kristi. (Ezekiel 34:22-24) Jehobah ne yake da tumakin, waɗanda “ya sayi da jinin [Ɗansa,]” kuma masu kula ne za su ba da lissafi game da yadda suke kula da garkensa, wanda ya kamata su “kewaye.” (Ayukan Manzanni 20:28, 29) Hakika, dukanmu za mu ba da lissafi ga Jehobah game da yadda muka bi umurninsa. (Romawa 14:10-12) Idan muka yi biyayya ga dattawa da aka naɗa za mu nuna muna bin umurnin Kristi, Shugaban ikilisiya.—Kolossiyawa 2:19.

14. Menene zai sa masu kula Kirista su yi hidima da “baƙinciki,” kuma menene sakamakon?

14 Bulus ya ba da dalili na huɗu da ya sa ya kamata mu bi umurnin masu kula da tawali’u. Ya rubuta: Don “su yi shi da farinciki, ba da baƙinciki ba: gama wannan mara-anfani ne gareku.” (Ibraniyawa 13:17) Dattawa Kirista suna da aiki sosai saboda suna koyarwa, suna ziyara, suna ja-gora a aikin wa’azi, suna kula da iyalinsu, da kuma sasanta matsaloli a cikin ikilisiya. (2 Korinthiyawa 11:28, 29) Idan muka ƙi mu ba su haɗin kai, muna ƙara musu aiki ne. Wannan zai sa su “baƙinciki.” Jehobah ba ya farin ciki idan muka ƙi ba da haɗin kai, kuma yin haka ba zai amfane mu ba. Maimakon haka, idan muka yi biyayya muka kuma ba da haɗin kai, dattawa za su yi aikinsu da farin ciki, kuma wannan zai sa waɗanda suke cikin ikilisiya su yi aikin wa’azin Mulki da haɗin kai da kuma farin ciki.—Romawa 15:5, 6.

Nuna Biyayyarmu

15. Ta yaya ne za mu nuna cewa muna yin biyayya kuma muna bin umurni?

15 Akwai hanyoyi da yawa da za mu iya ba wa masu kula haɗin kai. Idan dattawa sun shirya a yi taron wa’azi a rana da lokacin da ya shafi tsarinmu, saboda a daidaita da sabon yanayi na yankinmu, bari mu sa ƙwazo don mu ba da haɗin kai ga wannan sabon shirin. Wataƙila za mu samu albarka. Idan mai kula da hidima zai ziyarci rukunin Nazarin Littafi na Ikilisiyarmu, ya kamata mu ba da haɗin kai a aikin wa’azi a makon nan. Ka samu aiki a Makarantar Hidima ta Allah? Ya kamata ka tabbata ka halarci taron kuma ka yi aikin da aka ba ka. Mai kula da rukunin Nazarin Littafi na Ikilisiya ya yi sanarwa cewa rukuninmu ne suke da sharan Majami’ar Mulki? Bari mu ba shi haɗin kai, daidai gwargwadonmu. Ta waɗannan hanyoyi da kuma wasu, za mu nuna cewa muna bin umurnin mazan da Jehobah da Ɗansa suka naɗa don su kula da garken.

16. Idan dattijo bai yi abubuwa kamar yadda aka ce ya yi ba, me ya sa bai kamata mu yi tawaye ba?

16 Wani lokaci, dattijo ba zai yi abin da rukunin bawan nan mai aminci da Hukumar Mulki suka umurce shi ba. Idan ya ci gaba da yin hakan, dole zai ba da lissafi ga Jehobah, ‘Makiyayi da mai tsaron rayukanmu.’ (1 Bitrus 2:25) Amma duk kuskuren da wani dattijo ya yi ba zai dace mu yi tawaye ba. Jehobah ba ya taimakon masu rashin biyayya da masu tawaye.—Litafin Lissafi 12:1, 2, 9-11.

Jehobah Yana Yi wa Waɗanda Suka ba da Haɗin kai da Son Rai Albarka

17. Ta yaya ya kamata mu ɗauki masu kula?

17 Jehobah Allah ya san cewa mutanen da ya naɗa a matsayin masu kula ajizai ne. Yana amfani da su, kuma ta wurin ruhunsa, yana kula da mutanensa na duniya. Gaskiya ne cewa ikon da mu da dattawa muke da shi ‘mafificin ikon na Allah ne, ba namu ba.’ (2 Korinthiyawa 4:7) Saboda haka ya kamata mu yi godiya ga Jehobah saboda abin da ya yi ta wurin masu kula masu aminci, kuma mu ba su haɗin kai.

18. Idan muka bi umurnin masu kula, umurnin wa muke bi?

18 Masu kula suna iya ƙoƙarinsu don su yi rayuwa daidai da kwatancin da Jehobah ya yi game da makiyayi da aka naɗa bisa garken a zamani na ƙarshe, kamar yadda Irmiya 3:15 ta ce: “In ba ku makiyaya bisa ga nufin zuciyata, waɗanda za su yi kiwonku da ilimi da fahimi.” Hakika, dattawa waɗanda suke tsakaninmu suna aiki mai kyau na koyarwa da kuma tsare tumakin Jehobah. Bari mu ci gaba da nuna godiya da aikin da suke yi ta wurin ba su haɗin kai, mu yi musu biyayya kuma mu bi umurninsu. Ta haka, za mu nuna godiyarmu ga Makiyayinmu na samaniya, Jehobah Allah da Yesu Kristi.

Domin Maimaitawa

• Ta yaya ne Jehobah da Yesu suka nuna cewa su Makiyaya ne masu ƙauna?

• Ƙari ga yin biyayya me ya sa ya kamata mu bi umurni?

• Ta waɗanne hanyoyi ne na zahiri za mu nuna cewa muna bin umurni?

[Hoto a shafi na 27]

Dattawa Kirista suna yin biyayya ga shugabancin Kristi

[Hotuna a shafi na 29]

Akwai hanyoyi da yawa da za mu nuna cewa muna biyayya ga makiyayan da Jehobah ya naɗa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba