Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 5/1 pp. 26-30
  • Matasa, Ku Biɗi Makasudan Da Za Su Daraja Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Matasa, Ku Biɗi Makasudan Da Za Su Daraja Allah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Asalin Timoti
  • Ka Amfana Daga Rinjaya Mai Kyau
  • Ka Yi Nazarin “Littattafai Masu-Tsarki”
  • “Ka Yi Yaƙin Kirki”
  • Ka Mai da Hankali ga Makasudai na Ruhaniya
  • Albarka a Yanzu da Kuma Nan Gaba
  • “Dana Cikin Ubangiji, Kaunatacce, Mai-Aminci.”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Timoti Ya Taimaki Mutane
    Ku Koyar da Yaranku
  • Timothawus Yana Shirye Ya Yi Hidima
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Bulus da Timotawus
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 5/1 pp. 26-30

Matasa, Ku Biɗi Makasudan Da Za Su Daraja Allah

“Ka wasa kanka zuwa ibada.”—1 TIMOTHAWUS 4:7.

1, 2. (a) Me ya sa Bulus ya yaba wa Timoti? (b) Ta yaya ne matasa a yau suke ‘wasa kansu zuwa ibada’?

“GAMA ba ni da kowa wanda hankalinsa ya yi daidai da nasa ba, wanda za ya yi tattalin zamanku da gaskiya. . . . Kamar da ɗa ya ke bauta ma uba, haka ya yi bauta tare da ni zuwa yaɗuwar bishara.” (Filibbiyawa 2:20, 22) Manzo Bulus ya haɗa wannan yabo mai kyau a cikin wasiƙarsa ga Kiristoci na ƙarni na farko da suke Fillibi. Wanene ya yaba wa haka? Timoti ne matashi, abokin tafiyarsa. Babu shakka, wannan ƙauna da amincewa da Bulus ya nuna ya faranta zuciyar Timoti!

2 Kamar Timoti, matasa masu tsoron Allah sun zama masu tamani a cikin mutanen Jehobah. (Zabura 110:3) A yau, ƙungiyar Allah tana da matasa masu yawa da suke hidimar majagaba, masu wa’azi a ƙasashen waje, masu yin gini, da kuma Bethelites. Waɗanda kuma za a yaba wa sosai su ne, waɗanda suke saka hannu sosai a ayyukan ikilisiya yayin da suke kula da wasu hakkoki. Irin waɗannan matasan suna samun gamsuwa mai kyau da ke fitowa daga biɗar makasudan da suke daraja Ubanmu na sama, Jehobah. Hakika suna ‘wasa kansu zuwa ibada.’—1 Timothawus 4:7, 8.

3. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Matasa, kuna ƙoƙarin cim ma wasu makasudai na ruhaniya kuwa? A ina ne za ku iya samun taimako da ƙarfafa na yin haka? Ta yaya ne za ku iya tsayayya wa matsin wannan duniyar? Waɗanne albarka ne za ka samu idan ka biɗi makasudan da suke daraja Allah? Bari mu amsa waɗannan tambayoyin ta wajen tattauna rayuwa da kuma aikin Timoti.

Asalin Timoti

4. Ka ɗan bayyana rayuwar Timoti na Kirista.

4 Timoti ya girma ne a Listira, wani ƙaramin gari a lardin Roma da ke Galatiya. Wataƙila ya zama Kirista ne sa’ad da yake cikin shekarunsa na goma sha, a lokacin da Bulus ya yi wa’azi a Listira wajen shekara ta 47 A.Z. Nan da nan Timoti ya yi suna mai kyau tsakanin ’yan’uwa Kiristoci da ke birnin. Bayan shekara biyu, Bulus ya koma Listira kuma da ya ji irin ci gaban da Timoti ya yi, Bulus ya zaɓe shi ya zama abokin tafiyarsa zuwa wa’azi a ƙasashen waje. (Ayukan Manzanni 14:5-20; 16:1-3) Yayin da Timoti ya manyanta, an ba shi hakkoki masu yawa, har da aiki mai muhimmanci na ƙarfafa ’yan’uwa. Timoti ya riga ya zama dattijo a Afisa sa’ad da Bulus ya yi masa wasiƙa daga kurkuku a Roma a wajen shekara ta 65 A.Z.

5. In ji 2 Timothawus 3:14, 15, waɗanne dalilai biyu ne suka sa Timoti ya biɗi makasudai na ruhaniya?

5 Timoti ya zaɓi ya biɗi makasudai na ruhaniya. Amma me ya sa ya yi haka? A cikin wasiƙarsa ta biyu ga Timoti, Bulus ya ambata dalilai biyu. Ya rubuta: ‘Ka lizima kai a cikin al’amuran da ka koyo, waɗanda ka tabbata da su kuma, ka sani wurin ko waɗannene ka koye su; tun kana jariri fa ka san littattafai masu-tsarki.’ (2 Timothawus 3:14, 15) Bari mu bincika yadda wasu Kiristoci suka rinjayi zaɓen da Timoti ya yi.

Ka Amfana Daga Rinjaya Mai Kyau

6. Wane irin koyarwa ne Timoti ya samu, kuma menene ya yi?

6 An haifi Timoti ne a cikin iyalin da addininsu ya bambanta. Babansa Baheleni ne, kuma mahaifiyarsa, Afiniki, da kuma kakarsa, Loyis Yahudawa ne. (Ayukan Manzanni 16:1) Tun yana ƙarami, Afiniki da Loyis suka koya wa Timoti gaskiya daga Nassosin Ibrananci. Bayan sun zama Kirista, babu shakka, ba su ɓata lokaci ba wajen rinjayarsa ya amince da koyarwar Kirista. Hakika, Timoti ya amfana sosai daga wannan koyarwar. Bulus ya ce: “An tuna mini da bangaskiya marar-riya wadda ke cikinka; bangaskiya wadda ta fara zama cikin kakarka Lois, da uwarka Afniki; har a cikinka kuma, na kawarda shakka.”—2 Timothawus 1:5.

7. Wane albarka ne matasa da yawa suke mora, kuma ta yaya hakan zai amfane su?

7 A yau, matasa masu yawa suna amfana sosai domin suna da iyaye da kakanni masu tsoron Allah kamar Loyis da Afiniki, waɗanda suka san muhimmancin makasudai na ruhaniya. Alal misali, Samira ta tuna irin doguwar hirar da take yi da iyayenta sa’ad da take ƙarama. “Mamata da Babana sun koyar da ni in kasance da ra’ayin Jehobah game da abubuwa kuma in mai da aikin wa’azi abu na farko a rayuwata,” in ji ta. “A kowane lokaci suna ƙarfafa ni in biɗi hidima na cikakken lokaci.” Samira ta bi shawarar da iyayenta suka ba ta, kuma yanzu tana more gatar yin hidima a Bethel a ƙasarsu. Idan iyayenka suka ba ka shawarar biɗar makasudai na ruhaniya, ka yi tunani sosai a kan shawarar da suka ba ka. Suna son ka sami farin ciki ne a rayuwa.—Misalai 1:5.

8. Ta yaya ne Timoti ya amfana daga tarayya mai kyau na Kirista?

8 Yana da muhimmanci ka biɗi abokan da za su ƙarfafa ka a cikin ’yan’uwa Kirista. Timoti ya zama sananne ga Kiristoci dattawa da ke ikilisiyarsu da kuma waɗanda ke Ikoniya, wadda take da nisan kusan kilomita 30. (Ayukan Manzanni 16:1, 2) Ya zama abokin Bulus na kud da kud, mutum mai ƙwazo. (Filibbiyawa 3:14) Wasiƙun Bulus sun nuna cewa Timoti yana bin shawara kuma yana shirye ya bi misalan masu bangaskiya. (1 Korinthiyawa 4:17; 1 Timothawus 4:6, 12-16) Bulus ya ce: “Ka bi koyarwata, da tasarrufina, da nufina, da bangaskiyata, da tsawon jimrewata, da ƙaunata, da haƙurina.” (2 Timothawus 3:10) Hakika, Timoti ya bi misalin Bulus sawu da kafa. Hakazalika, idan ka kusanci mutane masu ruhaniya a cikin ikilisiya, za su taimaka maka ka kafa makasudai masu kyau na ruhaniya.—2 Timothawus 2:20-22.

Ka Yi Nazarin “Littattafai Masu-Tsarki”

9. Ban da zaɓan abokan kirki, menene kuma kake bukatar ka yi don ka ‘wasa kanka zuwa ibada’?

9 Za a iya cim ma makasudai na ruhaniya ne kawai ta wajen yin tarayya mai kyau? A’a. Kamar Timoti, kana bukatar ka bincika “littattafai masu-tsarki” sosai. Wataƙila ba ka son yin karatu, amma ka tuna cewa Timoti ya ‘wasa kansa zuwa ibada.’ Masu wasan guje-guje suna horar da kansu har tsawon watanni don su cim ma makasudinsu. Hakazalika, cim ma makasudai na ruhaniya na bukatar sadaukarwa da ƙoƙari sosai. (1 Timothawus 4:7, 8, 10) Amma kana iya cewa, ‘Ta yaya ne yin nazarin Littafi Mai Tsarki zai taimaka mini in cim ma makasudai na?’ Bari mu tattauna hanyoyi uku.

10, 11. Me ya sa Nassosi za su motsa ka ka cim ma makasudai na ruhaniya? Ka ba da misali.

10 Na farko, Nassosi za su motsa ka. Nassosi sun bayyana halaye masu kyau na Ubanmu na samaniya, ƙauna mafi girma da ya nuna mana, da kuma farin ciki na dindindin da ke jiran bayinsa masu aminci. (Amos 3:7; Yohanna 3:16; Romawa 15:4) Yayin da saninka na Jehobah ke ƙaruwa, haka ma ƙaunarsa da kake yi da kuma muradinka na keɓe masa kanka za su ci gaba da ƙaruwa.

11 Yawancin matasa sun ce yin nazarin Littafi Mai Tsarki kullum shi ne ya taimaka musu su mai da gaskiya tasu. Alal misali, iyayen Adele Kiristoci ne, amma ba ta taɓa kafa makasudi na ruhaniya ba. “Iyayena suna kai ni Majami’ar Mulki,” in ji ta, “amma ba na nazari ko kuwa in saurari abin da ake faɗa a taro.” Bayan da ’yar’uwarta ta yi baftisma, sai Adele ta soma ɗaukan gaskiya da muhimmanci. “Na yi shawarar zan karanta Littafi Mai Tsarki gabaki ɗaya. Ina karanta kaɗan sai in rubuta kalami a kan abin da na karanta. Abubuwan da na rubuta suna nan har yanzu. Na karance Littafi Mai Tsarki a cikin shekara ɗaya.” Saboda haka, Adele ta keɓe rayuwarta ga Jehobah. Duk da cewa ta naƙasa, a yanzu majagaba ce ta cikakken lokaci.

12, 13. (a) Waɗanne canje-canje ne Littafi Mai Tsarki zai taimaka wa matashi ya yi, kuma ta yaya? (b) Ka ba da misalin hikima mai amfani da ke cikin Kalmar Allah.

12 Na biyu, Littafi Mai Tsarki zai taimaka maka ka yi canje-canjen da kake bukata a halayenka. Bulus ya gaya wa Timoti cewa “littattafai masu-tsarki” “mai-amfani ne ga koyarwa, ga tsautawa, ga kwaɓewa, ga horo kuma da ke cikin adalci: domin mutumin Allah shi zama kamili, shiryayye sarai domin kowane managarcin aiki.” (2 Timothawus 3:16, 17) Ta wajen yin bimbini a kai a kai a kan batutuwan da suka shafi Kalmar Allah da kuma yin amfani da mizanan Littafi Mai Tsarki, hakan zai sa ruhu mai tsarki ya gyara halinka. Za ka kasance da halaye masu muhimmanci, kamar tawali’u, naci, ƙwazo, da kuma ƙauna ta gaskiya ga ’yan’uwa Kiristoci. (1 Timothawus 4:15) Timoti yana da waɗannan halayen, shi ya sa ya zama mutum mai tamani ga Bulus da kuma ikilisiyar da yake hidima.—Filibbiyawa 2:20-22.

13 Na uku, Kalmar Allah tana ƙunshe da hikima mai amfani. (Zabura 1:1-3; 19:7; 2 Timothawus 2:7; 3:15) Za ta taimaka maka ka zaɓi abokan kirki, nishaɗi mai kyau, da kuma magance matsaloli masu yawa. (Farawa 34:1, 2; Zabura 119:37; 1 Korinthiyawa 7:36) Yanke shawarwari masu kyau na da muhimmanci yanzu idan kana son ka cim ma makasudanka na ruhaniya.

“Ka Yi Yaƙin Kirki”

14. Me ya sa biɗan makasudai na ruhaniya ba abu ba ne mai sauƙi?

14 Saka makasudai masu daraja Jehobah abu na farko a rayuwa shi ne zaɓi mafi kyau, amma hakan ba shi da sauƙi. Alal misali, idan za ka zaɓi aikin da za ka yi, kana iya fuskantar matsi mai girma daga ’yan’uwanka, abokanka, da kuma malaman makaranta da suke ƙaunarka waɗanda suka gaskata cewa ƙarin ilimi da kuma aiki mai kyau su ne hanyoyin yin nasara da farin ciki. (Romawa 12:2) Kamar Timoti, kana bukatar ka “yi yaƙin kirki na imani” don “ka ribce rai na har abada” da Jehobah zai ba ka.—1 Timothawus 6:12; 2 Timothawus 3:12.

15. Wane irin hamayya ne ƙila Timoti ya fuskanta?

15 Gwaji yana iya zama mai tsanani musamman sa’ad da ’yan’uwanka marasa bi suka ƙi amincewa da zaɓinka. Wataƙila, Timoti ya fuskanci irin wannan matsin. In ji wani littafi, wataƙila iyalin Timoti “suna cikin mutane masu ilimi da kuma arziki.” Ƙila ubansa ya so ya je ya ƙaro ilimi kuma ya ci gaba da kula da kasuwancin iyalin.a Ka yi tunanin abin da baban Timoti ya yi sa’ad da ya ji cewa Timoti ya fi son ya bi Bulus zuwa aikin wa’azi a ƙasashen waje!

16. Ta yaya ne wani matashi ya bi da hamayya daga iyaye?

16 Kiristoci matasa a yau suna fuskantar irin waɗannan matsalolin. Matthew, wanda yake hidima a ofishin reshe na Shaidun Jehobah, ya ce: “A lokacin da na fara hidima na majagaba, hakan ya ɓata wa mahaifi na rai. Yana ganin na ‘ɓata’ ilimin da nike da shi ta wajen yin aikin goge-goge don na taimaka wa kaina a hidima. Yana zolaya na, kuma yana tuna mini irin kuɗin da zan samu idan na nemi aiki na cikakken lokaci.” Ta yaya Matthew ya bi da wannan hamayyar? “Na ci gaba da karanta Littafi Mai Tsarki sosai kuma ina yin addu’a kowane lokaci, musamman lokacin da na ga cewa zan yi fushi.” An albarkaci ƙudurin Matthew. Bayan wani lokaci, dangantakarsa da mahaifinsa ya kyautata. Matthew kuma ya kusanci Jehobah. “Jehobah ya yi mini tanadin abin da nike so, ya ƙarfafa ni, kuma ya kāre ni daga yin mummunar shawara,” in ji Matthew. “Da ban shaida duka waɗannan abubuwan ba da a ce ban biɗi makasudai na ruhaniya ba.”

Ka Mai da Hankali ga Makasudai na Ruhaniya

17. Ta yaya ne wasu cikin rashin sani za su iya sa waɗanda suke shirin shiga hidima na cikakken lokaci sanyin gwiwa? (Matta 16:22)

17 ’Yan’uwa masu bi ma suna iya hana ka biɗar makasudai na ruhaniya cikin rashin sani. Wasu suna iya tambayarka ‘Me ya sa za ka zama majagaba?’ Kana iya rayuwarka kuma ka yi aikin wa’azi. Ka nemi aiki mai kyau don ka zama mai kuɗi.’ Kana iya tunanin cewa wannan shawara ce mai kyau, amma za ka wasa kanka zuwa ibada idan ka bi wannan shawarar?

18, 19. (a) Ta yaya za ka iya mai da hankali ga makasudai na ruhaniya? (b) Ka bayyana sadaukarwa da kake yi a matsayinka na matashi domin Mulki.

18 Wasu Kiristoci a zamanin Timoti sun kasance da irin wannan ra’ayin. (1 Timothawus 6:17) Don ya taimaka wa Timoti ya mai da hankali ga makasudai na ruhaniya, Bulus ya ƙarfafa shi yana cewa: “Mayaƙin da ke a kan sha’anin yaƙi ba za ya nannaɗe kansa da al’amuran wannan rai ba; gama yana so ya gami wanda ya rubuta shi mayaƙi.” (2 Timothawus 2:4) Sojan da ke bakin aiki ba zai yarda abubuwan duniya da fararen hula suke biɗa su ɗauke masa hankali ba. Rayuwarsa da ta wasu ta dangana ne a kan kasancewarsa a shirye ya bi umurnin shugabansa. Da yake kai sojan Kristi ne, dole ne ka guje wa nannaɗe kanka da neman abin duniya marar amfani wadda za ta hana ka cim ma hidimarka ta ceton rai.—Matta 6:24; 1 Timothawus 4:16; 2 Timothawus 4:2, 5.

19 Maimakon ka mai da rayuwar jin daɗi makasudinka, ka biɗi halin saɗaukar da kai. “Ka yi shirin shan wuya, a matsayin sojan Kristi Yesu.” (2 Timothawus 2:3, The English Bible in Basic English) Sa’ad da yake tare da Bulus, Timoti ya koyi asirin wadatar zuciya har ma a lokacin wahala mai tsanani. (Filibbiyawa 4:11, 12; 1 Timothawus 6:6-8) Kai ma kana iya yin haka. Za ka so ka yi sadaukarwa domin Mulki?

Albarka a Yanzu da Kuma Nan Gaba

20, 21. (a) Ka kwatanta wasu albarkatai da ake samu idan aka biɗi makasudai na ruhaniya. (b) Menene ka ƙudurta cewa za ka yi?

20 Timoti ya yi wajen shekaru 15 yana aiki tare da Bulus. Timoti ya ga yadda aka kafa sababbin ikilisiyoyi sa’ad da bishara ta yaɗu zuwa duka arewacin yankin Bahar Rum. Rayuwarsa ta cika da farin ciki da kuma gamsuwa waɗanda suka fi duk wani abin da zai samu da a ce ya zaɓi rayuwa “ta yau da kullum.” (2 Korinthiyawa 11:26, 27) Idan ka biɗi makasudai na ruhaniya, kai ma za ka sami albarka ta ruhaniya masu tamani. Za ka kusanci Jehobah kuma ’yan’uwa Kiristoci za su ƙaunace ka kuma su daraja ka. Maimakon baƙin ciki da takaici da ke tattare da biɗar abin duniya, za ka more farin cikin da ake samu don rashin son kai. Mafi muhimmanci ma, za ka sami “rai wanda shi ke hakikanin rai,” wato, rai na dindindin a aljanna a duniya.—1 Timothawus 6:9, 10, 17-19; Ayukan Manzanni 20:35.

21 Idan ba ka yi haka ba, muna ƙarfafa ka ka soma wasa kanka zuwa ibada. Ka kusanci ’yan’uwa a cikin ikilisiya da za su taimaka maka ka cim ma makasudanka na ruhaniya, kuma ka nemi ja-gorancinsu. Ka ɗauki yin nazarin Kalmar Allah kowace rana da muhimmanci. Ka ƙudurta yin tsayayya da halin neman abin duniya. Kuma ka dinga tuna cewa Allah “wanda ke ba mu kome a yalwace mu ji daɗinsu” ya yi maka alkawarin albarka a yanzu da kuma nan gaba idan ka biɗi makasudan da suke daraja shi.—1 Timothawus 6:17.

[Hasiya]

a Helenawa suna ɗaukan ilimi da muhimmanci. Plutarch wanda tsaran Timoti ne, ya ce: “Samun ilimi shi ne tushen dukan wani abin kirki. . . . Shi ke sa mutane su kasance da ɗabi’a mai kyau da kuma farin ciki. . . . Dukan sauran abubuwan ba su da muhimmanci.”—Moralia, I, “The Education of Children.”

Ka Tuna?

• A ina ne matasa za su iya samun taimako don su biɗi makasudai na ruhaniya?

• Me ya sa yin nazarin Littafi Mai Tsarki yake da muhimmanci?

• Ta yaya ne matasa za su iya tsayayya wa tasirin neman abin duniya?

• Waɗanne albarka ne ake samu idan aka biɗi makasudai na ruhaniya?

[Hoto a shafi na 26]

Timoti ya biɗi makasudai masu kyau

[Hotuna a shafi na 27]

Wane rinjaya ne na kirki ya taimaki Timoti?

[Hotuna a shafi na 28]

Kana biɗar makasudai na ruhaniya kuwa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba