Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 8/1 pp. 24-28
  • Kai ‘Mawadaci Ne Ga Allah’?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kai ‘Mawadaci Ne Ga Allah’?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Wani Mutumin da ke da Matsala
  • Me Ya Sa Ya Zama “Wawa”?
  • Zama Mawadaci ga Allah
  • Zama Mawadaci a Gaban Allah
  • Mene ne Yake Da Muhimmancin Gaske?
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • Su Waye Ne Mai Arzikin Nan da Liꞌazaru da Yesu Ya Ambata?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 8/1 pp. 24-28

Kai ‘Mawadaci Ne Ga Allah’?

“Hakanan ne mai-ajiye wa kansa dukiya, shi kuwa ba mawadaci ba ne ga Allah.”—LUKA 12:21.

1, 2. (a) Mutane suna shirye su yi sadaukarwa a kan menene? (b) Wane ƙalubale da haɗari ne Kiristoci suke fuskanta?

TUN da daɗewa mutane a ƙasashe masu yawa, suna aiki tuƙuru don su zama masu arziki. Alal misali, filin zinariya da aka gano a ƙarni na 19 a Australiya, Afirka ta Kudu, da kuma Amirka ya jawo hankalin mutane daga ƙasashe masu nisa da suke shirye su bar gida da waɗanda suke ƙauna don su nemi dukiya a wurin da ba su sani ba, wani lokaci a ƙasashe da ba sa karɓan baƙi. Hakika, mutane da yawa suna shirye su sa ransu cikin haɗari kuma su yi sadaukarwa mai girma domin su sami dukiyoyin da suke so.

2 Ko da yake yawancin mutane a yau ba sa zuwa su haƙa ƙasa don su nemi zinari, amma suna aiki tuƙuru don su biya bukatun rayuwa. Yin hakan a wannan zamanin yana da wuya, kuma yana ɗaukan lokaci. Yana da sauƙi mutum ya damu da neman abinci, sa tufafi, da wurin kwanciya kuma ya yi watsi ko ya manta da abubuwan da suka fi muhimmanci. (Romawa 14:17) Yesu ya ba da kwatanci, ko almara da ta kwatanta wannan hali na ’yan adam. Almarar tana cikin Luka 12:16-21.

3. Ka ɗan ba da labarin kwatancin Yesu da ke rubuce a Luka 12:16-21.

3 Yesu ya ba da wannan kwatancin a lokacin da ya yi magana a kan bukatar tsare kanmu daga yin ƙyashi, da muka bincika dalla-dalla a talifin da ya shige. Bayan ya yi gargaɗi game da yin ƙyashi, Yesu ya yi magana game da wani mawadaci da bai gamsu da rumbunansa da ke cike da kaya masu kyau ba amma ya rushe su kuma ya gina manya domin ya ƙara tara abubuwa masu kyau. A lokacin da yake ganin cewa yana shirye ya more rayuwarsa, Allah ya gaya masa cewa zai mutu, kuma wani ne zai ci dukan abubuwa masu kyau da mutumin ya tara. Sai Yesu ya kammala da waɗannan kalmomin: “Hakanan ne mai-ajiye wa kansa dukiya, shi kuwa ba mawadaci ba ne ga Allah.” (Luka 12:21) Wane darassi ne za mu iya koya daga wannan almarar? Ta yaya za mu yi amfani da wannan darasin a rayuwarmu?

Wani Mutumin da ke da Matsala

4. Wane irin mutumi ne za mu iya cewa an kwatanta a cikin almarar Yesu?

4 Mutane da yawa suna sane da kwatancin da Yesu ya ba da. Mun lura cewa Yesu ya gabatar da labarin ta wajen cewa: “Ƙasar wani mawadaci ta bada amfani dayawa.” Yesu bai ce mutumin ya samu dukiyarsa ta hanyar cuta ko kuma a hanyar da ba ta dace ba. Wato, ba a ce mutumin mugu ba ne. Hakika, daga abin da Yesu ya ce, ya dace a ce mutumin cikin almarar ya yi aiki sosai. Mun fahimci cewa mutumi ne da yake shiri kuma yake tara abubuwa don nan gaba, wataƙila don jin daɗin iyalinsa. Da haka, daga ra’ayin duniya za a iya cewa shi mutum ne mai aiki sosai wanda ya ɗauki hakkinsa da muhimmanci.

5. Wace matsala ce mutumin da ke cikin almarar Yesu ya fuskanta?

5 Ko yaya dai, Yesu ya kira mutumin cikin almarar mawadaci, wato wanda yake da dukiyoyi masu yawa. Amma, yadda Yesu ya kwatanta mawadacin ya nuna cewa yana da matsala. Ya sami amfanin gona fiye da yadda yake zato kuma ba zai iya kula da su ba. Da me ya kamata ya yi?

6. Wane zaɓi ne bayin Allah da yawa suke fuskanta a yau?

6 Bayin Jehobah da yawa a yau suna fuskantar yanayi da ya yi kama da na wannan mawadacin. Kiristoci na gaskiya suna ƙoƙarin faɗin gaskiya, kuma suna aiki da kyau. (Kolossiyawa 3:22, 23) Ko suna yi wa wani aiki ko a nasu kasuwanci, suna yin nasara har ma su zama ƙwararru. Suna fuskantar tsai da shawara idan aka ba su ƙarin matsayi ko sa’ad da suka sami wata dama. Za su karɓi matsayin ne kuma su sami ƙarin kuɗi? Hakanan ma, matasa Shaidu da yawa suna yin ƙoƙari sosai a makaranta. Saboda haka, ana iya ba su lada ko kuma sukolashif don su ƙaro ilimi a babban makarantu. Za su bi tafarkin da yawancin mutane suke bi ne kuma su karɓi abin da aka ba su?

7. Ta yaya ne mutumin da ke cikin almarar Yesu ya magance matsalarsa?

7 A kwatancin Yesu, menene mawadacin ya yi sa’ad da ya sami amfanin gona da yawa har ya zama cewa ba shi da inda zai ajiye abubuwan da ya girbe? Ya tsai da shawara ya rushe rumbunansa kuma ya gina manya don ya tara hatsi da wadatarsa duka. Wannan shirin ya ba shi kwanciyar hankali da gamsuwa da ya sa ya yi tunani: “In ce ma raina kuma, Ya raina, kana da wadata mai-yawa a ajiye da za ta kai shekaru dayawa; yi hutunka, ka ci, ka sha, ka yi annishuwa.”—Luka 12:19.

Me Ya Sa Ya Zama “Wawa”?

8. Wane abu mai muhimmanci ne mutumin da ke cikin almarar Yesu ya yi watsi da shi?

8 Amma, kamar yadda Yesu ya faɗa, shirin da mawadacin ya yi bai kawo masa kwanciyar rai ba. Ko da yake kamar shirin yana da kyau, bai haɗa da wani abu mai muhimmanci ba, wato, nufin Allah. Mutumin ya yi tunanin kansa kaɗai, yadda zai shaƙata, ya ci, ya sha, kuma ya ji daɗin ransa. Ya yi tunanin cewa tun da yana da “wadata mai-yawa” zai yi “shekaru dayawa.” Amma, abin baƙin ciki, abubuwa ba su faru yadda yake so ba. Kamar yadda Yesu ya ce da farko, “ba da yalwar dukiya da mutum ya ke da ita ransa ke tsayawa ba.” (Luka 12:15) A wannan daren, duk aikin da mutumin ya yi ya ƙare farat ɗaya, domin Allah ya ce masa: “Kai wawa, yau da daren nan ana biɗan ranka a gareka; abin da ka shirya fa, ga wa su ke?”—Luka 12:20.

9. Me ya sa aka kira mutumin cikin almarar wawa?

9 A nan mun kai darasi mai muhimmanci na kwatancin Yesu. Allah ya kira mutumin wawa. Ƙamus nan Exegetical Dictionary of the New Testament ya bayyana cewa irin wannan kalmar Helenanci da aka yi amfani da ita “tana nufin rashin fahimi.” Ƙamus ɗin ya faɗi cewa a wannan almarar, an kwatanta Allah kamar yana amfani da wannan kalmar ya fallasa “rashin amfanin shirin da mawadata suke yi don nan gaba.” Wannan furcin ba ya maganar wanda ba shi da basira, amma “wanda ya ƙi dogara ga Allah.” Kwatancin Yesu game da mawadacin ya tuna mana abin da ya gaya wa Kiristocin da ke ikilisiyar Laodicea na Asiya Ƙarama a ƙarni na farko: “Domin kana cewa, Na wadata, na sami dukiya, ban bukaci kome ba; ba ka sani ba malalacin nan ne kai, abin tausayi, matalauci, makaho, tsirara.”—Ru’ya ta Yohanna 3:17.

10. Me ya sa tara “wadata mai-yawa” ba tabbacin samun “shekaru dayawa” ba ne?

10 Ya kamata mu yi bimbini a kan wannan darassin. Za mu iya zama kamar mutumin cikin almarar, mu yi aiki tuƙuru don mu tabbata cewa muna da “wadata mai-yawa” duk da haka mu kasa yin abin da ya dace don mu sami begen yin “shekaru dayawa”? (Yohanna 3:16; 17:3) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wadata ba ta anfana komi a ranar hasala” kuma “wanda ya dogara ga wadatarsa za ya fāɗi.” (Misalai 11:4, 28) Saboda haka, Yesu ya daɗa gargaɗi na ƙarshe a wannan almarar: “Hakanan ne mai-ajiye wa kansa dukiya, shi kuwa ba mawadaci ba ne ga Allah.”—Luka 12:21.

11. Me ya sa abin banza ne mutum ya sa bege da samun kwanciyar rai a dukiya?

11 Sa’ad da Yesu ya ce “hakanan ne,” yana nuna cewa abin da ya faru da mawadacin cikin kwatancin zai faru da waɗanda suka kafa rayuwarsu, wato begensu da kwanciyar ransu a kan abin duniya kawai. Laifin ba a kan ‘ajiye wa kanmu dukiya’ ba ne amma a kan rashin zama “mawadaci . . . ga Allah.” Almajiri Yaƙub ya yi irin wannan gargaɗin sa’ad da ya rubuta: “Tafi, ku da ku ke cewa, Ko yau ko gobe za mu tafi cikin wannan birni, mu yi shekara a wurin, mu yi ciniki, mu ci riba: ku kuwa ba ku san abin da za ya faru gobe ba.” Me ya kamata su yi? “Da ma kun ce, Idan Ubangiji ya yarda, za mu yi rai, mu yi abu kaza da kaza.” (Yaƙub 4:13-15) Komi yawan kuɗin mutum da arzikinsa, duk za su zama banza idan ba mawadaci ba ne a gun Allah. To, menene ake nufi da mutum ya zama mawadaci a gun Allah?

Zama Mawadaci ga Allah

12. Yin menene zai sa mu zama mawadaci ga Allah?

12 A furcin Yesu, an bambanta zama mawadaci ga Allah da mutum ya tara wa kansa dukiya, ko kuma ya zama mai arziki. Da haka, Yesu yana cewa ne bai kamata tara dukiya ko kuma jin daɗin abin da muka tara ya zama ainihin damuwarmu a rayuwa ba. Maimakon haka, ya kamata mu yi amfani da dukiyarmu mu kyautata ko kuma mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah. Yin hakan zai sa mu zama mawadaci ga Allah. Me ya sa? Domin zai sa mu sami albarka da yawa daga wajensa. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana: “Albarkar Ubangiji ta kan kawo wadata, ba ya kan haɗa ta da baƙinciki ba.”—Misalai 10:22.

13. Ta yaya albarkar Jehobah take “kawo wadata”?

13 Sa’ad da Jehobah ya albarkace mutanensa, yana ba su abin da ya fi kyau a kowane lokaci. (Yaƙub 1:17) Alal misali, sa’ad da Jehobah ya ba Isra’ilawa inda za su zauna, ya ba su ƙasa “mai-zuba da madara da zuma.” Ko da yake an kwatanta ƙasar Masar kamar haka, ƙasar da Jehobah ya ba Isra’ilawa dabam take a hanya ta musamman. Musa ya gaya wa Isra’ilawa cewa ƙasa ce ‘wadda Ubangiji Allahnsu ya ke lura da ita.’ Wato, za su yi nasara domin Jehobah zai kula da su. Muddin Isra’ilawa suka kasance da aminci ga Jehobah, ya albarkace su sosai kuma sun more rayuwa da ta fi ta dukan al’ummai da suka kewaye su. Hakika, albarkar Jehobah “ta kan kawo wadata”!—Litafin Lissafi 16:13; Kubawar Shari’a 4:5-8; 11:8-15.

14. Menene mawadata a gun Allah suke morewa?

14 Ana iya fassara furci zama ‘mawadaci ga Allah’ zuwa ‘mai tanadi a gun Allah.’ (LMT) Masu arziki suna damuwa da yadda za su bayyana a gaban mutane. Sau da yawa ana ganin wannan ta salon rayuwarsu. Suna son su burge mutane da abin da Littafi Mai Tsarki ya kira “darajar rai ta wofi.” (1 Yohanna 2:16) Akasin haka, mawadata a gun Allah suna more amincewar Allah, tagomashinsa, da alherinsa masu yawa kuma suna da dangantaka na kud da kud da shi. Kasancewa a irin wannan yanayi mai tamani na sa su farin ciki da kwanciyar rai, fiye da wadda kowace irin dukiya za ta ba su. (Ishaya 40:11) Tambayar da ta rage ita ce, Menene dole mu yi domin mu zama mawadata a gaban Allah?

Zama Mawadaci a Gaban Allah

15. Menene dole mu yi don mu zama mawadata a gaban Allah?

15 A kwatancin Yesu, mutumin ya yi shiri kuma ya yi aiki tuƙuru don ya azurtar da kansa, kuma an kira shi wawa. Saboda haka, don mu zama mawadata a gun Allah dole ne mu yi aiki tuƙuru kuma mu sa hannu a cikin ayyuka masu amfani da daraja a gaban Allah. Wannan yana cikin umurnin da Yesu ya ba da: “Ku tafi fa, ku almajirtadda dukan al’ummai.” (Matta 28:19) Za a iya kamanta yin amfani da lokacinmu, kuzarinmu, da iyawarmu, don wa’azin Mulki da aikin almajirantarwa da zuba jari ba don kyautata rayuwarmu ba. Waɗanda suka yi hakan sun sami albarka mai yawa a ruhaniya kamar yadda labarai na gaba suka nuna.—Misalai 19:17.

16, 17. Wane labari za ka ba da don ka nuna hanyar rayuwa da ke sa mutum ya zama mawadaci a gaban Allah?

16 Ka yi la’akari da labarin wani Kirista a wata ƙasar Asiya. Yana gyara na’aurar kwamfuta kuma aikin na ba shi kuɗi. Amma, aikinsa na ɗaukan dukan lokacinsa kuma hakan ya sa ya ji ba shi da ruhaniya. A ƙarshe, maimakon ya ci gaba da aikinsa, ya yi murabus kuma ya soma yin askirim yana sayarwa a kan titi don ya samu isashen lokaci ya kula da bukatunsa na ruhaniya da hakkinsa. Abokan aikinsa na dā suka yi masa ba’a, amma menene sakamakon? Ya ce: “Na fi samun kuɗi yanzu fiye da lokacin da nake gyaran na’aurar kwamfuta. A yanzu farin cikina ya ƙaru domin ba ni da matsi da damuwa da nake da shi a aikina na dā. Kuma mafi muhimmanci, na fi kusa da Jehobah yanzu.” Wannan canjin ya taimaki wannan Kirista ya shiga hidima ta cikakken lokaci, kuma yanzu yana hidima a ofishin reshe na Shaidun Jehobah a ƙasarsu. Hakika, albarkar Jehobah tana kawo wadata.

17 Wani misali kuma na wata mata ce da ta yi girma a iyalin da ake ɗaukan ilimi da muhimmanci ƙwarai. Ta je jami’u a Faransa, Mexico, da Swizerland kuma tana da damar samun aikin da zai sa ta sami kuɗi sosai. Ta ce, “na yi nasara; ana daraja ni kuma ana ba ni zarafi na musamman, amma a zuciyata, ba ni da gamsuwa.” Sai ta koya game da Jehobah. Ta ce: “Da na ci gaba a ruhaniya, sha’awar faranta wa Jehobah rai da kuma son na mayar masa kaɗan cikin abubuwa da ya ba ni ya taimake ni na ga tafarkin da zan bi wato hidima ta cikakken lokaci.” Ta bar aikinta kuma ba da daɗewa ba ta yi baftisma. Shekara 20 yanzu tana farin ciki a hidima na cikakken lokaci. Ta ce: “Wasu suna ganin na yi watsi da ilimina, amma sun gane cewa ina farin ciki, kuma suna son ƙa’idodi da ke ja-gorar rayuwata. Kowace rana ina addu’a ga Jehobah ya taimake ni na kasance da tawali’u don na samu amincewarsa.”

18. Kamar Bulus, ta yaya za mu zama mawadata a gaban Allah?

18 Saul wanda ya zama manzo Bulus, yana da damar samun aikin da zai azurtar da shi. Duk da haka, ya rubuta: “Hakika, ina lissafa dukan abu hasara kuma bisa ga fifikon sanin Kristi Yesu Ubangijina.” (Filibbiyawa 3:7, 8) A wurin Bulus, arzikin da ya samu ta wurin Kristi ya fi duk wani abin da zai samu daga duniya. Hakanan ma, ta wurin barin kowane buri na son kai da kuma biɗan rayuwa ta ibada, mu ma za mu more rayuwa ta arziki a gaban Allah. Kalmar Allah ta tabbatar mana cewa: “Ladar tawali’u da tsoron Ubangiji Dukiya ne, da girma, da rai.”—Misalai 22:4.

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Wace matsala ce mutumin da ke cikin kwatancin Yesu yake da ita?

• Me ya sa aka kira mutumin cikin almarar wawa?

• Me yake nufi mutum ya zama mawadaci ga Allah?

• Ta yaya za mu zama mawadata ga Allah?

[Hoto a shafi na 24]

Me ya sa aka kira mawadacin mutumin nan wawa?

[Hoto a shafi na 25]

Ta yaya ne zarafin samun cin gaba zai zama gwaji?

[Hoto a shafi nas 26, 27]

“Albarkar Ubangiji ta kan kawo wadata”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba