Jehobah Yana Son Adalci
‘Ni, Ubangiji, ina ƙaunar adalci.’—ISHAYA 61:8.
1, 2. (a) Menene kalmomin nan ‘adalci’ da ‘rashin adalci’ suke nufi? (b) Menene Littafi Mai Tsarki ya ce game da Jehobah da kuma halinsa na adalci?
ADALCI na nufin ‘rashin son kai, da kuma yin nagargarun abubuwa.’ Rashin adalci ya ƙunshi nuna bambanci, mugunta da kuma cutar da wasu ba gaira ba dalili.
2 Kusan shekaru 3,500 da suka wuce, Musa ya rubuta game da Jehobah Mamallakin Dukan Halitta, ya ce: ‘Dukan tafarkunsa adalci ne: Shi Allah mai-aminci ne, mara-mugunta.’ (Kubawar Shari’a 32:4) Fiye da ƙarnuka bakwai da suka wuce, Allah ya umurci Ishaya ya rubuta waɗannan kalaman: ‘Ni, Ubangiji, ina ƙaunar adalci.’ (Ishaya 61:8) Sa’an nan a ƙarni na farko, Bulus ya furta: “Da rashin adalci tare da Allah? Daɗai!” (Romawa 9:14) A wannan lokacin ne kuma Bitrus ya faɗi cewa: “Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowace al’umma, wanda ya ke tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gareshi.” (Ayukan Manzanni 10:34, 35) Hakika, ‘Ubangiji yana ƙaunar adalci.’—Zabura 37:28; Malachi 3:6.
Rashin Adalci ya Zama Gama Gari
3. Yaya ne rashin adalci ya soma a duniya?
3 Ba a yin adalci a yau. Za mu iya fuskantar rashin adalci a wurin aiki, a makaranta, a wajen sha’ani da shugabannai, da kuma waɗansu hanyoyi, har ma a cikin iyali. Hakika, irin waɗannan rashin adalci ba sabon abu ba ne. Rashin adalci ya soma ne a lokacin da Shaiɗan Iblis ya rinjayi iyayenmu na fari suka yi tawaye kuma suka zama marasa adalci. Adamu, da Hauwa’u da kuma Shaiɗan sun nuna rashin adalci da suka wulaƙanta ’yancin da Jehobah ya ba su. Mummunan aikinsu ya jawo wa dukan mutane wahala mai tsanani da kuma mutuwa.—Farawa 3:1-6; Romawa 5:12; Ibraniyawa 2:14.
4. Yaushe ne rashin adalci ya soma a tarihin ’yan adam?
4 Bayan shekaru 6,000 da aka yi tawaye a Adnin, rashin adalci ya kasance a duniya. Wannan ba abin mamaki ba ne saboda Shaiɗan ne allan wannan zamanin. (2 Korinthiyawa 4:4) Shi maƙaryaci ne kuma uban ƙarya, mai tsegumi kuma mai hamayya da Jehobah. (Yohanna 8:44) Koyaushe yana yin rashin adalci. Alal misali, saboda yadda Shaiɗan ya rinjayi mutane kafin rigyawa a zamanin Nuhu, Allah ya lura cewa “muguntar mutum ta yi yawa cikin duniya, kuma kowace shawara ta tunanin zuciyarsa mugunta ce kaɗai kullayaumi.” (Farawa 6:5) Wannan yanayin ya ci gaba har zamanin Yesu. Ya ce: “Wahalar yini ta ishe shi,” wahala wato rashin adalci. (Matta 6:34) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Dukan talikai suna nishi suna naƙuda tare da mu har yanzu.”—Romawa 8:22.
5. Me ya sa ake nuna rashin adalci a zamaninmu fiye da dā?
5 Saboda haka, mugayen abubuwa suna faruwa a dukan tarihin ’yan adam don rashin adalci. Yanzu yanayin ya fi na dā. Me ya sa? Saboda tun shekaru da yawa da suka shige wannan zamanin marar ibada yana cikin ‘kwanakinsa na ƙarshe,’ na “miyagun zamanu.” Littafi Mai Tsarki ya ce, a wannan zamanin, mutane za su zama “masu-son kansu, masu-son kuɗi, masu-ruba, masu-girman kai, masu-zagi, . . . marasa-godiya, marasa-tsarki, Marasa-ƙauna irin na tabi’a, masu-baƙar zuciya, masu-tsegumi, marasa-kamewa, masu-zafin hali, marasa-son nagarta, masu-cin amana, masu-taurin kai, masu-kumbura.” (2 Timothawus 3:1-5) Waɗannan mugayen halayen suna jawo rashin adalci iri-iri.
6, 7. Wane irin mugun rashin adalci ne ya shafi ’yan adam a zamaninmu?
6 Rashin adalci ya ƙaru a cikin shekaru ɗari da suka wuce fiye da dā. Wani dalili shi ne a waɗannan shekarun an yi yaƙe-yaƙe fiye da kowane zamani. Alal misali, waɗansu ’yan tarihi sun ce a Yaƙin Duniya na biyu kaɗai, an kashe mutane wajen miliyan 60, waɗanda yawancinsu fararen hula ne maza da mata da yara marasa laifi. Bayan da aka ƙare wannan yaƙin, an kashe miliyoyin mutane a yaƙe-yaƙe dabam dabam, waɗanda yawancinsu fararen hula ne. Shaiɗan ya yaɗa irin waɗannan rashin adalci saboda ya fusata sosai ne, ya san cewa ba da daɗewa ba Jehobah zai kawar da shi gaba ɗaya. Annabci na Littafi Mai Tsarki ya ce: “Shaiɗan ya sauko wajenku, hasala mai-girma kuwa gareshi, domin ya sani sauran zarafinsa kaɗan ne.”—Ru’ya ta Yohanna 12:12.
7 A kowace shekara ana kashe kusan dala biliyan sau biliyan a kan sojoji da kayan yaƙi. Miliyoyin mutane ba su da abubuwa na biyan bukatar rayuwa, saboda haka ka yi tunanin amfanin da dukan kuɗin nan zai yi idan aka kashe su wajen neman abin biyan bukata. Kusan mutane biliyan ɗaya ne ba su da isashen abinci, yayin da wasu suna da abinci da yawa. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce, a kowace shekara yara kusan miliyan biyar ne suke mutuwa domin rashin abinci. Wannan rashin adalci ne! Ka yi tunanin jarirai da yawa da ake kashewa ta wurin zubar da ciki. A kowace shekara an kimanta cewa ana kashe jarirai wajen miliyan 40 zuwa miliyan 60 a dukan duniya! Wannan mugun rashin adalci ne!
8. Ta yaya ne kawai ’yan adam za su sami adalci na gaskiya?
8 Shugabanni ba sa neman magance matsalar da ke damun mutane a yau; kuma ƙoƙarce-ƙoƙarcen da mutane suke yi ba zai kyautata yanayin ba. Kalmar Allah ta annabta cewa a lokacinmu “miyagun mutane da masu-hila za su daɗa mugunta gaba gaba, suna ruɗi, ana ruɗinsu.” (2 Timothawus 3:13) Rashin adalci ya zama yanayin rayuwa na yau da kullum da mutane ba za su iya kawar da shi ba. Allah na adalci ne kaɗai zai iya kawar da rashin adalci. Shi kaɗai ne zai cire Shaiɗan, da aljanu, da kuma miyagun mutane.—Irmiya 10:23, 24.
Damuwa da ta Dace
9, 10. Menene ya sa Asaph ya yi sanyin gwiwa?
9 A dā, wasu marubutan Littafi Mai Tsarki sun yi tunanin abin da ya sa Allah bai sa hannu a harkokin ’yan adam ba don ya kawo adalci na gaskiya. Alal misali, ka yi la’akari da rubutu na sama na Zabura ta 73 a cikin NWT da ya ambata sunan Asaph, wanda wataƙila yana nuni ne ga wani shahararren mawaƙi Balawi a lokacin sarautar Sarki Dauda ko kuma mawaƙan da suke gidan da Asaph ne shugaba. Asaph da zuriyarsa sun rubuta waƙoƙi da yawa da ake amfani da su a wajen bauta. A wani lokaci a rayuwarsa, marubucin wannan zabura ya yi kasala a bautarsa. Ya ga yadda miyagun mutane suke cin gaba, ya kuma lura cewa suna yin rayuwa mai gamsarwa, ba sa fuskantar wani mugun sakamako.
10 Mun karanta: “Na ji kishin zuci ga masu-girman kai, sa’anda na ga arzikin masu-mugunta. Gama a cikin mutuwassu babu mirkaki: Ƙarfinsu yana cike. Ba su cikin wahala kamar sauran mutane; Ba a yi masu masibu kamar sauran mutane ba.” (Zabura 73:2-8) Amma daga baya marubucin ne Littafi Mai Tsarki ya fahimci cewa irin wannan tunanin ba shi da kyau. (Zabura 73:15, 16) Mai zabura ya gyara tunaninsa, amma bai fahimci abin da ya sa miyagu suke nasara wajen aikata mugunta ba yayin da mutane masu zuciyar kirki suna shan wahala.
11. Menene mai zabura Asaph ya fahimta daga baya?
11 Daga baya wannan mutumin mai aminci ya fahimci abin da aka shirya wa miyagu, wato Jehobah zai daidaita abubuwa. (Zabura 73:17-19) Dauda ya rubuta: “Ka yi sauraro ga Ubangiji, ka kiyaye tafarkinsa, shi kuma za ya ɗaukake ka ka gaji ƙasar: Lokacinda an datse miyagu, ka gani.”—Zabura 37:9, 11, 34.
12. (a)Menene nufin Jehobah game da mugunta da rashin adalci? (b) Menene ra’ayinka game da yadda za a magance rashin adalci?
12 Hakika, nufin Jehobah ne ya kawar da miyagu da rashin adalci daga wannan duniya idan lokacinsa ya yi. Wannan shi ne abin da ya kamata Kiristoci masu aminci su dinga tunawa koyaushe. Jehobah zai kawar da waɗanda ba su bi nufinsa ba, kuma zai albarkaci waɗanda suka bi nufinsa. “Idanunsa suna duban ’yan adam, maƙyaptansa suna gwada su. Ubangiji yana gwada mai-adalci: amma mai-mugunta da mai-son zalunci ransa yana ƙinsu. Za ya zubo da tarkuna bisa masu-mugunta; Wuta da ƙibiritu da iska mai-ƙuna . . . Gama Ubangiji mai-adalci ne; yana ƙaunar adalci.”—Zabura 11:4-7.
Sabuwar Duniya ta Adalci
13, 14. Me ya sa adalci zai kasance a sabuwar duniya?
13 Sa’ad da Jehobah ya halaka wannan zamani na rashin adalci da Shaiɗan yake ja-gora, Zai kawo sabuwar duniya mai ɗaukaka. Mulkin Allah na samaniya wanda Yesu ya koya wa mabiyansa su yi addu’a ya zo ne zai ja-gorance ta. Gaskiya da kuma adalci za su kasance maimakon mugunta, sa’an nan addu’ar nan za ta cika: “Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya.”—Matta 6:10.
14 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana irin shugabancin da za mu yi begensa, wato shugabancin da dukan mutane masu zuciyar kirki suke ɗokinsa. Sa’an nan Zabura 145:16 za ta cika: “[Jehobah Allah] kana buɗe hannunka, kana biya ma kowane mai-rai muradinsa.” Bugu da ƙari, Ishaya 32:1 ta ce: “DUBA, wata rana wani sarki [Yesu Kristi da ke sama] za ya yi mulki cikin adalci, hakimai [wakilan Kristi a duniya] kuma za su yi mulki da shari’a.” Game da Sarki Yesu Kristi, Ishaya 9:7 ta ce: “Ƙaruwar mulkinsa da salama ba ta da iyaka, a bisa kursiyin Dauda, da bisa mulkinsa, domin a kafa shi, a tabbatadda shi ta wurin gaskiya da adalci daga nan gaba kuma har abada. Himmar Ubangiji mai-runduna za ya aikata wannan.” Kana ganin za ka kasance a ƙarƙashin wannan shugabanci mai kyau?
15. Menene Jehobah zai yi wa mutane a sabuwar duniya?
15 A sabuwar duniya ta Allah, ba za a sami dalilin furta kalaman da suke cikin Mai-Wa’azi 4:1 ba: “Na kuma duba, na ga dukan irin zilama da a ke yi a cikin duniya: duba, ga hawayen waɗannan da a ke zalumtassu, ba su da mai-taimako; a wajen masu-zalumtassu kuma ga iko, amma ba su da mai-taimako.” Hakika, saboda mu ajizai ne, zai yi wuya mu yi tunanin yadda sabuwar duniya ta adalci za ta kasance. Mugunta ba za ta ƙara kasancewa ba, amma kowace rana za ta kasance da abubuwa masu kyau. Hakika, Jehobah zai gyara dukan abubuwa marasa kyau, zai yi haka ne fiye da yadda muke tsammani. Ya dace da Jehobah Allah ya aririce manzo Bitrus ya rubuta: “Bisa ga alkawarinsa, muna sauraron sabobin sammai da sabuwar duniya, inda adalci yake zaune.”—2 Bitrus 3:13.
16. Ta yaya ne aka kafa “sabobin sammai” kuma ta yaya ne ake shirya “sabuwar duniya” a yau?
16 Hakika, an kafa wannan “sabobin sammai,” wato gwamnatin Allah na samaniya da ke hannun Kristi. An tattara mutane kaɗan masu zuciyar kirki a wannan zamani na ƙarshe a “sabuwar duniya.” Mutanen sun kusan miliyan bakwai a ƙasashe 235 cikin ikilisiyoyi guda 100,000. Waɗannan miliyoyin mutanen suna koyon hanyoyin Jehobah na adalci, a sakamakon haka, dukan duniya suna more haɗin kai da ke bisa ƙauna ta Kirista. Ana ganin haɗin kai da jimrewa da suke yi a tarihi na duniya, haɗin kai da ya fi duk wani abin da talakawan Shaiɗan suke da shi. Wannan ƙauna da haɗin kai suna nuna irin rayuwa mai kyau da za a yi a sabuwar duniya ta Allah, wadda za ta kasance da gaskiya da kuma adalci.—Ishaya 2:2-4; Yohanna 13:34, 35; Kolossiyawa 3:14.
Shaiɗan ba Zai Yi Nasara a Farmakinsa Ba
17. Me ya sa Shaiɗan ba zai yi nasara ba a farmakin ƙarshe da zai kai wa mutanen Jehobah?
17 Ba da daɗewa ba Shaiɗan da mabiyansa za su so su halaka masu bauta wa Jehobah. (Ezekiel 38:14-23) Wannan yana cikin abin da Yesu ya kira “ƙunci mai-girma, irin da ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har yanzu, ba kuwa za a yi ba daɗai.” (Matta 24:21) Shaiɗan zai yi nasara a wannan farmakin kuwa? A’a. Kalmar Allah ta ba mu tabbaci cewa: “Ubangiji yana son shari’a, kuma ba ya yarda tsarkakansa ba; ana kiyaye su har abada: amma za a datse zuriyar miyagu. Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.”—Zabura 37:28, 29.
18. (a)Menene Allah zai yi game da farmakin da Shaiɗan zai kai wa mutanensa? (b) Me ya sa yana da kyau ka sake karanta wannan bayani da ke cikin Littafi Mai Tsarki game da cin nasara na adalci?
18 Farmakin da Shaiɗan zai kai tare da mutanensa masu yawa bisa mutanen Jehobah ne zai zama ta ƙarshe. Ta wurin Zechariah Jehobah ya ce: “Wanda ya taɓa ku, ya taɓa ƙwayar idonsa.” (Zechariah 2:8) Kamar wani yana saka yatsunsa ne a cikin idon Jehobah. Zai ɗauki mataki nan da nan kuma ya halaka masu aikata laifi. Bayin Jehobah su ne suka fi nuna ƙauna, haɗin kai, salama, da kuma bin doka a duniya. Shi ya sa bai cancanta a kai musu farmaki ba. Mai ‘son adalci’ ba zai yarda ba. Matakin da zai ɗauka zai kai ga halaka maƙiyan mutanensa, cikin adalci zai ceci waɗanda suke bauta wa Allah makaɗaici na gaskiya. Abubuwa masu ban sha’awa suna nan tafe a gaba!—Misalai 2:21, 22.
Yaya Za Ka Amsa?
• Me ya sa rashin adalci ya zama gama gari?
• Ta yaya ne Jehobah zai magance rashin adalci a duniya?
• Menene ya burge ka a wannan nazari game yadda adalci zai ci nasara?
[Hoto a shafi na 9]
Mugunta ta yi yawa kafin Rigyawa, kuma ta ƙaru a wannan “kwanaki na ƙarshe”
[Hoto a shafi na 10]
A sabuwar duniya ta Allah, gaskiya da kuma adalci za su kasance maimakon mugunta