An “Rubuta Su Domin Koyarwarmu”
“YIN littattafai ba shi da iyaka.” (Mai-Wa’azi 12:12) Littattafai masu yawa da ake da su a yau sun sa waɗannan kalaman su kasance kamar yadda suke a lokacin da aka rubuta su. Ta yaya ne mai karatu zai iya zaɓan abin da ya kamata ya karanta?
Sa’ad da suke tunanin littafin da za su karanta, yawancin masu karatu za su so su san wani abu game da mawallafin. Waɗanda suka buga littafi suna iya rubuta ɗan bayanin da ke ƙunshe da garin mawallafin, digirorin da ya samu a makaranta, da kuma sunayen littattafan da ya wallafa a dā. Sanin mawallafi yana da muhimmanci, domin a ƙarnuka na farko, matan da suke wallafa littafi suna canja sunayensu zuwa na maza saboda kada waɗanda za su karanta littafin su ƙasƙantar da shi domin mace ce ta wallafa shi.
Abin baƙin ciki, kamar yadda aka ambata a talifin da ya gabata, wasu sun yi watsi da Nassosin Ibrananci domin sun gaskata cewa Allahn da aka ambata a ciki mugu ne wanda yake hallakar da magabtansa babu tausayi.a Bari mu tattauna abin da Nassosin Ibrananci da kuma Nassosin Kirista na Helenanci suka gaya mana game da Mawallafin Littafi Mai Tsarki.
Game da Mawallafin Littafi Mai Tsarki
In ji Nassosin Ibrananci, Allah ya gaya wa al’ummar Isra’ila cewa: “Ni Ubangiji ba mai-sakewa ba ne.” (Malachi 3:6) Bayan shekara 500, marubucin Littafi Mai Tsarki Yaƙub ya rubuta game da Allah: “Sakewa ba ta yiwuwa gareshi, ba kuwa inuwa ta juyawa.” (Yaƙub 1:17) To, me ya sa wasu suke ganin cewa Allahn da aka bayyana a Nassosin Ibrananci ya bambanta da Allahn da ke cikin Nassosin Kirista na Helenanci?
Amsar ita ce, an bayyana fasaloli dabam dabam na halayen Allah a sashe dabam dabam na Littafi Mai Tsarki. A cikin littafin Farawa kaɗai, an kwatanta cewa an “ɓata masa zuciya,” shi ne “Mai-sama da ƙasa,” da kuma “Mai-shari’an dukan duniya.” (Farawa 6:6; 14:22; 18:25) Waɗannan kwatanci dabam dabam suna nuni ne ga Allah ɗaya? Ƙwarai kuwa.
Ga misali: Waɗanda aka taɓa kai wa gaban wani alƙali suna iya ganin cewa shi mutum ne mai bin doka. A wani ɓangaren kuma, yaransa na iya ɗaukansa uba mai ƙauna kuma mai karimci. Abokansa na kud da kud na iya ganin cewa mutum ne mai fara’a kuma mai ban dariya. Wannan alƙali, uba, da kuma aboki duk mutum ɗaya ne. Sai dai kawai fasaloli dabam dabam na halayensa sukan bayyana ne a yanayi dabam dabam.
Hakazalika, Nassosin Ibrananci sun kwatanta Jehobah a matsayin “Allah [mai] cike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinƙai da gaskiya.” Duk da haka, mun koyi cewa “ba shi kuɓutadda mai-laifi ko kaɗan.” (Fitowa 34:6, 7) Waɗannan fasalolin guda biyu sun nuna ma’anar sunan Allah. “Jehobah” na nufin “Yana Sa Ya Kasance.” Wato, Allah yana zama duk wani abin da ake bukata don ya cika alkawuransa. (Fitowa 3:13-15) Kuma har ila shi ne Allah. Yesu ya ce: “Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne.”—Markus 12:29.
An Canja Nassosin Ibrananci Ne?
Ba sabon abu ba ne ba a yau a canja littattafai sa’ad da aka yi sabon bincike ko kuwa sa’ad da ra’ayin mutane ya canja. Nassosin Kirista na Helenanci ya canja Nassosin Ibrananci ne? A’a.
Da Yesu yana son labarin hidimarsa da kuma rubuce-rubucen almajiransa su canja Nassosin Ibrananci, da ya bayyana hakan. Amma, game da Yesu jim kaɗan kafin ya koma sama, labarin Luka ya ce: “Ya soma kuwa tun daga Musa da dukan annabawa [da ke cikin Nassosin Ibrananci], cikin dukan littattafai yana fasalta musu [almajiransa biyu] al’amura na bisa kansa.” Bayan haka, Yesu ya bayyana ga manzanninsa masu aminci da kuma wasu mutane. Labarin ya ci gaba: “Ya ce musu kuma, Waɗannan su ne kalmomina da na yi muku, tun ina tare da ku tukuna, cewa, Dukan abin da aka rubuta a kaina a cikin Attaurat ta Musa, da Annabawa, da Zabura, dole a cika su.” (Luka 24:27, 44) Me zai sa Yesu ya yi ƙaulin Nassosin Ibrananci a ƙarshen hidimarsa a duniya da a ce sun zama tsohon yayi?
Bayan da aka kafa ikilisiyar Kirista, mabiyan Yesu sun ci gaba da yin amfani da Nassosin Ibrananci su bayyana annabce-annabcen da ba su cika ba, mizanai daga Dokar Musa da suka koyar da darussa masu amfani, da kuma labaran bayin Allah na dā waɗanda misalansu masu kyau suka ƙarfafa Kiristoci su kasance da aminci. (Ayukan Manzanni 2:16-21; 1 Korinthiyawa 9:9, 10; Ibraniyawa 11:1–12:1) Manzo Bulus ya rubuta cewa: ‘Kowane nassi hurarre daga wurin Allah mai-amfani ne.’b (2 Timothawus 3:16) Ta yaya ne Nassosin Ibrananci suke da amfani a yau?
Shawara Game da Rayuwa Ta Yau da Kullum
Yi la’akari da matsalar ƙabilanci a yau. A wani birni a Gabashin Turai, wani Bahabashe ɗan shekara 21 ya ce: “Idan muna son mu fita ko’ina, dole ne mu kasance da yawa. Wataƙila idan muna da yawa ba za su kawo mana hari ba.” Ya ci gaba: “Ba za mu iya fita waje bayan ƙarfe 6 na yamma ba, musamman bin hanyar jirgin ƙasa da aka yi a cikin ƙasa. A duk lokacin da mutane suka kalle mu, suna mai da hankali ne kawai a kan launin fatarmu.” Nassosin Ibrananci sun yi magana a kan wannan matsalar mai wuya kuwa?
An gaya wa Isra’ilawa na dā cewa: “Idan kuwa baƙo ya sabka wurinka a cikin ƙasarku, ba za ku yi masa mugunta ba. Baƙon da ke sabke a wurinku za ya zama maku kamar ɗan da aka haifa a wurinku, za ka ƙaunace shi kamar kanka: gama ku dā baƙi ne cikin ƙasar Masar.” (Leviticus 19:33, 34) Hakika, a Isra’ila ta dā wannan dokar ta bukaci Isra’ilawa su girmama baƙin haure, kuma tana cikin Nassosin Ibrananci. Ka yarda cewa mizanan da ke cikin wannan dokar za su iya magance matsalar nuna ƙabilanci a yau?
Ko da yake ba su ba da wata taƙaitacciyar shawara ba game da kuɗi, Nassosin Ibrananci sun ƙunshi ja-goranci masu kyau game da yadda za a bi da kuɗi. Alal misali, a Misalai 22:7, mun karanta cewa: “Mai-cin bashi kuma bawa ne ga mai-bada bashi.” Yawancin masu ba da shawara game da kuɗi sun yarda cewa yawan cin bashi na iya jawo hasara.
Ƙari ga haka, Sarki Sulemanu wanda yana ɗaya daga cikin mutane mafi kuɗi a tarihi ya kwatanta neman kuɗi ko ta yaya, wanda ya zama gama gari a wannan duniyar. Ya rubuta: “Wanda ya ke ƙaunar azurfa ba za ya ƙoshi da azurfa ba; wanda ya ke neman yalwa kuma ba za ya ƙoshi da ƙaruwa ba: wannan kuma banza ne.” (Mai-Wa’azi 5:10) Wannan gargaɗi ne mai kyau!
Bege na Nan Gaba
Littafi Mai Tsarki gabaki ɗayansa yana da jigo ɗaya tak: Mulki a ƙarƙashin Yesu Kristi shi ne hanyar da za a kunita ikon mallakar Allah da kuma tsarkake sunansa.—Daniel 2:44; Ru’ya ta Yohanna 11:15.
Ta hanyar Nassosin Ibrananci, mun koyi abubuwa masu yawa game da yadda rayuwa za ta kasance a ƙarƙashin Mulkin Allah kuma hakan ya ƙarfafa mu kuma ya jawo mu kusa da Jehobah Allah, Tushen wannan ƙarfafar. Alal misali, annabi Ishaya ya annabta cewa salama za ta kasance tsakanin dabbobi da mutane: “Kerkeci za ya zauna tare da ɗan rago, damisa kuma za ta kwanta tare da ɗan akuya; da ɗan maraƙi da ɗan zaki da kiyayayyen ɗan sā za su zauna wuri ɗaya; ɗan yaro kuwa za ya bishe su.” (Ishaya 11:6-8) Wannan bege ne mai kyau!
Waɗanda ƙabilanci, mugun rashin lafiya, ko kuwa talauci ya shafa sosai fa? Nassosin Ibrananci sun yi wannan annabcin game da Yesu Kristi: “Za ya ceci fakiri sa’anda ya yi kuka: matalauci kuma wanda ba shi da mai-taimako. Za ya nuna tausayi ga matalauci da mai-mayata, za ya kuwa ceci rayukan fakirai.” (Zabura 72:12, 13) Waɗannan alkawuran suna da amfani domin suna sa waɗanda suka ba da gaskiya da su su kasance da bege da kuma tabbaci.—Ibraniyawa 11:6.
Babu shakka, shi ya sa aka hure manzo Bulus ya rubuta: ‘Iyakar abin da aka rubuta a dā aka rubuta su domin koyarwarmu, domin ta wurin haƙuri da ta’aziyar litattafai mu zama da bege.’ (Romawa 15:4) Hakika, Nassosin Ibrananci har yanzu sashe ne mai muhimmanci na hurarriyar Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki. Suna da tamani sosai a gare mu a yau. Begenmu shi ne za ka ci gaba da ƙoƙarin ƙara koyon ainihin abin da Littafi Mai Tsarki gabaki ɗayansa yake koyarwa kuma ka kusanci Mawallafinsa, Jehobah Allah.—Zabura 119:111, 112.
[Hasiya]
a A wannan talifin, za mu kira Tsohon Alkawari, Nassosin Ibrananci. (Ka duba akwatin nan “Tsohon Alkawari ko kuwa Nassosin Ibrananci?” da ke shafi na 6.) Hakazalika, Shaidun Jehobah suna kiran Sabon Alkawari, Nassosin Kirista na Helenanci.
b Nassosin Ibrananci suna ɗauke da mizanai masu amfani sosai a yau. Amma, ya kamata a lura cewa Kiristoci ba sa ƙarƙashin Dokar da Allah ya ba al’ummar Isra’ila ta hanyar Musa.
[Akwati a shafi na 6]
TSOHON ALKAWARI KO KUWA NASSOSIN IBRANANCI?
Furcin nan “tsohon alkawari” ya bayyana ne a cikin 2 Korinthiyawa 3:14. A wannan fassarar, “alkawari” na wakiltar kalmar Helenanci di·a·theʹke. Menene ma’anar furcin nan “tsohon alkawari” da ke cikin 2 Korinthiyawa 3:14?
Mawallafin ƙamus Edward Robinson ya ce: “Tun da yake alkawari na dā yana cikin littattafan Musa, [di·a·theʹke] yana wakiltar littafin alkawari, rubuce-rubucen Musa, alal misali, doka.” A 2 Korinthiyawa 3:14, manzo Bulus yana nuni ne ga Dokar Musa, wadda sashe ce na Nassosin kafin Kiristanci.
Wane suna ne ya fi dacewa da littattafai 39 na farko na Littafi Mai Tsarki? Maimakon su nuna cewa wannan sashe na Littafi Mai Tsarki ya zama tsohon yayi, Yesu Kristi da mabiyansa sun kira wannan sashen “Litattafai” da kuma “litattafai masu-tsarki.” (Matta 21:42; Romawa 1:2) Saboda haka, cikin jituwa da waɗannan hurarrun kalamai, Shaidun Jehobah suna kiran Tsohon Alkawari Nassosin Ibrananci domin ainihi wannan sashe na Littafi Mai Tsarki an rubuta shi ne a yaren Ibrananci. Hakazalika, suna kiran Sabon Alkawari, Nassosin Helenanci, domin mazan da Allah ya hure su rubuta wannan sashen na Littafi Mai Tsarki sun yi amfani ne da yaren Helenanci.
[Hotuna a shafi na 4]
Ana iya sanin mutum a matsayin alƙali mai bin doka, uba mai auna, da kuma aboki
[Hoto a shafi na 5]
Yesu ya yi amfani da Nassosin Ibrananci a lokacin hidimarsa
[Hotuna a shafi na 7]
Waɗanne mizanan Littafi Mai Tsarki ne za su iya taimaka wa mutum ya yanke shawarar da ta dace?