Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w07 9/1 p. 18-p. 20 par. 11
  • Darussa Daga Littafin Daniel

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Darussa Daga Littafin Daniel
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • MENENE LABARIN DA AKA TSARA YA KOYA MANA?
  • (Daniel 1:1–6:28)
  • MENENE WAHAYIN DANIEL YA NUNA?
  • (Daniel 7:1–12:13)
  • Jehobah Yana Yi Wa ‘Waɗanda Ke Tsoronsa Albarka’
  • Ka Mai Da Hankali Ga Kalmomin Annabci Na Allah Don Kwanakinmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Abin da Littafi Mai Tsarki ya Ce Game da Daniyel?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ka Yi Koyi da Daniyel
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Wani Annabi da ke Zaman Bauta Ya Sami Wahayi Game da Gaba
    Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
w07 9/1 p. 18-p. 20 par. 11

Maganar Jehobah Rayayya Ce

Darussa Daga Littafin Daniel

“LITTAFIN Daniel yana ɗaya daga cikin littattafai masu kayatarwa a cikin Littafi Mai Tsarki,” in ji littafin nan Holman Illustrated Bible Dictionary. “Littafin yana cike da gaskiya na dindindin.” Labarin Daniel ya soma ne a shekara ta 618 K.Z., sa’ad da Sarki Nebuchadnezzar na Babila ya kai wa Urushalima hari, kuma ya ɗauki “waɗansu daga cikin ’ya’yan Isra’ila” zuwa bauta a Babila. (Daniel 1:1-3) Daniel matashi yana cikinsu, wataƙila yana ɗan shekara goma sha a lokacin. Daniel ya kammala littafin a Babila. A yanzu ya kusan ɗan shekara 100, Daniel ya sami alkawari daga wurin Allah: “Za ka huta, ka tsaya a cikin rabonka, a ƙarshen kwanaki.”—Daniel 12:13.

Ko da yake ɓangaren farko na littafin Daniel an gabatar da shi ne a jerin yadda abubuwa suka faru kuma ana maganar wani ne, a ɓangare na ƙarshen mai rubutun ne ke ba da labarin kansa. Daniel ne marubucin, kuma littafin yana ɗauke da annabce-annabce game da tasowa da kuma faɗuwar ƙasashe masu ƙarfi, lokacin da Almasihu zai bayyana, da kuma abubuwan da za su faru a zamaninmu.a Tsohon annabin ya tuna shekarun da ya yi a duniya kuma ya faɗi abubuwan da suka faru da za su ƙarfafa mu mu zama maza da mata masu aminci. Saƙon Daniel rayayye ne kuma yana da iko.—Ibraniyawa 4:12.

MENENE LABARIN DA AKA TSARA YA KOYA MANA?

(Daniel 1:1–6:28)

A shekarar 617 K.Z., Daniel da abokansa matasa uku, Shadrach, Meshach, da Abednego, suna cikin fadar Babila. A cikin shekaru uku da aka yi a ilimantar da su game da rayuwar fada, matasan sun kasance da amincinsu ga Allah. Wajen shekara takwas bayan haka, Sarki Nebuchadnezzar ya yi wani mugun mafarki. Daniel ya faɗi mafarkin kuma ya ba da ma’anarsa. Sarkin ya yarda cewa Jehobah “shi ne Allah na allohi, Ubangijin sarakuna kuwa, mai-bayana asirai.” (Daniel 2:47) Ba da daɗewa ba, Nebuchadnezzar ya manta wannan darassin. A lokacin da abokan Daniel su uku suka ƙi bauta wa wani babban gunki, sarkin ya sa aka jefa su cikin tandun wuta. Allah na gaskiya ya cece su, kuma hakan ya tilasta wa Nebuchadnezzar ya san cewa “babu wani allah wanda ya ke da iko shi yi ceto bisa ga wannan kwatanci.”—Daniel 3:29.

Nebuchadnezzar ya sake yin wani mafarki mai muhimmanci. Ya ga wani babban ice wanda aka sare kuma aka hana shi girma. Daniel ya faɗi ma’anar wannan mafarkin. Sashen mafarkin ya cika sa’ad da Nebuchadnezzar ya haukace kuma ya warke. Shekaru da yawa bayan haka, Sarki Belshazzar ya shirya wa hakimansa wata babbar liyafa kuma cikin raini ya yi amfani da tasoshin da aka ɗauko daga haikalin Jehobah. A wannan daren aka kashe Belshazzar kuma Darius Bamedi ya karɓi mulkin. (Daniel 5:30, 31) A zamanin Darius, sa’ad da Daniel yake cikin shekarunsa na 90, wasu shugabanni masu kishi suka yi ƙulli don a kashe shi. Amma Jehobah ya cece shi “daga ikon zakuna.”—Daniel 6:27.

Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:

1:11-15—Kayan lambun da matasa huɗu ’yan Yahuda suka ci ne ya sa fuskarsu ta yi kyau? A’a. Babu kayan lambun da zai kawo irin wannan canjin a cikin kwana goma kawai. Jehobah ne ya sa fuskar waɗannan matasa Ibraniyawa ta yi kyau, wanda ya albarkace su don sun dogara da shi.—Misalai 10:22.

2:1—A wane lokaci ne Nebuchadnezzar ya yi mafarkin babban gunki? Labarin ya ce hakan ya faru ne “a cikin shekara ta biyu ta mulkin Nebuchadnezzar.” Ya zama sarki a shekara ta 624 K.Z. Hakan yana nufin cewa shekararsa ta biyu ta sarauta ta soma a shekara ta 623 K.Z., wato, shekaru masu yawa kafin ya kai wa Yahuda hari. A wannan lokacin, Daniel ba ya Babila balle ya ba da ma’anar mafarkin. Babu shakka, an soma ƙirga “shekara ta biyu” ce daga shekara ta 607 K.Z. sa’ad da sarkin Babila ya halakar da Urushalima kuma ya zama sarkin duniya.

2:32, 39—Ta wace hanya ce mulkin kan zinariya ya fi na azurfa, kuma ta yaya ne mulkin azurfa ya fi na jan ƙarfe? Babila wato, kan zinariya ta fi daular Midiya da Farisa wanda ke wakiltar sashen azurfa da ke jikin gunkin, domin ba ta da damar halaka Yahuda. Ƙasa mai iko da ta bi bayanta ita ce Hellas, wadda jan ƙarfe ke wakilta. Hellas tana ƙasa da Midiya da Farisa, kamar yadda jan ƙarfe ke ƙasa da azurfa. Ko da yake Daular Hellas tana da girma sosai, ba ta sami gatar ’yantar da mutanen Allah daga bauta ba kamar Midiya da Farisa.

4:8, 9—Da gaske ne Daniel ya zama ubangijin masu sihiri? A’a. Furcin nan “ubangijin masu-sihiri” yana nuni ne ga matsayin Daniel, wato, “babban mai-mulki kuma bisa dukan masu-hikima na Babila.”—Daniel 2:48.

4:10, 11, 20-22—Menene babban icen da Nebuchadnezzar ya gani a mafarkinsa yake wakilta? A dā icen na wakiltar Nebuchadnezzar wanda ke mulka ƙasa mafi iko a duniya. Tun da sarautar ta kai “har iyakar duniya,” icen na nuni ga wani abu mai girma sosai. Daniel 4:17 ta haɗa mafarkin da sarautar “Maɗaukaki” bisa ’yan adam. Icen kuma yana wakiltar ikon mallakar dukan sararin samaniya na Jehobah, musamman game da duniya. Saboda haka, mafarkin yana da cikawa guda biyu, wato, a sarautar Nebuchadnezzar da kuma a ikon mallakar Jehobah.

4:16, 23, 25, 32, 33—Menene tsawon ‘lokatai guda bakwai’? Duka canje-canjen da suka bayyana a fasalin Sarki Nebuchadnezzar sun nuna cewa ‘lokatai bakwai’ ɗin sun wuce kwana bakwai kawai. A nasa batun, waɗannan lokatan suna nufin shekaru bakwai masu kwana 360 kowacce, ko kuwa kwanaki 2,520. A cika mai girma, ‘lokatai bakwai’ na nufin shekaru 2,520. (Ezekiel 4:6, 7) Sun soma ne sa’ad da aka halakar da Urushalima a shekara ta 607 K.Z., kuma sun ƙare sa’ad da aka naɗa Yesu a matsayin Sarki a sama a shekara ta 1914 A.Z.—Luka 21:24.

6:6-10—Tun da yin addu’a ga Jehobah ba ya bukatar tsayuwa ta musamman, me ya sa Daniel bai yi addu’a ba a ɓoye a waɗannan kwanaki 30? Mutane sun san cewa Daniel yana yin addu’a sau uku a rana. Shi ya sa waɗanda suka yi ƙullin suka sa aka kafa dokar hana yin addu’a. Idan Daniel ya canja tsarinsa na yin addu’a hakan zai zama cewa ya karya ƙa’idarsa kuma da hakan ya nuna cewa ya daina bauta wa Jehobah.

Darussa Dominmu:

1:3-8. Ƙudurin da Daniel da abokansa suka yi na kasancewa da aminci ga Jehobah ya nuna irin koyarwar da suka samu daga iyayensu. Sa’ad da iyaye masu tsoron Allah suka mai da abubuwa na ruhaniya abin farko a rayuwarsu, kuma suka koya wa ’ya’yansu su yi haka, yaransu za su iya yin tsayayya da kowane irin gwaje-gwaje da matsin da za su iya tasowa a makaranta ko a wani waje dabam.

1:10-12. Daniel ya fahimci dalilin da ya sa “ubanɗakin babanni” yake jin tsoron sarki kuma ya daina roƙonsa. Amma, daga baya Daniel ya je ya sami “wakili” wanda wataƙila yana da sauƙin kai kaɗan. Sa’ad da muka fuskanci yanayi mai wuya, ya kamata mu aikata da fahimi da kuma hikima.

2:29, 30. Kamar Daniel, ya kamata mu yaba wa Jehobah domin kowane sani, halaye, da iyawa da muke da shi, sun samu ne domin mun yi amfani da tanadodi na ruhaniya.

3:16-18. Da a ce waɗannan Ibraniyawa guda uku sun karya ƙa’idodinsu game da irin abincin da za su ci, da sun kasa ba da amsa da gaba gaɗi kamar haka. Ya kamata mu ma mu yi ƙoƙari mu kasance “masu-aminci cikin dukan al’amura.”—1 Timothawus 3:11.

4:24-27. Yin shelar saƙon Mulki, wanda ya haɗa da hukunci mai tsanani na Allah, yana bukatar irin bangaskiya da gaba gaɗin da Daniel ya nuna wajen sanar da abin da zai sami Nebuchadnezzar da kuma abin da sarkin zai yi don ‘a tsawonta kwanciyar ransa.’

5:30, 31. ‘Habaicin da aka yi bisa sarkin Babila’ ya zama gaskiya. (Ishaya 14:3, 4, 12-15) Shaiɗan Iblis, wanda yake yin fahariya irin ta sarakunan Babila, zai yi faɗuwar kunya.—Daniel 4:30; 5:2-4, 23.

MENENE WAHAYIN DANIEL YA NUNA?

(Daniel 7:1–12:13)

Sa’ad da Daniel ya sami wahayinsa na farko a shekara ta 553 K.Z., yana cikin shekarunsa na 70. Daniel ya ga manyan dabbobi guda huɗu waɗanda suke wakiltar ƙasashen duniya masu iko tun daga zamaninsa zuwa namu. A wahayin wani abu da ke faruwa a sama, ya ga wani “mai-kama da ɗan mutum” wanda aka ba madawwamiyar ‘sarauta.’ (Daniel 7:13, 14) Shekaru biyu bayan haka, Daniel ya sami wahayin da ya shafi Midiya da Farisa, Hellas, da kuma wani dabam da ya zama “sarki mai-zafin fuska.”—Daniel 8:23.

Yanzu shekara ta 539 K.Z. ce. Babila ta riga ta faɗi, kuma Darius Bamedi ya zama sarkin masarautar Kaldiyawa. Daniel ya yi addu’a ga Jehobah game da sake gina ƙasarsu. A lokacin da yake cikin addu’a, Jehobah ya aika mala’ika Jibrailu ya sa Daniel ya sami “hikimar ganewa” game da zuwan Almasihu. (Daniel 9:20-25) Daga nan sai shekara ta 536/535 K.Z. Wasu ’yan raguwa sun riga sun koma Urushalima. Amma ana hamayya da aikin gina haikalin. Wannan ya zama abin damuwa ga Daniel. Ya yi addu’a game da batun, kuma Jehobah ya aika mala’ika mai matsayi sosai ga Daniel. Bayan ya ƙarfafa Daniel, mala’ikan ya faɗi annabcin da ya bayyana kokawar samun girma tsakanin sarkin arewa da na kudu. Rigimar da ke tsakanin sarakunan biyu ta soma ne tun daga lokacin da aka raba mulkin Alexander Mai Girma tsakanin janarorinsa guda huɗu har zuwa lokacin da Babban Ɗan Sarki, Mika’ilu, “za ya tashi tsaye.”—Daniel 12:1.

Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:

8:9—Mecece “Maɗaukakiya” take wakilta? A wannan batun, “Maɗaukakiya” tana wakiltar yanayin shafaffun Kiristoci a duniya a lokacin da Britaniya da Amirka suke mulka duniya.

8:25—Wanene “Sarkin sarakuna”? Kalmar Helenanci sar, da aka fassara “sarki,” tana nufin “shugaba.” Lakabin nan “Sarkin sarakuna” na Jehobah Allah ne kaɗai, wanda shi ne Shugaban dukan mala’iku sarakuna, har da “Michael, ɗaya daga cikin manyan sarakuna.”—Daniel 10:13.

9:21—Me ya sa Daniel ya kira mala’ika Jibrailu “mutumin nan”? Hakan ya faru ne domin Jibrailu ya zo masa ne a siffa irin ta mutane, kamar yadda ya bayyana ga Daniel a wahayi na farko.—Daniel 8:15-17.

9:27—Wane alkawari ‘mai ƙwari’ ne ya ci gaba da ci har ƙarshen makonni 70 na shekaru, ko shekara ta 36 A.Z.? An cire Dokar alkawarin a shekara ta 33 A.Z., sa’ad da aka tsire Yesu. Amma, ta wajen barin alkawarin da aka yi da Ibrahim ga Isra’ila ta jiki har shekara ta 36 A.Z., Jehobah ya miƙa tagomashi na musamman ga Yahudawa domin zuriyar Ibrahim ne su. Alkawarin da aka yi da Ibrahim ta ci gaba da ci ne a kan “Isra’ila na Allah.”—Galatiyawa 3:7-9, 14-18, 29; 6:16.

Darussa Dominmu:

9:1-23; 10:11. Saboda tawali’unsa, yadda yake bauta wa Allah, nazarin da yake yi, da kuma addu’ar da yake yi a kowane lokaci, duk sun sa Daniel ya zama ‘ƙaunatacce ƙwarai.’ Waɗannan halayen sun taimaka masa ya kasance da aminci ga Allah har ƙarshen rayuwarsa. Bari mu ƙudurta bin misalin Daniel.

9:17-19. Har ma a lokacin da muke yin addu’a game da zuwan sabuwar duniya ta Allah inda “adalci yake zaune,” ya kamata ainihin damuwarmu ta kasance tsarkake sunan Jehobah da kuma kunita ikon mallakarsa maimakon kawo ƙarshen wahalar da muke sha da kuma damuwarmu.—2 Bitrus 3:13.

10:9-11, 18, 19. Ta wajen yin koyi da mala’ikan da ya zo wurin Daniel, ya kamata mu ƙarfafa juna ta wajen taimaka wa juna da kuma faɗin kalamai masu ƙarfafawa.

12:3. A wannan zamani na ƙarshe, “waɗanda ke da hikima,” wato, shafaffun Kiristoci sun ci gaba da ‘haskakawa’ kuma sun jawo mutane “dayawa kuma zuwa adilci,” har da “taro mai-girma” na “waɗansu tumaki.” (Filibbiyawa 2:15; Ru’ya ta Yohanna 7:9; Yohanna 10:16) Shafaffun za su ‘haskaka kamar taurari’ a hanya mai girma a lokacin Sarautar Kristi ta Shekara Dubu sa’ad da suka haɗa hannu da Kristi wajen sa mutane masu biyayya da ke duniya su amfana daga albarkar fansa. Ya kamata “waɗansu tumaki” cikin aminci su haɗa kai da shafaffu, kuma su taimaka masu a kowace hanya da dukan zuciyarsu.

Jehobah Yana Yi Wa ‘Waɗanda Ke Tsoronsa Albarka’

Menene littafin Daniel ya koya mana game da Allahn da muke bautawa? Ka yi la’akari da annabce-annabcen da ke cikinsa, waɗanda suka cika da waɗanda za su cika. Duk sun nuna cewa Jehobah Mai Cika abin da ya ce ne!—Ishaya 55:11.

Menene sashen littafin Daniel da ya faɗi labarai ya nuna game da Allahnmu? Matasa huɗu Ibraniyawa da suka ƙi rayuwar fadar Babila sun sami ‘sani da gwaninta da hikima.’ (Daniel 1:17) Allah na gaskiya ya aika mala’ikansa ya ceci Shadrach, Meshach, da Abednego daga cikin tandun wuta. An ceci Daniel daga cikin kogon zaki. Jehobah yana ‘taimaka’ da kuma kāre waɗanda suka dogara da shi, kuma yana yi wa ‘waɗanda ke tsoronsa albarka.’—Zabura 115:9, 13.

[Hasiya]

a Don tattaunawar aya aya na littafin Daniel, ka duba Pay Attention to Daniel’s Prophecy! Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba