Tambayoyi Daga Masu Karatu
Menene Yesu yake nufi sa’ad da ya ce bawansa mai aminci zai kasance “mai-hikima”?
Yesu ya yi tambaya: “Wanene fa bawan nan mai-aminci, mai-hikima wanda ubangijinsa ya sanya shi bisa iyalin gidansa, domin shi ba su abincinsu a lotonsa?” (Matta 24:45) “Bawan” da zai ba da abinci na ruhaniya shi ne ikilisiyar Kiristoci shafaffu. Me ya sa Yesu ya kira su mai hikima?a
Za mu fi ma fahimtar ma’anar kalmar nan “hikima” daga abin da Yesu ya koyar. Alal misali, sa’ad da ya yi magana game da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima,” Yesu ya ba da almara ce ta budurwoyi goma da suke saurarar zuwan ango. Budurwoyin suna tuna mana da shafaffu Kiristoci kafin shekara ta 1914 da suke sauraron zuwan babban Ango, Yesu Kristi. Tsakanin budurwoyi goman, biyar ba su da isashen mai sa’ad da angon ya iso, saboda haka ba su sami shiga bikin aure ba. Saura biyar ɗin suka kasance masu hikima. Suka kasance da isashen mai saboda su ci gaba da ba da haske sa’ad da angon ya iso kuma aka ƙyale su suka shiga bikin auren.—Matta 25:10-12.
Sa’ad da Yesu ya isa cikin ikonsa na Mulki a shekara ta 1914, da yawa cikin shafaffu Kiristoci suna tsammanin za su tafi sama tare da shi. Amma kuma suna da aiki mai yawa a duniya, kuma wasu ba su yi shiri ba domin wannan. Kamar waɗannan budurwoyi marar hikima, ba su ƙarfafa kansu ba a ruhaniya a kan lokaci, saboda haka ba su da shirin ci gaba da ba da haske. Amma, kuma yawanci sun kasance da hikima, da basira da kuma hangen nesa, kuma sun ƙarfafa a ruhaniya. Sa’ad da suka fahimci cewa da aiki mai yawa a gaba, suka fara aikin da farin ciki domin su gama shi. Saboda haka, suka kasance “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.”
Ka yi kuma la’akari da yadda Yesu ya yi amfani da kalmar nan “mai-hikima” a Matta 7:24. Yesu ya ce: “Kowanene fa mai-jin waɗannan zantatukana, yana kuwa aikata su, za a kwatanta shi da mutum mai-hikima, wanda ya gina gidansa bisa pa.” Mutum mai hikima ya yi gini mai ƙarfi, domin yiwuwar hadari. Akasin haka, wawa kuma ya gina nasa gidan a kan yashi kuma ya yi rashinsa. Saboda haka, mabiyin Yesu mai hikima mutum ne wanda ya kasance mai hangen nesa wanda ke ganin mugun sakamakon bin hikimar mutane. Fahiminsa ya sa ya kafa bangaskiyarsa, ayyukansa, da koyarwarsa bisa abin da Yesu ya koyar. “Bawan nan mai-aminci, mai-hikima” haka yake yi.
Ka kuma lura da yadda aka yi amfani da kalmar nan “mai-hikima” a fassara dabam dabam na Nassosin Ibrananci. Alal misali, Fir’auna ya naɗa Yusufu shugaba bisa abinci a Masar. Wannan ɓangare ne na tsarin Jehobah domin ya yi tanadin abinci ga mutanensa. Me ya sa aka zaɓi Yusufu? Fir’auna ya ce masa: ‘Babu wani mai-basira mai-hakima kamarka.’ (Farawa 41:33-39; 45:5) Hakazalika, Littafi Mai Tsarki ya ce Abigail “mai-fahimi ce.” Ta yi tanadin abinci ga shafaffe na Jehobah, Dauda da kuma mutanensa. (1 Samuila 25:3, 11, 18) Yusufu da Abigail ana iya kiransu masu hikima domin sun fahimci nufin Allah kuma sun yi amfani da fahiminsu.
Saboda haka, sa’ad da Yesu ya kwatanta bawa mai-aminci, cewa mai-hikima ne, yana nufi ne cewa waɗanda suke wakiltar bawan nan za su nuna hikima, da fahimi domin sun kafa bangaskiyarsu da ayyukansu da kuma koyarwarsu bisa Kalmar Allah ta gaskiya.
[Hasiya]
a “Mai-hikima” fassara ce ta kalmar Hellenanci phroʹni·mos. In ji littafin nan Word Studies in the New Testament, na M. R. Vincent, ya ce wannan kalmar da ake amfani da ita sosai tana nufin basira da kuma hankali.