Ceto Daga Tarkunan Mai Farauta
“[Jehobah] za ya fishe ka daga tarkon mai-farauta.”—ZABURA 91:3.
1. Wanene “mai-farauta,” kuma me ya sa yake da haɗari?
DUKA Kiristoci na gaskiya suna fama da wani mafarauci wanda yake da fahimi da kuma wayo fiye da mutane. Zabura 91:3 ta kira shi “mai-farauta.” Wanene wannan maƙiyin? Tun fitowa na 1 ga Yuni, a shekara ta 1883, wannan jaridar ta bayyana cewa Shaiɗan Iblis ne. Kamar yadda mafarauci yake kafa tarko don ya kama tsuntsu, wannan mugun maƙiyin cikin dabara yana ƙoƙarin ya yaudari kuma ya kama mutanen Jehobah.
2. Me ya sa aka kwatanta Shaiɗan da mafarauci?
2 A zamanin dā, ana kama tsuntsaye ne domin kukansu mai daɗi, kyaun gashinsu, don a ci su da kuma yin hadaya. Amma, tsuntsaye halittu ne da ke mai da hankali sosai, kuma suna da wuyan kamawa. Saboda haka, mafarauci a lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki ya kan yi nazarin halayen irin tsuntsayen da yake son ya kama. Bayan haka, sai ya nemi dabarar yadda zai kama su. Ta wajen kamanta Shaiɗan da mafarauci, Littafi Mai Tsarki ya taimaka mana mu fahimci dabarunsa. Iblis yana yin nazarin halayen kowanenmu. Yana lura da halayenmu kuma ya kafa ɓoyayyun tarkuna don ya kama mu a raye. (2 Timothawus 2:26) Idan Shaiɗan ya kama mu, hakan zai lalata dangantakarmu da Allah kuma muna iya halaka har abada. Saboda haka, don mu sami kāriya, muna bukatar mu san dabaru dabam dabam na “mai-farauta.”
3, 4. A wane lokaci ne dabarun Shaiɗan suke kama da na zaki? da kumurci?
3 Ta hanyar kwatanci, mai zabura ya kwatanta dabarun Shaiɗan da na yaran zaki ko na kumurci. (Zabura 91:13) Kamar zaki, a wasu lokatai Shaiɗan yana kai hari na kai tsaye a kan mutanen Jehobah ta hanyar tsanantawa ko kuwa kafa dokar da za ta shafe su. (Zabura 94:20) Irin waɗannan hare-haren na kai tsaye suna iya sa wasu su daina bauta wa Jehobah. A yawancin lokaci kuwa, irin waɗannan hare-haren na kai tsaye suna kawo sakamako mai kyau domin suna haɗa kan mutanen Allah. Amma, dabarun Shaiɗan da suke kama da harin kumurci fa?
4 Iblis yana yin amfani da irin wayon da ya ɗara na mutane wajen yin yaudara da kuma kai mugun hare-hare kamar kumurci. Ta wannan hanyar, ya yi nasara wajen gurɓata tunanin wasu mutanen Allah, ya yaudare su su yi nufinsa maimakon na Jehobah, kuma sakamakon hakan ba shi da kyau. Abin farin ciki shi ne mun san makidodin Shaiɗan. (2 Korinthiyawa 2:11) Bari yanzu mu tattauna tarkuna masu haɗari guda huɗu da “mai farauta” yake amfani da su.
Jin Tsoron Mutum
5. Me ya sa tarkon “tsoron mutum” yake aiki sosai?
5 “Mai-farauta” ya san bukatunmu na son karɓuwa da amincewar mutane. Kiristoci ba sa nuna halin ko in kula ga tunanin mutane da kuma yadda waɗanda suke kewaye da su suke ji. Domin haka, Iblis zai so ya yi amfani da damuwarsu na yadda mutane suke ɗaukansu. Alal misali, yana kama wasu mutanen Allah ta wajen yin amfani da tarkon “tsoron mutum.” (Misalai 29:25) Idan domin jin tsoron mutum bayin Allah suka haɗa kai da wasu wajen yin abin da Jehobah ya hana ko kuwa suka ƙi yin abin da Kalmar Allah ta ce su yi, to sun riga sun faɗa cikin tarkon “mai-farauta.”—Ezekiel 33:8; Yaƙub 4:17.
6. Wane misali ne ya kwatanta yadda matashi ke iya faɗawa tarkon “mai-farauta”?
6 Alal misali, matashi yana iya faɗa wa matsi daga abokansa a makaranta kuma ya sha taba. Wataƙila bai taɓa tunanin cewa zai sha taɓa ba sa’ad da ya tafi makaranta. Ba da daɗewa ba, ya soma yin abin da zai shafi lafiyarsa da kuma abin da Allah ba ya so. (2 Korinthiyawa 7:1) Ta yaya aka jaraba shi? Wataƙila ya soma tarayya ne da abokan banza kuma ba ya son ya ɓata musu rai. Matasa, kada ku yarda “mai farauta” ya yi maku wayo kuma ku faɗa tarkonsa! Don kada ya kama ku a raye, ku mai da hankali ga faɗuwa a ƙananan abubuwa. Ku bi gargaɗin Littafi Mai Tsarki da ya ce ku guji abota marar kyau.—1 Korinthiyawa 15:33.
7. Ta yaya ne Shaiɗan zai iya sa wasu iyaye su yi rashin ruhaniyarsu?
7 Iyaye Kiristoci suna ƙoƙartawa sosai wajen cika hakkinsu da aka ambata a cikin Nassi na yi wa iyalansu tanadi. (1 Timothawus 5:8) Amma, abin da Shaiɗan yake so shi ne Kiristoci su mai da hankalinsu ga yin tanadin abubuwan duniya da suke bukata. Wataƙila ba sa samun damar zuwa taro a kai a kai domin sun faɗawa matsin shugaban aikinsu na yin ƙarin aiki. Suna iya jin tsoro su ce a ba su damar halartar duka sashen taron gunduma don bauta wa Jehobah tare da ’yan’uwansu. Abin da zai kāre mutum daga wannan tarkon shi ne “dogara ga Ubangiji.” (Misalai 3:5, 6) Bugu da ƙari, idan muka tuna cewa muna cikin iyalin Jehobah kuma ya ɗaura wa kansa nauyin kula da mu, hakan zai taimaka mana mu kasance da daidaita. Iyaye, kun yi imani cewa Jehobah zai kula da ku da iyalinku idan kuka yi nufinsa? Ko kuwa, Iblis zai kama ku a raye kuma ya sa ku yi nufinsa domin kuna jin tsoron mutum? Muna roƙonku ku yi addu’a kafin ku yi tunani a kan waɗannan tambayoyin.
Tarkon Neman Abin Duniya
8. Ta wace hanya ce Shaiɗan yake amfani da neman abin duniya?
8 Shaiɗan kuma yana yin amfani da abin duniya don ya kama mu a tarkonsa. Tsarin kasuwanci na wannan duniyar yana ɗaukaka hanyoyin yin kuɗi dare ɗaya wanda ke iya yaudarar wasu cikin mutanen Allah. A wasu lokatai, ana iya ariritar mutum: “Ka yi aiki sosai. A lokacin da ka yi kuɗi, kana iya hutawa kuma ka ji daɗin rayuwarka. Kana ma iya zama majagaba.” Irin waɗannan kalaman na iya zama tunani marar kyau na wasu da suke son su ci cikin arzikin ’yan’uwansu Kiristoci a cikin ikilisiya. Ka yi tunani sosai game da irin wannan shawarar. Irin wannan tunanin ya yi daidai da na “wawa” mai arziki na almarar Yesu ne?—Luka 12:16-21.
9. Me ya sa wasu Kiristoci suke iya faɗawa tarko ta wajen son abubuwa?
9 Shaiɗan yana tafiyar da wannan duniyar tasa a hanyar da ke sa mutane su yi sha’awar abubuwa. Wannan sha’awar tana iya shafar rayuwar Kirista a hanya marar kyau, tana iya sarƙe kalmar kuma ta “zama mara-amfani.” (Markus 4:19) Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu dangana da abinci da sutura. (1 Timothawus 6:8) Amma, yawanci sun faɗa tarkon “mai-farauta” domin sun ƙi bin wannan shawarar. Ɗaga kai ne ya sa suke ganin cewa suna bukatar su manne wa wani irin salon rayuwa? Mu kuma fa? Muradinmu na son tara abubuwa ya sa mun mai da abubuwan da suka shafi bauta ta gaskiya gefe ɗaya? (Haggai 1:2-8) Abin baƙin ciki, a lokacin da abubuwa suka yi wuya, waɗansu sun sadaukar da ruhaniyarsu domin su manne wa irin rayuwar da suka saba da ita. Irin wannan hali na tara abin duniya yana faranta wa “mai-farauta” rai!
Tarkon Nishaɗi Marar Kyau
10. Wane irin bincika kai ne ya kamata kowane Kirista ya yi?
10 Wata dabarar “mai-farauta” ita ce ɓata tunanin mutane na abin da ke da kyau da marar kyau. Masana’antun nishaɗi sun cika da irin tunani na mutanen Saduma da Gwamrata. Har ma labarai da ake nuna wa a kan talabijin da kuma jaridu suna nuna mugunta da kuma gamsar da sha’awar lalata. Yawancin abubuwan da ake nunawa don nishaɗi a kafofin labarai suna hana mutane su ‘rabe nagarta da mugunta.’ (Ibraniyawa 5:14) Amma ka tuna kalaman da Jehobah ya faɗa ta bakin annabi Ishaya: “Kaiton waɗannan da ke ce da mugunta nagarta; nagarta kuma mugunta.” (Ishaya 5:20) “Mai-farauta” ya shafi tunaninka da irin waɗannan nishaɗin marar kyau? Bincika kai yana da muhimmanci.—2 Korinthiyawa 13:5.
11. Wane gargaɗi ne wannan jaridar ta yi game da wasan kwaikwayon da ake nunawa a talabijin?
11 Kusan shekaru 25 da suka shige, cikin ƙauna Hasumiyar Tsaro ta gargaɗi masu bauta wa Allah na gaskiya game da wasan kwaikwayon da ake nunawa a talabijin.a An yi waɗannan kalaman da ke gaba game da yadda wasannin kwaikwaiyo da ake nunawa a talabijin suke shafan mutane cikin wayo: “Ana amfani da soyayya wajen ba da hujjar kowane irin hali. Alal misali, wata yarinya da ta yi cikin shege ta gaya wa kawarta cewa: ‘Ina son Victor. Ban damu ba. . . . Haifar masa ɗa shi ne abin da ya fi muhimmanci a gare ni!’ Ɗan sautin da ke tashi ya ɗauke hankalin mutane daga tafarki marar kyau da ta bi. Kai ma ka ji kana son Victor. Kuma ka ji tausayin yarinyar. Ka amince da tafarkin lalatar da suka bi. Wata da take kallon irin waɗannan wasannin a dā amma a yanzu ta dawo cikin hankalinta ta ce: ‘Babu wata hujjar da za ka iya ba da wa. Mun san cewa lalata ba ta da kyau. Amma sai na fahimci cewa a tunanina ina goyon bayan masu yin lalata.’”
12. Waɗanne batutuwa na gaskiya ne suka tabbatar da dacewar gargaɗin da aka yi game da wasu wasannin talabijin?
12 Tun lokacin da aka wallafa waɗannan talifofin, irin waɗannan wasannin marar kyau sai ƙaruwa suke yi. A wasu wurare, ana nuna waɗannan wasannin a awoyi 24 a rana. Maza da mata, da matasa da yawa suna cika zuciyarsu da waɗannan wasannin. Amma, kada mu yaudari kanmu da tunanin ƙarya. Ba zai dace ba idan muka yi tunanin cewa nishaɗin da ke gabatar da lalata ba zai shafe mu ba kamar wanda ake gani ido da ido. Kirista zai iya ba da hujjar zaɓan kallon wasannin irin mutanen da ba zai taɓa mafarkin gayyata zuwa cikin gidansa ba?
13, 14. Menene wasu suka ce game da yadda suka amfana daga gargaɗin da aka yi game da wasannin talabijin?
13 Yawanci sun amfana sa’ad da suka bi wannan gargaɗin da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ya yi. (Matta 24:45-47) Bayan sun karanta gargaɗi na kai tsaye da aka yi daga cikin Littafi Mai Tsarki, wasu sun rubuto wasiƙa don su faɗi yadda talifofin suka shafe su.b Wata a cikinsu ta ce: “Na yi shekara 13 ina mugun son waɗannan wasanni na talabijin. Na yi tunanin cewa babu abin da zai same ni domin ina halartar taron Kirista kuma ina zuwa hidimar fage a wasu lokatai. Amma, na bi wani irin hali da aka nuna a cikin wannan wasan cewa idan mijinki ya ƙi kula da ke ko kuwa idan ki ka ga cewa ba ya ƙaunarki, kina iya yin kwartanci, domin shi ke da laifi. Saboda haka, sa’ad da na ga cewa ina da ‘hujja’ sai na bi wannan mugun tafarkin kuma na yi zunubi ga Jehobah da kuma mijina.” An yi wa wannan matar yankan zumunci. Daga baya, ta dawo cikin hankalinta, ta tuba, kuma aka maido da ita. Talifofin da suka yi gargaɗi game da wasannin kwaikwayo da ake nunawa a cikin talabijin sun ƙarfafata ta guje wa kallon abin da Jehobah ya ƙi.—Amos 5:14, 15.
14 Wani mai karatu wanda kallon wasannin ya shafi rayuwarsa ya ce: “Na yi kuka sa’ad da na karanta waɗannan talifofin, domin na gane cewa ba ni da dangantaka mai kyau da Jehobah. Na yi wa Allahna alkawari cewa ba zan ƙara zama bawan waɗannan wasannin ba.” Bayan ta furta godiyarta domin waɗannan talifofin, wata mata Kirista ta faɗi yadda take mugun son wasannin kuma ta rubuta: “Na yi mamaki . . . idan hakan zai iya shafan dangantakata da Jehobah. Ta yaya zan yi abota da ‘su’ kuma na yi abota da Jehobah?” Idan irin waɗannan wasanni na talabijin suna ɓata tunanin mutum shekaru 25 da suka shige, wane irin tasiri ne suke da shi a yau? (2 Timothawus 3:13) Dole ne mu mai da hankali da tarkon Shaiɗan na duka ire-iren nishaɗi marar kyau, wato, wasannin kwaikwayo na talabijin, wasannin bidiyo na mugunta, ko kuwa waƙoƙin bidiyo na lalata.
Tarkon Samun Saɓani
15. Ta yaya ne Iblis ya kama wasu a raye?
15 Shaiɗan yana yin amfani da saɓani a matsayin tarko don ya jawo rarrabuwa tsakanin mutanen Jehobah. Muna iya faɗa wa wannan tarkon ko da wane irin gata na hidima ne muke da shi. Iblis ya kama wasu a raye domin sun ƙyale saɓani ya shafi salama da haɗin kai na ruhaniya mai ni’ima da Jehobah ya bayar.—Zabura 133:1-3.
16. Ta yaya ne Shaiɗan yake ƙoƙarin ya ɓata haɗin kanmu cikin dabara?
16 A lokacin Yaƙin Duniya na ɗaya, Shaiɗan ya yi ƙoƙarin ya halakar da sashen ƙungiyar Jehobah ta duniya ta wajen hari na kai tsaye, amma bai yi nasara ba. (Ru’ya ta Yohanna 11:7-13) Tun wannan lokacin, yana ta yin dabaru don ya ɓata haɗin kanmu. Idan muka ƙyale saɓani ya jawo rashin haɗin kai, mun riga mun ba “mai-farauta” dama ke nan. Da haka, muna iya hana ruhu mai tsarki ya yi aiki a rayuwarmu da kuma a ikilisiya. Idan hakan ya faru, Shaiɗan zai yi farin ciki domin idan babu salama da haɗin kai a cikin ikilisiya hakan zai shafi aikin wa’azi.—Afisawa 4:27, 30-32.
17. Menene zai taimaka wa waɗanda suka saɓa da juna don su magance ta?
17 Menene ya kamata ka yi idan ka saɓa da ɗan’uwa Kirista? Gaskiyar ita ce, yanayi ya bambanta. Amma, ko da yake za a iya samun dalilai masu yawa da za su iya jawo saɓani, babu wani dalilin da zai sa a ƙi warware saɓawa. (Matta 5:23, 24; 18:15-17) Shawarar da ke cikin Littafi Mai Tsarki hurarriya ce, kuma kamiltacciya. Idan muka yi amfani da mizanai na Littafi Mai Tsarki, ba za mu yi da na sani ba. Suna kawo sakamako mai kyau a kowane lokaci!
18. Me ya sa koyi da Jehobah zai taimaka mana mu warware saɓani?
18 Jehobah “mai-hanzarin gafartawa” ne, kuma yana yin “gafara.” (Zabura 86:5; 130:4) Za mu nuna cewa mu ƙaunatattun yaran Jehobah ne idan muka yi koyi da shi. (Afisawa 5:1) Mu duka masu zunubi ne kuma muna son Jehobah ya gafarta mana. Saboda haka, dole ne mu mai da hankali idan muka ji cewa ba ma son mu gafarta wa wani. Muna iya zama kamar bawan nan na cikin almarar Yesu wanda ya ƙi yafe ɗan mitsitsin bashin da bawa kamarsa ya ci idan aka haɗa da bashin da shugabansa ya riga ya yafe masa. Sa’ad da aka sanar da shugabansa, ya sa an jefa bawan nan wanda ba ya gafartawa a cikin kurkuku. Yesu ya kammala almararsa da cewa: “Hakanan kuma Ubana na sama za ya yi muku, idan cikin zuciyarku ba ku gafarta ma ’yan’uwanku.” (Matta 18:21-35) Yin bimbini a kan wannan kwatancin da kuma yin tunani a kan yawan lokacin da Jehobah ya riga ya gafarta mana zai taimaka mana a lokacin da muke son mu warware saɓani da muka samu da ’yan’uwanmu!—Zabura 19:14.
Kāriya a “Cikin Sitirar Maɗaukaki”
19, 20. Yaya ya kamata mu ɗauki “sitirar” da kuma “inuwar” Jehobah a wannan mugun lokacin?
19 Muna zaune ne a mugun lokaci. Da Shaiɗan ya riga ya halakar da dukanmu inda ba don kāriyar Jehobah ba. Don guje wa faɗawa cikin tarkon “mai-farauta,” dole ne mu zauna a wurin kāriya ta alama, wato, “zama cikin sitirar Maɗaukaki,” samun “dawwama a ƙarƙashin inuwar mai-iko duka.”—Zabura 91:1.
20 Bari mu ci gaba da ɗaukan tunasarwa da kuma ja-gorar da Jehobah yake yi a matsayin kāriya, ba hani ba. Mu duka muna fuskantar mafaraucin da ya fi mutane wayo. Idan ba taimakon da Jehobah yake bayarwa cikin ƙauna ba, babu wanda zai iya guje wa wannan tarkon. (Zabura 124:7, 8) Saboda haka, bari mu yi addu’a cewa Jehobah ya kāre mu daga tarkunan “mai-farauta.”—Matta 6:13.
[Hasiya]
a Hasumiyar Tsaro, 1 ga Disamba, 1982, shafuffuka na 3-7.
b Hasumiyar Tsaro, ta 1 ga Disamba, 1983, shafi na 23.
Ka Tuna?
• Me ya sa “tsoron mutum” mugun tarko ne?
• Ta yaya ne Iblis yake amfani da son abin duniya?
• Ta yaya ne Shaiɗan ya jefa wasu cikin tarkon nishaɗi marar kyau?
• Wane tarko ne Iblis yake amfani da shi don ya ɓata haɗin kanmu?
[Hoto a shafi na 27]
Wasu sun faɗa tarkon “tsoron mutum”
[Hoto a shafi na 28]
Kana jin daɗin abin da Jehobah ya ƙi?
[Hoto a shafi na 29]
Menene za ka yi idan ka saɓa da ɗan’uwa Kirista?