Maganar Jehobah Rayayya Ce
Darussa Daga Littattafan Nahum, Habakkuk, da Zephaniah
ƘASAR Assuriya wadda ita ce ƙasa mafi iko a duniya ta riga ta halaka Samariya, babban birnin masarautar ƙabilu goma na Isra’ila. Assuriya ta daɗe tana yi wa Yahuda barazana. Amma annabi Nahum Bayahude yana da saƙo game da babban birnin Assuriya, wato, Nineveh. An rubuta littafin Nahum na Littafi Mai Tsarki wanda ke ɗauke da wannan saƙon kafin shekara ta 632 K.Z.
Ƙasa mafi iko a duniya da ta sake tasowa ita ce Daular Babila, wadda a wani zubin sarakuna ’yan Kaldiya ne suka yi mulki. Littafin Habakkuk, wanda wataƙila an kammala shi a shekara ta 628 K.Z., ya annabta yadda Jehobah zai yi amfani da wannan ƙasa mafi iko wajen zartar da hukunci da kuma abin da zai sami Babila.
Annabi Zephaniah Bayahude ya yi nasa annabcin kafin Nahum da Habakkuk. A annabcinsa na shekara 40 da ya yi kafin a halaka Urushalima a shekara ta 607 K.Z., ya faɗi saƙon halaka da kuma bege ga Yahuda. Littafin Zephaniah da ke cikin Littafi Mai Tsarki ya kuma ƙunshi saƙon hukunci a kan sauran al’ummai.
“KAITON BIRNI MAI-JINI”
(Nahum 1:1–3:19)
Jehobah Allah wanda “mai-jinkirin fushi ne, mai-girma ne cikin iko” ya yi “jawabi . . . a kan Nineveh.” Za a halakar da Nineveh, duk da cewa Jehobah “kagara ne cikin ranar wahala” ga waɗanda suke neman mafaka a wurinsa.—Nahum 1:1, 3, 7.
“Ubangiji [zai] komo da darajar Yaƙub.” Kamar ‘zakin da yake yayyage abin da ya isa,’ Assuriya ta tsananta wa mutanen Allah. Jehobah zai ‘ƙone karusan [Nineveh] cikin hayaƙi; takobi kuma za ya ci yan zakin [Nineveh].’ (Nahum 2:2, 12, 13) “Kaiton birni mai-jini,” wato, Nineveh. ‘Dukan waɗanda suke jin labarinta za su yi tāfi’ da farin ciki.—Nahum 3:1, 19.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
1:9—Menene ‘tuƙewa sarai’ da za a yi wa Nineveh ke nufi ga Yahudawa? Hakan na nufin samun hutu na dindindin daga wahalar Assuriya; “wahala ba za ta taso so biyu ba.” Sa’ad da yake magana kamar an riga an halaka Nineveh, Nahum ya rubuta: “Duba, a bisa duwatsu ga sawayen mai-kawo bishara, mai-shelar salama! Ka kiyaye idodinka, ya Yahuda.”—Nahum 1:15.
2:6—Waɗanne “ƙofofin koguna” ne aka buɗe? Waɗannan ƙofofin suna nufin hanyar da ruwan rafin Tigris ta yi a jikin bangwayen Nineveh. Sa’ad da sojojin haɗin gwiwa na Babila da Midiya suka kai wa Nineveh hari a shekara ta 632 K.Z., hakan bai tsorata ta ba. Domin manyan bangwayenta, tana ganin cewa babu wanda zai iya shiga birnin. Amma, ruwan sama mai yawa ya sa rafin Tigris ya yi ambaliya. In ji ɗan tarihi Diodorus, ruwan “ya cika birnin kuma ya rushe bangwayen sosai.” Da haka, ƙofofin ruwan suka buɗe, kuma kamar yadda aka annabta, an kame Nineveh kamar yadda wuta take cin busasshiyar kara.—Nahum 1:8-10.
3:4—Ta yaya ne Nineveh ta zama kamar karuwa? Nineveh ta ruɗi al’ummai ta wajen yi masu alkawarin cewa za ta zama ƙawarsu kuma za ta taimaka musu, amma a zahiri tana ɗora musu wahala ne kawai. Alal misali, Assuriya ta ɗan taimaka wa Ahaz, Sarkin Yahuda sa’ad da Isra’ila da Suriya suka ƙulla mata maƙarƙashiya. Daga baya, ‘sarkin Assuriya ya zo wurin [Ahaz], ya kuwa wahalshe shi.’—2 Labarbaru 28:20.
Darussa Dominmu:
1:2-6. Matakin da Jehobah ya ɗauka a kan maƙiyansa da suka ƙi su bauta masa, ya nuna cewa yana son a bauta masa shi kaɗai.—Fitowa 20:5.
1:10. Manyan bangwaye da ɗarurruwan hasumiyoyi ba su hana kalmar Jehobah game da Nineveh cika ba. Maƙiyan mutanen Jehobah a yau ba za su iya guje wa hukuncin Allah ba.—Misalai 2:22; Daniel 2:44.
‘ADALI ZAI CI GABA DA RAYUWA’
(Habakkuk 1:1–3:19)
Surori biyu na farko na littafin Habakkuk suna ɗauke ne da tattaunawar da annabin ya yi da Jehobah Allah. Domin yana baƙin ciki game da abin da ke faruwa a Yahuda, Habakkuk ya tambayi Allah: “Don me ka ke nuna mini saɓo, ka sa ni in duba shiririta kuma?” Sai Jehobah ya amsa ya ce: “Ina tada Chaldiyawa, wannan al’umma mai-zafin rai.” Annabin ya yi mamakin cewa Allah zai yi amfani da “masu-cin amana” su hukunta Yahuda. (Habakkuk 1:3, 6, 13) Jehobah ya tabbatar wa Habakkuk cewa masu aminci za su ci gaba da rayuwa, amma maƙiyansa ba za su iya guje wa hukuncinsa ba. Bugu da ƙari, Habakkuk ya rubuta kaito guda biyar da za su faɗa wa Kaldiyawa.—Habakkuk 2:4.
A addu’ar da ya yi ta tausayi, Habakkuk ya ‘raira’ waƙar baƙin ciki kuma ya ambata yadda Jehobah ya nuna ƙarfinsa a dā a Jar Teku, a cikin jeji, da kuma Jericho. Annabin ya kuma annabta yadda Jehobah zai nuna fushinsa kuma ya halaka mugaye a Armageddon. Addu’ar ta kammala da waɗannan kalaman: “Jehovah, Ubangiji, shi ne ƙarfina, Yana maida sawayena kamar na bareyi, Za ya sa ni in riƙa tafiya bisa maɗaukakan wurarena.”—Habakkuk 3:1, 19.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
1:5, 6—Me ya sa Yahudawa ba su taɓa zaton cewa za a ta da Kaldiyawa bisa Urushalima ba? A lokacin da Habakkuk ya soma annabcinsa, Yahuda yana ƙarƙashin tasirin ƙasar Masar. (2 Sarakuna 23:29, 30, 34) Ko da yake Babiloniyawa suna cin gaba da samun ƙarfi, duk da haka, sojojinta ba su taɓa cin nasara bisa Fir’auna Neko ba. (Irmiya 46:2) Bugu da ƙari, haikalin Jehobah yana Urushalima, kuma zuriyar Dauda ne ke mulki. Shi ya sa Yahudawa a lokacin, ba su taɓa tunanin cewa Allah cikin ‘aikinsa’ zai ƙyale Kaldiyawa su halaka Urushalima ba. Duk da cewa ba su yarda da maganar Habakkuk ba, wahayin nan cewa Babiloniyawa za su halaka Urushalima “ta zo” a shekara ta 607 K.Z.—Habakkuk 2:3.
Darussa Dominmu:
1:1-4; 1:12–2:1. Habakkuk ya yi tambayoyi masu kyau, kuma Jehobah ya amsa masa. Allah na gaskiya yana sauraron addu’o’in bayinsa masu aminci.
2:1. Kamar Habakkuk, ya kamata mu kasance a faɗake a ruhaniya kuma mu ci gaba da yin hidimar Jehobah. Kuma muna bukatar mu daidaita tunaninmu cikin jituwa da [“gyaran”; NW] da aka yi mana.
2:3; 3:16. Yayin da muke jiran ranar Jehobah cikin bangaskiya, bari mu kasance da azancin gaggawa.
2:4. Idan muna son mu tsira a ranar hukuncin Jehobah, dole ne mu jimre cikin aminci.—Ibraniyawa 10:36-38.
2:6, 7, 9, 12, 15, 19. Kaito zai faɗa wa masu cin riba marar kyau, masu son mugunta, yin lalata, ko kuwa bauta wa gumaka. Muna bukatar mu kasance a faɗake don mu guje wa waɗannan halayen da ayyuka.
2:11. Idan muka ƙi fallasa muguntar wannan duniyar, “dutse za ya tada murya.” Yana da muhimmanci mu ci gaba da yin wa’azin Mulki da gaba gaɗi!
3:6. Babu abin da zai hana Jehobah ya zartar da hukuncinsa, har da ma ƙungiyoyin mutane waɗanda suke kama da manyan duwatsu da tsaunuka.
3:13. Muna da tabbaci cewa halaka a Armageddon ba zai kasance marar tsari ba. Jehobah zai ceci bayinsa masu aminci.
3:17-19. Ko da yake muna iya shan wahala kafin da kuma lokacin Armageddon, muna da tabbaci cewa Jehobah zai ba mu ‘ƙarfi’ yayin da muka ci gaba da bauta masa cikin farin ciki.
“RANAR UBANGIJI TA KUSA”
(Zephaniah 1:1–3:20)
Bautar Baal ta zama ruwan dare a Yahuda. Jehobah ya ce ta bakin annabinsa Zephaniah: “Zan miƙa hannuna kuma a bisa Yahuda, da bisa dukan mazaunan Urushalima.” Zephaniah ya yi gargaɗi: “Ranar Ubangiji ta kusa.” (Zephaniah 1:4, 7, 14) Waɗanda suke cika farillan Allah kaɗai ne za a “ɓoye” a wannan ranar.—Zephaniah 2:3.
“Kaiton . . . birni mawulakanciya,” wato, Urushalima! “In ji Ubangiji, ku dakanta mani, har randa zan tashi a kan ganiman; gama ƙudurina ke nan, in tattara al’ummai, domin . . . in zuba masu fushina.” Amma Allah ya yi alkawari: “Zan maishe ku suna, abin yabo kuma, a cikin dukan al’umman duniya, sa’anda na dawo da ku daga bauta a gaban idanunku.”—Zephaniah 3:1, 8, 20.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
2:13, 14—Wanene ‘muryarsa za ta rera’ waƙa a cikin Nineveh da aka halaka? Tun da Nineveh za ta zama inda manyan dabbobi da tsuntsaye za su zauna, muryar da za ta ci gaba da rera waƙa tana nufin kukan tsuntsu da kuma wataƙila ƙarar iskan da ke bin tagogin gidajen da babu kowa.
3:9—Menene “harshe mai-tsarki,” kuma yaya ake yin sa? Gaskiyar Allah ce da take cikin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Ya ƙunshi dukan koyarwa na Littafi Mai Tsarki. Muna yin sa ne ta wajen yin imani da gaskiya, koya wa mutane harshen yadda ya kamata, da kuma yin rayuwar da ta jitu da nufin Allah.
Darussa Dominmu:
1:8. Wasu a zamanin Zephaniah sun nemi amincewar al’umman da suka kewaye su ta wajen “yafe . . . tufafin baƙi.” Zai zama wawanci ga masu bauta wa Jehobah a yau su bi duniya a wannan hanyar!
1:12; 3:5, 16. Jehobah ya ci gaba da aika annabawansa su gargaɗi mutanensa game da hukuncinsa. Ya yi hakan duk da cewa, kamar diddigar da ta kwanta luɓus a ƙasan kwalbar inabi, yawancin Yahudawa suna ta annashuwa ne kuma sun ƙi su saurari saƙonsa. Yayin da ranar Jehobah take kusatowa, maimakon mu ƙyale halin ko in kula da mutane suke nunawa ya sa mu “yi kasala,” muna bukatar mu ci gaba da sanar da saƙon Mulki babu ja da baya.
2:3. Jehobah kaɗai ne zai iya cetonmu a ranar hukuncinsa. Don mu ci gaba da more dangantaka mai kyau da shi, muna bukatar mu “biɗi Ubangiji” ta wajen yin nazarin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki sosai, mu roƙe shi ya yi mana ja-gora, kuma mu kusance shi. Muna bukatar mu “biɗi adilci” ta wajen kasancewa da ɗabi’a mai tsabta. Kuma muna bukatar mu “biɗi tawali’u” ta wajen kasancewa masu sauƙin kai da biyayya.
2:4-15; 3:1-5. A ranar hukuncin Jehobah, ƙarshen Kiristendom da kuma dukan al’umman da suka zalunci mutanen Allah zai zama kamar na Urushalima da al’umman da suka kewaye ta. (Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16; 18:4-8) Muna bukatar mu ci gaba da sanar da hukuncin Allah babu tsoro.
3:8, 9. Yayin da muke jiran ranar Jehobah, muna shirin tsira ta wajen koyan “harshe mai-tsarki” da kuma ‘kiran sunan Allah’ ta wajen keɓe kanmu a gare shi. Muna kuma bauta wa Jehobah da “zuciya ɗaya” tare da mutanensa kuma muna miƙa masa “hadaya ta yabo.”—Ibraniyawa 13:15.
“Tana Kuwa Gaggabta Ƙwarai”
Mai zabura ya raira: “In an jima kaɗan, sa’annan mai-mugunta ba shi: hakika, da anniya za ka duba wurin zamansa, ba kuwa za ya kasance ba.” (Zabura 37:10) Sa’ad da muka yi tunani a kan abin da aka annabta game da Nineveh a cikin littafin Nahum da kuma game da Babila da Yahudawan da suka yi ridda a cikin littafin Habakkuk, muna da tabbaci cewa abin da mai zabura ya ce zai cika. Amma, har wane lokaci ne za mu ci gaba da jira?
“Babbar ranar Ubangiji ta kusa,” in ji Zephaniah 1:14. “Kurkusa ce, tana kuwa gaggabta ƙwarai.” Littafin Zephaniah ya kuma nuna mana yadda za mu tsira a wannan ranar da kuma abin da muke bukatar mu yi yanzu don mu tsira. Babu shakka, “maganar Allah mai-rai ce, mai-aikatawa.”—Ibraniyawa 4:12.
[Hotuna a shafi na 12]
Manyan bangwayen Nineveh ba su hana annabcin Nahum cika ba
[Inda aka Dauko]
Randy Olson/National Geographic Image Collection