Yaushe Mulkin Allah Zai Zo?
“UBANGIJI, a wannan lokaci ne ka ke mayar ma Isra’ila da mulki?” (Ayukan Manzanni 1:6) Manzannin suna so su san lokacin da Yesu zai kafa Mulkinsa. A yau, bayan shekara 2,000, mutane har ila suna so su sani: Yaushe Mulkin Allah zai zo?
Da yake Mulkin Allah shi ne jigon wa’azin Yesu, za ka yi tsammanin zai amsa wannan tambayar. Hakika ya yi haka! Ya yi magana sosai game da lokaci mai alamu da ya kira ‘bayyanuwarsa.’ (Matta 24:37) Wannan bayyanuwar tana da alaƙa da kahuwar Mulkin Almasihu. Menene wannan bayyanuwar? Bari mu dubi gaskiya huɗu da Littafi Mai Tsarki ya bayyana game da bayyanuwar Kristi.
1. Kristi zai bayyana ne bayan ya mutu da shekaru masu yawa. Yesu ya yi wani kwatanci wanda a ciki ya kwatanta kansa da wani mutumin da “ya tafi cikin wata ƙasa mai-nisa garin ya samo mulki.” (Luka 19:12) Ta yaya wannan kwatanci na annabci ya cika? Yesu ya mutu kuma aka tashe shi daga matattu; sai ya yi tafiya zuwa wata “ƙasa mai-nisa,” wato, sama. Kamar yadda Yesu ya faɗa a wani irin wannan kwatanci, bayyanuwarsa cikin ikon sarauta za ta faru ne “bayan da aka jima.”—Matta 25:19.
Wasu shekaru bayan Yesu ya koma sama, manzo Bulus ya rubuta: “[Yesu] ya miƙa hadaya guda ɗaya domin zunubai har abada, ya zauna ga hannun dama na Allah; daga nan gaba yana tsumayi har an mayarda maƙiyansa matashin sawayensa.” (Ibraniyawa 10:12, 13) Sa’ad da Yesu ya koma sama ya yi jira na dogon lokaci. Jiran a ƙarshe ya ƙare sa’ad da Jehobah Allah ya naɗa Ɗansa Sarkin Mulkin Almasihu da aka yi alkawarinsa da daɗewa. A wannan lokacin ne Kristi ya fara bayyanuwa. Mutane a duniya za su ga wannan abin ban sha’awa ne?
2. Bayyanuwar ba za a iya gani da idanu ba. Ka tuna Yesu ya yi bayani game da alamun bayyanuwarsa. (Matta 24:3) Idan mutane za su ga bayyanuwarsa, za su bukaci alamu ne? Alal misali: A ce ka yi tafiya domin ka ga teku. Za ka ga alamu a kan hanya suna nuna maka hanya, amma da zarar ka isa bakin taku, kana tsaye a bakin ruwan kana ganin ruwa babu iyaka, za ka bukaci alama ce da take ɗauke da kalmar nan “Teku” tana nuna maka ruwan? A’a! Ba za ka bukaci alama domin ya nuna maka abin da za ka gane da idanunka ba.
Yesu ya kwatanta alamar bayyanuwarsa, ba ya nuna abin da mutane za su iya gani da idanunsu ba ne, amma ya taimake su ne su fahimci abin da zai faru a samaniya. Saboda haka Yesu ya ce: “Ba da kallo mulkin Allah ke zuwa ba.” (Luka 17:20) Ta yaya, alamar za ta nuna wa waɗanda suke duniya cewa Yesu ya bayyana?
3. Bayyanuwar Yesu za ta fara ne da lokacin bala’i mai tsanani a nan duniya. Yesu ya ce in ya zama Sarki a sama, duniya za ta kasance cikin yaƙe-yaƙe, yunwa, girgizan ƙasa, annoba, da kuma yin laifi. (Matta 24:7-12; Luka 21:10, 11) Menene zai kawo dukan waɗannan wahala? Littafi Mai Tsarki ya yi bayani cewa Shaiɗan, “mai-mulkin wannan duniya” ya cika da fushi domin ya sani cewa lokacinsa kaɗan ya rage da yake Kristi ya zama Sarki. (Yohanna 12:31; Ru’ya ta Yohanna 12:9, 12) Irin waɗannan tabbaci na fushin Shaiɗan da kuma bayyanuwar Yesu suna da yawa a wannan lokacinmu. Musamman ma tun daga shekara ta 1914, shekarar da ’yan tarihi suka nuna cewa lokacin ne kome ya canja, kuma tabbacin bayyanuwarsa ya kasance sarai a dukan duniya.
Dukan waɗannan za su kasance kamar labari ne marasa daɗi, amma ba haka ba ne. Yana nufi ne cewa Mulkin Almasihu yana sarauta yanzu haka a samaniya. Ba da daɗewa ba, wannan gwamnatin za ta nuna ikonta bisa dukan duniya. Ta yaya mutane za su sani game da Mulkin domin su amince da ikonsa kuma su zama talakawansa?
4. Wata alamar bayyanuwar Yesu ita ce wa’azi a dukan duniya. Bayyanuwarsa za ta kasance kamar “yadda kwanakin Nuhu su ke.”a (Matta 24:37-39) Nuhu ba jirgi kawai ya gina ba; shi kuma “mai-shelan adalci” ne. (2 Bitrus 2:5) Nuhu ya yi wa mutane gargaɗi cewa hukuncin Allah yana tafe. Yesu ya ce mabiyansa a duniya za su yi irin wannan wa’azi a lokacin bayyanuwarsa. Ya annabta: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.”—Matta 24:14.
Kamar yadda muka gani a talifi da ya gabata, Mulkin Allah zai halaka dukan gwamnatocin wannan duniyar. Aikin wa’azi na sa mutane su sani cewa wannan gwamnati na samaniya ta kusa aikata wa, kuma ta ba mutane zarafin tsira daga halaka mai zuwa kuma su zama talakawan Mulkin. Tambaya mai muhimmanci ita ce, yaya za ka mai da martani?
Mulkin Allah Zai Kasance Labari ne Mai Daɗi a Gare ka Kuwa?
Saƙon begen da Yesu ya yi wa’azinsa, babu kamarsa. Bayan tawaye shekaru dubbai da suka shige Adnin, Jehobah Allah ya nufa zai kafa gwamnatin da za ta daidaita al’amura, ta mai da ’yan adam masu aminci zuwa yanayin da tun da daɗewa Allah yake so su kasance ciki na zama har abada cikin aljanna a nan duniya. Ba abin da ya fi sa mutum farin ciki kamar sanin cewa wannan gwamnati da aka yi alkawarinta tun da daɗewa tana sarauta yanzu a sama. Ba yanayin zuciya ba ne amma gwamnati ce ta gaske!
A yanzu haka, Sarkin da Allah ya naɗa yana sarauta a tsakiyar maƙiyansa. (Zabura 110:2) A wannan malalaciyar duniya da ke bare daga Allah, Almasihu yana cika muradin Ubansa na neman duka waɗanda suke son su san Allah yadda ainihi yake kuma su bauta masa “cikin ruhu da cikin gaskiya.” (Yohanna 4:24) An ba da Begen zama har abada a ƙarƙashin Mulkin Allah ga mutane da launin fatarsu, shekarunsu, da kuma matsayinsu ya bambanta. (Ayukan Manzanni 10:34, 35) Muna ariritarka ka amince da zarafi mai girma da aka miƙa maka. Ka koya game da Mulkin Allah yanzu, don ka more rayuwa a ƙarƙashin sarautarsa!—1 Yohanna 2:17.
[Hasiya]
a Kalaman Yesu sun taimaka wajen gyara ra’ayi da ba daidai ba da aka samu daga yadda wasu fassarar Littafi Mai Tsarki suka fassara wannan kalmar ‘bayyanuwa.’ Wasu sun fassara ta “zuwa,” ko kuma “dawowa,” dukan waɗannan suna nufin aukuwa ne na ɗan lokaci. Ka lura cewa Yesu bai kamanta bayyanuwarsa da Rigyawa na zamanin Nuhu ba, wato, aukuwa na sau ɗaya, amma ya kamanta shi da “kwanakin Nuhu,” wanda lokaci ne na ƙarshe. Kamar wannan lokaci na dā, bayyanuwar Kristi zai zama lokacin da mutane za su shaƙu da harkoki na kullum da ba za su kula da kashedi da ake sanarwa ba.
[Pictures on pages 8, 9]
Mugun labarin da muke ji kowace rana na nuna cewa abubuwa masu kyau za su zo ba da daɗewa ba
[Inda aka Dauko]
Gun: U.S. Army photo