Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 1/1 pp. 27-30
  • Samun Sauƙi Daga Matsala Na Matashi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Samun Sauƙi Daga Matsala Na Matashi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Na Faɗa Rayuwa Marar Ma’ana
  • Jehobah Ya Cece Ni
  • An Ceci Ƙaunatacciya
  • Yadda na Sha Kan Damuwa
  • Ki Gaya Masu Cewa Kina Kaunar Su
    Labarai
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 1/1 pp. 27-30

Samun Sauƙi Daga Matsala Na Matashi

Eusebio Morcillo ne ya ba da labarin

A watan Satumba ta shekara ta 1993, na ziyarci kurkuku mai tsaro sosai. Na yi ziyarar ne domin ƙanwata Marivi da ke kurkuku za ta yi baftisma. Wasu fursunoni da ma’aikata suna kallo sa’ad da na yi mata baftisma. Kafin na ba da labarin yadda ni da ita muka kasance a wannan wajen, bari na ba ku labarin sa’ad da muke yara.

AN HAIFE ni a Spain a ranar 5 ga Mayu, 1954, ni ne ɗan fari cikin yara takwas. Marivi ce ta uku. Kakarmu ta yi renonmu cikin addinin Katolika, kuma ina tuna yarantaka ta da farin ciki cewa na bauta wa Allah da zuciya ɗaya sa’ad da nake tare da ita. Amma iyayenmu ba su da ruhaniya. Koyaushe Baba na dūkan Mama kuma ya dūke mu. Kullum muna cikin tsoro, kuma ina baƙin ciki sosai ganin yadda Mama take wahala.

A makaranta ina fuskantar wasu yanayin da ke kashe mini gwiwa. Ɗaya cikin malamanmu, wanda firist ne, yana gwara kanmu da bango idan ba mu amsa tambaya da ya yi daidai ba. Wani firist kuma yana lalata da yaran makaranta sa’ad da yake duba aikin da ya ba su. Ƙari ga haka, koyarwar Katolika kamar su wutar jahannama tana rikita ni kuma tana tsoratar da ni. Ban ɓata lokaci wajen watsi da bautar Allah ba.

Na Faɗa Rayuwa Marar Ma’ana

Domin ba ni da ja-gora ta ruhaniya, sai na soma zama da mutane masu lalata, masu nuna ƙarfi a wajen disko. Sau da yawa, akan soma faɗa da wuƙaƙe, sarƙa, kwalabe, da kujeru. Ko da yake ba na shiga faɗan sosai, an taɓa bugu na har na sume.

Daga baya sai na gaji da irin wannan wajen na nemi wajen disko da ba a tashin hankali sosai. Ko a wannan wurin ma, ana shan ƙwayoyi. Amma maimakon na sami gamsuwa da kwanciyar hankali, ƙwayoyin suna sa ni mugun mafarki da alhini.

Ko da yake ban gamsu ba, na rinjayi ƙane na, José Luis da Miguel abokina na kud da kud a cikin wannan salon rayuwa. Tare da wasu matasa da yawa a Spain, mun faɗa cikin lalaci. Ina yin kome don na samu kuɗin sayen ƙwayoyi. Mutuncina ya zube gaba ɗaya.

Jehobah Ya Cece Ni

A wannan lokacin, na yi magana sau da yawa da abokai na game da wanzuwar Allah da ma’anar rayuwa. Sai na soma biɗan Allah ta wajen neman wanda zan gaya wa yadda nake ji. Na lura cewa wani abokin aikina mai suna Francisco ya bambanta da sauran. Yana da farin ciki, mai gaskiya ne, kuma yana da kirki, sai na gaya masa abin da ke damuna. Francisco Mashaidin Jehobah ne, sai ya ba ni Hasumiyar Tsaro da ke ɗauke da wani talifi game da ƙwayoyi.

Bayan na karanta talifin, na yi wa Allah addu’a ya taimake ni: “Ubangiji, na san kana wanzuwa, kuma ina son in sanka kuma na yi nufinka. Don Allah ka taimake ni!” Francisco da wasu Shaidu suka yi amfani da Littafi Mai Tsarki suka ƙarfafa ni kuma suka ba ni littattafai in karanta. Sai na fahimci cewa suna ba ni taimakon da na roƙa daga wurin Allah ne. Sai na soma gaya wa abokane na da kuma José Luis abubuwan da nake koya.

Wata rana bayan ni da abokai na muka gama kallon mawaƙa, sai na ware kaina daga rukunin. Na kalle su daga nesa, sai na ga yadda halinmu ya zama abin ƙyama domin shan ƙwayoyi. Nan take, na tsai da shawara ba zan bi wannan salon rayuwar ba, zan zama Mashaidin Jehobah.

Na gaya wa Francisco ya ba ni Littafi Mai Tsarki sai ya ba ni guda tare da littafin nan Gaskiya Mai Bishe Zuwa Rai Madauwami.a Sa’ad da na karanta game da alkawarin Allah cewa zai share hawaye kuma ya cire mutuwa, ban yi shakka ba cewa na sami gaskiya da za ta iya ’yantar da ’yan adam. (Yohanna 8:32; Ru’ya ta Yohanna 21:4) Sai daga baya, na halarci taro a Majami’ar Mulki na Shaidun Jehobah. Abokantaka da fara’a da na gani a wajen ya burge ni sosai.

Da yake ina ɗokin gaya wa mutane abin da na gani a Majami’ar Mulki, nan da nan na gaya wa José Luis da abokai na. Bayan wasu kwanaki dukanmu muka halarci taro. Wata yarinya da take zaune a gaba ta kalle mu. Ta yi mamakin ganin waɗannan mutane masu dogon gashi, sai ta yi ƙoƙari ba ta sake juyawa ta kalle mu ba. Babu shakka ta yi mamaki sa’ad da muka halarci taro a Majami’ar Mulki mako na gaba, amma a wannan lokacin mun sa sutura mai kyau.

Ba da daɗewa ba bayan haka, ni da Miguel muka halarci taron da’ira na Shaidun Jehobah. Ba mu taɓa ganin irin wannan taron mutane, manya da yara waɗanda ’yan’uwa ne da gaske ba. Abin mamaki kuma an yi taron a ɗakin wasa inda muka gama kallon mawaƙa ba da daɗewa ba. Amma a wannan lokacin, yanayin ya bambanta kuma waƙar da muka ji ta ƙarfafa mu.

Dukanmu muka soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Bayan watanni takwas, a ranar 26 ga Yuli, 1974, ni da Miguel muka yi baftisma. A lokacin muna ’yan shekaru 20 ne. Wasu huɗu a cikin rukuninmu suka yi baftisma bayan ’yan watanni. Abin da na koya daga Littafi Mai Tsarki ya motsa ni na soma taimakon mamata da ta daɗe tana wahala da aikace-aikacen gida kuma ina gaya mata wasu sababbin abubuwa da na yi imani da su. Muka zama abokai na kud da kud. Na kuma ba da lokaci sosai wajen taimakon ƙanne na.

Da shigewar lokaci, mamata da dukan ƙanne na suka koyi gaskiya game da Littafi Mai Tsarki ban da ɗaya kawai kuma aka yi musu baftisma suka zama Shaidun Jehobah. A shekara ta 1977, na auri Soledad. Ita ce yarinya da ta yi mamaki sa’ad da ta ganmu a lokacin da muka halarci taronmu na farko a Majami’ar Mulki. Bayan ’yan watanni dukanmu muka zama majagaba, yadda Shaidun Jehobah suke kiran masu wa’azin bishara na cikakken lokaci.

An Ceci Ƙaunatacciya

An zalunci ƙanwata Marivi da lalata sa’ad da take yarinya, kuma wannan mugun abin da ta fuskanta ya shafe ta sosai. Lokacin da take yarinya ta bi salon rayuwa da ya haɗa da shan ƙwayoyi, sata, da kuma karuwanci. Da take ’yar shekara 23 aka saka ta cikin kurkuku kuma a nan ma ta ci gaba da iskancinta.

A lokacin ina hidima na mai kula mai ziyara, wato mai ziyartar ikilisiyoyin Shaidun Jehobah. A shekara ta 1989, aka tura mu mu yi hidima a inda kurkukun da ake tsare da Marivi yake. Ba da daɗewa ba hukuma ta kwace ɗanta daga wurinta, kuma hakan ya sa ta baƙin ciki sosai har ba ta so ta ci gaba da rayuwa. Wata rana na ziyarce ta kuma na gaya mata mu soma nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ta yarda. Bayan ta yi nazari na wata ɗaya sai ta daina shan ƙwayoyi da taba. Na yi farin ciki sosai da ganin yadda Jehobah ya ƙarfafa ta ta yi waɗannan canje-canje a rayuwarta.—Ibraniyawa 4:12.

Ba da daɗewa ba bayan ta soma nazari, Marivi ta soma gaya wa waɗanɗa suke tare a kurkuku da kuma ma’aikatan gaskiya game da Littafi Mai Tsarki. Ko da yake ana sake mata kurkuku ta ci gaba da aikinta na wa’azi. A wani kurkuku ta yi wa’azi kofa kofa a cikin kurkukun. Cikin shekaru da yawa, Marivi ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki da waɗanɗa take tare da su a kurkuku dabam dabam.

Wata rana Marivi ta gaya mini tana son ta keɓe kanta ga Jehobah kuma ta yi baftisma. Amma ba a bata izinin barin kurkukun ba, kuma ba a bari kowa ya shiga ya yi mata baftisma ba. Ta jimre wasu ƙarin shekara huɗu a cikin wannan wuri na lalaci. Menene ya taimake ta ta riƙe bangaskiyarta? A daidai lokacin da ikilisiyar da ke wurin take yin taronta, sai ta bi abin da ake nazari a kai a cikin ɗakinta na kurkuku. Kuma tana da tsarin yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma addu’a kullum.

Da shigewar lokaci, aka kai Marivi wani kurkuku mai tsaro sosai kuma yana da wurin iyo. Ta ga cewa wannan sabon yanayi zai sa yin baftismarta ta yiwu. Kuma hakan ya faru, daga baya aka ba Marivi izini ta yi baftisma. Hakan ya kasance na ba da jawabin baftismarta. Ina tare da ita a lokacin da ya fi muhimmanci a rayuwarta.

Domin irin rayuwa da ta yi a dā, Marivi ta kamu da ƙanjamau. Duk da haka, halinta mai kyau ya sa aka sake ta daga kurkuku a Maris ta shekara 1994. Ta zauna tare da mamarmu kuma ta kasance da ƙwazo a hidima har mutuwarta bayan shekara biyu.

Yadda na Sha Kan Damuwa

Ni ma ban guje wa sakamakon salon rayuwata ta dā ba. Zalunci da na sha a hannun babana da kuma salon rayuwata da nake yaro sun shafi halina. Da na girma, sau da yawa ina jin ina da laifi kuma ina jin ban cancanta ba. Wani lokaci ina sanyin gwiwa sosai. Duk da haka, Kalmar Allah ta taimake ni sosai wajen yaƙi da wannan damuwa. Yin bimbini a kan nassosi kamar su Ishaya 1:18 da Zabura 103:8-13 a kai a kai ya taimake ni na rage damuwa game da jin ina da laifi.

Addu’a wata hanya ce na ruhaniya da nake amfani da ita wajen kawar da ra’ayin jin ban cancanta ba. Sau da yawa, ina addu’a ga Jehobah da idanuna cike da hawaye. Amma kalmomi da ke rubuce a 1 Yohanna 3:19, 20 sun ƙarfafa ni: “Saboda wannan za mu sani muna wajen gaskiya, mu rinjayi zuciyarmu a gabansa kuma, dukan inda zuciyarmu ta kashe mu; gama Allah ya fi zuciyarmu girma, ya kuwa san abu duka.”

Tun da yake na kusaci Allah da “karyayyar zuciya” na fahimci cewa ni ba mugu ba ne yadda nake tunani. Littafi Mai Tsarki ya tabbatar wa dukan waɗanda suke biɗan Jehobah cewa ba ya rena waɗanda suka yi nadama da gaske don halinsu na dā kuma suka soma yin nufinsa.—Zabura 51:17.

A duk lokacin da na fara shakkan kaina, ina ƙoƙari in cika zuciya ta da abubuwa na ruhaniya masu kyau da aka ambata a Filibbiyawa 4:8. Na haddace Zabura sura 23 da kuma Huɗuba a kan Dutse. Sa’ad da na fara damuwa, sai in maimaita wa kaina waɗannan ayoyin Nassosi. Cire wannan daga zuciyata yana da taimako musamman sa’ad da na kasa barci.

Wani wurin da na ke samun taimako kuma ya kasance yabo daga matata da wasu Kiristoci da suka ƙware. Ko da yake da farko ya yi mini wuya in amince da kalmominsu na ƙarfafa, amma Littafi Mai Tsarki ya taimake ni na fahimci cewa ƙauna tana “gaskata abu duka.” (1 Korinthiyawa 13:7) A hankali cikin tawali’u na amince da kasawata.

Amfani da na samu daga ƙoƙari da na yi na kawar da wannan damuwa ya taimake ni na zama mai kula mai ziyara mai juyayin wasu. Ni da matata mun yi kusan shekara 30 a hidimar bishara na cikakken lokaci. Farin cikin da na samu a wajen taimakon wasu ya taimake ni na kawar da damuwata da tunanin munanan abubuwa da na fuskanta.

Sa’ad da na yi tunanin dukan albarkar da Jehobah ya ba ni, suna motsa ni in yi furci kamar na mai Zabura: “Ka albarkaci Ubangiji . . . Shi da ke gafarta dukan laifofinka; Mai-warkadda dukan ciciwutanka: Mai-pansar ranka daga mahallaka; Mai-yi maka dajiya da rahama da jiyejiyenƙai.”—Zabura 103:1-4.

[Hasiya]

a Shaidun Jehobah ne suka wallafa amma ba a bugawa yanzu.

[Bayanin da ke shafi na 30]

Sau da yawa na damu da jin cewa ina da laifi kuma ina jin ban cancanta ba, amma Kalmar Allah ta taimake ni na kawar da wannan damuwar

[Hotuna a shafi na 27]

Ƙanina José Luis da kuma aboki na Miguel sun bi misalina mai kyau da marar kyau

[Hoto a shafi nas 28, 29]

Iyalin Morcillo a shekara ta 1973

[Hoto a shafi na 29]

Sa’ad da Marivi take kurkuku

[Hoto a shafi na 30]

Ni da matata Soledad

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba