Abin Da Muka Koya Daga Wurin Yesu
Game da Allah na Gaskiya
Allah yana da suna kuwa?
Yesu ya koyar da cewa Allah yana da suna. Yesu ya ce: “Da hakanan fa za ku yi addu’a: Ubanmu wanda ke cikin sama, A tsarkake sunanka.” (Matta 6:9) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah ne sunan Allah. (Zabura 83:18) Da yake magana game da almajiransa, Yesu ya faɗa sa’ad da yake addu’a ga Ubansa yana cewa: “Na kuma sanar masu da sunanka.”—Yohanna 17:26.
Wanene Jehobah?
Yesu ya kira Jehobah “Allah makaɗaici mai-gaskiya,” domin Jehobah shi ne Mahalicci. (Yohanna 17:3) Yesu ya ce: “Ba ku karanta ba, shi wanda ya yi su tun farko, namiji da tamata ya yi su.” (Matta 19:4) Yesu ya kuma faɗi cewa: “Allah ruhu ne.” (Yohanna 4:24) Saboda haka ba za mu iya ganin Allah ba.—Fitowa 33:17-20.
Menene Allah yake bukata a gare mu?
Sa’ad da wani ya tambayi Yesu wace doka ce ta fi muhimmanci, ya ba da amsa cewa: “Ta fari ke nan, Ku ji ya Isra’ila; Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne: kuma ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka, da dukan ƙarfinka. Ta biyu ke nan kuma, Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.”—Markus 12:28-31.
Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar Allah?
Yesu ya ce: “Ina ƙaunar Uba.” Ta yaya ya nuna ƙaunarsa? Ya ce: “Yadda Uba ya ba ni umurni, haka ni ke yi.” (Yohanna 14:31) Ya kuma faɗi cewa: “Kullum ina aika abin da ya gamshe shi.” (Yohanna 8:29) Muna iya faranta wa Allah rai ta wajen koya game da shi. Sa’ad da yake addu’a domin almajiransa, Yesu ya ce: “Rai na har abada ke nan, su san ka, Allah makaɗaici mai-gaskiya.”—Yohanna 17:3; 1 Timothawus 2:4.
Ta yaya za mu iya koya game da Allah?
Hanya ɗaya da za mu san Allah ita ce ta wajen lura da abubuwan da ya halitta. Alal misali, Yesu ya ce: “Ku duba tsuntsaye na sama, ba su kan yi shuka ba, ba su kan yi girbi ba, ba su kan tattara cikin rumbuna ba; amma Ubanku na sama yana ciyarda su. Ku ba ku fi su daraja dayawa ba?” Menene Yesu yake son mu koya daga wannan? Bai kamata mu bar alhini game da bukatu na zahiri ya hana mu bauta wa Allah ba.—Matta 6:26-33.
Hanya mafi kyau ta sanin Jehobah ita ce ta yin nazarin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Yesu ya kira Nassosi “maganar Allah.” (Luka 8:21) Yesu ya ce wa Allah: “Maganarka ita ce gaskiya.”—Yohanna 17:17; 2 Bitrus 1:20, 21.
Yesu ya taimaki mutane su koyi gaskiya game da Jehobah. Game da Yesu, ɗaya daga cikin almajiransa ya ce: “Zuciyarmu ba ta ƙuna daga cikinmu ba, sa’anda yana yi mamu zance a kan hanya, yana bayyana mamu littattafai?” (Luka 24:32) Don mu koya game da Allah, dole ne mu kasance masu tawali’u, waɗanda suke son a koyar da su. Yesu ya ce: “In ba ku juyo ba, ku komo kamar yara ƙanƙanana, ba za ku shiga cikin mulkin sama ba daɗai.”—Matta 18:3.
Me ya sa sanin Allah zai kawo farin ciki?
Allah yana biyan bukatunmu don mu fahimci manufar rayuwa. Yesu ya ce: “Masu-albarka ne masu-ladabi a ruhu.” (Matta 5:3) Jehobah yana koya mana hanya mafi kyau na rayuwa. Yesu ya ce: “Gwamma dai waɗannan da suna jin maganar Allah, suna kiyaye ta kuma.”—Luka 11:28; Ishaya 11:9.
Don ƙarin bayani, ka duba babi na 1 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?a
[Hasiya]
a Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
[Hoto a shafi na 6]
“Na kuma sanar masu da sunanka.” —Yohanna 17:26.
[Hotuna a shafuffuka na 6, 7]
Za mu iya koya game da Jehobah daga halittu da kuma Littafi Mai Tsarki