Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 4/1 pp. 8-10
  • Magance Matsaloli

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Magance Matsaloli
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Fahimtar Matsalolin
  • Ku Yi Ƙoƙarin Magance Matsalolin Tare
  • Abin da Zai Sa Ku Yi Nasara Shi ne Gujewa Yi wa Juna Ɓaƙar Magana
  • Yadda Za Ka Daraja Matarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Zaman Aure
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Aure Kyauta Ne Daga Allah
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Yadda Kiristoci Za Su Yi Nasara a Aurensu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 4/1 pp. 8-10

Abubuwan Da Ke Kawo Farin Ciki A Iyali

Magance Matsaloli

Ya ce: “Bayan da muka yi aure, ni da matata mun tare ne a gidan iyayena. Wata rana budurwar ƙanina ta ce in kai ta gida a cikin motarmu. Ina son na taimaka mata sai na tafi tare da ɗana. Amma sa’ad da na dawo, matata ta yi fushi. Muka soma musu, kuma a gaban iyalina ta kira ni mai son mata. Na yi fushi sosai kuma na gaya mata maganganu da suka ƙara ba ta haushi.”

Ta ce: “Ɗanmu yana rashin lafiya sosai, kuma a lokacin ba mu da kuɗi. Saboda haka, lokacin da mijina ya bar gida da budurwar ƙaninsa da ɗanmu, na yi fushi sosai don dalilai da yawa. Sa’ad da ya dawo gida, na gaya masa yadda na ji. Mun yi jayayya sosai kuma muka zagi juna. Bayan jayayyar na yi baƙin ciki sosai.”

IDAN ma’aurata suka yi jayayya, hakan na nufin cewa ba sa ƙaunar juna ne? A’a! Ma’auratan da aka ambata a sama suna ƙaunar juna sosai. Duk da haka, a cikin aure da ake farin ciki da akwai lokacin da za a yi jayayya.

Me ya sa ake jayayya, kuma menene za ku iya yi don ku hana wannan halaka aurenku? Tun da yake Allah ne ya tsara aure, yana da kyau mu bincika abin da Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki ta ce a kan wannan batun.—Farawa 2:21, 22; 2 Timothawus 3:16, 17.

Fahimtar Matsalolin

Yawancin ma’aurata suna ƙaunar juna kuma suna son su kula da juna sosai. Amma, Littafi Mai Tsarki ya faɗi sarai cewa “dukan mutane sun yi zunubi, sun kasa kuma ga darajar Allah.” (Romawa 3:23) Saboda haka, sa’ad da aka soma jayayya, yana da wuya mu riƙe kanmu. Kuma idan aka soma hakan, yana yi wa wasu wuya sosai su guji yin kururuwa da zage-zage. (Romawa 7:21; Afisawa 4:31) Waɗanne abubuwa ne kuma za su iya jawo matsala?

Yadda mata da miji sau da yawa suke faɗin abubuwa ya bambanta da juna. Michikoa ta ce: “Sa’ad da muka yi aure, na fahimci cewa yadda muke tattauna abubuwa ya bambanta da juna. Ina son faɗin abin da ya faru da kuma dalilin da ya sa ya faru da kuma yadda abin ya faru. Mijina kuma yana son ya ji yadda abin ya ƙare ne kawai.”

Ba Michiko kaɗai ba ce take da irin wannan matsalar. A yawancin aure, wataƙila mutum ɗaya yana son a tattauna rashin jituwar sosai, amma shi kuwa ɗayan ba ya son jayayya kuma ya guji tattauna batun. A wani lokaci, idan mutum ɗaya yana son a yi magana a kan batun, ɗayan kuma yana daɗa ƙoƙarin ya guji batun. Ka lura da wannan yanayin a cikin aurenka? Ɗaya a cikinku yana son a tattauna batun, yayin da ɗayan kuma a kowane lokaci yana ƙoƙarin ya guji tattauna batun?

Wani abu kuma da za a yi la’akari da shi, shi ne cewa yanayin iyalin da aka haifi mutum zai iya shafan ra’ayinsa ko nata game da yadda ya kamata ma’aurata su yi magana da juna. Justin da ya yi aure shekaru biyar da suka shige ya ce: “Na fito ne daga cikin iyalin da ba sa yawan magana kuma hakan ya sa yana yi mini wuya in gaya wa mutane yadda nake ji. Wannan ya sa matata baƙin ciki. Iyalinta kuma masu yawan magana ne, kuma ba ta da matsala wajen gaya mini yadda take ji.”

Ku Yi Ƙoƙarin Magance Matsalolin Tare

Masu bincike sun fahimci cewa abin da ya fi nuna cewa ma’aurata suna farin ciki ba yawan yadda suke faɗin cewa suna ƙaunar juna ba ne. Jima’i da isashen kuɗi ba su ba ne abubuwan da suka fi muhimmanci ba. Maimakon haka, abin da ke sa a yi nasara cikin aure shi ne yadda mata da miji suke magance matsaloli idan suka taso.

Ƙari ga haka, Yesu ya ce sa’ad da ma’aurata suka yi aure, Allah ne ya haɗa su ba mutum ba. (Matta 19:4-6) Saboda haka, aure mai kyau yana daraja Allah. A wani ɓangare kuma, idan miji ya ƙi nuna ƙauna da sanin ya kamata ga matarsa, Jehobah Allah yana iya ƙin sauraron addu’arsa. (1 Bitrus 3:7) Idan mata ta ƙi yi wa mijinta ladabi, Jehobah ne take ƙin yi wa ladabi, wanda shi ne ya naɗa mijin shugaban iyalin.—1 Korinthiyawa 11:3.

Abin da Zai Sa Ku Yi Nasara Shi ne Gujewa Yi wa Juna Ɓaƙar Magana

Ko da yaya ku ke magana da juna ko kuma yanayin iyalin da kuka fito, ya kamata ku guji baƙar magana idan kuna son ku bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kuma ku magance matsaloli da kyau. Ku yi wa kanku waɗannan tambayoyin:

▪ ‘Ina guje wa son ramawa kuwa?’ “Murdan hanci kuma ya kan jawo jini: Hakanan kuma tsanantar fushi ta kan tada sabobi,” in ji ƙarin magana. (Misalai 30:33) Menene wannan yake nufi? Ka yi la’akari da wannan misalin. Ra’ayin da aka soma furtawa na yadda za a kashe kuɗi a iyali, kamar (“muna bukatar mu kula da yadda muke kashe kuɗi”) zai iya juyawa ya zama zagi, kamar (“ba ka san ciwon kanka ba”). Hakika, idan abokiyar aurenka ta ‘murde hancinka’ ta wajen zagin irin halinka, kai ma za ka ji kamar ka ‘murde’ nata nan da nan. Amma ramawa zai jawo fushi da kuma ƙaruwar rashin jituwa.

Yakubu marubucin Littafi Mai Tsarki ya ba da gargaɗi: “Duba yadda wuta ƙanƙanuwa ta kan kunna babban kurmi!” (Yaƙub 3:5, 6) Idan ma’aurata suka kasa riƙe harshensu, ɗan rashin jituwar da suka samu za ta iya zama babbar matsala. Ma’auratan da suke yawan gaya wa juna baƙar magana ba sa kafa yanayin da zai sa su ci gaba da nuna wa juna ƙauna.

Maimakon ka rama, za ka iya yin koyi da Yesu, wanda sa’ad da aka zage shi “ba ya mayarda zagi ba”? (1 Bitrus 2:23) Hanya mafi sauri ta kawar da jayayyar da kuke yi ita ce yin la’akari da ra’ayin abokiyar aurenka kuma ka nemi gafara don abin da ka yi da ya jawo matsalar.

KA GWADA WANNAN: Idan jayayya ta sake tasowa, ka tambayi kanka: ‘Menene amincewa da damuwar abokiyar aure na zai cire a jikina? Menene na yi da ya jawo wannan matsalar? Menene ya hana ni neman gafara don kurakuran da na yi?’

▪ ‘Ba na damuwa da yadda abokiyar aure na take ji ne?’ Kalmar Allah ta ba da umurni cewa: “Dukanku ku zama hankalinku ɗaya, masu-juyayi.” (1 Bitrus 3:8) Ka yi la’akari da dalilai biyu da za su sa ka ƙi yin amfani da wannan shawarar. Ɗaya shi ne wataƙila ba ka san zuciyar matarka ba ko kuma yadda take ji. Alal misali, idan matarka ta fi nuna damuwa game da wani abu fiye da kai, kana iya cewa, “Kin cika damuwa.” Wataƙila kana son ka taimaki abokiyar aurenka ta ɗauki matsalar a hanyar da ta dace ne. Amma, mutane kaɗan ne kawai irin wannan furcin zai iya ƙarfafawa. Matan aure da magidanta suna bukatar su san cewa mutanen da suke ƙauna sun fahimce su kuma suna tausaya musu.

Yin fahariya ainun yana iya sa mutum kada ya ɗauki yadda matarsa take ji da muhimmanci. Mai fahariya yana ɗaukaka kansa ta wajen ƙaskantar da mutane. Yana iya yin haka ta wajen kiranta da sunanyen banza ko kuma ya kwatanta ta da abin da bai da kyau. Ka yi la’akari da misalin Farisawa da marubuta na zamanin Yesu. Sa’ad da wani har da Bafarisi ya furta ra’ayin da ya bambanta da na sauran farisawa masu fahariya, sai su soma kiransa da sunayen banza kuma su ƙaskantar da shi. (Yohanna 7:45-52) Yesu bai yi haka ba. Ya ji tausayin mutane sa’ad da suka gaya masa damuwarsu.—Matta 20:29-34; Markus 5:25-34.

Ku yi tunanin yadda kuke aikatawa sa’ad da aboki ko abokiyar aurenku ya ko ta faɗi ra’ayinta. Kalamanka, ko kuma muryarka, da fuskarka suna nuna tausayi? Ko kuwa kana saurin son kawar da yadda abokiyar aurenka take ji?

KA GWADA WANNAN: A cikin makonni masu zuwa, ka lura da yadda kake yi wa matarka magana. Idan ka nuna rashin damuwa ko kuwa ka faɗi wani abu mai ƙasƙantarwa, ka nemi gafara nan da nan.

▪ ‘Ina yawan tunanin cewa ra’ayin abokiyar aurena na son kai ne?’ “A banza ne Ayuba ya ke tsoron Allah? Ba ka kewaye shi da shinge ba, da shi da gidansa, da dukan abin da ya ke da shi, a kowane sassa?” (Ayuba 1:9, 10) Da waɗannan kalaman, Shaiɗan ya ƙalubalanci muradin Ayuba mutum mai aminci.

Idan ma’aurata ba su mai da hankali ba, su ma za su iya yin haka. Alal misali, idan abokiyar aurenka ta yi maka wani abu mai kyau, kana tunanin ko akwai abin da take ƙoƙarin ɓoyewa ne? Idan abokiyar aurenka ta yi kuskure, hakan na sa ka yi tunanin cewa tana nuna son kai kuma ba ta nuna kula? Kana tuna irin waɗannan kurakuren da ta yi a dā kuma ka ƙi mancewa?

KA GWADA WANNAN: Ka rubuta abubuwa masu kyau da abokiyar aurenka ta yi maka da kuma muradi mai kyau da ya sa ta yi waɗannan abubuwa.

Manzo Bulus ya rubuta: “Ƙauna . . . ba ta yin nukura.” (1 Korinthiyawa 13:4, 5) Ƙauna ta gaskiya ta san muna kuskure. Amma ba ta yin nukura. Bulus ya kuma ce ƙauna “tana gaskata abu duka.” (1 Korinthiyawa 13:7) Ba wai irin wannan ƙaunar tana sa mutane su amince da duk wani abin da aka gaya musu ba, amma tana shirye ta gaskata da mutane. Ba ta rashin aminci da kuma zargi. Irin ƙauna da Littafi Mai Tsarki yake ƙarfafa tana shirye ta gafarta laifi kuma ba ta shakkar muradin wasu. (Zabura 86:5; Afisawa 4:32) Sa’ad da ma’aurata suka nuna wa juna irin wannan ƙaunar, za su yi farin ciki a cikin aurensu.

KA TAMBAYI KANKA . . .

▪ Waɗanne kurakurai ne ma’auratan da aka yi kaulinsu a farkon wannan talifin suka yi?

▪ Yaya zan guje wa yin irin waɗannan kurakuran a cikin aurena?

▪ Waɗanne batutuwan da aka ambata a wannan talifin ne nake bukatar na fi yin amfani da su?

[Hasiya]

a An canja sunayen

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba