Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 4/1 pp. 20-22
  • Markus Bai Karaya Ba

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Markus Bai Karaya Ba
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Makamantan Littattafai
  • Markus ‘Yana da Amfani Wajen Hidima’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Waɗanda Suka Rubuta Labarin Yesu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 4/1 pp. 20-22

Ka Koya Wa Yaranka

Markus Bai Karaya Ba

MARKUS ya rubuta ɗaya daga cikin littattafai huɗu na Littafi Mai Tsarki da suke ɗauke da labarin rayuwar Yesu. Shi ne gajere a cikinsu kuma mafi sauƙin karantawa. Wanene Markus? Kana ganin ya san Yesu?—a Bari mu ga irin jarraba masu wuya da Markus ya fuskanta kuma mu koyi dalilin da ya sa Markus bai karaya ba a matsayin Kirista.

An fara ambata sunan Markus ne a cikin Littafi Mai Tsarki bayan da Sarki Hirudus Agaribas ya jefa manzo Bitrus a cikin kurkuku. Daddare wata rana wani mala’ika ya saki Bitrus, kuma nan da nan ya je gidan Maryamu, mamar Markus, wadda take da zama a Urushalima. An saki Bitrus daga kurkuku misalin shekaru goma bayan da aka kashe Yesu a Idin Ƙetarewa na shekara ta 33 A.Z.—Ayukan Manzanni 12:1-5, 11-17.

Ka san abin da ya sa Bitrus ya je gidan Maryamu?—Wataƙila domin ya san waɗanda suke cikin iyalinta kuma ya san cewa almajiran Yesu suna yin taro a gidanta. Markus ɗan’uwan Barnaba ya daɗe da zama almajiri, tun Idin Fentakos na shekara ta 33 A.Z. An ambata alherin da ya yi a wannan lokacin ga sababbin almajirai a cikin Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, wataƙila Yesu ya san Barnaba da kuma ’yar’uwarsa Maryamu da ɗanta Markus.—Ayukan Manzanni 4:36, 37; Kolossiyawa 4:10.

A cikin Linjilarsa, Markus ya rubuta cewa a daren da aka kama Yesu, wani matashi da ke “yafe da zane” yana wurin. Markus ya rubuta cewa matashin ya gudu sa’ad da maƙiya suka kama Yesu. A ganinka, wanene wannan matashin?— Hakika, wataƙila Markus ne! Sa’ad da Yesu da manzanninsa suka bar gidan da suka yi taro a wannan daren, sai Markus ya yafa zane kuma ya bi su.—Markus 14:51, 52.

An haifi Markus ne a iyalin da ke da ruhaniya sosai. Wataƙila yana nan sa’ad da almajiran Yesu suka sami ruhu mai tsarki a Fentakos na shekara ta 33 A.Z., kuma yana da dangantaka na kud da kud da bayin Allah masu aminci, kamar Bitrus. Ya raka ɗan’uwansa Barnaba, wanda ya taimaka wa Shawulu ta wajen gabatar da shi ga Bitrus bayan shekaru uku da Yesu ya bayyana wa Shawulu a wahayi. Bayan shekaru masu yawa, an tura Barnaba zuwa Tarsus don ya nemo Shawulu.—Ayukan Manzanni 9:1-15, 27; 11:22-26; 12:25; Galatiyawa 1:18, 19.

A shekara ta 47 A.Z., an naɗa Barnaba da Shawulu su tafi su yi aikin wa’azi a ƙasashen waje. Sun tafi tare da Markus, amma domin wasu dalilan da ba a ambata ba a cikin Littafi Mai Tsarki, Markus ya ƙyale su kuma ya koma Urushalima. Shawulu, wanda aka soma kiransa da sunansa na Roma Bulus, ya yi fushi. Kuma Bulus bai yi watsi ba da abin da yake ganin kasawa ce a ɓangaren Markus.—Ayukan Manzanni 13:1-3, 9, 13.

Sa’ad da suka dawo daga ƙasashen wajen, Bulus da Barnaba sun ba da rahoton nasarori masu ban al’ajabi da suka samu. (Ayukan Manzanni 14:24-28) Bayan watanni, su biyun suka yi shirin sake ziyartar sababbin almajiran da suke wuraren da suka yi wa’azi. Barnaba yana son ya tafi da Markus, amma ka san abin da Bulus ya ce?— ‘Ya ga bai dace ba ya tafi da su’ domin Markus ya ƙyale su ya koma gida. Abin da ya faru bayan haka ya sa Markus baƙin ciki!

Bayan fushi da kuma ‘jayayyar’ da suka yi, sai Bulus da Barnaba suka rabu. Barnaba ya ɗauki Markus suka tafi yin wa’azi a Kubrus, shi kuma Bulus ya zaɓi Sila kuma suka sake ziyartar sababbin almajirai kamar yadda suka shirya a dā. Markus ya yi baƙin ciki sosai domin matsalar da ya jawo a tsakanin Bulus da Barnaba!—Ayukan Manzanni 15:36-41.

Ba mu san dalilin da ya sa Markus ya ƙyale su ya koma gida ba. Wataƙila a ganinsa yana da ƙwaƙƙwaran dalilin yin hakan. Ko yaya dai, Barnaba ya tabbata cewa hakan ba zai sake faruwa ba. Kuma hakan gaskiya ne. Markus bai karaya ba! Bayan haka ya yi aikin wa’azi na ƙasashen waje da Bitrus a can ƙasar Babila. Daga wurin, Bitrus ya aika gaisuwa, kuma ya daɗa cewa: ‘Hakanan kuma Markus ɗana.’—1 Bitrus 5:13.

Bitrus da Markus sun kasance da dangantaka na kud da kud domin sun bauta wa Allah tare! Kuma hakan ya bayyana sa’ad da muka karanta Linjilar Markus. A nan Markus ya nuna abubuwan da Bitrus ya koya daga wurin Yesu. Ga misali, yi la’akari da labarin raƙumin ruwan da aka yi a Tekun Galili. Markus ya daɗa yin bayani game da wurin da Yesu ya kwanta a cikin kwalekwalen da kuma kan abin da ya kwanta, abubuwan da mutum mai kama kifi kamar Bitrus zai lura da su. Bari mu karanta waɗannan labaran da ke cikin littafin Matta 8:24; Markus 4:37, 38; da kuma Luka 8:23 a cikin Littafi Mai Tsarki kuma mu gwada su.

Daga baya, sa’ad da aka jefa Bulus cikin kurkuku a Roma, ya yaba wa Markus don taimaka masa da ya yi. (Kolossiyawa 4:10, 11) Kuma sa’ad da aka sake jefa Bulus a cikin kurkuku, ya rubuta wasiƙa ga Timothawus kuma ya ce masa ya kawo Markus, domin: “Yana da amfani gare ni wajen yi mini hidima.” (2 Timothawus 4:11) Hakika, Markus ya mori gata mai yawa domin bai karaya ba!

[Hasiya]

a Idan kana wannan karatun ne da ɗan ƙaramin yaro, wannan karan ɗaurin tunasarwa ne na dakatawa don ka ƙarfafa yaron ya faɗi abin da ke zuciyarsa.

Tambayoyi:

○ Ina ne Markus yake da zama, kuma me ya sa za ka iya cewa ya san Yesu?

○ Wanene ainihi ya taimaki Markus kuma ya tallafa masa?

○ Da menene zai sa Markus ya karaya?

○ Yaya muka sani cewa daga baya manzo Bulus ya amince da Markus?

[Hoto a shafi na 21]

Wanene wannan matashin? Menene ke faruwa a gare shi, kuma me ya sa?

[Hoto a shafi na 22]

Waɗanne albarka ne Markus ya samu saboda bai karaya ba?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba