Wasiƙa Daga Jamhuriyar Dominica
“Ba a Taɓa Nuna Mini Irin Wannan Ƙaunar Ba”
NIURKA ta ba da jawabi na Littafi Mai Tsarki na farko a wannan makon a ikilisiyarmu. Ta shirya ta wajen rubuta abin da za ta faɗa da rubutun makafi, sai ta haddace su. Ina kan bagadin magana tare da ita, ina kwaikwayon wadda take so ta koyi gaskiya ta Littafi Mai Tsarki. Tana jin murya ta ta hedfon ɗinta. Sa’ad da muka gama, domin ƙarar tafin masu sauraro yana da ƙarfi sosai har ta ji su. Murmushi da ta yi ya nuna fari ciki da gamsuwarta. Ni ma na yi farin ciki. Hidima ta ta mai wa’azi a ƙasashen waje tana da ban albarka.
Na tuna da lokacin da na haɗu da Niurka da farko. Shekaru biyu ne da suka shige. Bayan mun yi tafiya a mota na minti 30 a kan hanya mai ƙura, na ganta. Tana zaune a kan dakali a gaban wani gida da aka gina da katako da kuma bulo kuma rufin ya riga ya yi tsatsa. Da alamar zomaye, awaki, da karnuka a wajen. Niurka tana zauna ta kife fuskanta, alamar wadda ta kaɗaita kuma tana baƙin ciki. Tsufanta ya fi na shekarunta 34.
Da na taɓa kafaɗarta a hankali sai ta taga idanunta da suka daina gani shekaru 11 da suka shige ta kalle mu. Na gabatar da kaina da abokin wa’azina ta wajen ɗaga murya a kunnuwanta. Daga baya muka fahimci cewa Niurka ta yi wani ciwo mai makantarwa kuma mai kurmantar da mutum. Niurka kuma tana da ciwon sigari da ke bukata kula ƙwarai.
Da na saka Littafi Mai Tsarki a hannunta ta gane Littafi Mai Tsarki ne kuma ta ce ta ji daɗin karatun Nassosi kafin ta makance. To ta yaya zan koyar da gaskiyar Kalmar Allah mai faranta rai ga wannan halittar? Tun da ta san baƙaƙe, sai na fara saka baƙaƙe na roba a hannunta. Jin kaɗan sai ta gane su. Sai ta taɓa hannuna sa’ad da na yi alama, ta haka ta koyi baƙaƙen yaren kurame na Amirka. A hankali ta koyi wasu alamun. Tun da ni ma bai daɗe ba na fara koyon yaren, kowane lokacin nazari yana bukatar shiri na awoyi. Da yake ni da Niurka muna da muradin mu koyi yaran ƙwarai, hakan ya sa muka koyi yaren na alama da wuri.
Da wata ƙungiya ta bai wa Niurka na’ura mai taimakawa wajen sauraro ya kyauta ci gabanta. Ko da yake ba na’urar zamani ba ce, ta taimaka ƙwarai. Da yake ta fi shekara goma cikin duhu kuma ba ji, ta janye kanta daga mutane. Amma ruhun Allah ya motsa zuciyarta, kuma ya cika ta da sani, da bege da ƙauna. Ba da daɗewa ba, tare da taimakon sanda Niurka ta fara yawo a unguwarsu tana gaya wa wasu gaskiyar Littafi Mai Tsarki.
Niurka ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki da babarta da kuma ’ya’yan babar tata biyu mata. Tana yin shiri da kyau ta haddace kowane darasi a kan kari. Ɗaliban za su karanta sakin layin, sai ita kuma Niurka ta karanta tambaya daga littafinta na makafi. Sai abokiyar tafiyarta ta gaya wa Niurka amsar ta wajen yin magana a kunnenta ko kuma ta yi mata alama a hannunta.
Dukan ikilisiya suka taimaki Niurka kuma suka ƙarfafata. ’Yan’uwanta Kiristoci da yawa suna taimakon ta zuwa taro da kuma manyan tarurruka. Wasu suna zuwa hidima tare da ita. Ba da daɗewa ba Niurka ta ce mini: “Ba a taɓa nuna mini irin wannan ƙaunar ba.” Tana begen yin baftisma a taronmu na gunduma mai zuwa.
Sa’ad da muka shiga cikin layin gidansu Niurka, muka ganta tana zaune a kan dakali a cikin rana fuskanta sama tana murmushi. Na tambaye ta me ya sa take murmushi. Ta ce: “Ina tunani ne yadda duniya za ta zama aljanna a nan gaba. Kuna ina ganin kaina ne a can.”
[Hoto a shafi na 25]
Niurka da wasu ’yan ikilisiyarmu a gaban Majami’ar Mulki
[Hoto a shafi na 25]
Niurka tana gaya wa wasu abin da ta koya