Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 3/15 pp. 7-11
  • Ka Kasance Da Farin Ciki A Aurenka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Kasance Da Farin Ciki A Aurenka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Bin Ja-goran Jehobah
  • Menene Ke Sa Aure Ya Yi Nasara?
  • Ku Kasance da Haɗin Kai a Aure
  • Kada Ka Ba Iblis Dama
  • Yadda Kiristoci Za Su Yi Nasara a Aurensu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Aure Kyauta Ne Daga Allah
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Zaman Aure
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Ka Riƙe “Igiya Riɓi Uku” Cikin Aure
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 3/15 pp. 7-11

Ka Kasance Da Farin Ciki A Aurenka

“Ta wurin hikima a ke ginin gida: Ta wurin fahimi kuma a ke kafassa.”—MIS. 24:3.

1. Ta yaya ne Allah ya nuna hikima game da mutum na farko?

UBANMU mai hikima da ke sama ya san abin da ya dace da mu. Alal misali, Allah ya ga cewa idan yana son ya cim ma manufarsa, bai zai dace “ba mutum shi kasance shi ɗaya” a cikin lambun Adnin. Ainihin dalilin wannan manufar shi ne ma’aurata su haifi yara kuma su “mamaye duniya.”—Far. 1:28; 2:18.

2. Wane shiri ne Jehobah ya yi don amfanin dukan mutane?

2 Jehobah ya ce: “Sai in yi masa mataimaki mai-dacewa da shi.” Allah ya sa mutum na farko ya yi barci mai zurfi, kuma ya cire haƙarƙari guda daga jikin kamiltaccen mutumin, sai Allah ya mai da wannan haƙarƙarin mace. Sa’ad da Jehobah ya kawo wannan kamiltacciyar macen, Hauwa’u, ga Adamu, sai Adamu ya ce: “Wannan yanzu ƙashi ne daga ƙasusuwana, nama ne daga namana: za a ce da ita Mace, domin daga cikin Namiji aka ciro ta.” Hauwa’u ta dace ƙwarai da Adamu. Kowannensu zai kasance da halaye dabam dabam, duk da haka, su kamiltattu ne kuma an halicce su ne a cikin surar Allah. Saboda haka, Jehobah ne ya ɗaura aure na farko. Adamu da Hauwa’u ba su yi gardamar amincewa da wannan hurarren tsarin ba wanda zai sa su taimaka wa juna kuma su tallafa wa juna.—Far. 1:27; 2:21-23.

3. Yaya ne mutane da yawa suke bi da kyautar aure, kuma waɗanne tambayoyi ne hakan ya jawo?

3 Abin baƙin ciki shi ne, halin tawaye ne ya cika duniya a yau. Matsalolin da wannan halin ke jawowa ba daga Allah ba ne. Yawancin mutane sun raina kyautar aure da Allah ya bayar, suna ɗaukansa tsohon yayi, abin ban haushi ko rikici. Yawancin waɗanda suka yi aure suna kashe aurensu. Ana iya ƙin nuna wa yara ƙauna kuma iyaye suna iya yin amfani da yaransu don su amfane kansu. Yawancin iyaye ba sa nuna sauƙin hali, ko da yin hakan zai kawo salama da haɗin kai. (2 Tim. 3:3) Ta yaya ne za a ci gaba da kasancewa da farin ciki a aure a wannan lokaci mai wuya? Ta yaya ne kasancewa da haɗin kai zai iya sa a kawar da duk wani abin da zai iya raba aure? Menene za mu iya koya daga misalai na zamani na waɗanda suke farin ciki a aurensu?

Bin Ja-goran Jehobah

4. (a) Wace ja-gora ce Bulus ya bayar game da aure? (b) Ta yaya ne Kiristoci masu biyayya suke bin ja-gorar Bulus?

4 Manzo Bulus Kirista ya ba da hurarren ja-gora ga gwaurayen da suke son su sake yin aure, ya ce su yi hakan ne kawai “cikin Ubangiji.” (1 Kor. 7:39) Wannan ba sabuwar koyarwa ba ce ga Kiristocin da suke ƙarƙashin Doka a dā. Dokar Allah ga Isra’ilawa ta bayyana dalla-dalla cewa kada su “yi surukuta” da duk wani mutumin da ke a ƙasashen da suka kewaye su, waɗanda ba sa bauta wa Allah. Jehobah ya daɗa yin bayanin da ya taƙaita haɗarin da ke tattare da taka wannan hurarren mizanin. “Gama [wanda ba Ba’isra’ile ba ne] za shi juyadda ɗanka ga barin bina, domin su bauta ma waɗansu alloli: hakanan fushin Ubangiji za ya yi ƙuna a kanku, ya hallaka ka farat ɗaya.” (K. Sha 7:3, 4) Wane irin mizani ne Jehobah yake son bayinsa na zamani su bi game da wannan batun? Babu shakka, bawan Allah zai zaɓi aboki ko abokiyar aure wadda take “cikin Ubangiji” ne kawai, mai bauta wa Allah wanda ya keɓe kansa kuma ya yi baftisma. Bin ja-gorar Jehobah game da wannan zaɓin shi ne tafarki mafi kyau.

5. Ta yaya ne Jehobah da Kiristoci ma’aurata suke ɗaukan alkawuran aure?

5 Alkawarin da aka ɗauka na aure yana da tsarki a gaban Allah. Sa’ad da yake yin nuni ga aure na farko, Ɗan Allah, Yesu, ya ce: “Abin da Allah ya gama fa, kada mutum shi raba.” (Mat. 19:6) Mai zabura ya tuna mana muhimmancin alkawari: “Bari ku miƙa wa Allah hadayarku ta godiya, Ku ba Mai Iko Dukka, dukan hadayun da kuka alkawarta.” (Zab. 50:14, Littafi Mai Tsarki) Ko da yake waɗanda suka auri juna suna iya samun farin ciki, alkawuran da aka ɗauka a ranar ɗaurin aure suna da muhimmanci sosai kuma suna tattare da hakki.—K. Sha 23:21.

6. Menene za mu iya koya daga misalin Jephthah?

6 Yi la’akari da Jephthah, wanda alƙali ne a Isra’ila a ƙarni na 12 K.Z. Ya yi wannan alkawarin ga Jehobah: “Idan dai hakika za ka bada ’ya’yan Ammon a cikin hannuna: sa’annan za ya zama, ko minene da za ya fito ta ƙofofin gidana garin ya tarbe ni, sa’anda na dawo lafiya daga bin sawun Ammon, za ya zama na Ubangiji, zan bada shi hadaya ta ƙonawa.” Sa’ad da ya ga cewa ɗiyarsa, wadda ita kaɗai ce ya haifa, ita ce ta fito ta same shi a lokacin da ya komo gidansa da ke Mizpa, Jephthah ya nemi ya ƙarya alkawarinsa ne? A’a. Ya ce: “Na rigaya na buɗe bakina wurin Ubangiji, ba shi kuwa yuwuwa in koma ta kai.” (Alƙa. 11:30, 31, 35) Jephthah ya cika alkawarin da ya yi wa Jehobah, duk da cewa ba shi da wanda zai ci gaba da amsa sunansa. Alkawarin da Jephthah ya yi ya ɗan bambanta da alkawuran aure, amma cika alkawarin da ya yi ya zama misali mai kyau ga Kiristoci magidanta da matan aure game da alkawuran da suka ɗauka.

Menene Ke Sa Aure Ya Yi Nasara?

7. Waɗanne canje-canje ne sababbin ma’aurata suke bukatar su yi?

7 Yawancin ma’aurata suna yin farin ciki sosai sa’ad da suka tuna lokacin da suke zawarci. Abin farin ciki ne su san wanda za su aura nan gaba! Yawan lokacin da suke kasancewa tare zai sa su san juna sosai. Ko da sun yi zawarci na dogon lokaci ko a’a, yin wasu canje-canje na da muhimmanci a lokacin da suka zama mata da miji. Wani miji ya ce: “Babban matsalar da muka samu a farkon aurenmu ita ce sanin cewa muna bukatar mu nemi ra’ayin juna. Ya ɗan yi mana wuya mu ci gaba da riƙe dangantakar da ke tsakaninmu da abokanmu da kuma iyalanmu.” Wani miji, wanda ya yi aure shekaru 30 da suka shige ya fahimci cewa idan yana son ya kasance da daidaituwa a aurensa, yana bukatar ya yi “tunani game da mutum biyu.” Kafin ya amince da wani gayya ko ya ɗauki alkawari, ya kan tuntuɓi matarsa, bayan hakan sai ya yanke shawara, domin yana la’akari da abubuwan da su biyun suke so. A irin wannan yanayin, haɗin kai yana taimakawa.—Mis. 13:10.

8, 9. (a) Me ya sa tattaunawa tare yana da muhimmanci? (b) A waɗanne ɓangarori ne kasancewa da sauƙin hali zai iya taimakawa, kuma me ya sa?

8 A wasu lokatai aure yana haɗa mutane biyu da suke da al’adu dabam dabam. Game da wannan, suna bukatar su tattauna da juna sosai. Yadda suke magana da juna zai bambanta. Mai da hankali ga yadda abokiyar aurenka take magana da ’yan’uwanta zai taimaka maka ka san wadda za ka aura sosai. A wasu lokatai ba abin da aka ce ba amma yadda aka faɗi abin ne zai bayyana irin tunanin mutum. Kuma za a iya koyan abubuwa masu yawa daga abin da ba a ce ba. (Mis. 16:24; Kol. 4:6) Ana bukatar fahimi idan ana son a kasance da farin ciki.—Ka karanta Misalai 24:3.

9 Idan ya zo ga zaɓan irin wasa da nishaɗin da za a yi, yawanci sun ga cewa nuna sauƙin hali yana da muhimmanci. Kafin ku yi aure, wataƙila abokin aurenki yana yin wasu irin wasanni na guje-guje ko nishaɗi. Zai dace a yi wasu ’yan canje-canje a yanzu? (1 Tim. 4:8) Wannan tambayar ta shafi yawan lokacin da ake yi wajen dangi. Babu shakka, ma’aurata suna bukatar lokaci don su kasance tare wajen biɗar abubuwa na ruhaniya da sauransu.—Mat. 6:33.

10. Ta yaya ne kasancewa da sauƙin hali zai sa dangataka mai kyau ta kasance a tsakanin iyaye da ’ya’yansu da suka yi aure?

10 A lokacin da namiji ya yi aure, zai rabu da ubansa da uwarsa, ita ma matar haka. (Ka karanta Farawa 2:24.) Duk da haka, dokar Allah da ta ce mutum ya daraja ubansa da uwarsa ba ta da iyaka. Ko bayan sun yi aure, za su so su ɗan ziyarci iyayensu da kuma surukansu. Wani maigida, wanda ya yi aure shekaru 25 da suka shige ya ce: “A wasu lokatai, yana da wuya mutum ya biya bukatu dabam dabam na matarsa da na iyaye, ƙanne, da surukai. Farawa 2:24 tana taimaka mini sosai a lokacin da nake son na yanke shawarar yadda zan bi da wannan yanayin. Mutum yana bukatar ya cika hakkokin sauran ’yan’uwa da ke rataye a wuyansa, duk da haka wannan ayar ta nuna mini cewa cika hakkokin matata shi ne kan gaba.” Saboda haka, iyaye Kiristoci masu sauƙin hali za su fahimci cewa ’ya’yansu da suka yi aure a yanzu suna cikin iyali wadda mijin ne ke da ainihin hakkin yi wa iyalin ja-gora.

11, 12. Me ya sa nazari na iyali da kuma addu’a suke da muhimmanci ga ma’aurata?

11 Yin nazari na iyali yana da muhimmanci sosai. Abubuwan da yawancin iyalan Kiristoci suka shaida ya tabbatar da hakan. Wataƙila soma irin wannan nazarin ko kuwa ci gaba da yin sa a kowane lokaci ba zai yi sauƙi ba. Wani maigida ya ce: “Idan akwai abin da za mu iya canjawa, za mu so mu tabbatar da cewa mun manne wa tsari mai kyau na nazarin iyali a tun lokacin da muka yi aure.” Ya daɗa: “Abu ne mai ban al’ajabi in ga irin farin cikin da matata take yi sa’ad da ta karanta wasu abubuwa na ruhaniya masu motsawa a lokacin da muke yin nazari tare.”

12 Yin addu’a tare shi ma yana taimakawa. (Rom. 12:12) Idan miji da matarsa suna bauta wa Jehobah tare, dangantaka na kud da kud da suke da shi da Allah zai iya ƙarfafa dangantakar da suke morewa a aure. (Yaƙ. 4:8) Wani maigida Kirista ya ce: “Ba da haƙuri nan da nan domin kurakuran da aka yi da kuma ambata waɗannan kurakuran sa’ad da kuke yin addu’a tare wata hanya ce ta nuna baƙin ciki a kan ƙananan batutuwan da suke jawo fushi.”—Afis. 6:18.

Ku Kasance da Haɗin Kai a Aure

13. Wace shawara ce Bulus ya bayar game da dangantaka na kud da kud a aure?

13 Kiristoci ma’aurata suna bukatar su guje wa ayyukan da ke ƙasƙantar da dangantakar aure, kamar waɗanda suka zama gama gari a wannan duniyar da ta cika da lalata. Bulus ya ba da shawara game da wannan batun: “Mijin shi ba matatasa abin da ya wajabce ta: matan kuma hakanan ga mijinta. Matan ba ta da ikon jiki nata, sai miji: hakanan kuma mijin ba shi da ikon jiki nasa, sai matan.” Bayan haka, Bulus ya ba da wannan ja-gorar dalla-dalla: “Kada ku hana ma juna, sai dai da yardan juna domin kwanaki.” Me ya sa? “Da za ku maida kanku ga addu’a, ku sake gamuwa, domin kada Shaiɗan ya jarabce ku ta wurin rashin daurewarku.” (1 Kor. 7:3-5) Ta wajen ambata addu’a, Bulus ya nuna abin da ya kamata ya fi muhimmanci ga Kirista. Amma kuma ya bayyana dalla-dalla cewa kowane Kirista da ke da aure ya ko ta mai da hankali sosai ga bukatu na zahiri da ta zuciya na aboki ko abokiyar aurensa.

14. Ta yaya ne mizanan da ke cikin Nassi ya shafi dangantaka na kud da kud a aure?

14 Mata da miji suna bukatar su dinga gaya wa juna gaskiya, kuma suna bukatar su fahimci cewa nuna rashin kula a dangantakarsu yana iya jawo matsaloli. (Ka karanta Filibiyawa 2:3, 4; ka gwada da Matta 7:12.) Hakan ya tabbata a cikin ma’auratan da ɗaya a cikinsu ba ya cikin gaskiya. Ko da an sami rashin fahimta, Kirista zai iya daidaita al’amura ta wajen kasancewa da hali mai kyau, nuna alheri, da haɗin kai. (Ka karanta 1 Bitrus 3:1, 2.) Ƙaunar da muke yi wa Jehobah da kuma wadda mutum ya aura, tare da haɗin kai, duk za su taimaka a wannan ɓangaren na aure.

15. Wane gurbi ne daraja yake cikawa a aure mai farin ciki?

15 A sauran fasaloli ma, maigida mai kirki zai daraja matarsa. Alal misali, zai yi la’akari da yadda take ji, har ma a ƙananan batutuwa. Wani maigida da ya yi aure shekaru 47 da suka shige ya ce: “Har yanzu ban ƙware ba a wannan ɓangaren.” An umurci Kiristoci mata su daraja maigidansu. (Afis. 5:33) Faɗin abin da bai dace ba game da mijinsu, da kuma faɗin kurakuransa a gaban mutane ba ya nuna daraja. Misalai 14:1 ta tunasar da mu cewa: “Kowace mace mai-hikima ta kan gina ɗakinta: Amma mai-wauta ta kan rushe shi da hannuwa nata.”

Kada Ka Ba Iblis Dama

16. Ta yaya ne ma’aurata za su iya yin amfani da Afisawa 4:26, 27 a aurensu?

16 “Ku yi fushi, amma kada ku yi zunubi: kada rana ta faɗi kuna kan fushinku: kada kuwa ku ba Shaiɗan dama.” (Afis. 4:26, 27) Idan muka yi amfani da waɗannan kalaman, za su taimaka mana mu magance ko kuwa mu kauce wa samun matsala a aure. “Ban taɓa tuna lokacin da ni da maigidana muka sami wani saɓani kuma a ce ba mu tattauna batun tare ba ko da hakan zai ɗauki sa’o’i masu yawa don mu magance matsalar,” in ji wata ’yar’uwa. A lokacin da suka yi aure, ita da maigidanta sun ƙudurta cewa ba za su yarda rana ɗaya ta wuce ba tare da sun magance matsalolinsu ba. “Mun yanke shawara cewa, ko da mecece matsalar da muka samu, za mu yafe wa juna kuma mu mance matsalar don mu tashi washegari babu matsala.” Da haka, sun ƙi su “ba Shaiɗan dama.”

17. Ko da ma’aurata ba su dace da juna ba, menene zai iya taimaka musu?

17 Idan ka soma tunanin cewa da ka sani ba ka auri wadda ka aura ba fa? Kana iya samun kanka a cikin dangatakar da daɗinta bai kai na wasu ba. Duk da haka, tuna ra’ayin Mahalicci game da aure zai taimake ka. Bulus ya ba Kiristoci wannan hurarriyar shawarar: “Aure shi zama abin darajantuwa a wajen dukan mutane, gado kuma shi kasance mara-ƙazanta: gama da fasikai da mazinata Allah za shi shar’anta.” (Ibran. 13:4) Kuma kalaman da bai kamata a yi watsi da su ba su ne: “Igiya riɓi uku kuma ba shi tsunkuwa da sauri ba.” (M. Wa. 4:12) Idan mata da miji suka mai da hankali sosai ga tsarkake sunan Jehobah, za su manne wa junansu da kuma Allah. Suna bukatar su sa aurensu ya yi nasara, domin hakan zai ɗaukaka Jehobah, wanda shi ne Tushen aure.—1 Bit. 3:11.

18. Menene ya kamata ka gaskata game da aure?

18 Babu shakka, Kiristoci za su iya samun farin ciki a aurensu. Hakan na bukatar ƙoƙari da kuma nuna halayen Kirista, wanda ɗaya a cikinsu shi ne nuna sauƙin hali. A yau, ma’aurata marar iyaka da suke cikin ikilisiyoyin Shaidun Jehobah da ke dukan duniya sun tabbatar da cewa hakan zai yiwu.

Mecece Amsarka?

• Me ya sa samun farin ciki a aure abu ne da zai yiwu?

• Menene zai taimaka a samu nasara a aure?

• Waɗanne halaye ne ma’aurata suke bukatar su nuna?

[Hoto a shafi na 9]

Ma’aurata suna tattaunawa kafin su amince da gayyata ko kuwa ɗaukan alkawari

[Hoto a shafi na 10]

Ku yi ƙoƙarin warware matsaloli a ranar da kuka same ta, don kada ku ‘ba Iblis dama’

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba