Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 3/15 pp. 25-28
  • Kana Ɗaukan Mutane Yadda Jehobah Ya Ɗauke su?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kana Ɗaukan Mutane Yadda Jehobah Ya Ɗauke su?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Jehobah Yake Ɗaukan ’Yan’uwanmu
  • Ka Ɗauki ’Yan’uwanka Yadda Jehobah Ya Ɗauke Su
  • Yin Koyi da Jehobah a Hidimarmu
  • ‘’Yar Ruhu’ Tana Ɗaukaka Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ku Kasance da Hadin Kai a Ikilisiya
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Kada Ku Shari’anta Mutane Bisa Abin da Kuka Gani
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Kana da Muhimmanci a Kungiyar Jehobah!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 3/15 pp. 25-28

Kana Ɗaukan Mutane Yadda Jehobah Ya Ɗauke su?

“Kada rashin haɗa kai ya kasance ga jiki, sai dai gaɓoɓin su kula da juna, kula iri ɗaya.”—1 KOR. 12:25, Littafi Mai Tsarki.

1. Yaya ka ji sa’ad da ka fara shiga aljanna ta ruhaniya?

SA’AD da muka ware kanmu daga wannan muguwar duniyar kuma muka soma tarayya da mutanen Jehobah, wataƙila mun yi farin cikin shaida ƙauna da kulawar da Shaidun Jehobah suke nuna wa juna. Sun bambanta da mutanen da ke ƙarƙashin ikon Shaiɗan, waɗanda ba su da kunya, sun ƙi jinin juna kuma ba su yarda da juna ba! Mun shiga cikin aljanna ta ruhaniya wadda take cike da kwanciyar hankali da kuma haɗin kai.—Isha. 48:17, 18; 60:18; 65:25.

2. (a) Menene zai iya shafan ra’ayinmu game da wasu? (b) Menene muke bukatar mu yi?

2 Amma bayan wasu lokatai, muna iya soma kasancewa da ra’ayin da bai dace ba game da ’yan’uwanmu saboda ajizancinmu. Ajizancinmu yana iya sa mu faɗaɗa laifuffukan ’yan’uwanmu maimakon mu mai da hankali ga halayensu masu kyau. Gaskiyar ita ce, mun daina ɗaukansu yadda Jehobah ya ɗauke su. Idan hakan ya faru gare mu, muna bukatar mu mai da hankali ga ra’ayinmu kuma mu sa ra’ayinmu ya jitu da na Jehobah.—Fit. 33:13.

Yadda Jehobah Yake Ɗaukan ’Yan’uwanmu

3. Da menene Littafi Mai Tsarki ya kwatanta ikilisiyar Kirista?

3 Kamar yadda aka rubuta a 1 Korinthiyawa 12:2-26, manzo Bulus ya kwatanta ikilisiyar shafaffun Kiristoci da jikin da ke da “gaɓaɓuwa dayawa.” Kamar yadda gaɓaɓuwan jiki suka bambanta da juna, halaye da ƙwarewar waɗanda suke cikin ikilisiya su ma sun bambanta sosai. Duk da haka, Jehobah ya amince da dukan waɗanda suke cikin ikilisiya. Yana ƙaunarsu kuma yana ɗaukan kowannensu da tamani. Saboda haka, Bulus ya shawarce mu cewa dukan waɗanda suke cikin ikilisiya suna bukatar “su kula da juna, kula iri ɗaya.” Hakan na iya kasancewa da wuya domin halayen wasu suna iya bambanta da na mu.

4. Me ya sa muke bukatar mu daidaita ra’ayinmu game da ’yan’uwanmu?

4 Muna iya son mai da hankali ga kasawar ’yan’uwanmu. Idan muka yi haka, muna mai da hankali ne kawai ga ɓangare guda na hoton da muke kallo. Amma ra’ayin Jehobah ya bambanta sosai domin shi ya ga hoton gabaki ɗaya. Muna iya mai da hankali ga wani abin da ba ma so, amma shi kuwa Jehobah ya san komi game da mutumin, har da halayensa masu kyau. Idan muka ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu wajen yin koyi da Jehobah, hakan zai sa mu ɗaukaka ƙauna da kuma haɗin kai da ke cikin ikilisiya.—Afis. 4:1-3; 5:1, 2.

5. Me ya sa bai dace ba mu hukunta wasu?

5 Yesu ya san cewa mutane ajizai akwai su da son sūka. Ya gargaɗe mu: “Kada ku zartar, domin kada a zartar muku.” (Mat. 7:1) A yare na asali Yesu bai ce: “Kada ku zartar” ba, abin da ya ce shi ne: “Ku daina zartar.” Ya san cewa yawancin masu sauraronsa suna da halin sūkar wasu. Muna da irin wannan halin? Idan muna da irin wannan halin, muna bukatar mu ƙoƙarta sosai don mu canja halinmu, domin kada a yi mana hukunci mai tsanani. To wanene mu da za mu hukunta wanda Jehobah ya naɗa kuma yake amfani da shi a wani matsayi ko kuwa mu ce bai kamata ya kasance a cikin ikilisiya ba? Wataƙila ɗan’uwa yana da wasu kasawa, amma idan Jehobah ya ci gaba da amincewa da shi, zai dace mu ƙi shi ne? (Yoh. 6:44) Mun gaskata ƙwarai cewa Jehobah yana yi wa mutanensa ja-gora kuma idan ana bukatar a yi gyara, zai ɗauki mataki a lokacin da yake so?—Ka karanta Romawa 14:1-4.

6. Yaya ne Jehobah yake ɗaukan bayinsa?

6 Wani abin al’ajabi game da Jehobah shi ne cewa yana iya ganin abin da kowane Kirista zai iya zama sa’ad da ya zama kamili a sabuwar duniya. Kuma ya san irin ci gaban da suka riga suka samu a ruhaniya. Saboda haka, ba ya bukatar ya mai da hankali ga kowanne kasawa na mutum. Zabura 103:12 ta ce: “Kamar nisan gabas da yamma, hakanan ya kawar da saɓe saɓenmu, ya nisantadda su.” Ya kamata mu yi godiya sosai game da wannan!—Zab. 130:3.

7. Menene muka koya daga yadda Jehobah ya ɗauki Dauda?

7 Nassosi ya nuna mana cewa Jehobah yana mai da hankali ne ga halaye masu kyau na mutum. Allah ya kira Dauda “bawana Dauda . . . , wanda ya kiyaye dokokina, ya bi ni da dukan zuciyassa, domin shi yi abin da ke daidai a idanuna kaɗai.” (1 Sar. 14:8) Hakika, mun san cewa Dauda ya yi wasu abubuwan da ba su dace ba. Duk da haka, Jehobah ya zaɓi ya mai da hankali ga halayensa masu kyau domin ya san cewa Dauda yana da zuciya mai kyau.—1 Laba. 29:17.

Ka Ɗauki ’Yan’uwanka Yadda Jehobah Ya Ɗauke Su

8, 9. (a) Ta wace hanya ce za mu iya zama kamar Jehobah? (b) Da me za a iya kwatanta hakan, kuma wane darassi ne muka koya?

8 Jehobah yana iya karanta zuciyar mutum, amma mu ba za mu iya ba. Wannan ma wani dalili ne mai kyau da ya kamata ya hana mu hukunta wasu. Ba mu san dukan muradin mutum ba. Muna bukatar mu yi koyi da Jehobah ta wajen ƙin mai da hankalinmu ga ajizancin mutane, wanda zai ɓace nan da nan ba da daɗewa ba. Ba abu mai kyau ba ne mu yi koyi da Jehobah a wannan batun? Yin hakan zai sa mu kasance da dangantaka mai kyau da ’yan’uwanmu maza da mata.—Afis. 4:23, 24.

9 Alal misali, a ce akwai wani gidan da yake gab da faɗuwa, indararon duk sun kusan gama faɗuwa, tagogin duk sun ɓalle, kuma ruwa ya lalata silin. Yawancin mutane suna iya cewa a rushe gidan domin ba shi da kyaun gani. Amma wani yana iya ganin gidan kuma ya kasance da ra’ayi dabam. Yana iya ƙin mai da hankali ga yanayin gidan daga waje domin ya lura cewa ginin yana da ƙwari kuma zai gyaru. Ya sayi gidan kuma ya gyara shi kuma gidan ya yi kyau sosai. Bayan haka, masu wucewa suka ce gidan ya yi kyau sosai. Za mu iya zama kamar wannan mutumin wanda ya yi aiki tuƙuru don ya gyara wannan gidan? Maimakon mu mai da hankali ga kasawar ’yan’uwanmu, za mu iya duba halayensu masu kyau da kuma damar da suke da ita na samun ci gaba a ruhaniya? Idan muka yi haka, kamar Jehobah, za mu ƙaunaci ’yan’uwanmu domin halayensu.—Ka karanta Ibraniyawa 6:10.

10. Ta yaya ne shawarar da ke Filibbiyawa 2:3, 4 za ta taimaka mana?

10 Manzo Bulus ya ba da wasu shawarwarin da za su iya taimaka mana a dangantakarmu da dukan waɗanda suke cikin ikilisiya. Ya aririci Kiristoci: “Kada a yi kome domin tsaguwa, ko girman kai, amma a cikin tawali’u kowa ya maida wani ya fi kansa; ba dai kowa yana lura da nasa abu ba, amma kowane a cikinku yana lura da na waɗansu kuma.” (Filib. 2:3, 4) Tawali’u zai taimaka mana mu kasance da ra’ayin da ya dace game da wasu. Nuna cewa mun damu da wasu da kuma mai da hankali ga halayensu masu kyau zai taimaka mana mu ɗauki mutane yadda Jehobah ya ɗauke su.

11. Waɗanne canje-canje ne suka shafi wasu ikilisiyoyi?

11 Abubuwan da ke faruwa a duniya a ’yan kwanakin nan sun sa mutane sun ƙaura zuwa wurare dabam dabam. Wasu birane suna cike ne da mutanen da suka fito daga ƙasashe dabam dabam. Wasu a cikin mutanen da suka ƙaura zuwa yankinmu sun koyi gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki, kuma sun soma bauta wa Jehobah tare da mu. Waɗannan mutane ne daga “dukan kabilai da al’ummai da harsuna.” (R. Yoh. 7:9) A sakamakon haka, yawancin ikilisiyoyinmu suna cike ne da mutanen da suka fito daga ƙasashe dabam dabam.

12. Wane irin ra’ayi ne ya kamata mu kasance da shi game da juna, kuma me ya sa hakan zai iya zama ƙalubale a wasu lokatai?

12 A cikin ikilisiyarmu, wataƙila muna bukatar mu mai da hankali sosai ga kasancewa da ra’ayin da ya dace game da juna. Hakan ya tuna mana bin shawarar manzo Bitrus na nuna “sahihiyar ƙauna ta ’yan’uwa” kuma mu ‘yi ƙaunar junanmu daga zuciya mai-gaskiya.’ (1 Bit. 1:22) Nuna ƙauna ta gaskiya da kuma kula zai iya zama ƙalubale a wurin da mutanen da suka fito daga ƙasashe dabam dabam suke tare. Al’adar ’yan’uwanmu masu bi zai iya bambanta sosai da namu, kuma hakan zai iya haɗa da iliminsu, tattalin arzikinsu, da kuma yarensu. Yana yi maka wuya ka fahimci yadda wasu masu bi da suka fito daga wata ƙasa suke tunani da kuma yin abubuwa? Wataƙila su ma haka suke ji game da kai. Duk da haka, an umurci dukanmu: “Ku ƙaunaci [dukan] yan’uwanci.”—1 Bit. 2:17.

13. Wane irin gyara ne ya kamata mu yi wa tunaninmu?

13 Zai dace mu daidaita tunaninmu don mu ƙara faɗaɗa ƙaunar da muke yi wa dukan ’yan’uwanmu. (Ka karanta 2 Korinthiyawa 6:12, 13.) Mun taɓa samun kanmu muna cewa “Ni ba na nuna ƙabilanci, amma . . . ” sa’an nan mu soma ambata halaye marar kyau waɗanda muke ganin cewa sun zama ruwan dare a tsakanin wata kabila? Irin wannan tunanin zai iya nuna mana cewa muna bukatar kawar da halin ƙabilanci da ke zuciyarmu. Muna iya tambayar kanmu: ‘Ina yin iya ƙoƙarina a kowane lokaci don na san mutanen da suka fito daga wata ƙabilar dabam?’ Irin wannan bincika kai zai iya taimaka mana mu amince kuma mu ƙaunaci ’yan’uwanmu na dukan duniya.

14, 15. (a) Ka ba da misalin waɗanda suka daidaita ra’ayinsu game da wasu? (b) Ta yaya za mu iya yin koyi da su?

14 Littafi Mai Tsarki ya ba mu misalai masu kyau na waɗanda suka daidaita ra’ayinsu, ɗaya daga cikinsu shi ne manzo Bitrus. A matsayinsa na Bayahude, wataƙila Bitrus ba ya shiga gidan ’yan Al’ummai. Ka yi tunanin yadda ya ji sa’ad da aka ce masa ya ziyarci gidan ɗan Al’umma Karniliyus marar kaciya! Bitrus ya daidaita ra’ayinsa, domin ya fahimci cewa nufin Allah ne mutanen dukan al’ummai su zama sashen ikilisiyar Kirista. (A. M. 10:9-35) Shawulu, wanda ya zama manzo Bulus, shi ma ya daidaita tunaninsa kuma ya daina nuna ƙabilanci. Ya yarda cewa a dā yana ƙin jinin Kiristoci har ma ya “riƙa tsananta wa ikilisiyar Allah ƙwarai da gaske, har [yana] ta watsa ta.” Duk da haka, sa’ad da Ubangiji Yesu ya daidaita tunanin Bulus, ya yi canje-canje masu yawa har ma ya soma bin ja-gorar waɗanda yake tsanantawa a dā.—Gal. 1:13-20, Littafi Mai Tsarki.

15 Babu shakka, mu ma muna iya gyara halinmu da taimakon ruhun Jehobah. Idan muka ga cewa har yanzu muna ɗan nuna ƙabilanci, bari mu yi iya ƙoƙarinmu don mu kawar da irin wannan tunanin kuma mu “kiyaye ɗayantuwar Ruhu cikin ɗaurin salama.” (Afis. 4:3-6) Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu “yafa ƙauna, gama ita ce magamin kamalta.”—Kol. 3:14.

Yin Koyi da Jehobah a Hidimarmu

16. Menene nufin Allah ga mutane?

16 Manzo Bulus ya rubuta cewa: “A wurin Allah babu tara [nuna bambanci].” (Rom. 2:11) Nufin Jehobah ne cewa mutanen dukan al’ummai su zo su bauta masa. (Ka karanta 1 Timothawus 2:3, 4.) Saboda haka, ya shirya a yi “bishara ta har abada” ga “kowane iri da ƙabila da harshe da al’umma.” (R. Yoh. 14:6) Yesu ya ce: “Gona duniya ce.” (Mat. 13:38) Menene muhimmancin wannan a gare ka da iyalinka?

17. Ta yaya za mu iya taimaka wa dukan mutane?

17 Ba kowa ba ne zai iya zuwa wasu ƙasashe masu nisa don yin bisharar Mulki ga mutane ba. Duk da haka, muna iya yin wannan bisharar ga mutanen da suka fito daga wurare dabam dabam da suke zaune a yankinmu. Muna amfani da kowane zarafi na yin wa’azi ga dukan mutane, ba kawai waɗanda muka saba yi wa wa’azi ba? Me ya sa ba za ka ƙudurta ba cewa za ka yi wa’azi ga mutanen da ba a taɓa yi wa wa’azi ba sosai?—Rom. 15:20, 21.

18. Wane irin damuwa ne Yesu ya nuna wa mutane?

18 Yesu yana son ya taimaka wa dukan mutane. Hakan ya sa bai yi wa’azi a yanki ɗaya ba kawai. Wani labari a cikin Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa “ya yi yawo cikin dukan birane da ƙauyuka.” Bayan haka, “sa’anda ya ga taron, ya yi juyayi a kansu” kuma ya taimaka musu.—Mat. 9:35-37.

19, 20. Ta waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna damuwar da Jehobah da kuma Yesu suke nuna wa dukan mutane.

19 A waɗanne hanyoyi ne za ka iya nuna irin wannan halin? Wasu suna zuwa yin wa’azi a wasu sashen da ke yankinsu da ba a yawan zuwa wa’azi. Wannan zai iya haɗa da wuraren da ake kasuwanci, wuraren hutawa, tasoshin mota, ko kuwa a gaban manyan gidajen zama da ba su da sauƙin shiga. Wasu sun koyi sabon yare don su yi wa’azi ga masu yin wani yare dabam da suke zaune a yankinsu ko kuwa wasu rukunonin da ba a yawan yi musu wa’azi a dā. Koyar yadda ake gai da waɗannan mutanen da yarensu zai iya nuna musu cewa ka damu da su sosai. Idan ba za mu iya koyan wani yare ba, za mu iya ƙarfafa waɗanda suke yin hakan? Ba za mu so mu yi wasu maganganun da ba su dace ba ko kuwa mu tuhumi waɗanda suke koyan wani yare don su yi wa’azi ga mutanen da suka fito daga wata ƙasa. Dukan mutane suna da tamani a wurin Allah, kuma mu ma muna son mu kasance da irin wannan ra’ayin.—Kol. 3:10, 11.

20 Kasancewa da irin ra’ayin da Allah yake da shi game da mutane yana nufin yin wa’azi ga kowa, ko menene yanayinsu. Wataƙila wasu ba su da gidan kwana, ba su da tsabta, ko kuwa ’yan iska ne. Idan wasu mutane suka yi mana abin da ba ma so, ba zai dace ba mu kasance da ra’ayoyi marar kyau game da ƙasarsu ko kuwa wannan ƙabilar gabaki ɗaya ba. Akwai wasu mutanen da suka yi wa Bulus abin da bai dace ba, amma hakan bai hana shi yin wa’azi ga mutanen wannan ƙasar ba. (A. M. 14:5-7, 19-22) Ya tabbata cewa wasu za su saurare shi sosai.

21. Ta yaya ne kasancewa da ra’ayin Jehobah game da wasu zai taimake ka?

21 A yanzu mun fahimci cewa muna bukatar mu kasance da ra’ayin da ya dace, wato, ra’ayin Jehobah, a yadda muke bi da ’yan’uwa da ke ikilisiyarmu, ’yan’uwanmu da suka fito daga wasu ƙasashe, ko kuwa mutanen da muke saduwa da su a hidima. Idan muka ci gaba da nuna ra’ayin Jehobah sosai, hakan zai sa mu ƙarfafa salama da haɗin kai a tsakaninmu. Kuma za mu iya taimaka wa mutane su ƙaunaci Jehobah, Allahn da bai taɓa nuna ‘tara [son kai]’ ba amma yana ci gaba da nuna ƙauna ga kowa, “gama dukansu aikin hannuwansa ne.”—Ayu. 34:19.

Mecece Amsarka?

• Wane irin ra’ayi ne ya kamata mu kawar game da ’yan’uwanmu?

• Ta yaya za mu iya yin koyi da Jehobah a yadda muke ɗaukan ’yan’uwanmu?

• Waɗanne darussa ne ka koya game da yadda muke ɗaukan ’yan’uwanmu da suka fito daga ƙasashe dabam dabam?

• Ta yaya ne za mu iya yin koyi da ra’ayin Jehobah game da mutane sa’ad da muke yin wa’azi?

[Hoto a shafi na 26]

Ta yaya ne za ka iya sanin mutanen wata ƙabilar sosai?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba