Armageddon Yaƙin Allah Na Kawar Da Dukan Yaƙe-yaƙe
“A gare su mugunta ce ƙwarai mutum ya ƙashe ɗan’uwansa taliki; saboda haka a gare su yaƙin abin ƙyama ne marar kan gado, a abin da a yarensu ba su da kalmarsa.” KWATANCIN MUTANEN INUIT NA GREENLAND DA MAI BINCIKE FRIDTJOF NANSEN YA YI KE NAN A SHKEARA TA 1888.
WAYE ba zai so ya rayu a tsakanin jama’a da a gare su “yaƙi abin ƙyama ne kuma marar kan gado ba”? Waye ba zai so ya rayu a duniya ba, da kalmar nan yaƙi ba a san ta ba, domin ba a san yaƙi ba? Irin wannan duniya za ta kasance mafarki ne kawai, musamman ma idan muka sa rai mutane ne za su mai da duniyar ta kasance haka.
Amma, a annabcin Ishaya, Allah da kansa ya yi alkawari zai sa irin wannan duniya ta kasance: “Za su kuma bubbuge takubansu su zama garmuna, māsunsu kuma su zama lauzuna: al’umma ba za ta zāre ma al’umma takobi ba, ba kuwa za a ƙara koya yaƙi nan gaba ba.”—Ishaya 2:4.
A bayyane yake cewa a yau da duniya take da sojoji miliyan 20 da suke bakin aiki da kuma yaƙe-yaƙe ashirin da ake gabzawa a yanzu dole ne abubuwa su canja domin wannan alkawari ya cika. Ba abin mamaki ba ne cewa Jehobah Allah Maɗaukakin Sarki, zai saka hannu cikin sha’anin ’yan adam. Saka hannu da Jehobah zai yi cikin al’amuran ’yan adam ne Littafi Mai Tsarki ya kira Armageddon.—Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16.
Ko da yake kalmar nan “Armageddon” a baya bayan nan an yi amfani da ita wajen kwatanta duniya da ta ƙone da wutar nukiliya, wani ƙamus ya bayyana cewa ainihin ma’anar kalmar ita ce: “Yaƙi na ƙarshe tsakanin dakarun nagarta da ta mugunta.” Shin da gaske ne nagarta za ta yi nasara bisa mugunta, ko kuma dai irin wannan yaƙi ƙage ne kawai?
Sanin cewa Littafi Mai Tsarki ya yi magana a kai a kai game da ƙarshen mugunta ya kamata ya ƙarfafa mu. Mai zabura ya ce: “Masu-yin zunubi suke ƙare cikin duniya, masu-mugunta kuma kada su ƙara kasancewa.” (Zabura 104:35) Littafin misalai kuma ya ce: “Masu-adalci za su zauna cikin ƙasan, kamilai kuma za su wanzu a cikinta. Amma za a datse miyagu daga cikin ƙasan, za a tumɓuke masu-cin amana kuma.”—Misalai 2:21, 22.
Littafi Mai Tsarki ya nuna a bayyane cewa miyagu ba za su ba da kansu cikin salama ba; saboda haka za a bukaci yaƙi na Allah da zai kawar da mugunta haɗe da muguntar yaƙi. (Zabura 2:2) Sunan da Littafi Mai Tsarki ya bai wa wannan yaƙi na musamman, wato, Armageddon yana da muhimmanci ƙwarai.
Yaƙe-Yaƙe da Aka Yi a Dā Kusa da Megiddo
Kalmar nan “Armageddon” tana nufi “Dutsen Megiddo.” Birim Megiddo na dā, da filayen da suka kewaye shi na Jezreel, suna da tarihin yaƙe-yaƙe da gefe ɗaya ya yi nasara ƙwarai. “A dukan tarihi, Megiddo da kuma ƙwarin Jezreel wurare ne da aka yi yaƙe-yaƙe da suka canja hanyar rayuwar ’yan adam,” haka ɗan tarihi Eric H. Cline ya rubuta a cikin littafinsa (Yaƙe-Yaƙen Armageddon) The Battles of Armageddon.
Kamar yadda Cline ya nuna, yaƙe-yaƙe da aka yi a Meggido sau da yawa sun kasance da nasara. Sojojin Mangol da suka ci yawancin Asiya a yaƙi a ƙarni ta 13, an yi nasara na farko a kansu ne a wannan ƙwarin. A kusa da Megiddo, sojojin Britaniya a ƙarƙashin shugabancin Janar Edmond Allenby suka yi nasara bisa mutanen Turks a Yaƙin Duniya na Ɗaya. Wani ɗan tarihin sojoji ya kwatanta nasarar Allenby da cewa yana “ɗaya daga cikin yaƙe-yaƙen da aka ci da sauri kuma wanda aka yi nasara sosai a dukan tarihi.”
Yaƙe-yaƙen da aka yi nasara ƙwarai na Littafi Mai Tsarki ma an yi su kusa da Megiddo. A nan ne Alƙali Barak ya yi nasara bisa sojojin Kan’aniyawa a ƙarƙashin shugabancin Sisera. (Alƙalai 4:14-16; 5:19-21) Gideon da mutanansa 300, ya ci sojoji masu yawa na Midiyanawa a wannan wurin. (Alƙalai 7:19-22) Sarki Saul da ɗansa Jonathan sun mutu a Dutsen Gilboa da ke kusa, sa’ad da sojojin Filistiyawa suka yi nasara bisa sojojin Isra’ila.—1 Sama’ila 31:1-7.
Domin inda yake, Megiddo da kuma ƙwari na kusa sun ga yaƙe-yaƙe masu yawa a cikin shekaru 4,000 da suka shige. Wani ɗan tarihi ya ƙirga aƙalla 34!
Tarihin Megiddo da kuma wurin da ya kasance ya shafi yadda aka yi amfani da wannan kalmar “Armageddon” a alamance. Ko da yake kalmar ta bayyana sau ɗaya ne kawai cikin Littafi Mai Tsarki, yadda ta bayyana a cikin littafin Ru’ya ta Yohanna ya nuna ƙwarai cewa Armageddon zai taɓa rayuwar mutane da yawa a duniya.
Abin da Armageddon Yake Nufi a Littafi Mai Tsarki
Ko da yake yawancin yaƙe-yaƙe da aka yi a Megiddo sun kasance da nasara, babu ko ɗaya cikinsu da ya kawar da mugunta. Babu wanda da ya kasance na sojojin nagarta ne da sojojin mugunta da gaske. Hakika, irin wannan yaƙin babu shakka zai kasance ne daga Allah. Kamar yadda Yesu ya taɓa cewa, “Babu wani managarci sai ɗaya, Allah.” (Luka 18:19) Bugu da ƙari, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Armageddon yaƙin Allah ne.
A cikin Littafi Mai Tsarki, littafin Ru’ya ta Yohanna ta ce za a tattara “sarakunan dukan duniya” zuwa yaƙin babbar rana ta Allah Mai-iko duka.” (Ru’ya ta Yohanna 16:14) Sai annabcin ya ce: “Aka tattara su a wurin da a ke ce da shi da Ibrananci Har–Magedon” ko kuma Armageddon.a (Ru’ya ta Yohanna 16:16) Daga baya, Ru’ya ta Yohanna ya yi bayani cewa “sarakunan duniya, da rundunoninsu, sun taru su yaƙi wanda ke kan dokin, da kuma runduna tasa.” (Ru’ya ta Yohanna 19:19) Kuma wannan mutumin da ke kan doki, ba wani ba ne Yesu Kristi ne.—1 Timothawus 6:14, 15; Ru’ya ta Yohanna 19:11, 12, 16.
Me za mu ce daga waɗannan ayoyin? Armageddon yaƙi ne tsakanin Allah da rundunonin ’yan adam marasa biyayya. Me ya sa Jehobah da kuma Ɗansa, Yesu Kristi , za su yi wannan yaƙin? Abu ɗaya da Armageddon zai yi shi ne zai “hallaka masu hallaka duniya.” (Ru’ya ta Yohanna 11:18) Ƙari ga haka, zai kawo duniya mai zaman lafiya, “bisa ga alkawarinsa, muna sauraron . . . sabuwar duniya, inda adalci yake zaune.”—2 Bitrus 3:13.
Me Ya Sa ake Bukatar Armageddon?
Yana da wuya ka yi tunanin cewa Jehobah, ‘Allah na ƙauna’ zai yi amfani da Ɗansa, “sarkin salama” ya yi yaƙi? (2 Korinthiyawa 13:11; Isha. 9:6) Fahimtar dalilansu babu shakka zai taimaka wajen fahimtar dalilin haka. Littafin Zabura ya kwatanta Yesu da jarimi. Me ya sa yake yaƙi? Zabura ta bayyana cewa, Kristi ya hau, “domin gudunmuwar gaskiya da tawali’u da adilci.” Yana yaƙi ne domin ya ƙi mugunta kuma yana ƙaunar adalci.—Zabura 45:4, 7.
Hakan nan kuma Littafi Mai Tsarki ya kwatanta yadda Jehobah yake ji game da rashin adalci da yake gani a duniya ta yau. Annabi Ishaya ya rubuta: “UBANGIJI ya gani, ya ji haushi kuma, da ya ga babu gaskiya.” Ya sa adilci kamar sulke, kwalkwalin ceto kuma a bisa kansu; ya sa tufafi na ɗaukar pansa domin rufin sutura, himma kuma misalin alkyabba.”—Isha. 59:15, 17.
Idan har miyagu ne suke riƙe da mulki, mutane masu adalci ba za su sami salama da kāriya ba. (Misalai 29:2; Mai Wa’azi 8:9) Ba za mu iya raba miyagun mutane da yin lalaci da kuma mugunta ba. Saboda haka, salama da yin adalci na dindindin za su kasance sa’ad da aka kawar da miyagu. Sulemanu ya rubuta cewa: “Mai-mugunta abin pansa ne domin mai-adilci.”—Misalai 21:18.
Tun da Allah ne zai yi hukunci, mu tabbata cewa duk hukunci da zai yi wa mugu zai kasance mai adalci ne. Ibrahim ya yi tambaya: “Mai-shari’an dukan duniya ba za ya yi daidai ba?” Amsa da Ibrahim ya samu ita ce Jehobah mai adalci ne a kullum! (Farawa 18:25) Bugu da ƙari, Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa Jehobah ba ya jin daɗin halaka miyagu; yana yin haka ne sa’ad da babu wani mafita.—Ezekiel 18:32; 2 Bitrus 3:9.
Fahimci Cewa Armageddon Yaƙi ne na Gaske
A ɓangaren wanene za mu kasance a lokacin wannan yaƙi? Yawancinmu muna tsammanin cewa muna tare ne da dakarun adalci. Amma ta yaya za mu tabbata hakan? “Ku biɗi adilci, ku biɗi tawali’u” in ji annabi Zephaniah. (Zephaniah 2:3) Nufin Allah ne dukan ire-iren “mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.”—1 Timothawus 2:4.
Fahimtar gaskiya game da Jehobah da kuma niyarsa na kawar da mugunta daga duniya ita ce matakin farko na samun ceto. Aikata nagarta kuma ita ce mataki na biyu, da za ta sa mu sami tagomashin Allah da kuma kāriyarsa.
Idan muka ɗauki waɗannan matakai masu muhimmnaci, to, za mu iya sauraron Armageddon, yaƙin da zai kawo ƙarshen dukan yaƙe-yaƙe na ’yan adam. Sa’ad da wannan yaƙin ya ƙare, mutane a ko’ina za su fahimci cewa lalle yaƙi abin ƙyama ne marar kan gado. ‘Ba kuwa za su ƙara koyon yaƙi ba.’—Ishaya 2:4.
[Hasiya]
a Domin bayani a kan ko Armageddon wuri ne na zahiri, dubi talifin nan “Masu Karatu Sun Yi Tambaya,” da ke shafi na 29.
[Bayanin da ke shafi na 3]
An kira lokaci da Allah zai saka hannu a al’amuran ’yan adam Armageddon
[Hoto a shafi na 5]
Sa’ad da wannan yaƙin ya ƙare, mutane a ko’ina za su fahimci cewa lalle yaƙi abin ƙyama ne marar kan gado