Ka Kusaci Allah
Mai Lura da Ya San Tamaninmu Luka 12:6, 7
‘ZUCIYARMU ta ba mu laifi.’ Da wannan kalmomin, Littafi Mai Tsarki ya nuna mana cewa a wasu lokatai zuciyarmu za ta iya sa mu riƙa ganin muna da laifi. Hakika, tana iya sa ma mu ji ba mu cancanci Allah ya ƙaunace mu ko ya kula da mu ba. Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya ba mu wannan tabbacin: “Allah ya fi zuciyarmu girma, ya kuwa san abu duka.” (1 Yohanna 3:19, 20) Allah ya san mu fiye da yadda muka san kamu. Yadda yake ganinmu ya bambanta ƙwarai da yadda muke ganin kanmu. To yaya tamaninmu a idanun wanda ya fi muhimmanci, Jehobah Allah? Za a sami amsa daga cikin wani kwatanci da Yesu ya yi amfani da shi a wasu lokatai biyu.
Yesu ya taɓa cewa “a kan sayarda gwarare biyu a bakin penny guda.” (Matta 10:29, 31) A Luka 12:6, 7, Yesu ya ce: “Ba a kan sayar da gwara biyar a bakin anini huɗu ba? ko ɗaya kuwa a cikinsu ba a manta da shi wurin Allah ba.” Wannan kwatanci mai sauki amma mai ma’ana ya koyar da mu yadda Jehobah yake ganin kowane bawansa.
Gwarare su ne tsuntsaye mafiya araha da ake ci. Babu shakka cewa Yesu ya lura da mata matalauta, wataƙila mamarsa ma, suna sayan waɗannan tsuntsayen domin su yi wa iyalansu abinci. Da saba ɗaya na assariyon, wanda bai fi naira shida ba a kuɗin zamani, mai saye sai ya sayi gwarare biyu. Waɗannan tsuntsaye domin araharsu, da saba biyu sai mai saye ya sayi ba gwarare huɗu ba amma guda biyar, ƙarin ɗayan gyara ne.
Yesu ya yi bayani cewa ko gwara ɗaya cikinsu “ba a manta da shi wurin Allah” kuma ba ya faɗuwa ‘ƙasa sai da sanin’ Uban ba. (Matta 10:29) Dukan lokaci da gwara ɗaya ta faɗi ƙasa wataƙila domin ta ji ciwo ko kuma ta sauka domin ta nemi abinci Jehobah yana da sani. Ƙanƙanuwar tsuntsuwa da Jehobah ya halitta, ko yaya ƙanƙantan ta Jehobah ba zai manta ta ba. Hakika, suna da muhimmanci a gare shi, domin halittu ne masu rai. Ka fahimci manufar kwatancin Yesu?
A koyarwarsa Yesu sau da yawa yana amfani da kwatanci, ya kwatanta manyan abubuwa da ƙananan abubuwa. Alal misali, Yesu ya ce: “Hankaki! Ai, ba sa shuka, ba sa girbi, ba su da taska ko rumbu, amma kuwa Allah yana cishe su. Sau nawa martabarku ta ninka ta tsuntsaye!” (Luka 12:24) A yanzu darasin kalmomin Yesu game da gwarare ya bayyana: Idan Jehobah yana kula da waɗannan ƙananan tsuntsaye, ai zai fi ma kula da mutane da suke ƙaunarsa kuma suke bauta masa!
Bisa ga kalmomin Yesu, bai kamata mu ji cewa ba mu cancanci kula daga Allah wanda ya fi “zuciyarmu” ba. Ba abin farin ciki ba ne mu fahimci cewa Mahaliccinmu yana ganin tamaninmu fiye da yadda muke ganin tamanin kanmu?
[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 15]
Sparrows: © ARCO/D. Usher/age fotostock