Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 4/1 pp. 11-14
  • Ya Gani, Kuma Ya Jira

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ya Gani, Kuma Ya Jira
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Halin Yin Addu’a
  • Yana da Tabbaci Yana Kuma a Faɗake
  • Jehobah Ya Kawo Sauki da Albarkatai
  • Ya Lura, Kuma Ya Jira
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Ya Sami Ƙarfafawa Daga Wajen Allahnsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Allahnsa Ya Ƙarfafa Shi
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Ya Kāre Bauta ta Gaskiya
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 4/1 pp. 11-14

Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu

Ya Gani, Kuma Ya Jira

ILIYA yana da muradin ya kaɗaita cikin Addu’a ga Ubansa na samaniya. Amma taron jama’a da ta kewaye shi ba da daɗewa ba ta ga annabin gaskiya na Jehobah ya kira wuta daga sama, babu shakka mutane da yawa cikinsu suna so su sami tagomashinsa. Kafin Iliya ya hau sololon Dutsen Kamel kuma ya yi addu’a ga Jehobah, ya faskanci wani aiki marar daɗi. Dole ya yi magana da Sarki Ahab.

Bambanci tsakanin waɗannan mutane biyu babu iyaka. Ahab da ke sanye da tufafi masu kyau na sarauta, mai haɗama ne, ɗan ridda mai raunannan ƙuduri. Iliya kuma yana sanye da tufafin annabi, wanda wataƙila aka yi da gashin rakumi ko kuma na akuya, mutum ne mai gaba gaɗi, aminci, da kuma bangaskiya. Wannan rana da ta kusa faɗuwa ta bayyana irin halin waɗannan mutane biyu.a

Wannan rana ce ta kunya ga Ahab da kuma masu bautar Ba’al. Addinin arna da Ahab da matarsa, Sarauniya Jezebel suke yaɗawa a masaurata ƙabila goma ta Isra’ila an tabbatar na ƙarya ne. An falasa Ba’al. Wannan allah marar rai ya kasa ta da wuta wajen amsa roƙo, rawa da kuma zubar da jini na annabawansa. Ba’al ya kasa ceton waɗannan mutane 450 daga halakarsu. Amma wannan allah na ƙarya ya kasa kuma a wata hanya dabam. Fiye da shekara uku, annabawan Ba’al suna roƙonsa ya kowa ƙarshen fari da ya addabi ƙasar, amma Ba’al ya kasa yin haka. Ba da daɗe wa ba, Jehobah kansa zai nuna cewa shi ne Allah na gaskiya ta wajen kawo ƙashen farin.—1 Sar. 16:30–17:1; 18:1-40.

Amma yaushe ne Jehohah zai yi haka? Wane hali ne Iliya zai nuna kafin zuwa wannan lokaci? Kuma menene za mu koya daga wannan mutumin mai bangaskiya? Bari mu gani yayin da muka bincika larabi da ke rubuce cikin 1 Sarakuna 18:41-46.

Halin Yin Addu’a

Iliya ya tunkari Ahab ya ce: “Ka hau, ka ci, ka sha; gama da motsin ruwan sama mai-yawa.” (Aya ta 41) Wannan mugun sarki ya koyi wani abu kuwa daga abin da ya faru a wannan rana? Labarin bai faɗa dalla-dalla ba, kuma daga labarin ba mu ga wata kalma ta tuba ba, ko kuma roƙo ga annabi ya roƙi Jehobah ya gafarta masa. A’a, Ahab dai kawai “ya hau garin ya ci ya sha.” (Aya ta 42) Iliya kuma fa?

“Amma Iliya ya hau ƙwanƙolin Karmel; ya sunkuyadda kansa a ƙasa, ya sa fuskatasa tsakanin guwawunsa.” Sa’ad da Ahab ya tafi ya cika tumbinsa, Iliya ya sami zarafin ya yi addu’a ga Ubansa. Ka lura da yadda ya yi zaman tawali’u a nan, Iliya yana zaune a ƙasa ya sunkuyar da kansu kusa da gwiwowinsa. Menene Iliya yake yi? Hakika mun sani. Littafi Mai Tsarki a Yaƙub 5:18, ya gaya mana cewa Iliya ya yi addu’a ya roƙi a kawo ƙarshen farin. Kuma babu shakka ya yi wannan addu’ar ce a sololon Kamel.

Da farko, Jehobah ya ce: “ni ma in aike da ruwa a bisa ƙasa.” (1 Sar. 18:1) Saboda haka iliya ya yi addu’a saboda nufin Ubansa ya cika, kamar yadda Yesu ya koyar da mabayansa shekara dubu ɗaya daga baya.—Matta 6:9, 10.

Misalin Iliya ya koya mana abubuwa da yawa game da addu’a. Abin da ya cika tunanin Iliya shi ne a cika nufin Ubansa. Sa’ad da muka yi addu’a, yana da kyau tu nuna cewa: “Idan mun roƙi komi daidai da nufinsa [Allah], yana jinmu.” (1 Yoh. 5:14) A bayyane yake cewa, muna bukatar mu san nufin Allah domin mu yi addu’a da zai ji, hakan dalili ne kuwa mai kyau na sa karatun Littafi Mai Tsarki ya kasance bangaren rayuwarmu na kullum. Babu shakka, Iliya ma yana so ya ga cewa an kawo ƙarshen farin domin wahala da mutanen ƙasarsu suke sha. Wataƙila kuma ya yi godiya ƙwarai ganin mu’ujiza da Jehobah ya aikata a wannan rana. Damuwa da yanayin wasu da kuma godiya ya kamata su kasance cikin addu’o’inmu muma.—2 Korinthiyawa 1:11; Filibbiyawa. 4:6.

Yana da Tabbaci Yana Kuma a Faɗake

Iliya ya tabbata cewa Jehobah zai kawo ƙarshen wannan farin, amma ba shi da tabbaci ko yaushe Jehobah zai yi haka. To, menene annabin ya yi kafin lokacin? Ka lura da abin da aya ta 43 ta ce: “Ya ce ma baransa, Ka hau yanzu, ka duba wajen teku. Ya hau, ya duba, ya ce, Babu komi. Ya ce, Ka sake tafiya har so bakwai.” Misalin Iliya ya koya mana akalla abubuwa biyu. Na farko, ka lura da tabbacin annabin. Da kuma yadda yake a faɗake.

Iliya ya yi ɗokin ganin tabbaci cewa Jehobah ya yi kusa ya aikata, saboda haka ya aiki baransa ya hau wuri mai tudu ya dubi alamun ruwan sama. Da baran ya dawo ya ba shi wannan rahoto mai kashe gwiwa: “Babu komi.” Hakika kuwa babu kome, babu ma alamar hadari. Yanzu, ka lura da wani abu na musamman? Ka tuna, Iliya ba da daɗewa ba ya gaya wa Sarki Ahab: “Gama da motsin ruwan sama mai-yawa.” Me ya sa annabin zai faɗi haka tun da babu ma ko alamar hadari?

Iliya ya san alkawari da Jehobah ya yi. Da yake shi annabin Jehobah ne kuma waƙilinsa, ya tabbata cewa Allahsa zai cika alkawarinsa. Iliya yana da tabbaci mai ƙarfi sosai kamar ma yana jin ruwan yana zuba. Zai tuna mana yadda Littafi Mai Tsarki ya kwatanta Musa: “Ya jimre, kamar yana ganin wanda ba shi ganuwa.” Haka Allah yake a gare ka? Ya ba mu dalilai masu yawa na ba da irin wannan bangaskiya a gare shi da kuma alkawuransa.—Ibranawa 11:1, 27.

Sai, ka lura da yadda Iliya yake a faɗake. Ya aiki baransa, ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba, amma har sau bakwai! Muna iya tunanin baran ya gaji da irin wannan aiki ɗaya, amma Iliya ya ci gaba da ɗokin ganin alama kuma bai yi sanyin gwiwa ba. A ƙarshe, bayan tafiyarsa ta bawai, baran ya ba da rahoto: “Ga shi, wani girgije yana tasowa daga cikin teku, ƙanƙani kamar tafin hannun mutum.” (Aya ta 46) Za ka iya tunanin yadda wannan baran ya miƙa hannunsa yana kwatanta girma girgije da ya gani a wuraran Babban Teku?b Wataƙil hakan bai burge baran ba. Amma ga Iliya wannan girgijen yana da muhimmnaci ƙwarai. Sai ya ba wa baransa umurni na gaggawa: “Tashi, ka ce ma Ahab, Ka shirya karusarka, ka gangara, kada ruwa ya tare ka.”

Har ila, Iliya ya kafa mana misali mai kyau a yau. Muma yanzu muna rayuwa ne a lokacin da Allah zai aikata domin ya cika nufinsa. Iliya ya jira ƙarshen fari; bayin Allah a yau suna jiran ƙarshen wannan malalaciyar duniya. (1 Yoh. 2:17) Har sai Jehobah Allah ya aikata, muna bukatar mu kasance a faɗake, kamar yadda iliya ya kasance a faɗake. Ɗan Allah Yesu, Ya shawarci mabiyansa: “Ku yi tsaro fa: gama ba ku sani ba cikin kowace rana Ubangijinku ke zuwa.” (Mat. 24:42) Yesu yana nufi ne cewa mabiyansa za su kasance cikin duhu game da lokacin da matuƙa za ta so? A’a, domin ya yi bayani na dogon lokaci game da yadda kwanaki na ƙarshe za su kasance. Kowanenmu zai iya koyo game da wannan alamun “cikar zamani.”—Matta 24:3-7.c

Kowane ɓangaren waɗannan alamun sun ba da tabbaci mai ƙarfi. Irin wannan tabbci sun isa ne su motsa mu mu kasance cikin gaggawa? Ɗan ƙaramin girgije da ya tashi ya tabbatar wa Iliya cewa Jehobah ya kusa ya aikata. Shin wannan annabi mai bangaskiya ya ji kunya ne?

Jehobah Ya Kawo Sauki da Albarkatai

Labarin ya ci gaba: “Ya zama kuwa kamin an jima kaɗan, sararin sama ya yi baƙi ƙirin da hadari da iska, aka yi babban ruwa kuwa. Ahab ya hau, ya tafi Jezreel.” (Aya ta 45) Abubuwa suka soma faruwa cikin hanzari. Sa’ad da baran Iliya yana idar da saƙon annabin ga Ahab, wannan ƙaramin girgijen ya zama da yawa, ya cika kuma ya duhunta dukan sama. Iska mai ƙarfi ta busa. A ƙarshe, bayan shekaru uku da rabi, ruwan sama ya zuba a kan ƙasar Isra’ila.d Busashiyar ƙasa ta sha ruwa. Da ruwan saman ya yi ƙarfi, kogin Kishon ta cika, babu shaka ta wanke jinin annabawan Ba’al da aka kashe. Kuma aka bai wa Isra’ilawa ’yan tawaye zarafin wanke hannunsu daga bautar Ba’al a ƙasar.

Hakika Iliya ya yi begen cewa abubuwa za su kasance haka! Shin Ahab zai tuba kuwa daga bautar Ba’al? Abubuwa da suka faru a wannan rana sun isa su kawo irin wannan canji. Hakika ba za mu iya sanin abin da Ahab yake tunaninsa ba a wannan lokaci. Labari kawai ya gaya mana cewa sarki “ya hau, ya tafi Jezreel.” Ya koyi wani abu kuwa? Ya ƙuduri aniyar canja halinsa kuwa? Abubuwa da suka faru daga baya sun nuna cewa amsar a’a ce. Duk da haka rana ba ta faɗi ba tukuna ga Ahab, ko kuma Iliya.

Annabin Jehobah ya bi wannan hanyar da Ahab ya bi. Doguwar tafiya tana gabansa. Amma wani abin mamaki ya faru.

“Hannun Ubangiji kuwa yana bisan Iliya; ya kuwa ɗamarce gidinsa, ya yi gudu a gaban Ahab har ƙofar Jezreel.” (Aya ta 46) A bayyane yake cewa “Hannun Ubangiji” ya yi aiki bisa Iliya a hanya ta musamman. Jezreel tana da nisan mil 20, kuma Iliya ba matashi ba ne.e Ka yi tunanin wannan annabin yana ɗaure doguwar rigarsa a kwankwasonsa, domin ƙafafunsa su sami damar tafiya, sai kuma ya fara gudu a hanyar da ta cika da ruwa, yana gudu da sauri har ya tarar kuma ya wuce karusar sarki!

Hakika wannan albarka ce ga Iliya! Jin irin wannan ƙarfi a jikinsa, wataƙila fiye ma da yadda ya ji sa’ada da yake matashi, hakika zai kasance abu ne na farin ciki. Hakan zai tuna mana annabce-annabce da suka ba da tabbacin cikakken lafiya da ƙarfi ga masu aminci a aljanna a duniya da take zuwa. (Isha. 35:6; Luk 23:43) Babu shakka, sa’ad da Iliya yana gudu a wannan jikakkiyar hanya ya sani cewa Ubansa, Allah kaɗai na gaskiya, ya aminci da sa shi!

Jehobah yana shirye ya ba da albarka. Motsawa domin mu sami waɗannan albarkatu sun cancani dukan wani ƙoƙari da za mu yi. Kamar Iliya, muna bukatar mu kasance a faɗake, muna gwada tabbaci mai ƙarfi da suka nuna cewa Jehobah ya yi kusa ya aikata a waɗannan miyagun lokatai na gaggawa. Kamar Iliya, muna da cikakkun dalilai na tabbaci ga alkawuran Jehobah, “Allah na gaskiya.”—Zabura 31:5.

[Hasiya]

a Domin ƙarin bayani, dubi talifin nan “Ya Kāre Bauta ta Gaskiya,” a Hasumiyar Tsaro ta Janairu-Maris 2008.

b A yau, wannan Babbar Teku ita ce Meditareniya.

c Domin ƙarin bayani game da tabbacin cewa kalmomin Yesu suna faruwa a yau, dubi babi na 9 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka buga.

d Wasu suna mamaki ko Littafi Mai Tsarki ya yi baki biyu ne game da tsawon lokacin farin. Dubi akwati da ke shafi na 13.

e Ba da daɗewa ba bayan wannan Jehobah ya umurci Iliya ya ƙoyar da Elisha, wanda za a sani da “wanda dā ya kan zuba ruwa a hannuwan Iliya.” (2 Sar. 3:11) Elisha ya zama baran Iliya, hakika yana taimakon mutumin don ya tsofa.

[Box/Hoto a shafi na 13]

Yaya Tsawon Lokacin Fari na Zamanin Iliya?

Iliya annabin Jehobah ya sanar da Sarki Ahab cewa farin nan na dogon lokaci zai ƙare ba da daɗewa ba. Wannan ya faru ne a “cikin shekara ta uku” wato an ƙirga daga ranar da Iliya ya sanar da aukuwan farin. (1 Sar. 18:1) Jehobah ya sa aka yi ruwan sama bayan Iliya ya ce hakan zai faru. Wasu za su ce, farin ya ƙare ne a cikin shekararsa ta uku saboda haka bai kai shekara uku ba. Amma kuma, Yesu da kuma Yaƙub sun gaya mana cewa farin “shekara uku ne da wata shidda.” (Luka 4:25; Yaƙub 5:17) Wannan ba baki biyu ba ne?

A’a. Domin lokacin rani a Isra’ila ta dā yana da tsawo ƙwarai yana kai wa wata shida. Babu shakka cewa Iliya ya zo wurin Ahab ne ya sanar da shi game da farin sa’ad da rani ya riga ya yi nisa sosai. Wato, farin ya riga ya fara ne da kusan rabin shekara. Saboda haka, sa’ad da Iliya ya sanar da ƙarshen farin “a cikin shekara ta uku” daga lokacin da ya sanar da shi, farin ya riga ya yi shekara uku da rabi. “Shekara uku da wata shida” sun riga sun cika sa’ad da mutanen suka taru su ga gwaji mai girma a kan Dutsen Kamel.

Ka lura da lokacin da Iliya ya ziyarci Ahab da farko. Mutanen sun gaskata cewa Ba’al “shi ke tafi kan girgije,” allahn da zai kawo ruwan sama domin ya kawo ƙarshen rani. Idan rani ya wuce lokacinsa, mutane sai su fara mamaki: ‘Ina Ba’al? Yaushe ne zai kawo damina?’ Da Iliya ya sanar cewa ba za a yi ruwa ba ko raɓa sai ya faɗa hakika ya dami masu bauta wa Ba’al.— 1 Sarakuna 17:1.

[Inda aka Dauko]

Pictorial Archive (Near Eastern History) Est.

[Hoto a shafi na 12]

Addu’ar Iliya ta nuna muradinsa na son ganin an yi nufin Allah

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba