Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 5/15 pp. 21-25
  • Ka Sami Ci Gaba A Ruhaniya Ta Wajen Bin Misalin Bulus

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Sami Ci Gaba A Ruhaniya Ta Wajen Bin Misalin Bulus
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Tsarin Nazari na Bulus
  • Shawulu ya Koyi ya Yi Ƙaunar Mutane
  • Yadda Bulus ya Ɗauki Kansa
  • Ka Yi “Tseren . . . da Jimiri”
  • Ka Yi Ƙarfin Zuciya, Jehobah Zai Taimake Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Sa’ad da Ba Ni da Karfi Ne Nake da Karfi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Yesu Ya Zabi Shawulu
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 5/15 pp. 21-25

Ka Sami Ci Gaba A Ruhaniya Ta Wajen Bin Misalin Bulus

“Na yi yaƙi mai-kyau, na kure fagen, na kiyaye imani.”—2 TIM. 4:7.

1, 2. Waɗanne canje-canje ne Shawulu mutumin Tarsus ya yi a rayuwarsa, kuma wane aiki mai muhimmanci ne ya karɓa?

MUTUMIN yana da ƙwaƙwalwa sosai kuma yana ɗaukan mataki. Amma ‘yana zamansa a dā a cikin sha’awoyin jikinsa.’ (Afis. 2:3) Daga baya ya kira kansa “mai-saɓo ne dā, mai-tsanani, mai-ɓatanci.” (1 Tim. 1:13) Wannan shi ne Shawulu mutumin Tarsus.

2 Da sannu-sannu, Shawulu ya yi canje-canje a rayuwarsa. Ya yi watsi da hanyoyin rayuwarsa ta dā kuma ya ƙoƙarta sosai don kada ya ‘biɗa wa kansa amfani, amma abin da za ya amfane mutane masu-yawa.’ (1 Kor. 10:33) Ya zama mutum mai hankali kuma ya nuna ƙauna ga waɗanda suka sha wahalar ƙiyayyarsa a dā. (Ka karanta 1 Tassalunikawa 2:7, 8.) Ya rubuta cewa: ‘[Na zama] mai-hidima,’ ya kuma daɗa, “Ni, wanda na zama koma bayan baya cikin tsarkaka duka, a gareni aka bada wannan alheri, in yi wa’azin wadatar Kristi wurin Al’ummai, wadata wadda ta fi ƙarfin a biɗa.”—Afis. 3:7, 8.

3. Ta wace hanya ce yin nazarin wasiƙun Bulus da kuma labarin hidimarsa zai taimaka mana?

3 Shawulu, wanda aka san shi da sunan nan Bulus, ya sami fitaccen ci gaba a ruhaniya. (A. M. 13:9) Wata tabbatacciyar hanya guda na hanzarta ci gabanmu a gaskiya ita ce, yin nazarin wasiƙun Bulus da kuma labaran hidimarsa kuma mu bi misalin bangaskiyarsa. (Ka karanta 1 Korinthiyawa 11:1; Ibraniyawa 13:7.) Bari mu ga yadda yin hakan zai motsa mu mu kasance da tsarin yin nazari mai kyau, mu ƙaunaci mutane sosai, kuma mu kasance da ra’ayin da ya dace game da kanmu.

Tsarin Nazari na Bulus

4, 5. Ta yaya Bulus ya amfana ta wajen yin nazari?

4 Bulus yana ɗan ilimin Nassi domin shi Bafarisi ne da aka koyar “a wurin sawayen Gamaliel, aka karantadda [shi] bisa ga tsararren riƙo na shari’ar ubanninmu.” (A. M. 22:1-3; Filib. 3:4-6) Nan da nan bayan baftismarsa ya “tafi . . . cikin Arabiya,” wataƙila Hamada na Suriya ko kuma wani waje da babu surutu a ƙasar da ta kutsa cikin Teku na Arabiya da ya dace don yin bimbini. (Gal. 1:17) Mai yiwuwa Bulus yana son ya yi bimbini a kan nassosin da suka tabbatar da cewa Yesu ne Almasihu. Bugu da ƙari, Bulus yana son ya shirya don aikin da ke gabansa. (Ka karanta A. M. 9:15, 16, 20, 22.) Bulus ya yi ƙoƙari sosai don ya yi bimbini a kan abubuwa na ruhaniya.

5 Ilimi na Nassi da fahimi da Bulus ya samu daga yin nazari ya taimake shi ya koyar da gaskiya da kyau. Alal misali, a majami’ar da ke Antakiya a Bisidiya, Bulus ya yi amfani da aƙalla ayoyi biyar da ya yi ƙaulinsu daga Nassosi na Ibrananci da suka tabbatar da cewa Yesu ne Almasihu. Bulus ya ambata ayoyin nassosi sau da yawa ba tare da ya yi ƙaulinsu kai tsaye ba. Ayoyin Littafi Mai Tsarki da ya yi amfani da su don ƙaryata musunsu ya rinjayi mutane sosai wanda hakan ya sa “Yahudawa da yawa, da kuma waɗanda suka shiga Yahudanci, masu ibada, suka bi Bulus da Barnaba,” don su ƙara koyo. (A. M. 13:14-44) Shekaru da yawa bayan haka sa’ad da rukunin Yahudawan da ke zaune a ƙasar Roma suka je wajensa a masaukinsa, Bulus ya yi musu bayani “yana shaida mulkin Allah, yana nema ya rinjaye su a kan zancen Yesu, daga cikin Attaurat ta Musa da annabawa kuma.”—A. M. 28:17, 22, 23.

6. Menene ya taimaki Bulus ya kasance da aminci sa’ad da yake fuskantar gwaji?

6 Sa’ad da yake fuskantar gwaji, Bulus ya ci gaba da bincika Nassosi kuma ya samu ƙarfi daga saƙonsu da aka hure. (Ibran. 4:12) Sa’ad da aka kama shi a Roma kafin a kashe shi, Bulus ya gaya wa Timothawus ya kawo masa “littattafai” da kuma ‘fatu masu rubutu.’ (2 Tim. 4:13) Wataƙila waɗannan littattafan sashen Nassosi na Ibrananci ne da Bulus ya yi amfani da su wajen yin nazarinsa mai zurfi. Tsarin nazarin Littafi Mai Tsarki ya taimaki Bulus ya samu sani na Nassosi kuma hakan yana da muhimmanci don ya kasance da aminci.

7. Ka ambata amfanin da za ka samu idan kana yin nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai.

7 Nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai, tare da yin bimbini sosai zai taimake mu mu samu ci gaba a ruhaniya. (Ibran. 5:12-14) Mai zabura ya rera waƙa game da amfanin Kalmar Allah yana cewa: “A gareni shari’ar bakinka Ta fi dubban zinariya da azurfa. Dokokinka sun hikimtadda ni, har na fi maƙiyana; Gama suna tare da ni tuttur. Na kawasda sawayena daga kowace hanyar mugunta, domin in lura da maganarka.” (Zab. 119:72, 98, 101) Kana da tsarin nazarin Littafi Mai Tsarki? Kana shirin yin aiki a hidimar Allah a nan gaba ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki a kullum da kuma yin bimbini a kan abin da ka karanta?

Shawulu ya Koyi ya Yi Ƙaunar Mutane

8. Ta yaya Shawulu ya bi da waɗanda ba sa bin Yahudanci?

8 Kafin ya zama Kirista, Shawulu yana da himma don addininsa, amma ba ya ƙaunar mutanen da ba sa bin Yahudanci. (A. M. 26:4, 5) Da amincewarsa, ya kalli yadda wasu Yahudawa suka jefi Istafanus. Hakan ya ƙarfafa Shawulu, domin yana ganin ya dace da aka kashe Istafanus. (A. M. 6:8-14; 7:54–8:1) Hurarren labarin ya ce: “Amma Shawulu ya ɓarnatadda ekklesiya, yana shiga kowane gida, yana jawo maza da mata, yana jefa su a kurkuku.” (A. M. 8:3) Ya “bi su da tsanani har ga waɗansu birani na ƙetaren iyaka.”—A. M. 26:11.

9. Menene ya faru da Shawulu da ya sa ya sake bincika yadda yake bi da mutane?

9 Sa’ad da Ubangiji Yesu ya bayyana a gaban Shawulu, yana kan hanyar zuwa Dimashƙa don ya tsananta wa almajiran Kristi. Mafificin hasken Ɗan Allah ya makantar da Shawulu kuma ya dangana da taimakon mutane. Sa’ad da Jehobah ya yi amfani da Hananiya don ya buɗe idon Shawulu, halin Shawulu game da mutane ya canja gabaki ɗaya. (A. M. 9:1-30) Sa’ad da ya zama mabiyin Kristi, ya yi iya ƙoƙarinsa ya bi da dukan mutane yadda Yesu yake bi da su. Hakan na nufin zai daina mugunta kuma ya zauna “lafiya da dukan mutane.”—Ka karanta Romawa 12:17-21.

10, 11. Ta yaya Bulus ya nuna wa mutane ƙauna ta gaskiya?

10 Bulus bai gamsu kawai da zaman lafiya da mutane ba. Yana son ya nuna musu ƙauna ta gaskiya, kuma hidimar Kirista ta ba shi wannan zarafin. A tafiyar hidimarsa ta farko, ya yi wa’azin bishara a Asiya Ƙarama. Duk da tsanantawa mai tsanani, Bulus da abokansa sun mai da hankali ga taimaka wa masu tawali’u su soma bin Kiristanci. Sun sake ziyartar Listra da Ikoniya, duk da cewa ’yan hamayya a waɗannan biranen sun nemi su kashe Bulus a dā.—A. M. 13:1-3; 14:1-7, 19-23.

11 Daga baya, Bulus da abokansa suka nemi masu zuciyar kirki a birnin Makidoniya da ke Filibbi. Wata da ta soma bin addinin Yahudawa, mai suna Lidiya ta saurari bishara kuma ta zama Kirista. Hukumomi sun yi wa Bulus da Sila bulala kuma suka jefa su kurkuku. Amma Bulus ya yi wa yarin wa’azi, a sakamakon hakan, shi da iyalinsa suka yi baftisma kuma suka soma bauta wa Jehobah.—A. M. 16:11-34.

12. Menene ya motsa Shawulu mai wulakantar da mutane ya zama manzo mai nuna ƙauna na Yesu Kristi?

12 Me ya sa Shawulu mai tsananta wa mutane a dā ya soma bin imanin waɗanda yake tsananta ma wa? Menene ya motsa wannan mutum mai wulakantar da mutane ya zama manzo mai kirki da ƙauna, wanda yake shirye ya sadaukar da ransa don mutane su koyi gaskiya game da Allah da Kristi? Bulus da kansa ya ba da amsa: “Amma sa’anda Allah, wanda . . . ya kira ni kuma bisa ga alherinsa, yana nufi ya bayana Ɗansa a cikina.” (Gal. 1:15, 16) Bulus ya rubuta wa Timothawus: “Na sami jinƙai dalilin wannan, domin ta wurina, ni da ke babba, Yesu Kristi shi bayana tsawon haƙurinsa duka, domin gurbi ga waɗannan da za su bada gaskiya gareshi gaban nan zuwa rai na har abada.” (1 Tim. 1:16) Jehobah ya gafarta wa Bulus, kuma samun irin wannan alheri da jin ƙai sun motsa shi ya nuna wa mutane ƙauna ta wajen yi musu wa’azin bishara.

13. Menene ya kamata ya motsa mu mu nuna wa mutane ƙauna, kuma ta yaya za mu yi hakan?

13 Jehobah yana gafarta mana zunubanmu da kurakuranmu. (Zab. 103:8-14) Mai zabura ya yi tambaya: “Idan kai, ya Ubangiji, za ka ƙididdiga laifofi, wa za ya tsaya, ya Ubangiji?” (Zab. 130:3) Idan ba don jin ƙan Allah ba, da babu wani a cikinmu da zai sami farin cikin yin bauta mai tsarki, ko kuwa mu sa ran samun rai madawwami. Allah ya yi mana alheri sosai. Saboda haka, kamar Bulus, ya kamata mu nuna wa mutane ƙauna ta wajen yi musu wa’azi da kuma koya musu gaskiya da kuma ƙarfafa ’yan’uwanmu masu bi.—Ka karanta Ayukan Manzanni 14:21-23.

14. Ta yaya za mu iya faɗaɗa hidimarmu?

14 Bulus yana son ya samu ci gaba a matsayin mai wa’azin bishara, kuma misalin Yesu ya taɓa zuciyarsa. Ɗaya a cikin hanyoyin da Ɗan Allah ya nuna ƙauna da babu kamarta ga mutane ita ce ta aikinsa na wa’azi. Yesu ya ce: “Girbi hakika yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. Ku yi addu’a fa ga Ubangijin girbi, shi aike ma’aikata cikin girbinsa.” (Mat. 9:35-38) Bulus ya aikata cikin jituwa da duk wani roƙon da ya yi don samun ƙarin ma’aikata ta wajen zama mai aiki da himma. Kai kuma fa? Za ka iya kyautata hidimarka? Ko kuwa za ka ƙara lokacin da ka ke yi a aikin wa’azin Mulki, wataƙila ta wajen tsara rayuwarka don ka zama majagaba? Bari mu nuna ƙauna ta gaskiya ga mutane ta wajen taimaka musu su “riƙe . . . maganar rai kankan.”—Filib. 2:16; Littafi Mai Tsarki.

Yadda Bulus ya Ɗauki Kansa

15. Ta yaya Bulus ya ɗauki kansa idan aka gwada da ’yan’uwansa Kiristoci?

15 A matsayin Kirista mai hidima, Bulus ya kafa mana misali na musamman a wata hanyar kuma. Duk da cewa yana da gata masu yawa a cikin ikilisiyar Kirista, Bulus ya san cewa bai cancanci samun wannan albarka ba kuma ba wai ya same su ba ne domin iyawarsa. Ya fahimci cewa ya sami albarka ne domin alherin Allah. Bulus ya fahimci cewa sauran Kiristocin su ma masu hidimar bishara ne da suka ƙware. Duk da matsayin da yake da shi a cikin mutanen Allah, ya kasance mai tawali’u.—Ka karanta 1 Korinthiyawa 15:9-11.

16. Ta yaya Bulus ya nuna tawali’u da filako game da batun kaciya?

16 Ka yi la’akari da yadda Bulus ya magance matsalar da ta taso a birnin Suriya ta Antakiya. Ikilisiyar Kirista da ke wurin ta rabu don batun kaciya. (A. M. 14:26–15:2) Tun da yake an naɗa Bulus ya yi ja-gora wajen yi wa ’yan Al’umma marar kaciya wa’azi, zai iya ɗaukan kansa a matsayin wanda ya ƙware wajen bi da waɗanda ba Yahudawa ba ne da kuma magance matsaloli. (Ka karanta Galatiyawa 2:8, 9.) Sa’ad da ƙoƙarce-ƙoƙarcensa bai magance batun ba, cikin tawali’u da filako ya bi shawarar da aka bayar ta zuwa wajen hukumar mulki da ke Urushalima don tattauna batun. Sa’ad da hukumar mulki ta saurari batun kuma ta yanke shawara, Bulus ya ba da haɗin kai sosai kuma suka naɗa shi ya zama ɗaya cikin ’yan saƙonsu. (A. M. 15:22-31) Ta hakan Bulus ya ‘gabatar da kansa’ wajen ban girma ga ’yan’uwansa.—Rom. 12:10b.

17, 18. (a) Wane irin hali ne Bulus ya nuna wa waɗanda suke cikin ikilisiyoyi? (b) Menene abin da dattawan Afisa suka yi sa’ad da Bulus yake son ya tafi ya koya mana game da halinsa?

17 Bulus mai tawali’u bai nisanta kansa daga ’yan’uwansa da ke cikin ikilisiyoyi ba. Maimakon haka, ya kusance su sosai. A ƙarshen wasiƙar da ya rubuta wa Romawa, ya gai da fiye da mutane 20 kuma ya ambata sunansu. Ba inda aka sake ambata sunayen yawancinsu a cikin Nassosi, kuma kaɗan ne kawai suke da gata na musamman. Amma su bayin Jehobah ne masu aminci, kuma Bulus ya ƙaunace su sosai.—Rom. 16:1-16.

18 Halin tawali’u da abokantaka na Bulus ya ƙarfafa ikilisiyoyi. Bayan saduwarsa ta ƙarshe da dattawan da suka fito daga Afisa, sun “fāɗa ma wuyan Bulus, suna sumbatasa, yawancin baƙinzuciya da su ke yi domin kalma ne wadda ya faɗi, cewa, ba za su ƙara ganin fuskatasa ba.” Tafiyar mutum mai fahariya da ba ya kusantar mutane ba zai sa su yi hakan ba.—A. M. 20:37, 38.

19. Ta yaya za mu nuna “tawali’u” a yadda muke bi da Kiristoci masu bi?

19 Dole ne dukan waɗanda suke son su sami ci gaba a ruhaniya su kasance da tawali’u yadda Bulus ya yi. Ya gargaɗi Kiristoci masu bi kada su yi “kome domin tsaguwa, ko girman kai, amma a cikin tawali’u kowa ya maida wani ya fi kansa.” (Filib. 2:3) Ta yaya za mu bi wannan shawara? Hanya ɗaya ita ce ta wajen ba da haɗin kai ga dattawan ikilisiyarmu, mu bi ja-gorarsu kuma mu amince da shawarar da suka tsai da. (Ka karanta Ibraniyawa 13:17.) Wata hanya kuma ita ce ta wajen daraja dukan ’yan’uwanmu a cikin ikilisiya. Ikilisiyoyin mutanen Jehobah sun ƙunshi mutanen da suka fito daga ƙasashe, al’adu, kabilu da kuma wurare dabam dabam. Kamar Bulus, bai kamata ba ne mu ma mu koyi yadda za mu bi da dukan mutane cikin ƙauna ba tare da son kai ba? (A. M. 17:26; Rom. 12:10a) An ƙarfafa mu mu “karɓi juna, kamar yadda Kristi kuma ya karɓe [mu], zuwa ga darajar Allah.”—Rom. 15:7.

Ka Yi “Tseren . . . da Jimiri”

20, 21. Menene zai taimake mu mu yi nasara a tseren rayuwa?

20 Ana iya kamanta rayuwar Kirista da tsere mai nisa. Bulus ya rubuta: “Na kure fagen, na kiyaye imani: saura, an ajiye mini rawanin adalci, wanda Ubangiji, adalin mai-shari’a, za ya ba ni a wannan rana: ba kuwa ni kaɗai ba, amma dukan waɗanda sun ƙaunaci bayyanuwassa.”—2 Tim. 4:7, 8.

21 Bin misalin Bulus zai taimake mu mu yi nasara a tseren rai madawwami. (Ibran. 12:1) Bari mu yi iya ƙoƙarinmu mu ci gaba da samun cin gaba a ruhaniya ta wajen samun tsarin nazari mai kyau, ta wajen nuna ƙauna ga mutane sosai, da kuma kasancewa da halin tawali’u.

Yaya Za Ka Amsa?

• Ta yaya Bulus ya amfana daga yin nazarin Nassosi a kai a kai?

• Me ya sa nuna ƙauna ga mutane sosai yake da muhimmanci ga Kiristoci na gaskiya?

• Samun waɗanne halaye ne zai taimake ka ka bi da mutane ba son kai?

• Ta yaya misalin Bulus zai taimake ka ka ba da haɗin kai ga dattawan ikilisiyarka?

[Hoto a shafi na 23]

Ka samu ƙarfafa daga Nassosi kamar Bulus

[Hoto a shafi na 24]

Ka nuna wa mutane ƙauna ta wajen yi musu wa’azin bishara

[Hoto a shafi na 25]

Ka san abin da ya sa Bulus ya kusance ’yan’uwansa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba