Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 7/1 p. 11
  • Allah Mai Hanzarin Gafartawa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Allah Mai Hanzarin Gafartawa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Makamantan Littattafai
  • Ya Koyi Gafartawa Daga Wurin Ubangijinsa
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Ya Koyi Gafartawa Daga Wurin Ubangijinsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ya Kasance da Aminci a Lokacin Gwaji
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Za Ka Iya Ci Gaba da Yin Kokari Kamar Bitrus
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 7/1 p. 11

Ka Kusaci Allah

Allah Mai Hanzarin Gafartawa

Yohanna 21:15-17

“KAI, ya Ubangiji, mai-hanzarin gafartawa kuwa.” (Zabura 86:5) Da waɗannan kalmomi masu ƙarfafawa, Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa Jehobah Allah ne mai karimci wajen gafartawa. Wani abin da ya faru a rayuwar manzo Bitrus ya nuna cewa Jehobah yana yin “gafara a yalwace.”—Ishaya 55:7.

Bitrus yana ɗaya daga cikin abokanan Yesu na kusa. Duk da haka, a daren ƙarshe na rayuwar Yesu a duniya, Bitrus ya ji tsoro kuma ya yi zunubi mai tsanani. A farfajiyar da ke kusa da fadar da ake tuhumar Yesu, Bitrus ya musanci sanin Yesu a fili, ba sau ɗaya ba har sau uku. Bayan da Bitrus ya musanci sanin Yesu na uku, Yesu ya “waiwaya, ya dubi Bitrus.” (Luka 22:55-61) Za ka iya yin tunanin yadda Bitrus ya ji sa’ad da Yesu ya zuba masa idanu? Da ya fahimci tsananin zunubin da ya yi, sai Bitrus ya “fashe da kuka.” (Markus 14:72, Littafi Mai Tsarki) Wannan manzon da ya tuba ƙila ya yi tunani ko musun sanin Yesu da ya yi sau uku ya sa Allah ba zai gafarta masa ba.

Bayan tashinsa daga matattu, tattaunawar da Yesu ya yi da Bitrus babu shakka ya kawar masa da dukan wata shakka game da ko an gafarta wa Bitrus. Yesu bai yi masa baƙar magana ba ko kuma ya la’ance shi. Maimakon haka, ya tambayi Bitrus: ‘Kana ƙaunata?’ Bitrus ya amsa: “I, Ubangiji; ka sani ina sonka.” Yesu ya ce masa: “Ka yi kiwon ’ya’yan tumakina.” Yesu ya sake tambayar, kuma Bitrus ya sake ba da amsa kamar dā, wataƙila da ƙarin kuzari. Yesu ya ce: “Ka zama makiyayin tumakina.” Sai kuma Yesu ya sake tambayar ta uku: “Kana sona?” Yanzu “zuciyar Bitrus ta ɓāci” ya ce: “Ubangiji, ka san abu duka: ka sani ina sonka.” Yesu ya amsa: “Ka yi kiwon ’yan tumakina.”—Yohanna 21:15-17.

Me ya sa Yesu ya yi tambayoyin da ya riga ya san amsarsu? Yesu yana iya ganin abin da ke zuciyar mutum, saboda haka ya san cewa Bitrus yana ƙaunarsa. (Markus 2:8) Ta wajen yin waɗannan tambayoyin, Yesu ya bai wa Bitrus zarafin ya tabbatar da ƙaunarsa har sau uku. Kalmomin Yesu, “ka yi kiwon tumakina. . . . Ka zama makiyayin tumakina. . . . Ka yi kiwon ’yan tumakina,” sun tabbatar wa manzon da ya tuba cewa har yanzu an yarda da shi. Ga shi kuma, Yesu ya ba shi aikin ya kula da dukiyarsa mafi tamani, wato, mabiyan Yesu masu kama da tumaki. (Yohanna 10:14, 15) Hakika Bitrus ya sami kwanciyar hankali sanin cewa har Yanzu Yesu ya yarda da shi!

Babu shakka, Yesu ya gafarta wa manzonsa da ya tuba. Tun da yake Yesu yana kwaikwayon Ubansa ne sosai, za mu iya cewa Jehobah ma ya gafarta wa Bitrus. (Yohanna 5:19) Jehobah ba mai jinkirin gafarta wa ba ne, shi Allah ne mai jinƙai wanda yake “hanzarin gafarta” wa mai zunubin da ya tuba. Hakika, hakan yana da ban ƙarfafa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba