Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 6/15 pp. 22-26
  • Kada Ka Bar “Ƙaunarka Ta Fari”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kada Ka Bar “Ƙaunarka Ta Fari”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Menene ya Tabbatar Maka Cewa ka Sami Gaskiya?
  • Ka Ƙarfafa Ƙaunarka ta Fari
  • Ka Bincika Kanka
  • Abubuwa Masu Yawa da za Mu Yi Godiya Dominsu
  • Kada Ku Bar Ƙaunar da Kuke wa Juna ta yi Sanyi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • “Wajibi Ne Ka Ƙaunaci Jehobah Allahnka”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Jehobah Yana Kaunarka Sosai!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Ka Ƙaunaci Allah Da Yake Ƙaunarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 6/15 pp. 22-26

Kada Ka Bar “Ƙaunarka Ta Fari”

“Ka riƙe abin da ka ke da shi da kyau.”—R. YOH. 3:11.

1, 2. Yaya ka ji sa’ad ka tabbata cewa abin da kake koya game da Jehobah gaskiya ne?

K A TUNA lokacin da ka fara sanin abin al’ajabi da Jehobah ya ba mutane masu biyayya? Idan a dā kana cikin wani addini ne, yaya ka ji sa’ad da aka bayyana maka nufin Allah a cikin Nassi ko kuma sa’ad da aka bayyana maka wasu koyarwa na Nassi da suke da wuya a dā? Wataƙila ka fahimci cewa ba a koya maka gaskiya game da Allah ba. Amma kana jin daɗi yanzu don ka san gaskiya. Idan iyayenka Kiristoci ne, ka tuna yadda ka ji sa’ad da ka tabbata cewa abin da kake koya game da Allah gaskiya ne kuma kana iya ƙoƙarinka ka yi abin da ka koya?— Rom. 12:2.

2 Yawancin ’yan’uwa Kirista za su gaya maka cewa sun yi murnar yin kusa da Jehobah, kuma suna godiya da ya jawo su. (Yoh. 6:44) Farin cikin da suka yi ne ya motsa su su kasance a hidimar Kirista. Suna cike da farin ciki shi ya sa suke son su bayyana wa mutane abubuwan da suka koya. Ka taɓa jin haka?

3. Menene yanayin ikilisiyar da ke Afisa sa’ad da Yesu ya aika musu saƙo?

3 Sa’ad da yake jawabi game da ikilisiyar Kirista na Afisa a ƙarni na farko, Yesu ya yi magana game da ‘ƙaunarsu ta fari.’ Afisawa suna da halaye masu kyau, duk da haka, ƙaunar da suka nuna wa Jehobah da farko ta yi sanyi. Saboda haka, Yesu ya ce musu: “Na san ayyukanka, da wahalarka da haƙurinka, na sani kuma ba ka iya jimrewa da miyagun mutane, ka kuma auna waɗanda ke ce da kansu manzanni, ba kuwa haka su ke ba, har ka iske su maƙaryata; ka yi haƙuri kuma, ka jimre sabili da sunana, ba ka gaji ba. Amma ina da wannan game da kai, da ka bar ƙaunarka ta fari.”—R. Yoh. 2:2-4.

4. Me ya sa saƙon da Yesu ya aika wa Afisawa yake da muhimmanci a yau?

4 Gargaɗin da Yesu ya yi wa Afisawa da kuma sauran ikilisiyoyi a cikin littafin Ru’ya ta Yohanna ya dace domin abubuwan da suka faru da suka ɗauki dogon lokaci a tsakanin shafaffun Kiristoci daga shekara ta 1914 har yanzu. (R. Yoh. 1:10) Duk da haka, a yau wasu Kiristoci za su iya “barin ƙaunarsu ta fari” ga Jehobah da kuma gaskiya. Don haka, bari mu tattauna yadda za ka iya mannewa, sabonta, da kuma daɗa ƙauna da ƙwazon da kake da ita a dā ga Allah na gaskiya, ta wajen tuna abubuwan da ka shaida kuma ka yi bimbini a kansu.

Menene ya Tabbatar Maka Cewa ka Sami Gaskiya?

5, 6. (a) Menene kowane Kirista ya kamata ya gaskata? (b) Menene ya sa ka gaskata cewa Shaidun Jehobah suna koyar da gaskiya? (c) Menene zai taimaki mutum ya riƙe ƙaunarsa ta fari?

5 Duk wanda ya keɓe kansa ga Jehobah yana bukatar ya fara “gwada” wa kansa “ko menene nufin nan na Allah mai-kyau, abin karɓa, cikakke.” (Rom. 12:1, 2) A wani ɓangaren kuma, hakan ya ƙunshi koyon gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Abin da ya sa wani ya tabbata cewa Shaidun Jehobah suna koyar da gaskiya zai iya bambanta da na wani. Wasu sun tuna cewa sun canja zuciyarsu ne sa’ad da suka karanta sunan Allah da ke cikin Littafi Mai Tsarki ko kuwa sa’ad da suka fahimci ainihin yanayin matattu. (Zab. 83:18; M. Wa. 9:5, 10) Abin da ya motsa wasu kuma ita ce ƙaunar da ke tsakanin mutanen Jehobah. (Yoh. 13:34, 35) Abin da ake nufi da ba na duniya ba ne ya motsa wasu mutane. Sun kammala cewa bai kamata Kiristoci na gaskiya su sa hannu a siyasa ko kuma yaƙe-yaƙe na kowace ƙasa ba.—Isha. 2:4; Yoh. 6:15; 17:14-16.

6 Ga mutane da yawa, fahimtar waɗannan abubuwa da kuma wasu ne ya sa suka ƙarfafa ƙaunarsu ta farko ga Allah. Ka ɗauki lokaci ka yi tunanin abin da ya sa ka gaskata da imaninka. Kai mutum ne mai yanayi da kuma hali dabam, saboda haka dalilan da ya motsa ka ka ƙaunaci kuma ka gaskata da alkawuran Jehobah mai yiwuwa sun bambanta da na wasu. Wataƙila, waɗannan dalilan suna nan kamar yadda suke a lokacin da ka koye su. Gaskiyar ba ta canja ba. Saboda haka, tunanin waɗannan abubuwa zai sa ka riƙe ƙaunarka ta fari ga gaskiya.—Ka karanta Misalai 119:151, 152; 143:5.

Ka Ƙarfafa Ƙaunarka ta Fari

7. Me ya sa muke bukatar mu ƙarfafa ƙaunarmu ta farko ga gaskiya, kuma ta yaya za mu iya yin haka?

7 Wataƙila abubuwa da yawa sun canja a rayuwarka tun da ka keɓe kanka ga Jehobah. Ƙaunarka ta fari don gaskiya tana da muhimmanci, amma da wucewar lokaci, kana bukatar ka ƙara ƙarfafa ƙaunarka don ka fuskanci sababbin ƙalubalen da za su jarraba bangaskiyarka. Amma, Jehobah zai taimake ka. (1 Kor. 10:13) Abubuwan da ka shaida a shekaru da suka wuce suna da muhimmanci a gare ka. Sun taimake ka ka ƙarfafa ƙaunarka ta fari, kuma waɗannan abubuwan wata hanya ce da za ka tabbatar wa kanka cewa kana yin abu mai kyau kuma abin karɓa ga Allah.—Josh. 23:14; Zab. 34:8.

8. Ta yaya ne Jehobah ya bayyana kansa ga Musa, kuma ta yaya Isra’ilawa suka san Allah sosai?

8 Alal misali, yi la’akari da yanayin da Isra’ilawa suka sami kansu sa’ad da Jehobah ya faɗi nufinsa na cetonsu daga bauta a ƙasar Masar. Allah ya bayyana kansa ga Musa yana cewa: “Zan kasance duk abin da ya kamata na kasance.” (Fit. 3:7, 8, 13, 14; NW) A nan, Jehobah yana cewa zai iya zama duk wani abin da ya kamata don ya ceci mutanensa. Ta abubuwan da suka faru bayan haka, Isra’ilawa sun ga yadda Jehobah ya bayyana halayensa dabam dabam, a matsayin Maɗaukaki Duka, Alƙali, Shugaba, Mai Ceto, Jarumi, da kuma Mai Tanadi.—Fit. 12:12; 13:21; 14:24-31; 16:4; Neh. 9:9-15.

9, 10. Wane yanayi ne zai iya taimaka wa mutum ya san Allah, kuma me ya sa yake da kyau a tuna waɗannan abubuwan?

9 Yanayinka ya bambanta da na Isra’ilawa na dā. Duk da haka, wataƙila ka shaida abubuwan da suka tabbatar da kai cewa Allah yana kula da kai, kuma hakan ya ƙarfafa bangaskiyarka. Wataƙila a wata hanya Jehobah ya zame maka Mai Tanadi, Mai Ƙarfafawa, ko kuwa Malami. (Ka karanta Ishaya 30:20b, 21.) Ko kuma ka ga amsar addu’arka. Wataƙila kana fuskantar ƙalubale, sai wani ɗan’uwa Kirista ya taimake ka. Ko kuma nazari na kai ya sa ka yi la’akari da wasu nassosin da suka dace da yanayinka.

10 Idan ka gaya wa mutane waɗannan labaran, wataƙila hakan ba zai motsa wasu ba. Waɗannan abubuwan da suka auku ba mu’ujizai ba ne. Amma a gare ka, suna da muhimmanci sosai. Hakika, Jehobah ya zama ainihin abin da yake so domin ka. Ka tuna shekarun da ka yi a cikin gaskiya. Za ka iya tuna lokacin da ka ga alamun cewa Jehobah yana kula da kai? Idan haka ne, ka tuna waɗannan abubuwan da suka auku da kuma yadda suka sa ka ji za su iya sa ka soma ƙaunar Jehobah a zuciyarka kamar dā. Ka ɗauki waɗannan abubuwan da tamani. Ka yi bimbini a kansu. Tabbaci ne cewa Jehobah yana kula da kai, kuma babu wanda zai sa ka daina gaskatawa da wannan tabbacin.

Ka Bincika Kanka

11, 12. Idan ƙaunar da Kirista yake yi wa gaskiya ta yi sanyi, menene zai iya jawo hakan, kuma wane gargaɗi ne Yesu ya yi?

11 Idan ka ji cewa ba ka ƙaunar Allah da kuma gaskiya kamar dā, hakan ba ya nufin cewa Jehobah ya canja. Jehobah ba ya canjawa. (Mal. 3:6; Yaƙ. 1:17) Kamar yadda ya kula da kai a dā, hakazalika zai kula da kai a yau. To, idan wani abu ya riga ya canja dangantakar ka da Jehobah fa? Kana ganin cewa kana fuskantar matsi ne sosai, ka fi damuwa da alhini na rayuwa? Wataƙila a dā kana yin addu’a sosai, kana yin nazari sosai, kuma kana yin bimbini a kai a kai. Kana ƙwazo a hidima da kuma halartar taro na ikilisiya a kai a kai fiye da yanzu?—2 Kor. 13:5.

12 Bayan ka bincika kanka, wataƙila ba za ka ga waɗannan kasawan ba, amma idan ka gani, menene ya jawo su? Abubuwa masu amfani, kamar su yi wa iyali tanadi yadda ya kamata, kula da lafiyar jikinka, ko irin waɗannan abubuwan, sun sa ka mance cewa ranar Jehobah tana gabatowa da gaggawa? Yesu ya gaya wa manzanninsa: “Ku yi hankali da kanku, kada ya zama zukatanku su yi nauyi da zarin ci da maye da shagulgula na wannan rai, har ranan nan ta hume ku, ba labari, kamar tarko: gama hakanan za ta humi dukan mazaunan fuskar duniya duk. Amma a kowane loto sai ku yi tsaro, kuna yin roƙo ku sami ikon da za ku tsere ma dukan waɗannan al’amuran da za su faru, ku tsaya kuma a gaban Ɗan mutum.”—Luka 21:34-36.

13. Da menene Yaƙubu ya kamanta Kalmar Allah?

13 Yaƙubu hurarren marubucin Littafi Mai Tsarki ya aririci ’yan’uwa masu bi su bincika kansu sosai ta wajen yin amfani da Kalmar Allah. Yaƙubu ya rubuta: “Ku zama masu-aika magana, ba masu-ji kaɗai ba, watau yaudara kanku ke nan. Gama idan kowa mai-jin magana ne, ba mai-aikawa ba, yana kama da mutum wanda yana duban halittaciyar fuskarsa a cikin madubi: gama ya duba kansa, kāna ya tafi, nan da nan kuwa ya manta irin mutum da ya ke. Amma wanda ya duba cikin cikakkiyar shari’a, shari’a ta yanci, ya lizima, shi kuwa ba mai-ji wanda ke mantawa ba ne, amma mai-yi ne wanda ke aikatawa, wannan za ya zama mai-albarka a cikin aikinsa.”—Yaƙ. 1:22-25.

14, 15. (a) Ta yaya Littafi Mai Tsarki zai taimake ka ka ƙarfafa ruhaniyarka? (b) Waɗanne tambayoyi ne ya kamata ka yi bimbini a kai?

14 Mutum zai iya yin amfani da madubi don ya tabbata ya yi ado mai kyau. Alal misali, idan namiji ya ga cewa tayen da ya ɗaura bai yi daidai ba, zai gyara shi. Idan mace ta ga cewa gashinta ya yi datti, za ta wanke shi. Hakazalika, Nassosi yana taimakonmu mu bincika kanmu. Sa’ad da muka kwatanta kanmu da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce, hakan zai nuna cewa muna amfani da ita kamar madubi. Amma menene amfanin kallon madubi idan ba mu gyara kuskuren da muka gani ba? Za mu zama masu hikima idan muka aikata a kan abin da muka gani a cikin ‘cikakkiyar shari’ar’ Allah, mu kasance ‘masu aikatawa.’ Saboda haka, duk wanda ya ga cewa ƙaunarsa ta fari ga Jehobah da gaskiya ta yi sanyi, ya kamata ya yi la’akari da waɗannan tambayoyin: ‘Waɗanne matsi ne ni ke fuskanta a rayuwa, kuma wane mataki ne na ɗauka? Wane mataki ne na ɗauka a dā? Wasu abubuwa sun canja ne?’ Idan waɗannan binciken sun nuna kasawa, kada ka yi banza da su. Idan kana bukatar gyara, ka yi su ba tare da ɓata lokaci ba.—Ibran. 12:12, 13.

15 Irin wannan bimbini zai iya taimakonka ka kafa makasudai masu kyau don ka ƙarfafa ruhaniyarka. Manzo Bulus ya ba wa abokin aikinsa Timothawus hurarren umurni game da yadda zai ƙarfafa hidimarsa. Bulus ya aririci matashin: “Ka yi ƙwazo cikin waɗannan al’amura; ka bada kanka garesu sosai; domin cigabanka ya bayyanu ga kowa.” Ya kamata mu ma mu sa ƙwazo ga Kalmar Allah, yin hakan zai sa mu ci gaba.—1 Tim. 4:15.

16. Wane haɗari ne kake bukatar ka mai da wa hankali sa’ad da ka ke bincika kanka ta wajen yin amfani da Nassosi?

16 Kowane bincike na kai zai nuna cewa kana da wasu kasawa. Hakan zai iya sa mutum ya yi sanyi, amma kada ka bari hakan ya faru da kai. Ban da haka ma, manufar bincika kai don a yi gyara ne. Hakika, Shaiɗan zai so Kirista ya ga kamar ba shi da amfani don ajizancinsa. Shaiɗan ya yi da’awar cewa Allah ba ya amince da duk wani ƙoƙarce-ƙoƙarcen da mutane suke yi don su bauta masa. (Ayu. 15:15, 16; 22:3) Wannan ƙarya ce da Yesu ya ƙalubalanta; Allah yana ɗaukan kowannenmu da tamani. (Ka karanta Matta 10:29-31.) Sanin ajizancinka ya kamata ya motsa ka ka ƙudurta cewa za ka ƙoƙarta sosai da taimakon Jehobah. (2 Kor. 12:7-10) Idan rashin lafiya ko shekaru suka rage abin da za ka iya yi, to, ka kafa makasudan da za ka iya cim ma wa, amma kada ka yi sanyin gwiwa ko ka sa ƙaunarka ta yi sanyi.

Abubuwa Masu Yawa da za Mu Yi Godiya Dominsu

17, 18. Waɗanne albarka ne za ka samu idan ka ƙarfafa ƙaunarka ta fari?

17 Za ka amfana sosai idan ka ci gaba da ƙarfafa ƙaunar da kake da ita a dā. Za ka iya daɗa iliminka game da Allah da kuma godiya ga ja-gorar da yake yi maka. (Ka karanta Misalai 2:1-9; 3:5, 6.) “Cikin kiyaye [dokokin Jehobah] da lada mai-girma,” in ji mai zabura. “Shaidar Ubangiji tabbataciya ce, tana sa mara-sani ya zama mai-hikima.” Ƙari ga haka, “masu-albarka ne waɗannan da ke kamilai cikin tafarki, waɗanda ke tafiya cikin shari’ar Ubangiji.”—Zab. 19:7, 11; 119:1.

18 Za ka yarda cewa kana da dalilai masu yawa na yin godiya. Ka fahimci abin da ya jawo abubuwan da suke faruwa a duniya a yau. Kana amfana daga kula ta ruhaniya da kuma tanadodin da Allah yake yi wa mutanensa a yau. Babu shakka kana godiya da Jehobah ya jawo ka zuwa ikilisiyarsa na dukan duniya kuma ya ba ka zarafin zama ɗaya daga cikin Shaidunsa. Kana godiya don abubuwa masu kyau a rayuwarka. Idan za ka lissafa su, wataƙila za su yi yawa. Yin haka a koyaushe zai taimake ka ka bi wannan umurnin: “Ka riƙe abin da ka ke da shi da kyau.”—R. Yoh. 3:11.

19. Ban da yin bimbini a kan dangantakarka da Allah, menene yake da muhimmanci don ka riƙe dangantakarka da Allah?

19 Yin bimbini a kan yadda bangaskiyarka ta ƙarfafa da shigewar lokaci yana ɗaya daga cikin abin da za ka yi don ya taimake ka ka riƙe abin da kake da shi. Sau da yawa wannan mujallar tana jawo hankalinmu ga abubuwa masu muhimmanci da za mu yi don mu riƙe dangantaka mai kyau da Jehobah. Waɗannan sun ƙunshi addu’a, halarta da yin kalami a taron Kirista da kuma kasancewa a hidimar fage. Waɗannan abubuwa za su taimake ka ka ci gaba da ƙarfafa da kuma riƙe ƙaunarka ta fari.—Afis. 5:10; 1 Bit. 3:15; Yahu. 20, 21.

Yaya Za Ka Amsa?

• Ta yaya ne dalilanka na ƙaunar Jehobah za su iya ƙarfafa ka yanzu?

• Yin tunani game da abubuwan da ka shaida shekaru da suka wuce za su sa ka gaskata menene?

• Me ya sa ya kamata ka bincika ƙaunarka ga Allah?

[Hoto a shafi na 23]

Menene ya motsa ka game da gaskiya kuma ya sa ka tabbata cewa wannan gaskiya ce?

[Hoto a shafi na 25]

Ka ga wasu abubuwa game da kanka da suke bukatar gyara?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba