Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 10/1 pp. 20-21
  • Sama’ila Ya Manne wa Nagarta

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sama’ila Ya Manne wa Nagarta
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Makamantan Littattafai
  • Sama’ila Ya Ci Gaba da Yin Abin da Ya Dace
    Ku Koyar da Yaranku
  • Ɗan Yaro Ya Bauta Wa Allah
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Ya Ci Gaba da Yin Girma a Gaban Jehobah
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Jehobah Ya Yi Magana da Sama’ila
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 10/1 pp. 20-21

Ka Koyar Da Yaranka

Sama’ila Ya Manne wa Nagarta

KA TAƁA ganin wasu suna yin abin da babu kyau?—a Sama’ila ya gani. Ya zauna a inda ba za ka sa tsammani mutane za su kasance da mummunan hali ba. Wajen nan mazaunin Allah ne ko wajen sujjadarsa a birnin Shiloh. Bari mu ga yadda Sama’ila ya koma da zama a mazauni fiye da shekaru 3,000 da suka gabata.

Kamin ta haifi Sama’ila, mamarsa Hannatu ta nemi haihuwa. Sa’ad da suka ziyarci mazauni, sai Hannatu ta roƙi Allah ya ba ta haihuwa. Tana addu’a da dukan zuciyarta har bakinta yana ta motsi. Hakan ya sa babban firist Eli ya yi zaton ta bugu. Amma da ya fahimci cewa ba ta bugu ba, tana baƙin ciki ne, sai Eli ya albarkace ta, ya ce: “Allah kuwa na Israila shi ba ki roƙonki da kika roƙa a gareshi.”—1 Sama’ila 1:17.

Daga baya sai ta haifi Sama’ila kuma Hannatu ta yi farin ciki sosai har ta gaya wa maigidanta, Elkanah: ‘Da zarar na yaye Sama’ila, zan kai shi mazauni domin ya bauta wa Allah a can.’ Hakika ta yi hakan! A lokacin wataƙila Sama’ila yana da shekara huɗu ko biyar.

Eli ya tsufa kuma yaransa maza Hophni da Phinehas ba sa bauta wa Jehovah a hanyar da ta dace. Har ma suna zina da mata da suke zuwa mazauni! Me kake gani babansu ya kamata ya yi?— Hakika, ya kamata ya yi musu horo kuma ya hana su yin waɗannan munanan abubuwa.

Sama’ila ya girma a mazauni, kuma wataƙila ya san munanan halayen ’ya’yan Eli. Sama’ila ya bi wannan mugun tafarki ne?— A’a, ya ci gaba da yin abin da ke nagari kamar yadda iyayensa suka koya masa. Saboda haka, babu mamaki da Jehobah ya yi fushi da Eli. Har ya aiki annabi ya gaya wa Eli cewa zai yi wa iyalin Eli horo, musamman ma ’ya’yansa masu mugun hali.—1 Sama’ila 2:22-36.

Sama’ila ya ci gaba da yin hidima tare da Eli a mazauni. Wata rana da Sama’ila yana barci, sai ya ji ana kiransa. Sai Sama’ila ya ruga wurin Eli amma Eli ya ce bai kira shi ba. Sai aka sake kiransa. Sa’ad da hakan ya sake faruwa na uku, sai Eli ya gaya wa Sama’ila ya ce: “Yi magana, ya Ubangiji: gama bawanka yana ji.” Da Sama’ila ya faɗi hakan sai Jehobah ya yi masa magana. Ka san abin da Jehobah ya gaya wa Sama’ila?—

Allah ya gaya wa Sama’ila nufinsa cewa zai yi wa iyalin Eli horo. Washegari sai Sama’ila ya ji tsoron ya gaya wa Eli abin da Jehobah ya faɗa. Amma Eli ya roƙi Sama’ila: “Kada ka ɓoye mani.” Daga baya sai Sama’ila ya gaya wa Eli dukan abin da Jehobah ya ce zai yi kamar yadda annabinsa ya rigaya ya gaya wa Eli. Sai Eli ya ce: “Ubangiji. . . shi yi abin da ya yi masa kyau.” Daga baya sai aka kashe Hophni da Phinehas kuma Eli ya mutu.—1 Samuila 3:1-18.

Ananan, sai Sama’ila “ya yi girma, Ubangiji yana tare da shi.” A lokacin wataƙila Sama’ila matashi ne, lokaci mai muhimmanci a rayuwar matasa da yawa. Kana gani ya kasance da sauƙi ga Sama’ila ya ci gaba da yin abin da ke mai kyau a lokacin da sauran mutane suna yin abin da babu kyau?— Ko da yake bai kasance da sauƙi ba, Sama’ila ya ci gaba da yi ma Jehobah hidima har ya mutu.— 1 Samuila 3:19-21.

To, kai fa? Za ka zama kamar Sama’ila, sa’ad da ka girma? Za ka ci gaba da yin abin da ke da kyau? Za ka manne wa koyarwar Littafi Mai Tsarki da kuma abin da iyayenka suka koya maka? Idan ka yi hakan, za ka faranta wa Jehobah da kuma iyayenka rai.

[Hasiya]

a Idan kana karanta wa yara, wannan alamar fid da ma’ana tana nufin ka dakata, ka yi masu tambayar.

Tambayoyi:

○ Yaya aka yi har Sama’ila ya yi hidima a mazaunin Jehobah?

○ Waɗanne ƙalubale ne Sama’ila ya fuskanta a wajen?

○ Wane misali ne Sama’ila ya kafa wa matasa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba