Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 8/15 p. 26-p. 28
  • Darussa Daga Littafin Galatiyawa, Afisawa, Filibiyawa, da kuma Kolosiyawa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Darussa Daga Littafin Galatiyawa, Afisawa, Filibiyawa, da kuma Kolosiyawa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • TA YAYA AKA SANAR DA MU MASU “BANGASKIYA”?
  • (Gal. 1:1–6:18)
  • “TATTARA DUKAN ABU CIKIN KRISTI”
  • (Afis. 1:1–6:24)
  • KU “CI GABA DA HAKA”
  • (Filib. 1:1–4:23)
  • KU ZAMA ‘KAFAFFU CIKIN BANGASKIYA’
  • (Kol. 1:1–4:18)
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Jehobah Yana Tattara Iyalinsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Darussa Daga Wasiƙu zuwa ga Tassalunikawa da Timothawus
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 8/15 p. 26-p. 28

Maganar Jehobah Rayayya Ce

Darussa Daga Littafin Galatiyawa, Afisawa, Filibiyawa, da kuma Kolosiyawa

SA’AD da manzo Bulus ya ji cewa Kiristoci suna barin bauta ta gaskiya don rinjayar masu bin Yahudanci, sai ya rubuta wasiƙa mai ƙarfi ga “ikilisiyoyin ƙasar Galatiya.” (Gal. 1:2) Wasiƙar da aka rubuta a kusan shekara ta 50 zuwa 52 K.Z., tana ɗauke da shawara da kuma gargaɗi mai ƙarfi.

Bayan shekara goma sa’ad da yake Roma “ɗamrarre na Kristi,” Bulus ya rubuta wa ikilisiyoyi da ke Afisa, Filibi, da kuma Kolossi, gargaɗi mai kyau kuma ya ƙarfafa su sosai. (Afis. 3:1) A yau za mu iya amfana idan muka karanta saƙon littattafan Galatiyawa, Afisawa, Filibiyawa da kuma Kolosiyawa.—Ibran. 4:12.

TA YAYA AKA SANAR DA MU MASU “BANGASKIYA”?

(Gal. 1:1–6:18)

Tun da masu bin Yahudanci suna neman su ƙasƙantar da Bulus, ya kāre aikinsa na manzo ta wajen ba su wasu labarai game da rayuwarsa. (Gal. 1:11–2:14) Don ya ƙaryata koyarwarsu na ƙarya, Bulus ya ce: “Mutum ba za shi barata bisa ga ayukan shari’a ba, sai ta wurin bangaskiya cikin Yesu Kristi.”—Gal. 2:16.

Bulus ya ce, Kristi ya “panshi waɗanda ke ƙalƙashin shari’a,” kuma ya cece su don su more ’yanci na Kirista. Ya gargaɗi Galatiyawa: “Ku tsaya fa da kyau, kada ku sake nannaɗewa cikin ƙangin bauta.”—Gal. 4:4, 5; 5:1.

Tambayoyin Nassi da aka Amsa:

3:16-18, 28, 29—Har ila ana bin alkawarin da aka yi wa Ibrahim ne? E. Dokar alkawari ba canji ba ne ga alkawarin da aka yi wa Ibrahim. Saboda haka, bayan da aka ‘kawar’ da Dokar an ci gaba da yin amfani da alkawarin da aka yi wa Ibrahim. (Afis. 2:15) Ainihin “zuriyar” Ibrahim wato, Yesu Kristi da waɗanda suke “na Kristi” za su sami amfanin alkawarin.

6:2—Mecece “shari’ar [dokar] Kristi”? Wannan dokar ta ƙunshi dukan abubuwan da Yesu ya koyar da kuma umurninsa. Musamman hakan ya ƙunshi dokar da ta ce a yi “ƙaunar juna.”—Yoh. 13:34.

6:8—Ta yaya muke ‘shuki ga ruhu’? Muna yin haka ta wurin barin ruhun Allah ya ja-gorance mu. Yin shuki ga ruhu ya ƙunshi kasancewa da ayyukan da za su sa ruhu ya yi aiki a gare mu.

Darussa Dominmu:

1:6-9. Ya kamata dattawa Kiristoci su aikata nan da nan sa’ad da matsala ta taso a cikin ikilisiya. Ta wajen yin amfani da Nassosi, za su taimaka wajen kawar da koyarwar ƙarya.

2:20. Fansa kyauta ce da Allah ya ba mu. Kuma ya kamata mu ɗauke ta hakan nan.—Yoh. 3:16.

5:7-9. Mugun tarayya zai iya ‘hana mu yin biyayya da gaskiya.’ Yana da kyau mu guji hakan.

6:1, 2, 5. “Masu-ruhaniya” za su iya taimakon mu ɗaukan nauyin abin da muke fuskanta, kamar matsalar da muke fuskanta don mu bi tafarkin da bai dace ba, ba da saninmu ba. Amma idan ya zo ga ɗaukan hakki na ruhaniya, kowa zai ɗauka da kansa.

“TATTARA DUKAN ABU CIKIN KRISTI”

(Afis. 1:1–6:24)

Don ya nanata yadda Kiristoci za su ba da haɗin kai, a wasiƙarsa ga Afisawa Bulus ya yi “wakilci na cikar wokatai, shi tattara dukan abu cikin Kristi, abubuwan da ke cikin sammai, da abubuwan da ke bisa duniya.” Yesu ya naɗa “kyautai ga mutane” don ya taimaki dukanmu mu “kai zuwa ɗayantuwar imani.”—Afis. 1:10; 4:8, 13.

Don su girmama Allah kuma su ba da haɗin kai, ya kamata Kiristoci su “yafa sabon mutum” kuma su ‘sarayadda kansu ga junansu cikin tsoron Kristi.’ Ya kamata kuma su yi “tsayayya da dabarun Shaiɗan” ta wajen kasancewa da dukan makamai na ruhaniya.—Afis. 4:24; 5:21; 6:11.

Tambayoyin Nassi da aka Amsa:

1:4-7—Ta yaya aka ƙaddara shafaffun Kiristoci kafin a haife su? Ana ƙaddara su tare ba ɗai-ɗai ba. Hakan ya faru ne kafin iyayenmu na fari su yaɗa zunubi sa’ad da suka haifi ɗansu na fari. An sanar da wannan annabcin da ke Farawa 3:15, kafin a haifi kowane ɗan adam, wanda ya ƙunshi nufin Allah don wasu mabiyan Kristi su yi sarauta da shi a sama.—Gal. 3:16, 29.

2:2—Ta yaya ne ruhun duniya take kama da sararin sama ko kuma iska, kuma ta yaya take iko bisa duniya? “Ruhun duniya,” wato, ruhun son ’yancin kai da kuma rashin biyayya yana ko’ina kamar iska da ake shaka. (1 Kor. 2:12) Yana amfani da ikonsa bisa duniya don rinjayarsa tana da ƙarfi kuma tana nacewa.

2:6—Ta yaya shafaffun Kiristoci suke “cikin sammai” ko da har ila suna duniya? Furcin nan “cikin sammai” ba ya nufin gadō na sama da aka yi musu alkawarinsa. Maimakon haka, yana nufin matsayinsu na ruhaniya a gaban Allah da ya sa aka ‘hatimce su da Ruhu Mai-tsarki.’—Afis. 1:13, 14.

Darussa Dominmu:

4:8, 11-15. Yesu Kristi ya ɗauki “rundunar bayi,” wato, ya janye mutane daga ikon Shaiɗan don ya yi amfani da su a matsayin kyauta ya ƙarfafa ikilisiyar Kirista. Muna iya mu yi “girma cikin abu duka zuwa cikin . . . Kristi” ta wajen zama masu biyayya da masu miƙa kai ga waɗanda suke shugabanci a tsakaninmu da kuma ba da haɗin kai ga shirye-shirye na ikilisiya.—Ibran. 13:7, 17.

5:22-24, 33. Ban da miƙa kai ga mijinta, mata za ta ba shi daraja. Za ta yi hakan ta wajen kasancewa da “ruhu mai-ladabi mai-lafiya” da kuma yin ƙoƙari ta daraja shi yayin da take magana mai kyau game da shi kuma ta ba da haɗin kai don shawarwarinsa su yi nasara.—1 Bit. 3:3, 4; Tit. 2:3-5.

5:25, 28, 29. Kamar yadda yake ‘ciyar’ da kansa, ya kamata miji ya zama mai yi wa matarsa tanadi mai kyau, a zahiri, a hankali, da kuma na ruhaniya. Ya kamata ya yi tattalinta ta wajen ba ta isashen lokaci da kuma bi da ita cikin ƙauna ta maganarsa da kuma ayyukansa.

6:10-31. Don mu yi tsayayya da aljannu, muna bukatar mu yafa makami na ruhaniya na Allah da dukan zuciyarmu.

KU “CI GABA DA HAKA”

(Filib. 1:1–4:23)

Bulus ya nanata ƙauna a dukan wasiƙunsa zuwa ga Filibiyawa. Ya ce: “Abin da ni ke addu’a ke nan, ƙaunarku ta yalwata har gaba gaba cikin sani da ganewa duka.” Don ya taimake su su guji yawan gaba gaɗi, ya gargaɗe su: “Ku yi aikin cetonku da tsoro da rawan jiki.”—Filib. 1:9; 2:12.

Bulus ya gargaɗi waɗanda suka manyanta su biɗi “ladan nasara na maɗaukakiyar kira ta Allah.” Ya ce: “Sai dai duk inda muka kai, mu ci gaba da haka.”—Filib. 3:14-16.

Tambayoyin Nassi da aka Amsa:

1:23—Waɗanne abubuwa “biyu” ne suka matsa wa Bulus, kuma me yake so? Domin yanayin da yake ciki, Bulus yana da matsi daga abubuwa biyu da suke gabansa, wato, rai ko mutuwa. (Filib. 1:21) Ko da yake bai faɗa abin da zai zaɓa ba, ya faɗa abin da yake so, wato, ya ‘tashi ya zauna tare da Kristi.’ (Filib. 3:20, 21; 1 Tas. 4:16) An cika wannan burin a bayanuwar Kristi sa’ad da ya samu ladar da Jehobah ya shirya masa.—Mat. 24:3.

2:12, 13—Ta yaya Allah yake sa mu ‘yi nufi kuma mu aikata’? Ruhu mai tsarki na Jehobah zai iya sa a zuciyarmu mu so yin iya ƙoƙarinmu a hidimarsa. Shi ya sa, ake taimakon mu ‘mu yi aikin cetonmu da tsoro da rawan jiki.’

Darussa Dominmu:

1:3-5. Ko da yake ba su da abin hannu, Filibiyawa sun kafa mana misali mai kyau wajen nuna karimci.—2 Kor. 8:1-6.

2:5-11. Yadda Yesu ya kafa mana misali, tawali’u ba alamar kumamanci ba ne amma ƙarfin ɗabi’a ne. Bugu da ƙari, Jehobah na ɗaukaka masu tawali’u.—Mis. 22:4.

3:13. “Abubuwa da ke baya” suna iya zama abubuwa kamar aiki mai kyau, kwanciyar hankali da ake samu daga kasancewa cikin iyali mai arziki, ko kuma zunubai masu tsanani na dā da muka tuba ‘amma aka wanke mu, aka tsarkake mu.’ (1 Kor. 6:11) Ya kamata mu manta waɗannan abubuwa, wato, mu daina damuwa game da su, kuma mu ‘kutsa zuwa ga waɗanda ke gaba.’

KU ZAMA ‘KAFAFFU CIKIN BANGASKIYA’

(Kol. 1:1–4:18)

A wasiƙarsa zuwa ga Kolossiyawa, Bulus ya fallasa ra’ayin ƙarya na malaman ƙarya. Ya faɗa cewa, ceto bai dangana bisa bukatu na Doka ba, amma bisa ‘lizima cikin bangaskiya.’ Bulus ya ƙarfafa Kolosiyawa su “yi tafiya a cikin [Kristi] hakanan, dasassu, ginannu kuma cikinsa, kafaffu cikin bangaskiyarku.” Ta yaya ya kamata wannan kafaffawa ya shafe su?—Kol. 1:23; 2:6, 7.

Bulus ya rubuta: “Gaba da dukan waɗannan kuma ku yafa ƙauna, gama ita ce magamin kamalta. Kuma bari salama ta Kristi ta yi mulki a cikin zukatanku.” Manzon ya ce musu: “Iyakar abin da ku ke yi, ku aika da zuciya ɗaya kamar ga Ubangiji, ba ga mutane ba.” Game da waɗanda ba sa cikin ikilisiya, ya ce: “Ku yi tafiya cikin hikima wajen” su.—Kol. 3:14, 15, 23; 4:5.

Tambayoyin Nassi da aka Amsa:

2:8—Menene “ruknai na duniya” da Bulus ya yi musu kashedi a kai? Abubuwa ne de ke cikin duniyar Shaiɗan, wato, ainihin abubuwa ko ƙa’idodi da ke ja-gora, ko motsa ta. (1 Yoh. 2:16) Abubuwan sun haɗa da falsafa, abubuwan malaka, da kuma addinan ƙarya na wannan duniya.

4:16—Me ya sa wasiƙa zuwa ga Lawudiyawa ba ta cikin Littafi Mai Tsarki? Domin wannan wasiƙar ba ta ƙunshi bayani da muke bukata a yau. Ko kuma an maimaita darussa ne daga wasu wasiƙu.

Darussa Dominmu:

1:2, 20. Tanadin fansa da Allah ya yi domin alherinsa, zai iya kawar da jin laifi da muke yi kuma ya ba mu kwanciyar hankali.

2:18, 23. “Tawali’u” na ƙarya, wato nuna tawali’u don a burge wasu wataƙila ta ƙin abin duniya ko kuma hana wa kanmu abubuwa sosai, na nuna cewa mutum na ‘kumburi kauwai bisa ga azancinsa bajiki.’

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba