Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 10/1 pp. 8-10
  • Annabcin Rayuwarmu Ta Nan Gaba

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Annabcin Rayuwarmu Ta Nan Gaba
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Albarka a Sabuwar Duniya
  • Annabta Rayuwa Mai Kyau Ta Nan Gaba
  • Rayuwa Cikin Sabuwar Duniya ta Salama
    Rayuwa Cikin Sabuwar Duniya ta Salama
  • Sabuwar Duniya—Za Ka Kasance A Can?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Sashe na 10—Sabuwar Duniya Mai-Ban Al’Ajibi Yin Allah
    Allah Yana Kula da Mu Kuwa da Gaske?
  • Sabonta Dukan Abubuwa —Kamar Yadda Aka Annabta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 10/1 pp. 8-10

Annabcin Rayuwarmu Ta Nan Gaba

SA’AD da yake tattaunawa game da rayuwar mutum da kuma abin da zai shafi duniya a nan gaba, manzo Bitrus ya rubuta: “Amma, bisa ga alkawarinsa [Allah], muna sauraron sabobin sammai da sabuwar duniya, inda adalci yake zaune.” (2 Bitrus 3:13) Annabi Ishaya ne ainihi ya fara annabta alkawari da aka yi game da “sabobin sammai da sabuwar duniya.” (Ishaya 65:17; 66:22) Sa’ad da ya ambata wannan annabci, Bitrus ya nuna cewa annabcin bai cika ba a zamaninsa.

Daga baya, a kusan shekara ta 96 A.Z., wahayi da aka ba wa manzo Yohanna ya kwatanta “sabuwar duniya” da albarkar da za a samu a Mulkin Allah. (Ru’ya ta Yohanna 21:1-4) Kalaman Yesu da na manzo Bulus game da yanayin duniya kafin zuwan Mulkin Allah suna cika yanzu. Saboda haka, za mu iya sa rai cewa wannan Mulkin zai kawo sabuwar duniya. Yaya wannan sabuwar duniya za ta kasance? Littafin Ishaya na Littafi Mai Tsarki ya gaya mana.

Albarka a Sabuwar Duniya

Salama a Dukan Duniya da Bauta Ɗaya. “Za su kuma bubbuge takubansu su zama garmuna, māsunsu kuma su zama lauzuna: al’umma ba za ta zāre ma al’umma takobi ba, ba kuwa za a ƙara koya yaƙi nan gaba ba.”—Ishaya 2:2-4.

Zaman Lafiya Tsakanin ’Yan adam da Dabbobi. “Kerkeci za ya zauna tare da ɗan rago, damisa kuma za ta kwanta tare da ɗan akuya; da ɗan maraƙi da ɗan zaki da kiyayayyen ɗan sā za su zauna wuri ɗaya; ɗan yaro kuwa za ya bishe su. Saniya da bear za su yi kiwo tare; ’ya’yansu kuwa za su kwanta wuri ɗaya: zaki kuwa za ya ci ciyawa kamar sā. . . . Ba za su yi ciwutaswa ba; ba kuwa za su yi ɓarna ko’ina cikin dutsena mai-tsarki ba: gama duniya za ta cika da sanin Ubangiji, kamar yadda ruwaye su ke rufe teku.”—Ishaya 11:6-9.

Abinci Mai Yawa Don Dukan Mutane. “A cikin wannan dutse Ubangiji mai-runduna za ya yi ma dukan al’ummai biki na abinci mai-mai, biki na ruwan anab ajiyayye da tsakinsa, na abinci mai-mai cike da laka, na ruwan anab gyartace sarai, ajiyayye da tsakinsa.”—Ishaya 25:6.

Ba Za a Yi Mutuwa Kuma Ba. “Ya [Allah] haɗiye mutuwa har abada: Ubangiji Yahweh za ya shafe hawaye daga dukan fuskoki: za ya kuma kawarda zargin mutanensa daga dukan duniya: gama Ubangiji ya faɗi.”—Ishaya 25:8.

Za a Ta da Matattu. “Matattunka za su yi rai: gawayena za su tashi. Ku farka, ku rera waƙa, . . . ƙasa kuwa za ta fitar da matattu.”—Ishaya 26:19.

Almasihu Alƙali ne Mai Adalci. “Ba za ya yi shari’a bisa ga abinda ya bayyana ga idanunsa ba, ba kuwa za shi yanka magana bisa ga abin da kunnensa ke ji ba: amma da adilci za ya yi ma talakawa shari’a, da daidaita kuma za ya yanka magana domin masu-tawali’u na duniya.”—Ishaya 11:3, 4.

Za a Warkar da Makafi da Kurame. “Sa’annan za a buɗe idanun makafi, kunnuwan kurame kuma za a buɗe.”—Ishaya 35:5.

Ƙasa Marar Albarka Za ta Zama Mai Albarka. “Jeji da ƙeƙasashiyar ƙasa za su yi farinciki; hamada kuma za ta yi murna, ta yi fure kamar rose. Za ta yi fure mai-yawa ta yi murna har da farinciki da rairawa.”—Ishaya 35:1, 2.

Sabuwar Duniya. “Gama, ga shi, sababbin sammai [sabuwar gwamnati na samaniya] da sabuwar duniya [da jami’iyyar ’yan adam masu adalci]; ni ke halitta: ba za a tuna da al’amura na dā ba, ba kuwa za su shiga zuciya ba. Amma sai ku yi murna ku yi farinciki har abada da abin da ni ke halittawa; . . . [waɗanda za su mallaki sabuwar duniya da Allah ya yi alkawari] za su gina gidaje, kuma za su zauna a ciki; su yi gonakin anab kuma, su ci amfaninsu. Ba za su yi gini, wani ya zauna ba: ba za su dasa, wani ya ci ba; gama kamar yadda kwanakin itace su ke, hakanan kwanakin mutanena za su zama, zaɓaɓuna kuma za su daɗe suna jin daɗin aikin hannuwansu. Ba za su yi aiki a banza ba, ba kuwa za su haifi ’ya’ya ga razana ba labari; gama zuriyar masu-albarka na Ubangiji ne su, ’ya’yansu kuma za su kasance tare da su. Za ya zama kuma, kamin su kira, in amsa; tun suna cikin magana kuma, in ji.” “Gama, yadda sababbin sammai da sabuwar duniya, waɗanda zan yi, za su dawwama a gabana, in ji Ubangiji, hakanan kuma zuriyarku da sunanku za su dawwama.”—Ishaya 65:17-25; 66:22.

Annabta Rayuwa Mai Kyau Ta Nan Gaba

Ba a cikin littafin Ishaya ne kawai aka annabta albarka ta nan gaba ba. Littafi Mai Tsarki yana cike da annabce-annabce da ta kwatanta abubuwan masu kyau da Allah zai cim ma ta wurin Mulkinsa da Yesu zai yi sarauta.a Za ka so ka yi rayuwa a aljanna kuwa? Zai yiwu! Ka bincika abin da ainihi Littafi Mai Tsarki yake koyarwa game da nufin Allah mai kyau na nan gaba, kuma ka koyi yadda za ka iya zama a aljanna. Shaidun Jehobah za su yi farin cikin taimakonka.

[Hasiya]

a Don ƙarin bayani game da Mulkin Allah da kuma abin da zai cim ma, dubi shafuffuka 78-85 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

[Hoto a shafi na 8]

’Yan adam za su yi zaman lafiya da juna da kuma dabbobi

[Hoto a shafi na 9]

Matattu za su rayu

[Hoto a shafi na 10]

Dukan duniya za ta zama aljanna

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba