Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 10/15 pp. 12-16
  • Amsar Jehobah Ga Addu’ar Da Aka Yi Da Zuciya Ɗaya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Amsar Jehobah Ga Addu’ar Da Aka Yi Da Zuciya Ɗaya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • An Ƙulla wa Mutanen Jehobah
  • Abu Mafi Muhimmanci
  • “Mazauninka Mai-Tsarki”
  • Abin da ya Faru a dā ya Nuna Cewa Jehobah Zai yi Nasara
  • Mu Yi Addu’a Don a Kunita Ikon Mallakar Jehobah
  • Wane ne Ya Fi Muhimmanci A Rayuwarka?
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
  • Sashe na 2
    Ka Saurari Allah
  • Armageddon Yaƙin Allah Na Kawar Da Dukan Yaƙe-yaƙe
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Armageddon Albishiri Ne!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 10/15 pp. 12-16

Amsar Jehobah Ga Addu’ar Da Aka Yi Da Zuciya Ɗaya

“Domin su sani kai, wanda sunanka Jehovah ne, kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan duniya.”—ZAB. 83:18.

1, 2. Menene mutane da yawa suka fuskanta, kuma waɗanne tambayoyi ne ya kamata a yi?

SEKARU da suka wuce, wata mata ta damu da wani abu da ya faru a unguwarsu. Da yake su ’yan Katolika ne, ta je ta sami Firist ya taimake ta, amma bai yi magana da ita ba. Sai ta yi wa Allah addu’a: “Ban san ko kai wanene ba . . . , amma na san kana nan. Ina roƙonka, ka sa na san ka.” Bayan ’yan kwanaki, Shaidun Jehobah suka ziyarce ta suka ƙarfafata kuma suka koya mata abin da take bukata. Sun kuma koya mata cewa Allah yana da suna, sunansa Jehobah ne. Hakan ya motsa ta sosai. Ta ce, “wannan ne Allahn da nake nema tun da nake ƙarama.”

2 Mutane da yawa suna farin ciki idan suka san sunan Allah. Sau da yawa ba su taɓa sanin sunan Allah ba sai da suka karanta Zabura 83:18 a cikin Littafi Mai Tsarki. Wannan ayar Littafi Mai Tsarki ta ce: “Domin su sani kai, wanda sunanka Jehovah ne, kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan duniya.” Ka taɓa tunanin abin da ya sa aka rubuta Zabura 83? Waɗanne abubuwa ne za su sa dukan mutane su san cewa Jehobah kaɗai ne Allah na gaskiya? Menene za mu koya daga wannan zaburar? Za mu tattauna waɗannan tambayoyin a wannan talifin.a

An Ƙulla wa Mutanen Jehobah

3, 4. Wanene ya rubuta Zabura 83, kuma wane matsi ne ya kwatanta?

3 Bisa ga rubutu na sama a cikin juyin Ibrananci na asali, Zabura ta 83 “waƙar Asaph” ce. Wataƙila wanda ya rubuta wannan zabura ya fito ne daga zuriyar Balawi Asaph, wani sanannen mai waƙa a lokacin da Sarki Dauda yake mulki. A wannan zaburar, mai zabura ya roƙi Jehobah ya aikata don a ɗaukaka ikon mallakarsa kuma a san sunansa. An rubuta zaburar bayan mutuwar Sulemanu ce. Me ya sa? Saboda a lokacin sarautar Dauda da Sulemanu, sarkin Taya abokin Isra’ila ne. Amma a lokacin da aka rubuta Zabura ta 83, mazauna a Taya sun juya wa Isra’ila baya kuma suka haɗa kai da abokan gaban Isra’ila.

4 Mai zabura ya lissafa ƙasashe goma da suka ƙulla wa mutanen Allah don su halaka su. Waɗannan maƙiyan suna ƙasashen da suka kewaye Isra’ila kuma an lissafa su haka: “Tents na Edom da na Ishma’ilawa: Moab da Hagarawa; Gebal, da Ammon, da Amalek; Philistia da mazaunan Tyre: Asshur kuma ta gama kai da su.” (Zab. 83:6-8) Wane aukuwa na tarihi ne zabura yake nufi? Wasu sun ce mai zaburar yana magana ne game da harin da rundunar haɗin gwiwa na Ammon, Moab, da mazaunan dutsen Seir a zamanin Jehoshaphat suka kai wa Isra’ila. (2 Laba. 20:1-26) Wasu sun gaskata cewa yana nufin hamayya da Isra’ila suka fuskanta ne daga maƙwabtansu a dukan tarihi.

5. Menene Kiristoci suke amfana a yau daga Zabura 83?

5 Koma menene, hakan ya nuna cewa Jehobah Allah ne ya hure a rubuta wannan zabura a lokacin da ƙasarsa take cikin haɗari. Mai zabura kuma ya ƙarfafa bayin Allah a yau, waɗanda a rayuwarsu sun fuskanci matsi daga maƙiya da suke so su halaka su. Kuma hakan zai ƙarfafa mu a nan gaba sa’ad da Gog na Magog ya tattara sojojinsa don ya halaka dukan masu bauta wa Allah cikin ruhu da gaskiya.—Ka karanta Ezekiel 38:2, 8, 9, 16.

Abu Mafi Muhimmanci

6, 7. (a) Menene mai zabura ya yi addu’a a kai a farkon kalmarsa a Zabura 83? (b) Menene mai zabura ainihi ya damu da shi?

6 Ka saurari yadda mai zabura ya nuna yadda yake ji a cikin addu’a: “Ya Allah, kada ka yi shuru: Kada ka yi kurum, ya Allah, kada ka kawaita. Gama, ga shi, abokan gabanka suna hargowa: Maƙiyanka sun tada kai. Suna yi ma mutanenka makirci, . . . Gama tare suka yi shawara da zuciya ɗaya; A kanka suna yin wa’adi.”—Zab. 83:1-3, 5.

7 Menene abu mafi muhimmanci ga zabura? Hakika, ya damu da ransa da na iyalinsa. Duk da haka, ya yi addu’a game da zargin da ake yi wa sunan Allah da kuma barazanar da ake yi wa mutanen Allah. Bari mu ma mu kasance da irin wannan hali yayin da muke jimre wa wahala a ƙarshen wannan tsohuwar duniya.—Ka karanta Matta 6:9, 10.

8. Wane dalili ne ya sa wasu ƙasashe suka ƙulla wa Isra’ila?

8 Mai zabura ya yi ƙaulin abin da abokan gaban Isra’ila suka ce: “Mu zo, mu datse su, kasancewarsu al’umma ta ƙare; Domin nan gaba kada a ƙara tuna da sunan Isra’ila.” (Zab. 83:4) Hakika, ƙasashen nan sun ƙi jinin mutanen Allah! Amma suna da wani dalilin da ya sa suka ƙi jinin su. Sun karɓi ƙasar Isra’ila kuma suka ce: “Bari mu karɓi mazaunan Allah Su zama namu na kanmu.” (Zab. 83:12) Irin wannan abu ya taɓa faruwa a zamanin mu kuwa? E.

“Mazauninka Mai-Tsarki”

9, 10. (a) A zamanin dā, menene mazauni mai tsarki na Allah? (b) A yau waɗanne albarka ne shafaffu da suka rage da “waɗansu tumaki” suke morewa?

9 A zamanin dā, ana kiran Ƙasar Alkawari mazauni mai tsarki na Allah. Ka tuna da waƙar da Isra’ilawa suka yi sa’ad da aka cece su daga ƙasar Masar: “Kai cikin jinƙanka ka biyar da mutane waɗanda ka fanshe su: Ka yi musu ja gaba da ƙarfinka har mazauninka mai-tsarki.” (Fit. 15:13) Daga baya, wannan ‘mazaunin’ ya ƙunshi haikali da firistoci da kuma babban birni wato, Urushalima, da kuma sarakuna da suka fito daga zuriyar Dauda da suke zaune a kan kursiyin Jehobah. (1 Laba. 29:23) Shi ya sa Yesu ya ce Urushalima “birnin maɗaukakin Sarki” ce.—Mat. 5:35.

10 A zamanin mu kuma fa? A shekara ta 33 K.Z., an haifi sabuwar ƙasa, wato, “Isra’ila na Allah.” (Gal. 6:16) Wannan ƙasar da ta ƙunshi shafaffun ’yan’uwan Yesu Kristi, sun cika aikin da Isra’ila ta zahiri ta kasa yi, wato na sanar da sunan Allah. (Isha. 43:10; 1 Bit. 2:9) Jehobah ya yi musu alkawari kamar yadda ya yi wa Isra’ila ta dā: ‘zan zama Allahnsu, su kuma su zama mutanena.’ (2 Kor. 6:16; Lev. 26:12) A shekara ta 1919, Jehobah ya sa raguwar “Isra’ila na Allah” cikin matsayi mai kyau, kuma suka karɓi “ƙasa,” wato, ayyuka na ruhaniya inda suka mori aljanna ta ruhaniya. (Isha. 66:8) Tun a shekara ta 1930, miliyoyin “waɗansu tumaki” sun haɗa hannu tare da su. (Yoh. 10:16) Farin ciki da kuma ci gaba a ruhaniya da Kiristoci na zamanin nan suke yi ya nuna cewa suna goyon bayan ikon mallaka na Jehobah. (Ka karanta Zabura 91:1, 2.) Hakan kuwa yana sa Shaiɗan ya yi fushi.

11. Menene ya ci gaba da zama ainihin nufin abokan gaban Allah?

11 A wannan zamani na ƙarshe, Shaiɗan yana amfani da waɗanda suke yin nufinsa a duniya su tsananta wa shafaffu da suka rage da abokansu waɗansu tumaki. Hakan ya faru a Yammancin Turai a ƙarƙashin mulkin Nazi, da kuma Gabashin Turai a ƙarƙashin gwamnatin Rasha ta dā. Hakan kuma ya faru a ƙasashe masu yawa, kuma zai sake faruwa, musamman ma a lokacin da Gog na Magog zai kai hari na ƙarshe. A wannan harin, ’yan hamayya za su ƙwace kayayyakin mutanen Jehobah, kamar yadda maƙiya suka yi a dā. Ainihin nufin Shaiɗan shi ne ya halaka mu duka don kada a sake tuna da wannan sunan ‘Shaidun Jehobah.’ Menene Jehobah ya yi game da ikon mallakarsa? Ka yi la’akari da abin da mai zabura ya ce.

Abin da ya Faru a dā ya Nuna Cewa Jehobah Zai yi Nasara

12-14. Waɗanne nasarori biyu da aka yi a kusa da birnin Magiddo ne mai zabura ya tuna mana?

12 Ka yi la’akari da irin bangaskiya mai girma da mai zabura yake da ita game da yadda Jehobah zai lalata shirin maƙiyan da suke ƙasar. Mai zabura ya haɗa nasarori guda biyu da Isra’ila suka yi bisa maƙiyansu a kusa da birnin Megiddo na dā, da aka sa ma sunan wani kwari. A lokacin rani, ana iya ganin ƙasan Kogin Kishon ta kwarin. Idan aka yi ruwan sama sai ruwan kogin ya cika kwarin. Wataƙila shi ya sa ake kiran kogin “ruwayen Megiddo.”—Alƙa. 4:13; 5:19.

13 Kusan kilomita 15 a ketaren kwarin Megiddo akwai wani tudun Moreh a inda sojojin Midiyanawa, Amalakawa da kuma waɗanda suke Gabas suka haɗa hannu a zamanin Alƙali Gidiyon suka yi yaƙi. (Alƙa. 7:1, 12) Sojojin Gidiyon guda 300 ne kawai, amma da taimakon Jehobah, sun yi nasara bisa sojojin maƙiyansu masu yawa. Ta yaya? Sun bi umurnin Allah, daddare suka kewaye sansanin maƙiyan suna riƙe da tuluna inda suka ɓoye tocila. Sa’ad da Gidiyon ya yi musu alama, mazan suka fashe tulunan suka fito da tocilan. A lokaci ɗaya, suka busa ƙahoninsu suka tada murya suka ce: “Ga takobin Ubangiji da na Gideon.” Hakan ya riƙitar da maƙiyan, suka soma kashe juna; waɗanda suka tsira kuma sun gudu zuwa tsallaken Kogin Urdun. Bayan haka, sai Isra’ilawa da yawa suka haɗa hannu suka kori maƙiyan. Gaba ɗaya sojoji 120,000 ne aka kashe.—Alƙa. 7:19-25; 8:10.

14 Dutsen Tabor yana kusan mil huɗu bayan Dutsen Moreh a ketaren kwarin Magiddo. A nan ne alƙali Barak ya tara sojojin Isra’ilawa 10,000 su yaƙi Jabin, sarkin Kan’aniyawa da ke Hazor, a ƙarƙashin dokar shugaban sojoji Sisera. Waɗannan rundunar Kan’aniyawa suna da karusan yaƙi 900 da suke da dogon takobi da suke juyawa da ƙafar karusar. Sa’ad da rundunar Isra’ilawa da ba su da isashen kayan yaƙi suka taru a Dutsen Tabor, sun rinjayi rundunar Sisera zuwa cikin kwarin. Sai “Ubangiji kuma ya pallasa Sisera da dukan karusansa da dukan rundunassa.” Wataƙila, ruwan sama da aka yi ne ya sa taɓo ya riƙe karusan domin Kogin Kishon ya cika sosai. Isra’ilawa suka kashe dukan rundunan.—Alƙa. 4:13-16; 5:19-21.

15. (a) Menene mai zabura ya yi addu’a Jehobah ya yi? (b) Menene sunan yaƙin Allah na ƙarshe ya tuna mana?

15 Mai zabura ya roƙi Jehobah ya ɗauki irin matakin da ya ɗauka a kan al’ummai da suka yi wa Isra’ilawa na zamaninsa barazana. Ya yi addu’a: “Ka yi masu kamar yadda ka yi ma Midian; Da Sisera, da Jabin, a kogin Kishon: Waɗanda suka hallaka cikin En-dor; Suka zama kamar tāki domin ƙasa.” (Zab. 83:9, 10) Hakika, ana kiran yaƙin Allah na ƙarshe a kan duniyar Shaiɗan Har–Magedon (a yare na Ibrananci sunan yana nufin “Dutsen Magiddo”), ko kuma Armageddon. Sunan nan yana tuna mana yaƙe-yaƙe masu muhimmanci da aka yi kusa da Magiddo. Nasara da Jehobah ya ci a waɗannan yaƙe-yaƙe na dā ya tabbatar mana cewa zai ci nasara a yaƙin Armageddon.— R. Yoh. 16:13-16.

Mu Yi Addu’a Don a Kunita Ikon Mallakar Jehobah

16. Ta yaya fuskokin masu hamayya suka ‘cika da ɗimuwa’ a yau?

16 A cikin wannan “kwanaki na ƙarshe,” Jehobah ya lalata dukan shiri da aka yi don a halaka mutanensa. (2 Tim. 3:1) Don haka, masu hamayya sun sha kunya. Zabura 83:16 ta annabta wannan sa’ad da ta ce: “Ka cika fuskokinsu da ɗimuwa; domin su biɗi sunanka, ya Ubangiji.” A cikin wasu ƙasashe, masu hamayya ba su yi nasara ba a shirinsu na sa Shaidun Jehobah su daina aikinsu. A waɗannan ƙasashen amincin masu bauta wa Allah makaɗaici na gaskiya da kuma jimirinsu ya zama shaida ga masu zuciyar kirki, kuma mutane da yawa sun ‘biɗi sunan Jehobah.’ Yanzu akwai mutane da yawa da suke yaba wa Jehobah da farin ciki a ƙasashe da yawa da a dā ana tsananta wa Shaidun Jehobah. Lallai wannan cin nasara ne ga Jehobah! Amma abin kunya ne ga magabtansa!—Ka karanta Irmiya 1:19.

17. Wane yanayi mai tsanani ne ’yan adam za su fuskanta, waɗanne kalmomi ne za mu tuna ba da daɗewa ba?

17 Hakika, mun san cewa masu hamayya za su ci gaba da tsananta mana. Kuma za mu ci gaba da wa’azin bishara ga masu hamayya. (Mat. 24:14, 21) Amma, ba da daɗewa ba zarafin da irin waɗannan masu hamayya suke da shi don su tuba kuma su sami ceto zai ƙare. Tsarkake sunan Jehobah ya fi muhimmanci da ceton ’yan adam. (Ka karanta Ezekiel 38:23.) Sa’ad da dukan al’ummai a duniya suka taru su halaka mutanen Allah, za mu tuna waɗannan kalmomi na addu’ar da mai zabura ya yi: “Bari su sha kumya da fargaba har abada: I, bari su ɗimota su hallaka.”—Zab. 83:17.

18, 19. (a) Menene ke jiran masu hamayya da ikon mallakar Jehobah? (b) Ta yaya kunita ikon mallakar Jehobah na ƙarshe zai shafe ka?

18 Waɗanda suka ci gaba da yin hamayya da ikon mallakar Jehobah za su halaka. Kalmar Allah ta bayana cewa waɗanda “sun ƙi yin biyayya da bisharar” kuma don haka aka halaka su a Armageddon za su “sha, madawamiyar hallaka.” (2 Tas. 1:7-9) Halakarsu da kuma ceton waɗanda suke bauta wa Jehobah zai ba da tabbaci cewa Jehobah ne Allah makaɗaici na gaskiya. A sabuwar duniya, ba za a manta da wannan babban nasara da aka ci. Waɗanda suka dawo a “tashin matattu, na masu-adalci da na marasa-adalci,” za su ji ayyuka masu girma da Jehobah ya yi. (A. M. 24:15) A sabuwar duniya, za su ga tabbacin hikima na rayuwa a ƙarƙashin ikon mallakar Jehobah. Kuma masu aminci a cikinsu nan da nan za su ga tabbaci cewa Jehobah ne Allah makaɗaici na gaskiya.

19 Ubanmu na sama mai ƙauna ya shirya wa masu bauta masa da aminci rayuwa mai kyau a nan gaba! Hakan ya motsa ka ka yi addu’a cewa Jehobah ba da daɗewa zai ba da amsa na ƙarshe ga addu’ar mai zabura: “Bari [abokan gabanka] su sha kumya da fargaba har abada: I, bari su ɗimota su hallaka: domin su sani kai, wanda sunanka Jehovah ne, kai kaɗai ne Maɗaukaki bisa dukan duniya.”—Zab. 83:17, 18.

[Hasiya]

a Kafin ka yi nazarin wannan talifin, zai yi kyau ka karanta Zabura 83 don ka fahimci abin da ke ciki.

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Wane yanayi ne Isra’ilawa suka fuskanta sa’ad da aka rubuta Zabura ta 83?

• Menene ainihin damuwar marubucin Zabura ta 83?

• Su waye ne ainihin magabtan Shaiɗan a yau?

• Ta yaya Jehobah zai amsa addu’ar da ke Zabura 83:18 a ƙarshe?

[Taswira a shafi na 15]

(For fully formatted text, see publication)

Ta yaya yaƙe-yaƙe da aka yi kusa da Magiddo na dā ya shafi rayuwarmu ta nan gaba?

Kogin Kishon

Harosheth

Dutsen Karmel

Kwarin Jezreel

Magiddo

Taanach

Dutsen Gilboa

Rijiyar Harod

Dutsen Moreh

En-dor

Dutsen Tabor

Tekun Galili

Kogin Urdun

[Hoto a shafi na 12]

Menene ya motsa wani mai zabura ya yi addu’a da dukan zuciyarsa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba