Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 10/15 p. 30-p. 32 par. 11
  • Darussa Daga Wasiƙu Zuwa ga Titus, Filimon, da Ibraniyawa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Darussa Daga Wasiƙu Zuwa ga Titus, Filimon, da Ibraniyawa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA ZAMA SAHIHI CIKIN BANGASKIYA
  • (Titus 1:1–3:15)
  • GARGAƊI “SABILI DA ƘAUNA”
  • (Fil. 1-25)
  • KU “NACE BI ZUWA KAMALA”
  • (Ibran. 1:1–13:25)
  • Bulus A Roma
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 10/15 p. 30-p. 32 par. 11

Maganar Jehobah Rayayya Ce

Darussa Daga Wasiƙu Zuwa ga Titus, Filimon, da Ibraniyawa

KAFIN a sake shi daga kurkuku na farko da ya shiga a Roma a shekara ta 61 A.Z., manzo Bulus ya ziyarci tsibirin Karita. Da Bulus ya lura cewa ikilisiyoyi da ke wajen suna bukatar su ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah, sai ya gaya wa Titus ya taimake su. Bayan haka, daga Makidoniya Bulus ya rubuta wa Titus wasiƙa don ya yi masa ja-gora a ayyukansa kuma ya taimake shi a wannan aikin.

Ba da daɗewa ba kafin a sake shi daga kurkuku a shekara ta 61 A.Z., Bulus ya rubuta wasiƙa zuwa ga Filimon, wani ɗan’uwa Kirista da ke zama a Kolosi. Wannan roƙo ne ga abokinsa.

A kusan shekara ta 61 A.Z., Bulus ya kuma rubuta wasiƙa ga ’yan’uwa Ibraniyawa masu bi da ke Yahudiya, wannan wasiƙar ta nuna cewa Kiristanci ta fi tsarin Yahudanci kyau. Duka wasiƙu ukun sun ƙunshi gargaɗi mai kyau a gare mu.—Ibran. 4:12.

KA ZAMA SAHIHI CIKIN BANGASKIYA

(Titus 1:1–3:15)

Bayan ya ba da ja-gorar yadda za a “kafa dattiɓai kuma cikin kowanne birni,” Bulus ya gargaɗi Titus ya “tsauta [wa masu taurin kai] da zafi, domin su zama sahihai cikin imani.” Ya gargaɗi dukan ikilisiyoyi da ke Karita su ‘ƙi rashin bin Allah . . . su kuma yi zamansu a duniyan nan da natsuwa.’—Titus 1:5, 10-13; 2:12; LMT.

Bulus ya ƙara ba da umurni don ya taimaki ’yan’uwa da ke Karita su riƙe ruhaniyarsu. Ya aririce Titus ya “guje ma tuhuma ta wauta . . . da jayayya a kan shari’a.”—Titus 3:9.

Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:

1:15—Ta yaya “ga masu-tsabta . . . dukan abu da tsabta ya ke,” amma marar tsabta ne “ga . . . ƙazamtattu da marasa-bangaskiya”? Don mu san amsar muna bukatar mu fahimci abin da Bulus yake nufi da “dukan abu.” Bulus ba ya magana a kan abubuwa da Kalmar Allah ta hana, amma yana magana ne a kan abubuwa da kowane ɗan’uwa mai bi zai tsai da shawara bisa ga lamirinsa. Ga mutumin da yake tunani daidai da ƙa’idar Allah, irin waɗannan abubuwa masu tsabta ne. Dabam yake da mutumin da yake yin mugun tunani kuma lamirinsa ta lalace.a

3:5—Ta yaya ne aka ceci shafaffun Kiristoci ta wurin ‘wanka’ kuma aka ‘sabonta su ta Ruhu mai tsarki’? An ‘cece su ta wurin wanka’ sa’ad da Allah ya yi musu wanka ko kuma ya tsabtace su da jinin Yesu don fansar hadaya. An ‘sabonta su ta ruhu mai-tsarki’ saboda sun zama “sabuwar halitta” a matsayin haifaffun ’ya’yan Allah na ruhu.—2 Kor. 5:17.

Darussa Dominmu:

1:10-13; 2:15. Dole ne Kiristoci masu kula su kasance da ƙarfin zuciya a wajen gyara abubuwa marasa kyau a cikin ikilisiya.

2:3-5. Kamar yadda yake a ƙarni na farko, ya kamata Kiristoci mata da suka manyanta su kasance da “ladabi cikin al’amuransu, ba masu-tsegumi ba, ba bayi ne ga yawan ruwan anab ba, masu-koyarda nagarta.” Ta haka, za su iya yi wa “ƙananan mata” a cikin ikilisiya gargaɗi.

3:8, 14. Mai da ‘hankalin mu lizimci nagargarun ayyuka’ yana da “kyau . . . kuma da amfani” saboda hakan zai taimake mu mu sami sakamako mai kyau a hidimar Allah kuma mu kasance dabam daga wannan muguwar duniya.

GARGAƊI “SABILI DA ƘAUNA”

(Fil. 1-25)

An yaba wa Filimon don ya nuna misali a wajen nuna ‘ƙauna da bangaskiya.’ Yadda ya wartsake ’yan’uwa Kiristoci ya sa Bulus ya yi “farinciki mai-yawa da ta’aziya.”—Fil. 4, 5, 7.

Hakan ya nuna wa dattawa misali mai kyau, Bulus ya sasanta matsala mai tsanani game da Unisimus ta wajen ba da gargaɗi ba doka ba “sabili da ƙauna.” Ya gaya wa Filimon: “Domin ina sakankancewa da biyayyarka ina rubuta maka, na fa sani za ka yi gaba da abin da ni ke faɗi.”—Fil. 8, 9, 21.

Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:

10, 11, 18—Ta yaya ne Unisimus “marar-amfani” a dā ya zama “mai-amfani”? Unisimus bawa ne da ya gudu daga gidan Filimon a Kolosi zuwa Roma. Wataƙila Unisimus ya saci kuɗi daga wajen shugabansa ne don ya biya kuɗin tafiyar da zai yi na mil 900. Hakika ba shi da amfani ga Filimon. A Roma, Bulus ya taimaki Unisimus ya zama Kirista. Yanzu da ya zama Kirista, wannan bawa “marar-amfani” a dā ya zama “mai-amfani.”

15, 16—Me ya sa Bulus bai roƙi Filimon ya gafarta wa Unisimus ba? Bulus yana so ya mai da hankali ga aikinsa na “wa’azin mulkin Allah, yana koyaswa da al’amura na wajen Ubangiji Yesu Kristi.” Saboda haka, ya zaɓi cewa ba zai mai da hankali ga al’amura na duniya ba, kamar zancen bayi.—A. M. 28:31.

Darussa Dominmu:

2. Filimon ya ba da gidansa don taron Kirista. Gata ne a yi taron fita wa’azi a gidanmu.—Rom. 16:5; Kol. 4:15.

4-7. Yana da kyau mu yaba wa ’yan’uwanmu masu bi waɗanda suka nuna misali mai kyau a wajen kasance da bangaskiya da ƙauna.

15, 16. Kada mu bari abubuwa da ba su da kyau da suke faruwa a rayuwa yanzu su sa mu damu ainun. Sakamakon zai iya zama da amfani kamar na Unisimus.

21. Bulus yana tsammanin cewa Filimon zai gafarta wa Unisimus ne. Muna bukatar mu gafarta wa ’yan’uwanmu da suka yi mana laifi.—Mat. 6:14.

KU “NACE BI ZUWA KAMALA”

(Ibran. 1:1–13:25)

Don ya nuna cewa bangaskiya ga hadaya ta Yesu ta fi ayyuka na Doka, Bulus ya nanata girman wanda ya Kafa Kiristanci, tsarin firistinsa, hadayarsa, da sabon alkawari. (Ibran. 3:1-3; 7:1-3, 22; 8:6; 9:11-14, 25, 26) Hakika, wannan ilimin ya taimaki Ibraniyawa su jimre tsanantawa da suka fuskanta a hannun Yahudawa. Bulus ya aririci ’yan’uwansa Ibraniyawa masu bi su “nace bi zuwa kamala”—Ibran. 6:1.

Menene muhimmancin bangaskiya ga Kirista? Bulus ya ce: “Ba shi kuwa yiwuwa a gamshe [Allah] ba sai tare da bangaskiya.” Ya ƙarfafa Ibraniyawa: “Tare da haƙuri kuma mu yi tseren da an sa gabanmu,” yin haka cikin bangaskiya.—Ibran. 11:6; 12:1.

Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:

2:14, 15—Da yake Shaiɗan yana da “ikon mutuwa” yana nufin cewa zai iya kashe duk wanda yake so ne? A’a, ba haka yake nufi ba. Amma, a farkon lokacin da Shaiɗan ya soma mugunta a Adnin, ƙaryar da ya yi ta jawo mutuwa saboda Adamu ya yi zunubi kuma ya ba wa ’yan adam zunubi da mutuwa. (Rom. 5:12) Bugu da ƙari, wakilan Shaiɗan da ke duniya sun tsananta wa bayin Allah har ga mutuwa, kamar yadda suka yi wa Yesu. Amma haka ba ya nufin cewa Shaiɗan yana da ikon da zai kashe kowa da yake so. Inda yana da ikon yin hakan, ai da ya kashe dukan masu bauta wa Jehobah tun da daɗewa. Jehobah yana kāre rukunin mutanensa kuma ba zai bari Shaiɗan ya halaka su ba. Ko da Allah ya ƙyale wasun mu su mutu don harin Shaiɗan, mu tabbata cewa Allah zai cire kowane irin mugunta da muke fuskanta.

4:9-11—Ta yaya muka ‘shiga cikin hutun’ Allah? A ƙarshen kwanaki shida na halitta, Allah ya huta daga aikinsa na halitta da tabbacin cewa nufinsa game da duniya da kuma ’yan adam za su cika. (Far. 1:28; 2:2, 3) Mun “shiga cikin wannan hutu” ta wurin ƙin yin ayyuka da muke so da kuma amincewa da fansa na Allah. Sa’ad da muka ba da gaskiya ga Jehobah kuma muka bi Ɗansa maimakon mu biɗi abubuwa na son kai, muna more albarka kowace rana.—Mat. 11:28-30.

9:16—Wanene “wasici” na sabon alkawari? Jehobah shi ne tushin sabon alkawari, Yesu kuma shi ne “wasici.” Yesu shi ne Matsakanci na alkawari, kuma ta mutuwarsa ya ba da kansa hadaya da ta nuna cewa alkawarin zai cika.—Luk 22:20; Ibran. 9:15.

11:10, 13-16—Wane “birni” ne Ibrahim yake jira? Wannan ba birni na zahiri ba ne, amma na alama. Ibrahim ya jira “Urushalima ta sama,” da take ɗauke da Yesu Kristi da kuma abokan sarautarsa guda 144,000. A cikin ɗaukakarsu na samaniya ana kiran waɗannan abokan sarauta “tsattsarkan birni kuma, Sabuwar Urushalima.” (Ibran. 12:22; R. Yoh. 14:1; 21:2) Ibrahim yana begen ganin rayuwa a ƙarƙashin Mulkin Allah.

12:2—Wane “farinzuciya . . . aka sa ga gaban [Yesu]” da ya sa ‘ya jimre giciye’? Wannan farin ciki ne na ganin abin da hidimarsa za ta cim ma har da yadda za a tsarkaka sunan Jehobah, a kunita ikon mallaka na Allah, da kuma ceton ’yan adam daga mutuwa ta wurin ba da ransa ta fansa. Yesu kuma yana begen ganin ladar da za a ba shi na zama Sarki da kuma zama Babban Firist don amfanin ’yan adam.

13:20—Me ya sa aka ce sabon alkawari zai zama na “madawwami”? Ga dalilai uku: (1) Ba za a taɓa canjawa ba, (2) abin da za ta cim ma na dindindin ne, kuma (3) bayan Armageddon “waɗansu tumaki” za su ci gaba da amfana daga wannan sabuwar tsarin alkawari.—Yoh. 10:16.

Darussa Dominmu:

5:14. Ya kamata mu zama ɗalibai na Littafi Mai Tsarki masu ƙwazo, kuma mu yi abin da muka koya daga ciki. Wannan hanya kawai da za mu iya zama waɗanda “hankulansu wasassu bisa ga aikaceya garin rabewar nagarta da mugunta.”—1 Kor. 2:10.

6:17-19. Kasancewa da bege bisa ga alkawarin Allah zai taimake mu don kada mu guje wa hanyar gaskiya.

12:3, 4. Maimakon mu ‘gaji, mu yi suwu cikin rayukanku’ don kalilan jarabobbi ko hamayya da muke fuskanta, ya kamata mu ci gaba a ruhaniya kuma mu ƙara ƙarfafa kanmu don mu iya jimre jarabobbi. Mu kuɗiri aniya mu yi tsayayya “har jini,” wato, har mutuwa.—Ibran. 10:36-39.

12:13-15. Kada mu bari wani “tushen ɗaci,” ko kuma wani a cikin ikilisiya da yake neman laifi da yadda ake yin abubuwa, ya hana mu ‘miƙa karabmu kuma domin sawayenmu.’

12:26-28. Za a halaka “abubuwan da aka halitta” da hannu, wato, dukan wannan mugun zamani har da mugun sama waɗanda ba Allah ba ne ya halicce su. Idan haka ya faru, abubuwa “da ba a raurawadda su,” ba, wato, Mulkin da kuma masu goyon bayansa, sune za su tsira. Abu mai muhimmanci ne mu yi wa’azin Mulki da himma kuma mu yi rayuwa bisa ga ƙa’idodinsa.

13:7, 17. Mai da hankali ga wannan umurnin na yin biyayya da kuma miƙa kai ga masu kula a cikin ikilisiya zai taimake mu mu ba da haɗin kai.

[Hasiya]

a Ka duba Hasumiyar Tsaro na 15 ga Oktoba, 2007, shafuffuka 26-27.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba