Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 12/15 pp. 12-16
  • Fahimtar Matsayin Yesu Na Musamman A Nufin Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Fahimtar Matsayin Yesu Na Musamman A Nufin Allah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Ɗa Haifaffe Kaɗai”
  • “Kalman”
  • “Amin”
  • ‘Matsakanci na Sabon Alkawari’
  • “Babban Firist”
  • ‘Zuriya’ da Aka Annabta
  • Wanda Dukan Annabawa Suka Yi Shaidarsa
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
  • Abin da Yesu Ya Koyar Game da Kansa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Jehobah Yana Daraja “Amin” da Muka Furta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 12/15 pp. 12-16

Fahimtar Matsayin Yesu Na Musamman A Nufin Allah

“Ni ne hanya, Ni ne gaskiya, Ni ne rai: ba mai-zuwa wurin Uban sai ta wurina.”—YOH. 14:6.

1, 2. Me ya sa za mu so mu bincika matsayin Yesu na musamman a nufin Allah?

A TARIHI, mutane da yawa sun ƙoƙarta sosai don su zama fitattu a cikin mutanen da suka kewaye su, amma kaɗan ne kawai suka yi nasara. Har ma wasu mutane ƙalilan sukan yi da’awar cewa sun fita dabam a wasu hanyoyi na musamman. Duk da haka, Yesu Kristi, Ɗan Allah, ya fita dabam a hanyoyi masu yawa.

2 Me ya sa za mu so matsayin Yesu na musamman? Domin hakan ya shafi dangantakarmu da Jehobah, Ubanmu na samaniya! Yesu ya ce: “Ni ne hanya, Ni ne gaskiya, Ni ne rai: ba mai-zuwa wurin Uban sai ta wurina.” (Yoh. 14:6; 17:3) Bari mu bincika wasu hanyoyin da Yesu ya fita dabam. Yin hakan zai sa mu fahimci matsayinsa a nufin Allah.

“Ɗa Haifaffe Kaɗai”

3, 4. (a) Me ya sa za mu ce Yesu ya fita dabam a matsayinsa na Ɗa makaɗaici? (b) Ta yaya ne matsayin Yesu a halitta ya fita dabam?

3 Yesu ba “Ɗan Allah” ba ne ba kawai. Abin da Shaiɗan ya kira Yesu ke nan sa’ad da yake jarraba shi. (Mat. 4:3, 6) Ana kiran Yesu “Ɗa haifaffe kaɗai na Allah.” (Yoh. 3:18) Kalmar Helenanci da aka fassara “haifaffe kaɗai” an ce tana nufin “irinsa kaɗai,” “irinsa kaɗai a dangi,” ko kuwa na “musamman.” Jehobah yana da miliyoyin ’ya’ya na ruhu. Ta yaya ne Yesu ya zama “irinsa kaɗai a cikin dangi”?

4 Yesu ya fita dabam domin shi kaɗai ne Ubansa ya halitta da hannunsa. Shi ne Ɗan fari. Gaskiyar ita ce, shi ne “ɗan fari . . . gaban dukan halitta.” (Kol. 1:15) Shi ne “farkon halittar Allah.” (R. Yoh. 3:14) Matsayin da Ɗa makaɗaici ya cika a halitta ya fita dabam. Ba shi ne Mahalicci ba, ko kuma Tushen halitta. Amma Jehobah ya yi amfani da shi ne ya halicci dukan abubuwa. (Karanta Yohanna 1:3.) Manzo Bulus ya rubuta: “Amma a garemu akwai Allah ɗaya, Uba ne, wanda dukan kome daga wurinsa ya ke, mu kuwa gareshi mu ke; da Ubangiji ɗaya kuma, Yesu Kristi, wanda dukan kome ta wurinsa ya ke, mu kuma ta wurinsa ne.”—1 Kor. 8:6.

5. Ta yaya Nassosi suka nanata hanyoyi da Yesu ya fita dabam?

5 Yesu ya fita dabam kuma a hanyoyi masu yawa. Nassosi sun kira shi da laƙabi da yawa ko kuma sunaye da suka nuna matsayinsa na musamman a nufin Allah. Yanzu bari mu ƙara bincika biyar cikin waɗannan sunayen da Nassosin Kirista na Helenanci suka yi amfani da su ga Yesu.

“Kalman”

6. Me ya sa ya dace da ake kiran Yesu “Kalman”?

6 Karanta Yohanna 1:14. Me ya sa aka kira Yesu “Kalman”? Wannan laƙabin ya nuna aikin da ya soma yi tun lokacin da aka halicci halittu masu basira. Jehobah ya yi amfani da Ɗansa ya isar da saƙo da umurni ga sauran ’ya’yan ruhu, kamar yadda Allah ya yi amfani da shi ya sanar da saƙonsa ga ’yan adam a duniya. An ga cewa Yesu ne Kalma ko kuma kakakin Allah sa’ad da Kristi ya gaya wa Yahudawa masu sauraronsa: “Abin da ni ke koyarwa ba nawa ba ne, amma nasa ne wanda ya aiko ni. Idan kowane mutum yana da nufi shi aika nufin Allah, shi za ya sani ko abin da ni ke koyarwa na Allah ne, ko domin kaina ni ke magana.” (Yoh. 7:16, 17) An ci gaba da kiran Yesu da wannan laƙabin “Kalmar Allah” har bayan da ya koma ɗaukakarsa ta samaniya.—R. Yoh. 19:11, 13, 16.

7. Ta yaya za mu yi koyi da tawali’un da Yesu ya nuna a matsayinsa na “Kalman”?

7 Ka yi tunanin abin da wannan laƙabin yake nufi. Ko da yake Yesu ne ya fi hikima a cikin dukan halittun Jehobah, bai dogara ga nasa hikimar ba. Ya faɗi abin da Ubansa ya umurce shi. A koyaushe yana jawo hankalin mutane ga Jehobah maimakon kansa. (Yoh. 12:50) Wannan misali ne mai kyau da za mu yi koyi da shi. Mu ma an ɗanka mana gata mai tamani na “bishara ta alheri!” (Rom. 10:15) Fahimtar misalin Yesu na tawali’u ya kamata ya motsa mu mu guji faɗan ra’ayinmu. “Kada [mu] zarce abin da an rubuta” sa’ad da muke sanar da saƙon Nassosi mai ceton rai.—1 Kor. 4:6.

“Amin”

8, 9. (a) Menene kalmar nan “amin” take nufi, me ya sa aka kira Yesu “Amin”? (b) Ta yaya Yesu ya cika hakkinsa a matsayin “Amin”?

8 Karanta Ru’ya ta Yohanna 3:14. Me ya sa aka kira Yesu “Amin”? Kalmar da aka fassara “amin” kalmar Ibrananci ne da ke nufin “ya kasance hakan,” ko kuma “hakika.” Tushen kalmar Ibrananci inda aka ɗauko ta tana nufin a “kasance da aminci” ko kuma “tabbatacciya.” Ana amfani da wannan kalmar sa’ad da ake kwatanta amincin Jehobah. (K. Sha 7:9; Isha. 49:7) Saboda haka, a wace hanya ce Yesu ya fita dabam sa’ad da aka kira shi “Amin”? Ka lura da yadda 2 Korinthiyawa 1:19, 20 ta ba da amsar: “Ɗan Allah, Yesu Kristi wanda aka yi wa’azinsa a cikinku . . . , ba i da a’a ba ne, amma cikinsa akwai i. Gama kome yawan alkawura na Allah, a cikinsa akwai i: domin wannan fa ta wurinsa akwai Amin.”

9 Yesu ne “Amin” ga dukan alkawuran Allah. Tafarkin rayuwarsa marar aibi a duniya, har da mutuwarsa ta hadaya, sun ba da tabbaci kuma sun sa ya yiwu a cika dukan alkawuran Jehobah Allah. Ta wajen kasancewa da aminci, Yesu ya kuma ƙaryata ɗa’awar da Shaiɗan ya yi da ke rubuce a littafin Ayuba, cewa idan bayin Allah suna cikin hani, wahala da gwaji za su ƙi Shi. (Ayu. 1:6-12; 2:2-7) A cikin dukan halittun Allah, Ɗansa na farko ne ya ba da amsa ta ƙwarai ga wannan da’awar. Ƙari ga haka, Yesu ya ba da tabbaci da ya fi kyau da ya goyi bayan Ubansa a batun ikon mallaka na Jehobah.

10. Ta yaya za mu iya yin koyi da Yesu a matsayinsa na “Amin”?

10 Ta yaya za mu yi koyi da Yesu a matsayinsa na “Amin”? Ta wajen kasancewa da aminci ga Jehobah da kuma tallafa wa ikon mallakarsa na sararin samaniya. Ta wurin yin hakan muna bin umurnin da ke rubuce a Misalai 27:11: “Ɗana, ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata: domin in mayarda magana ga wanda ya zarge ni.”

‘Matsakanci na Sabon Alkawari’

11, 12. Ta yaya matsayin Yesu na Matsakanci ya fita dabam?

11 Karanta 1 Timothawus 2:5, 6. Yesu ne “matsakanci ɗaya kuma tsakanin Allah da mutane.” Shi “matsakanci ne na sabon alkawali.” (Ibran. 9:15; 12:24) Amma, an kuma kira Musa matsakanci, wato na Dokar alkawari. (Gal. 3:19) To, ta yaya ne matsayin Yesu na Matsakanci ya fita dabam?

12 Yare na asali da aka fassara “matsakanci” kalma ce ta doka. Ya nuna cewa Yesu ne Matsakanci bisa doka (ko kuma a wani fanni wanda aka ba iko bisa doka) na sabon alkawari da ya sa ya yiwu aka kafa sabuwar al’umma, wato, “Isra’ila na Allah.” (Gal. 6:16) Wannan al’ummar ta ƙunshi shafaffu Kiristoci, waɗanda suke cikin “priesthood basarauci” na samaniya. (1 Bit. 2:9; Fit. 19:6) Dokar alkawari wadda Musa ne matsakancinta ba ta iya kafa irin wannan al’ummar ba.

13. Menene matsayin Yesu na Matsakanci ya ƙunsa?

13 Menene matsayin Yesu na Matsakanci ya ƙunsa? Jehobah ya yi amfani da darajar jinin Yesu ga waɗanda aka kawo cikin sabon alkawarin. Ta hakan, Jehobah ya mai da su masu adalci. (Rom. 3:24; Ibran. 9:15) Allah zai ɗauke su a matsayin waɗanda suka cancanci su shiga sabon alkawari da begen zama firistoci masu sarauta a sama! Da yake shi ne Matsakancinsu, Yesu ya taimake su su kasance da matsayi mai kyau a gaban Allah.—Ibran. 2:16.

14. Me ya sa ya kamata dukan Kiristoci, ko da menene begensu su nuna godiya ga matsayin Yesu na Matsakanci?

14 Waɗanda ba sa cikin sabon alkawarin kuma fa, wato, waɗanda suke da begen zama a duniya har abada, ba a sama ba? Ko da yake ba sa cikin sabon alkawari, suna amfana daga alkawarin. An gafarta musu zunubansu kuma an sanar da su masu adalci a matsayin abokan Allah. (Yaƙ. 2:23; 1 Yoh. 2:1, 2) Ko da begenmu na zuwa sama ne ko kuma na zama a duniya, muna da dalili mai kyau na nuna godiya ga matsayin Yesu na Matsakanci na sabon alkawari.

“Babban Firist”

15. Ta yaya matsayin Yesu na Babban Firist ya bambanta da na maza da suka yi hidima na babban firistoci?

15 Maza da yawa a dā sun yi hidima na babban firistoci, duk da haka, matsayin Yesu na Babban Firist ya fita dabam. Ta yaya? Bulus ya ba da bayani: “Wanda babu bukata gareshi kowace rana, kamar waɗannan manyan priests, shi miƙa hadayu, domin nasa zunubai tukuna, kāna domin na jama’a: gama wannan ya yi so ɗaya ɗungum, sa’anda ya miƙa kansa.”—Ibran. 7:27, 28.a

16. Me ya sa hadayar Yesu ta fita dabam?

16 Yesu kamiltaccen mutumi ne, wanda ya yi daidai da Adamu kafin ya yi zunubi. (1 Kor. 15:45) Da hakan, Yesu ne kaɗai zai iya ba da cikakkiyar hadaya, irin hadayar da ba a bukatar maimaitawa. A ƙarƙashin Dokar Musa, ana miƙa hadaya kowace rana. Irin waɗannan hadayun da kuma hidimomin firistoci suna nuna abin da za a yi ne a nan gaba, wato, abubuwan da Yesu zai cim ma. (Ibran. 8:5; 10:1) Saboda haka, domin Yesu ya cim ma abubuwa da yawa fiye da sauran firistoci kuma matsayinsa zai kasance na dindindin, matsayin Yesu na Babban Firist ya fita dabam.

17. Me ya sa ya kamata mu fahimci matsayin Yesu na Babban Firist, kuma ta yaya za mu yi hakan?

17 Muna bukatar hidimomin Yesu na Babban Firist don mu kasance da matsayi mai kyau a gaban Allah. Lallai muna da Babban Firist mai ban al’ajabi! Bulus ya rubuta: “Gama ba mu da babban priest wanda ba shi taɓuwa da tarayyar kumamancinmu ba: amma wanda an jarabce shi a kowace fuska kamarmu, sai dai banda zunubi.” (Ibran. 4:15) Hakika, ya kamata fahimtar wannan batun ya motsa mu ‘kada mu yi rayuwa don kanmu, amma ga wanda ya mutu ya kuwa tashi sabili da mu.’—2 Kor. 5:14, 15; Luk 9:23.

‘Zuriya’ da Aka Annabta

18. Wane annabci ne aka yi bayan da Adamu ya yi zunubi, kuma menene aka bayyana daga baya game da wannan annabcin?

18 A cikin Adnin, sa’ad da ya bayyana cewa ’yan adam sun yi hasarar kome, wato, tagomashi mai kyau a gaban Allah, rai madawwami, farin ciki, da kuma Aljanna, Jehobah Allah ya annabta cewa zai kawo Mai Ceto. An kira shi ‘zuriya.’ (Far. 3:15) Tun da daɗewa, wannan zuriyar da ba a ambata sunansa ba ya zama jigon annabce-annabcen masu yawa a cikin Littafi Mai Tsarki. Zai zama zuriyar Ibrahim, Ishaƙu, da kuma Yakubu. Zai kuma fito ne daga zuriyar Sarki Dauda.—Far. 21:12; 22:16-18; 28:14; 2 Sam. 7:12-16.

19, 20. (a) Wanene Zuriya da aka yi alkawarinsa? (b) Me ya sa za a ce ba Yesu kaɗai ba ne zuriyar da aka annabta?

19 Wanene wannan Zuriya da aka yi alkawarinsa? Za a iya samun amsar wannan tambayar a cikin Galatiyawa 3:16. (Karanta) Amma, daga baya cikin wannan sura, manzo Bulus ya gaya wa shafaffu Kiristoci cewa: “Idan kuma na Kristi ne, zuriyar Ibrahim ku ke kuma, magada bisa ga alkawali.” (Gal. 3:29) Ta yaya Kristi ya zama Zuriya da aka yi alkawarinta, kuma aka haɗa wasu a ciki?

20 Mutane da yawa sun yi da’awar cewa sun fito ne daga zuriyar Ibrahim, wasu suna aikatawa kamar annabawa. Wasu addinai sun ɗauki da’awar cewa annabawansu sun fito ne daga zuriyar Ibrahim da muhimmanci sosai. Amma dukan waɗannan ne Zuriya da aka yi alkawarinta? A’a. Kamar yadda Allah ya hure manzo Bulus ya rubuta, ba dukan zuriyoyin Ibrahim ba ne za su iya yin da’awar cewa su ne Zuriya da aka yi alkawarinta. Ba a yi amfani da sauran zuriyar ’ya’yan Ibrahim don a albarkaci ’yan adam ba. Za a sami zuriyar da za ta albarkaci mutane ne kawai ta wurin Ishaƙu kaɗai. (Ibran. 11:18) Mutum ɗaya ne kawai, Yesu Kristi, wanda ya fito daga zuriyar Ibrahim da aka rubuta cikin Littafi Mai Tsarki, shi ne ainihin sashen zuriyar da aka annabta.b Dukan sauran sun zama zuriyar Ibrahim ta biyu domin su “na Kristi ne.” Hakika, matsayin Yesu wajen cika wannan annabci ya fita dabam.

21. Menene ya burge ka game da yadda Yesu ya cika hakkinsa na musamman a nufin Jehobah?

21 Menene muka koya daga maimaita matsayin Yesu na musamman a nufin Jehobah? Tun daga lokacin halitta har zuwa yanzu, Ɗan Allah makaɗaici ya fita dabam, babu kamarsa. Amma, wannan Ɗan Allah na musamman da ya zama Yesu ya yi hidima da ta jitu da nufin Ubansa cikin tawali’u, bai nemi ya ɗaukaka kansa ba. (Yoh. 5:41; 8:50) Wannan misali ne mafi kyau a gare mu a yau! Kamar Yesu, bari ya zama makasudinmu mu “yi kome saboda ɗaukakar Allah.”—1 Kor. 10:31.

[Hasiya]

a In ji wani masanin Littafi Mai Tsarki, kalmar da aka fassara “sau ɗaya ɗungum” ta nuna kalmar Littafi Mai Tsarki mai muhimmanci da ke “nufin wanda ya fita dabam, ko kuma mutuwar Kristi wadda babu irinta.”

b Ko da yake Yahudawa a ƙarni na farko sun yi tunanin cewa a matsayin ’ya’yan Ibrahim na zahiri, za su samu tagomashi, sun saurari mutum ɗaya da zai zo a matsayin Almasihu, ko Kristi.—Yoh. 1:25; 7:41, 42; 8:39-41.

Ka Tuna?

• Menene ka koya game da matsayin Yesu na musamman daga laƙabinsa ko kuma sunayensa? (Ka duba akwati.)

• Ta yaya za ka yi koyi da misalin Ɗan Jehobah da babu kamarsa?

[Box/Hoto a shafi na 15]

Wasu Laƙabi da Suka Nuna Matsayin Yesu na Musamman a Nufin Allah

◼ Ɗa Haifaffe Kaɗai. (Yoh. 1:3) Yesu kaɗai ne Ubansa ya halitta kai tsaye.

◼ Kalman. (Yoh. 1:14) Jehobah ya yi amfani da Ɗansa a matsayin kakaki don ya sanar da bayanai da kuma umurni ga sauran halittu.

◼ Amin. (R. Yoh. 3:14) Tafarki mai kyau da Yesu ya bi sa’ad da yake duniya, har da mutuwarsa ta hadaya, sun tabbatar kuma za su sa alkawuran Jehobah Allah su cika.

◼ Matsakanci na Sabon Alkawari. (1 Tim. 2:5, 6) Da yake shi Matsakanci ne bisa doka, Yesu ya sa ya yiwu a kafa sabuwar al’umma, wato “Isra’ila na Allah,” da ta ƙunshi Kiristoci da za su kafa “priesthood basarauci” na samaniya.—Gal. 6:16; 1 Bit. 2:9.

◼ Babban Firist. (Ibran. 7:27, 28) Yesu ne kaɗai mutumin da zai iya miƙa cikakkiyar hadaya, wadda ba a bukatar maimaitawa. Zai iya tsabtace mu daga zunubi kuma ya ’yantar da mu daga mutuwa.

◼ Zuriya da Aka Yi Alkawarinta. (Far. 3:15) Yesu Kristi ne kaɗai ainihin sashen wannan zuriya da aka annabta. Duka sauran da suka zama sashe na biyu na zuriyar Ibrahim su na “Kristi ne.”—Gal. 3:29.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba