Kana Tsoron Matattu?
MUTANE da yawa suna amsawa , “A’a. Me ya sa zan ji tsoro?” Sun gaskata cewa mutanen sun mutu. Amma wasu miliyoyin mutane sun gaskata cewa matattu sun zama kurwa suna ci gaba da rayuwa.
A Afirka ta yamma, a ƙasar Benin, mutane da yawa sun gaskata cewa matattu za su iya dawowa su kashe sauran ’yan iyalinsu. Mutane suna sayar da mallakarsu ko kuma su ci bashi don su sayi dabba su yi hadaya don su faranta wa danginsu da suka mutu rai. Wasu mutane suna yin sihiri, wanda ya haɗa da ra’ayin cewa kurwar mutum ba ta mutuwa kuma za ta iya magana da waɗanda ke da rai. Sa’ad da wasu suka fuskanci mummunan abu sukan ce kurwan matattu ne suka haddasa hakan.
Wani mutum da ya fuskanci irin wannan yanayi, shi ne Agboola, yana da zama a kan iyakar ƙasar Benin da Nijeriya. Ya ce: “Sihiri abu ne na yau da kullum a yankinmu. Al’adar su ne su yi wa gawaye wanka, don su shirya su zuwa lardi na ruhu. Sau da yawa ina tattara raguwan sabulai da aka yi wankan gawaye da su in haɗa su da garin magani. Sa’an nan, in shafa magani a jikin bindigana na farauta, sai in kira irin dabban da nake so in harba. Irin waɗannan ayyuka ne na yau da kullum kuma suna da amfani ni. Amma, wasu bangaren sihiri suna da ban tsoro.
“Sa’ad da yarana biyu maza suka mutu ba dalili, na yi zaton wani ne ya yi mini sihiri. Don in bincika, sai na je wajen wani tsoho, sananne ne wajen sihiri. Ya gaya mini cewa kashe su aka yi. Abin baƙin ciki ma, ya ce yanzu ’ya’yana suna jira a duniyar iskoki su zama bayin wanda ya kashe su bayan ya mutu. Tsohon ya daɗa cewa ɗana na uku ma zai mutu. Bayan ɗan kwanaki, shi ma ya mutu.”
Sai Agboola ya sadu da John, wani Mashaidin Jehobah daga Nijeriya. Bayanin da John ya yi game da yanayin matattu daga cikin Littafi Mai Tsarki ne. Wannan bayani ya canja rayuwar Agboola. Zai iya canja na ka ma.
Matattu Suna Raye Ne?
Wanene ya cancanci ya amsa wannan tambayar? Ba mutum ba ne ko da sanannen wajen sihiri. Maimakon haka, mahaliccin duka rai “cikin sammai da bisa duniya kuma, abubuwa masu-ganuwa da abubuwa marasa-ganuwa,” ne zai iya ba da amsar. (Kolossiyawa 1:16) Ya halicci mala’iku don su zauna a sama kuma mutane da dabbobi su zauna a duniya. (Zabura 104:4, 23, 24) Rayuwa duka ta tabbata gare shi. (Ru’ya ta Yohanna 4:11) Ka yi la’akari da abin da Kalmar Allah Littafi Mai Tsarki ya ce game da mutuwa.
Jehobah ne ya fara magana game da mutuwa. Ya gargaɗi Adamu da Hauwa’u cewa za su mutu idan ba su yi biyayya gare shi ba. (Farawa 2:17) Me yake nufi? Jehobah ya yi bayani: “Turɓaya ne kai, ga turɓaya za ka koma.” (Farawa 3:19) Idan mutum ya mutu jikinsa yana zama turɓaya. Rai sai ya ƙare, ko kuma ana iya cewa, ya koma ga Mahalicci Wanda shi ne mai ba da rai. Saboda haka Zabura 104:29, 30 ta ce: “Ka swance lumfashinsu, sun mutu, Sun koma turɓayassu.”
Adamu da Hauwa’u sun yi zunubi da son ransu kuma saboda haka aka yi musu hukuncin kisa. Amma, ba su ba ne suka soma mutuwa. Ɗansu Habila ne ya soma mutuwa. Yayansa Kayinu ne ya kashe shi. (Farawa 4:8) Kayinu bai ji tsoron cewa ɗan’uwansa da ya mutu zai rama ba. Maimakon haka, Kayinu ya ji tsoron abin da mutanen da suke da rai za su yi masa.—Farawa 4:10-16.
Bayan ƙarnuka da yawa, Sarki Hirudus ya damu sa’ad da masana taurari suka gaya masa cewa an haifi “Sarkin Yahudawa” a ƙasarsa. Domin ya kashe wannan sarki da ƙila ya yi jayayya da shi, sai ya ba da doka a kashe duk wani yaro namiji ɗan shekara biyu zuwa kasa da haihuwa a Baitalami. Amma mala’ika ya umurci Yusufu ya ɗauki Yesu da Maryamu su “gudu zuwa cikin Masar.”—Matta 2:1-14.
Sa’ad da Hirudus ya mutu, mala’ika ya gaya wa Yusufu ya koma Isra’ila, “gama su waɗanda suka nemi ran ɗan yaron sun mutu.” (Matta 2:19, 20) Mala’ikan wanda shi kansa ruhun ne ya sani cewa Hirudus ba zai iya yi wa Yesu kome ba. Yusufu bai ji tsoron Sarki Hirudus da ya mutu ba. Amma, Yusufu ya ji tsoron abin da Arkila’us ɗan Hirudus zai iya yi. Yusufu ya kai iyalinsa Galili, inda sarautar Arkila’us bai kai ba.—Matta 2:22.
Labarin ya nuna mana cewa matattu ba su da iko. Amma, yaya za a iya bayyana abin da Agboola da waɗansu suka fuskanta?
“Aljanu,” ko kuma Iskoki
Sa’ad da yake matashi, Yesu ya haɗu da iskoki. Sun gane Yesu kuma sun kira shi “Ɗan Allah.” Yesu ma ya san su. Su ba kurwan mutanen da suka mutu ba ne. Maimakon haka, Yesu ya ce su “aljanu” ko kuma iskoki.—Matta 8:29-31; 10:8; Markus 5:8.
Littafi Mai Tsarki ya ambata mala’ikun da suka yi biyayya ga Allah da waɗanda suka yi tawaye. Littafin Farawa ya ce sa’ad da Jehobah ya kori Adamu da Hauwa’u daga lambun Adnin, ya sa kerub ko kuma mala’iku a gabashin lambun don su hana kowa shigan ciki. (Farawa 3:24) Wannan ne wataƙila lokaci na farko da mutane suka ga mala’iku.
Daga baya, wasu mala’iku suka zo duniya suka zama mutane. Jehobah bai ba su aiki a duniya ba. Amma, “suka rabu da nasu wurin zama” a sama. (Yahuda 6) Sun zo ne da mugun nufi. Suka auri mata, da suka haifi ’ya’ya da ake kira ƙattai. Ƙattan da iyayensu masu tawaye suka cika duniya da mugunta. (Farawa 6:1-5) Jehobah ya yi maganin wannan ta wajen kawo rigyawa a zamanin Nuhu. Ruwa ya halaka mugayen mutane har da ƙattan. Menene ya faru da mala’ikun?
Rigyawar ya sa suka koma sama. Amma, Jehobah ya hana su shiga cikin ainihin “matsayi nasu.” (Yahuda 6) Littafi Mai Tsarki ya ce: “Gama idan Allah ba ya keɓe mala’iku sa’anda suka yi zunubi ba, amma ya jefa su cikin Jahannama, ya sanya su kuma cikin ramummuka masu-dufu, ajiyayyu zuwa hakumci.”—2 Bitrus 2:4.
A Helenanci na ainihin, kalmar nan da ake kira “jahannama” a wannan aya ita ce Tar·ta·roʹsas, wannan ba wuri ba ne, amma yanayi ne da zai rage ayyukan waɗannan Aljanu. Aljanun ba za su iya zama mutane ba, amma suna da iko sosai kuma za su iya rinjayar mutane. Suna iya sauka bisa ’yan adam da dabbobi. (Matta 12:43-45; Luka 8:27-33) Suna iya ruɗan mutane ta wajen zama su ne kurwan waɗanda suka mutu. Me ya sa? Don su hana mutane bauta wa Jehobah a hanyar da ta gamshe shi kuma su rikiɗar da su game da ainihin yanayin matattu.
Yadda Za a Sha kan Tsoro
Agboola ya fahimci bayanin da Littafi Mai Tsarki ya yi game da matattu da kuma iskoki. Ya fahimci cewa yana bukatar ya kara iliminsa. Sai ya soma karanta Littafi Mai Tsarki da Littattafai da suke bayyana Littafi Mai Tsarki tare da John. Agboola ya sami kwanciyar rai da ya sani cewa ’ya’yansa suna barci ne a kabari, ba suna jira a wani wuri su zama bayin wanda ya kashe su ba.—Yohanna 11:11-13.
Agboola ya kuma fahimta cewa dole ne ya daina yin sihiri. Ya kona dukan kayan da yake da su na sihiri. (Ayukan Manzanni 19:19) Wasu a yankinsu suka yi masa gargaɗi cewa aljannun za su dame shi. Amma Agboola bai ji tsoro ba. Ya bi umurnin da ke cikin Afisawa 6:11, 12: “Ku yafa dukan makamai na Allah, . . . gama kokuwarmu na . . . rundunai masu-ruhaniya na mugunta.” Makamai na ruhaniya sun ƙunshi gaskiya, adalci, bishara na salama, bangaskiya, da kuma Kalmar Allah. Irin waɗannan makaman sun fito daga Allah kuma suna da ƙarfi.
Wasu abokanan Agboola da danginsa suka daina sha’ani da shi domin ya daina bin al’adarsu da ta ƙunshi sihiri. Amma, ya sami sababbin abokane a Majami’ar Mulki na Shaidun Jehobah, waɗanda suka gaskata abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa.
Yanzu Agboola ya sani cewa ba da daɗewa ba Jehobah zai tsabtacce duniya kuma zai tsayadda dukan ayyukan aljannu. Daga bisani, zai halaka su ɗungum. (Ru’ya ta Yohanna 20:1, 2, 10) A nan duniya Allah zai ta da “dukan waɗanda suna cikin kabarbaru.” (Yohanna 5:28, 29) Wannan zai haɗa da Habila, yaran da Sarki Hirudus ya kashe, da kuma miliyoyin mutane. Agboola ya gaskata cewa har da yaransa uku. Wataƙila ’yan’uwanka da suka mutu suna cikin waɗanda za a ta da. Dukan waɗanda aka ta da za su faɗi cewa sa’ad da suka mutu, ba su san abin da ke faruwa ba, wato, ba su san ko an yi musu biki ba.
Ba ka da dalilin jin tsoron matattu. Maimakon haka, ka yi kewar ganin waɗanda kake ƙauna. A wannan lokacin da ake ciki, me ya sa ba za ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki don ka ƙarfafa bangaskiyarka? Ka yi tarayya da waɗanda suka gaskata da abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. Idan kana yin sihiri, ka daina nan da nan. Ka tsare kanka daga aljanu ta wurin saka “makamai na Allah.” (Afisawa 6:11) Shaidun Jehobah za su yi farin cikin taimakonka. Suna yin nazarin Littafi Mai Tsarki kyauta da mutane da taimakon littafin nan Menene Ainihin Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?a
Yanzu Agboola ba ya jin tsoron matattu, kuma ya koyi yadda zai guje wa aljanu. Ya ce: “Ban san wanda ya kashe ’ya’yana uku ba. Amma tun da na soma bauta wa Jehobah, ina da ’ya’ya bakwai. Babu wanda ke cikin lardi na sama da ya kashe su.”
[Hasiya]
a Shaidun Jehobah ne Suka Wallafa.
[Bayanin da ke shafi na 14]
Kayinu bai ji tsoron cewa ɗan’uwansa zai rama mutuwarsa ba
[Hotunan da ke shafi na 15]
Yanzu Agboola ba ya jin tsoron mattatu, kuma ya koyi yadda zai guje wa aljanu