Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 1/15 pp. 17-20
  • “Wannan Ita Ce Hanya, Ku Bi Ta”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Wannan Ita Ce Hanya, Ku Bi Ta”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • An Gamsar da Muradinta na Ruhaniya
  • Sakamakon Hidimar Mulki
  • Taron Gunduma Ya Ƙarfafa Ta
  • Gileyad da Kuma Hidima a Ƙasashen Waje
  • Bala’i Ya Faɗa wa Iyalinmu
  • Sabon Aiki
  • Sun Bi ‘Hanyar’
  • Abin da Mama ta Bari
  • Na Kyautata Dangantakata da Allah da Kuma Mahaifiyata
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Me Zan Yi Idan Iyayena Ba Su da Lafiya?
    Tambayoyin Matasa
  • Abin da Iyaye Mata Za Su Iya Koya Daga Misalin Afiniki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 1/15 pp. 17-20

“Wannan Ita Ce Hanya, Ku Bi Ta”

Labarin Emilia Pederson

Ruth E. Pappas ce ta ba da labarin

AN HAIFI mahaifiyata Emilia Pederson, a shekara ta 1878. Ko da yake malamar makaranta ce, ainihin abin da take so shi ne ta yi amfani da rayuwarta wajen taimaka wa mutane su kusaci Allah. Alamar muradin Mama shi ne babban akwatin da ke gidanmu a wani ɗan ƙaramin birni mai suna Jasper, Minnesota, Amirka. Ta sayi akwatin ne don ta kwashe kayanta zuwa ƙasar Sin, inda take son ta yi hidima na masu wa’azi a ƙasashen waje. Amma, sa’ad da mahaifiyarta ta mutu, ta yi watsi da wannan shirin kuma ta tsaya a gida don ta kula da ƙannenta. A shekarata ta 1907, ta auri Theodore Holien. An haife ni a ranar 2 ga Disamba, 1925, kuma ni ce ’yar auta cikin ’ya’ya bakwai.

Mama tana da tambayoyi na Littafi Mai Tsarki waɗanda take neman amsarsu. Ɗaya daga cikin tambayoyin ita ce koyarwar da ake yi cewa miyagu za su shiga wutar jahannama. Ta tambayi wani mai ziyara na Cocin Lutheran inda za ita iya ganin wannan koyarwar a cikin Littafi Mai Tsarki. Ya gaya mata cewa abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa ba shi da muhimmanci, dole ne a koyar da wutar jahannama.

An Gamsar da Muradinta na Ruhaniya

Ba da daɗewa ba bayan shekara ta 1900, ƙanwar Mama, Emma, ta tafi Northfield, Minnesota, don ta karanto waƙa. Ta sauƙa a gidan malaminta, Milius Christianson, wanda matarsa Ɗaliba ce ta Littafi Mai Tsarki, kamar yadda ake kiran Shaidun Jehobah a wannan lokacin. Emma ta ambata cewa tana da yayar da take karanta Littafi Mai Tsarki sosai. Ba da daɗewa ba, matar Christianson ta yi wa Mama wasiƙa wadda take ɗauke da amsoshin tambayoyinta na Littafi Mai Tsarki.

Wata rana, wata Ɗaliba na Littafi Mai Tsarki mai suna Lora Oathout ta shiga jirgin ƙasa daga Sioux Falls, a Kudancin Dakota, don ta yi wa’azi a Jasper. Mama ta yi nazarin littafin da ke bayyana Littafi Mai Tsarki da ta karɓa daga wurinta, kuma a shekara ta 1915, ta soma gaya wa mutane gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki, kuma tana rarraba littattafan da Lora ta ba ta.

A shekara ta 1916, Mama ta ji cewa Charles Taze Russell zai zo taron gundumar da za a yi a Birnin Sioux, a Iowa. Tana son ta halarci taron. A wannan lokacin, Mama tana da ’ya’ya biyar, kuma Marvin, ɗan ƙaramin cikinsu, watansa biyar da haihuwa. Duk da haka, tare da dukan yaranta, ta yi tafiyar mil 100 a cikin jirgin ƙasa zuwa Birnin Sioux don ta halarci taron. Ta saurari jawaban Ɗan’uwa Russell, ta kalli “Photo-Drama of Creation,” kuma ta yi baftisma. Sa’ad da ta koma gida, ta rubuta wani talifi game da taron, wanda aka wallafa a cikin jaridar Jasper Journal.

A shekara ta 1922, Mama tana cikin mutane fiye da 18,000 da suka halarci taron gunduma a Cedar Point, Ohio. Bayan wannan taron, ba ta daina yin shelar Mulkin Allah ba. Saboda haka, misalinta ya ƙarfafa mu mu bi umurnin nan: “Wannan ita ce hanya, ku bi ta.”—Isha. 30:21.

Sakamakon Hidimar Mulki

A tsakanin shekara ta 1920 zuwa 1925, iyaye na sun ƙaura daga Jasper zuwa wani gida. Baba yana da kasuwancin da ke kawo kuɗi kuma yana da babban iyalin da zai kula da ita. Bai yi nazarin Littafi Mai Tsarki sosai kamar Mama ba, amma ya tallafa wa aikin wa’azi da dukan zuciyarsa kuma yana saukar da masu tafiya masu ziyara a gidanmu. A yawancin lokaci, sa’ad da ɗaya daga cikin waɗannan ’yan’uwa masu tafiya zai ba da jawabi a gidanmu, mutane ɗari ko fiye da haka suna halarta, suna cika falo, wurin cin abinci, da kuma ɗakin kwana.

Sa’ad da nike ’yar shekara bakwai, ƙanwar mahaifiyata, Lettie, ta yi waya kuma ta ce maƙwabtanta, Ed Larson da matarsa suna son su yi nazarin Littafi Mai Tsarki. Sun amince da gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki kuma daga baya suka gayyaci wata maƙwabciyarsu, Martha Van Daalen, mai ’ya’ya takwas ta zo su yi nazarin tare. Martha da dukan iyalinta sun zama Ɗaliban Littafi Mai Tsarki.a

A daidai wannan lokacin, Gordon Kammerud, wanda matashi ne da ke zaune nesa kaɗan daga wurin mu ya soma aiki da Baba. An riga an gargaɗi Gordon: “Ka mai da hankali da yaran shugabanka. Suna cikin wani irin addini.” Amma, Gordon ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ba da daɗewa ba ya gaskata cewa ya sami gaskiya. Ya yi baftisma bayan wata uku. Iyayensa sun zama masu bi, kuma iyalanmu, wato, iyalin Holien, iyalin Kammerud, da iyalin Van Daalen sun zama abokai na kud da kud.

Taron Gunduma Ya Ƙarfafa Ta

Taron gundumar da aka yi a Cedar Point ya ƙarfafa Mama sosai kuma hakan ya sa ba ta son ta rasa wani taron. Abubuwan da na tuna a lokacin shi ne yin doguwar tafiya don halartan waɗannan taron. Mafi muhimmanci shi ne taron da aka yi a Columbus, Ohio, a shekara ta 1931, domin a nan ne aka amince da sunan nan Shaidun Jehobah. (Isha. 43:10-12) Wani kuma da na tuna sosai shi ne taron da aka yi a Washington, D.C. a shekara ta 1935, inda aka ba da jawabi mai muhimmanci a tarihi wanda ya bayyana “taro mai-girma” da aka ambata a Ru’ya ta Yohanna. (R. Yoh. 7:9) Yayye na mata Lilian da Eunice suna cikin mutane fiye da 800 da suka yi baftisma a wurin.

Iyalinmu ta halarci taron gunduma a Columbus, Ohio, a shekara ta 1937; Seattle, Washington, a shekara ta 1938; da kuma Birnin New York a shekara ta 1939. Iyalin Van Daalen da Kammerud da kuma wasu sun bi mu, kuma muna kafa tanti a duk inda dare ya yi mana don mu kwana. Eunice ta auri Leo Van Daalen a shekara ta 1940, kuma suka zama majagaba. A wannan shekarar kuma, Lilian ta auri Gordon Kammerud, su ma suka zama majagaba.

Taron gunduma da aka yi a shekara ta 1941 a St. Louis, Missouri, na musamman ne. A wurin, dubban yara sun karɓi littafin nan Children. Wannan taron ne ya canja rayuwata. Ba da daɗewa ba, a ranar 1 ga Satumba, 1941, na zama majagaba tare da yaya na Marvin da matarsa. A lokacin shekaru na 15.

A yankinmu na manoma, ba shi da sauƙi dukan ’yan’uwa su halarci taron gunduma domin yana faɗawa ne lokacin girbi. Saboda haka, bayan taron gunduma, muna sake maimaita abubuwan da muka koya a taron gunduma a bayan gidanmu domin waɗanda ba su halarci taron ba su amfana. Waɗannan taron suna kawo farin ciki.

Gileyad da Kuma Hidima a Ƙasashen Waje

A watan Fabrairu na shekara ta 1943, an kafa Makarantar Gileyad don koyar da majagaba domin hidima ta masu wa’azi a ƙasashen waje. Mutane shida daga cikin iyalin Van Daalen ne suke cikin aji na farko, wato, Emil, Arthur, Homer, da Leo; ɗan’uwansu mai suna Donald; da kuma Eunice yayata, wadda ita matar Leo. Mun yi musu ban kwana cike da farin ciki da baƙin ciki, domin ba mu san sa’ad da za mu sake ganinsu ba. Bayan sun sauke karatu, an tura su shida zuwa ƙasar Puerto Rico, inda Shaidun da ke wurin ba su kai sha biyu ba.

Bayan shekara ɗaya, Lilian da Gordon da kuma Marvin da Joyce sun halarci aji na uku na Gileyad. Su ma an tura su ƙasar Puerto Rico. Bayan haka, a Satumba 1944, ina ’yar shekara 18, na halarci aji na huɗu na Gileyad. Bayan na sauke karatu a watan Fabrairu 1945, na je na sami ’yan’uwana a ƙasar Puerto Rico. Na shaida sababbin abubuwa a wannan wuri! Ko da yake koyan Sfanisanci ya zame mini ƙalubale, ba da daɗewa ba wasu a cikinmu suna nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane fiye da 20. Jehobah ya albarkaci aikin. A yau, akwai Shaidu wajen 25,000 a Puerto Rico!

Bala’i Ya Faɗa wa Iyalinmu

Leo da Eunice sun ci gaba da zama a Puerto Rico bayan haihuwar ɗansu, Mark, a shekara ta 1950. A shekara ta 1952 sun shirya zuwa hutu don su ziyarci ’yan’uwa a gida. A ranar 11 ga Afrilu, sun shiga jirgin sama. Abin baƙin ciki, ba da daɗewa ba da tashin jirgin, jirgin ya faɗa cikin teku. Leo da Eunice sun rasa ransu. An ga ɗansu Mark ɗan shekara biyu yana yawo a kan ruwa. Wani da ya tsira ya jefa shi cikin kwalekwale kuma aka ba shi na’urar numfashi, kuma ya rayu.b

Bayan shekara biyar, a ranar 7 ga Maris, 1957, Baba da Mama suna kan hanyarsu ta zuwa Majami’ar Mulki a cikin motarsu sai tayarsu ta yi faci. Sa’ad da yake canja tayar a gefen hanya, wata motar da ke wucewa ta buge Baba kuma ya mutu nan take. Mutane fiye da 600 ne suka halarci jawabin jana’izar, kuma an ba da shaida mai kyau ga yankin, inda ake daraja Baba sosai.

Sabon Aiki

Kafin Baba ya mutu, na sami aikin yin hidima a ƙasar Argentina. A watan Agusta ta 1957, na isa birnin Mendoza da ke kusa da Tuddan Andes. A shekara ta 1958, an tura George Pappas wanda ya sauke karatu a aji na 30 a Gileyad zuwa ƙasar Argentina. Ni da George mun zama abokai na kud da kud, kuma mun auri juna a watan Afrilu 1960. A shekara ta 1961, Mama ta mutu tana da shekara 83. Ta yi bauta ta gaskiya cikin aminci kuma ta taimaka wa mutane da yawa su yi hakan.

Ni da George mun yi hidima na shekara goma tare da wasu masu wa’azi a ƙasashen waje a wurare dabam-dabam. Bayan haka mun yi shekara bakwai a aikin masu kula da da’ira. Mun koma ƙasar Amirka a shekara ta 1975 don mu kula da masu rashin lafiya a iyalinmu. A shekara ta 1980, an gayyaci maigidana ya yi aikin mai kula da da’ira a yankin da ake Sfanisanci. A lokacin akwai ikilisiyoyin Sfanisanci wajen 600 a Amirka. Mun yi shekara 26 muna ziyartar yawancinsu kuma mun ga yadda ikilisiyoyin suka ƙaru zuwa fiye da 3,000.

Sun Bi ‘Hanyar’

Mama ta yi farin cikin ganin yadda matasa da ke cikin iyalinta suka shiga hidima ta cikakken lokaci. Alal misali, Carol, ɗiyar yayata, Ester, ta zama majagaba a shekara ta 1953. Ta auri Dennis Trumbore, kuma tun lokacin suna hidima ta cikakken lokaci. Lois, ɗiyar Ester, ta auri Wendell Jensen. Sun halarci ajin Gileyad na 41 kuma sun yi hidima na shekara 15 a matsayin masu wa’azi a ƙasashen waje a Nijeriya. Ƙanwar Leo, Ruth La Londe da mijinta, Curtiss ne suka yi renon Mark, wanda iyayensa suka mutu a haɗarin jirgin sama. Mark da matarsa, Lavonne, sun yi shekaru suna hidima ta majagaba kuma sun yi renon yaransu huɗu a cikin “hanya.”—Isha. 30:21.

Orlen, ɗan’uwana kaɗai da ya rage, yana da shekara fiye da 90. Har yanzu yana bauta wa Jehobah da aminci. Ni da maigidana George muna ci gaba da yin hidimarmu ta cikakken lokaci cike da farin ciki.

Abin da Mama ta Bari

A yanzu ina da ɗaya daga cikin abubuwan da Mama ta ɗauka da tamani, wato, teburinta. Kyauta ce da babana ya ba ta a ranar ɗaurin aurensu. Ɗaya daga cikin aljihun teburin yana ɗauke da tsohon littafin ajiyarta, wanda yake ɗauke da wasiƙu da kuma talifofin da ta rubuta da aka wallafa a cikin jaridu kuma suka ba da shaida mai kyau game da Mulki. Wasu a cikinsu an wallafa su ne a cikin shekara ta 1900. Akwai wasiƙu masu tamani a cikin aljihun teburin da yaran Mama da suke wa’azi a ƙasar waje suka rubuta mata. Ina jin daɗin karanta su a kai a kai! Kuma wasiƙun da ta rubuto suna da ban ƙarfafa, kuma cike suke da bayanai masu kyau. Mama ba ta cika muradinta na zama mai wa’azi a ƙasar waje ba. Amma, tana da ƙwazo na hidimar yin wa’azi a ƙasar waje wanda ya motsa zukatan zuriyoyin da suka rayu bayanta. Ina marmarin ganin lokacin da dukan iyalinmu za mu sake haɗuwa tare da Mama da Baba a aljanna a duniya!—R. Yoh. 21:3, 4.

[Hasiya]

a Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuni, 1983, shafuffuka na 27-30, don labarin rayuwar Emil H. Van Daalen, ɗaya daga cikin yaran Martha.

b Ka duba Awake!, na 22 ga Yuni, 1952, shafuffuka na 3-4.

[Hotunan da ke shafi na 17]

Emilia Pederson

[Hotunan da ke shafi na 18]

1916: Mama, Baba (riƙe da Marvin); ƙasa, daga hagu zuwa dama: Orlen, Ester, Lilian, Mildred

[Hotunan da ke shafi na 19]

Leo da Eunice, kafin su mutu

[Hotunan da ke shafi na 20]

A shekara ta 1950: Daga hagu zuwa dama, sama: Ester, Mildred, Lilian, Eunice, Ruth; ƙasa: Orlen, Mama, Baba, da Marvin

[Hotunan da ke shafi na 20]

George da Ruth Pappas a aikin kula da da’ira a shekara ta 2001

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba