Ka Kusaci Allah
“Na San Baƙinzuciyarsu”
Fitowa 3:1-10
“MAI-TSARKI, Mai-tsarki, Mai-tsarki ne, Ubangiji.” (Ishaya 6:3) Waɗannan hurarren kalmomi sun nuna cewa Jehobah Allah yana da tsabta da babu na biyunsa. Za ka iya tambaya, ‘shin tsarkinsa yana sa ya yi nesa ne da mutane?’ ‘Irin wannan Allah mai-tsarki zai damu kuwa da ni, mutum mai zunubi, ajizi?’ Bari mu bincika kalmomi masu ban ƙarfafa da Allah ya gaya wa Musa, da ke rubuce a Fitowa 3:1-10.
Wata rana da yake kiwon tumaki, Musa ya ga abin da bai taɓa gani ba, ɗan kurmi yana cin wuta, amma “ba ya ƙone ba.” (Aya ta 2) Ya yi mamaki, sai ya ratsa ya duba ya gani. Ta bakin mala’ika, Jehobah ya yi wa Musu magana daga cikin wutar: “Kada ka kusanci nan. Swance takalmanka daga sawayenka, gama wurin da ka ke tsayawa wuri mai-tsarki ne.” (Aya ta 5) Ka yi tunani, domin wakilin Allah ya kasance a wurin, ƙasar wajen ma ta kasance mai tsarki!
Allah mai tsarki yana da dalilin yin magana da Musa. Allah ya ce: “Hakika na ga ƙuncin mutanena waɗanda ke cikin Masar, na kuwa ji kukarsu sabada shugabanninsu na gandu; gama na san baƙinzuciyarsu.” (Aya ta 7) Allah ya san irin wahalar da mutanensa suke sha; kuma yana jin kukansu. Don haka, baƙin cikinsu ya zama na shi. Ka lura cewa Allah ya ce: “Na san baƙinzuciyarsu.” Game da wannan furci “na san,” wani aikin bincike ya ce: “Wannan furci yana nuna yadda yake ji, tausayi da kuma juyayi.” Kalmomin Jehobah ga Musa sun nuna cewa shi Allah ne mai kula da damuwar mutane ƙwarai.
Menene to Allah zai yi? Bai saurari kukansu da juyayi kawai ba. Hakan ya sa ya yi taimako. Ya tsai da shawara zai ceci mutanensa daga ƙasar Masar kuma ya kai su “ƙasa mai-kyau mai-faɗi, ƙasa mai-zubasda madara da zuma.” (Aya ta 8) Game da wannan, Jehobah ya aiki Musa, ya ce masa: “Ka fito da mutanena . . . daga cikin Masar.” (Aya ta 10) Da aminci ga wannan aiki, Musa ya fitar da Isra’ilawa daga ƙasar Masar a shekara ta 1513 K.Z.
Jehobah bai canza ba. Masu bauta masa a yau za su iya tabbata cewa yana ganin wahalarsu kuma yana jin kukansu na taimako. Ya san baƙin cikinsu. Amma ba Juyayi kawai Jehobah yake Yi ga bayinsa ba. Allah zai taimake su domin “yana kula” da su.—1 Bitrus 5:7.
Juyayin Allah ya ba mu dalilin bege. Da taimakonsa, mu mutane ajizai za mu iya ƙoƙari mu kasance da tsarki kuma ya amince da mu. (1 Bitrus 1:15, 16) Wata mace Kirista da ta yi fama da baƙin ciki da kasala ta sami ƙarfafa daga labarin Musu da kurmi mai cin wuta. Ta ce: “Idan Jehobah zai iya mai da wuri mai dauɗa ya zama da tsarki, to wataƙila ni ma zan kasance da ɗan bege. Wannan tunanin ya taimake ni ƙwarai da gaske.”
Za ka so ka koyi game da Allah mai tsarki, Jehobah? Za a iya kafa danganta ta kusa da shi, domin Jehobah ya “san tabi’ammu; Ya kan tuna mu turɓaya ne.”—Zabura 103:14.