Matasa, Ku Sa Ci Gabanku Ya Bayyanu
“Ka yi ƙwazo cikin waɗannan al’amura; ka bada kanka garesu sosai; domin cigabanka ya bayyanu ga kowa.”—1 TIM. 4:15.
1. Menene Allah yake so ga matasa?
“KA YI murna, ya kai saurayi, a cikin ƙuruciyarka; zuciyarka kuwa ta yi fari a kwanakin ƙuruciyarka.” (M. Wa. 11:9) Sarki Sulemanu mai hikima na Isra’ila ta dā ne ya rubuta hakan. Babu shakka, Tushen wannan saƙon, Jehobah Allah yana son ku matasa ku yi farin ciki. Ban da haka, Jehobah yana son ku ci gaba da farin ciki har sa’ad da kuka tsufa. Amma a lokacin ƙuruciya, sau da yawa matasa suna yin kurakurai da za su iya shafan farin cikinsu na nan gaba. Har Ayuba mai aminci ya yi baƙin ciki domin “alhakin laifin ƙuruciya[rsa].” (Ayu. 13:26) A lokacin ƙuruciya da kuma wasu ’yan shekaru bayan haka, matashi Kirista sau da yawa yana bukatar ya tsai da shawarwari masu muhimmanci. Yanke shawarwari marar kyau yana iya raunana zuciya sosai kuma ya haddasa matsalolin da za su iya shafan sauran rayuwarsa.—M. Wa. 11:10.
2. Bin wane gargaɗi na Littafi Mai Tsarki ne zai sa matasa su guji kurakurai masu tsanani?
2 Amma matasa suna bukatar su tsai da shawarwari masu kyau. Ka yi la’akari da shawarar da manzo Bulus ya ba Korantiyawa. Ya rubuta: “Ga wajen azanci kada ku zama masu-ƙuruciya . . . ga azanci kuwa ku zama cikakkun mutane.” (1 Kor. 14:20) Bin shawarar koyan yin tunani kamar cikakkun mutum zai taimaki matasa su guji yin kurakurai masu tsanani.
3. Menene za ka iya yi don ka manyanta a yadda kake tunani?
3 Idan kai matashi ne, ka tuna cewa koyan iya yin tunani sosai yana bukatar ƙoƙari. Bulus ya gaya wa Timoti: ‘Kada kowa shi rena ƙuruciyarka; amma ka zama gurbi ga masu-bada gaskiya, cikin magana, tasarrufi, ƙauna, bangaskiya, da tsabtar rai. Ka maida hankali ga karatu, da gargaɗi, da koyarwa, . . . ka yi ƙwazo cikin waɗannan al’amura; ka bada kanka garesu sosai; domin cigabanka ya bayyanu ga kowa.’ (1 Tim. 4:12-15) Kiristoci matasa suna bukatar su samu ci gaba kuma mutane su ga ci gabansu.
Menene Ci Gaba?
4. Menene ci gaba na ruhaniya ya ƙunsa?
4 Samun ci gaba na nufin “canjawa ta hanyar kyautatawa.” Bulus ya aririci Timoti ne ya mai da hankali domin ya samu ci gaba wajen yin magana, hali, ƙauna, bangaskiya da tsabtar rai, da kuma yadda yake cika hidimarsa. Zai yi ƙoƙari ya sa yadda yake rayuwa ya zama abin koyi. Saboda haka, Timoti yana bukatar ya samu ci gaba na ruhaniya.
5, 6. (a) A wane lokaci ne aka soma ganin ci gaban Timoti? (b) Game da samun ci gaba, yaya matasa a yau za su yi koyi da Timoti?
5 Sa’ad da Bulus ya rubuta wannan shawarar a tsakanin shekara ta 61 da 64 A.Z., Timoti ya riga ya zama ƙwararren dattijo. Ba lokacin ba ne ya soma samun ci gaba a ruhaniya. A shekara ta 49 ko 50 A.Z., sa’ad da Timoti wataƙila yake misalin ɗan shekara ashirin, “yan’uwa da ke cikin Listra da Ikoniya suna shaidassa,” domin sun lura cewa yana ci gaba a ruhaniya. (A. M. 16:1-5) A wannan lokacin, Bulus ya ɗauki Timoti suka tafi aikin wa’azi a ƙasar waje. Bayan ya lura da ci gaban Timoti a cikin ’yan watanni, Bulus ya aika shi zuwa Tassalunika domin ya ƙarfafa kuma ya sa Kiristocin da ke wannan birnin su kasance da ƙarfi. (Karanta 1 Tassalunikawa 3:1-3, 6.) Hakika, ci gaban da Timoti ya samu ya bayyana ga mutane tun sa’ad da yake matashi.
6 Ku matasa da ke cikin ikilisiya, ku yi aiki tuƙuru don ku kasance da halaye na ruhaniya da ake bukata yanzu, domin a gani dalla-dalla cewa kun samu ci gaba a hanyar rayuwa ta Kirista da kuma iyawarku ta koyar da gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Tun yana ɗan shekara 12, Yesu “ya yi ta ƙaruwa da hikima.” (Luk 2:52) Saboda haka, bari mu bincika yadda za ku bayyana ci gabanku a hanyoyi uku a rayuwarku: (1) sa’ad da kuke fuskantar matsala, (2) sa’ad da kuke shirin aure, da na (3) sa’ad da kuke ƙoƙari ku zama “nagarin mai-hidima.”—1 Tim. 4:6.
Ku Fuskanci Matsaloli da “Hankali”
7. Ta yaya ne yanayi mai wuya zai iya ya shafi matasa?
7 Wata Kirista matashiya ’yar shekara goma sha bakwai mai suna Carol ta ce, “A wasu lokatai, na kan ji cewa na gaji a motsin raina, a zahiri, da kuma yadda nake tunani da har ba na son na tashi da safe.”a Me ya sa ta baƙin ciki haka? Sa’ad da Carol take ’yar shekara goma, babanta da mamarta sun kashe aure, kuma ta kama zama da mamarta, wadda ta yi watsi da mizanan Littafi Mai Tsarki game da ɗabi’a. Kamar Carol, wataƙila kana fuskantar yanayi mai wuya wanda da kyar in zai gyaru.
8. Waɗanne matsaloli ne Timoti ya yi fama da su?
8 Sa’ad da yake samun ci gaba na ruhaniya, Timoti ya yi fama da yanayi mai wuya. Alal misali, ya fuskanci “yawan kumamanci” saboda matsalar ciwon ciki. (1 Tim. 5:23) Sa’ad da Bulus ya tura shi zuwa Koranti don ya magance wasu matsalolin da mutanen da ke ƙalubalantar ikon manzo suka jawo, Bulus ya aririci ikilisiyar ta ba da haɗin kai, domin Timoti ya kasance “ba tare da tsoro ba” a tsakaninsu. (1 Kor. 4:17; 16:10, 11) Babu shakka, Timoti mutumi ne mai jin kunya, ko kuma mai ɗari-ɗari.
9. Menene kasancewa da hankali ke nufi, kuma yaya hakan ya bambanta da ruhun tsoro?
9 Don ya taimaki Timoti, Bulus ya tuna masa: “Gama Allah ba ya ba mu ruhun tsorata ba; amma na iko da na ƙauna da [“hankali,” NW] na horo.” (2 Tim. 1:7) Kasancewa da “hankali” ya ƙunshi iya yin tunani da kyau. Ya ƙunshi iya jimre wa kowane yanayi kamar yadda yake har sa’ad da yanayinka ya zama yadda ba ka so. Wasu matasa da ba su manyanta ba suna nuna ruhun tsoro kuma su guji tunanin yanayi mai wuya ta wajen yawan barci ko kuma kallon talabijin, yawan shan ƙwaya ko kuma yin maye, zuwa fati a koyaushe, ko yin lalata. An gargaɗi Kiristoci su “rayu da hankali da adalci da ibada cikin wannan zamani na yanzu.”—Tit. 2:12.
10, 11. Ta yaya ne kasancewa da hankali yake taimakonmu mu zama Kiristoci masu ƙarfi?
10 Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa matasa “su kasance masu-hankali.” (Tit. 2:6) Bin wannan shawarar yana nufin cewa za ka yi addu’a kuma ka dogara ga ƙarfi da Allah yake bayarwa sa’ad da kake fuskantar matsaloli. (Karanta 1 Bitrus 4:7.) Ta yin haka, za ka koyi kasancewa da tabbaci a “ƙarfi wanda Allah ke bayarwa.”—1 Bit. 4:11.
11 Kasancewa da hankali da kuma addu’a ne suka taimaki Carol. “Ƙin bi salon rayuwar lalata na mamata yana ɗaya daga cikin abubuwa masu wuya sosai da na taɓa yi,” in ji ta. “Amma yin addu’a ya taimake ni sosai. Na san cewa Jehobah yana tare da ni, saboda haka ba na jin tsoro.” Ku tuna cewa wahala za ta iya mai da ku mutanen kirki kuma za ta iya ƙarfafa ku. (Zab. 105:17-19; Mak. 3:27) Komi matsalar da kuke fuskanta, Allah ba zai taɓa yasar da ku ba. Zai “taimake” ku sosai.—Isha. 41:10.
Yin Shiri don Samun Nasara a Aure
12. Me ya sa Kirista da yake son ya yi aure zai yi amfani da ƙa’idar da ke Misalai 20:25?
12 Wasu matasa sun yi aure da wuri, da nufin cewa hakan zai magance rashin farin ciki, kaɗaici, gundura, da kuma matsaloli a gida. Amma, yin wa’adi na aure batu ne mai muhimmanci. Wasu a zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki sun yi garaje sun yi wa Allah alkawari ba tare da yin tunanin abin da hakan ya ƙunsa sosai. (Karanta Misalai 20:25.) A wasu lokatai, matasa ba sa yin tunani sosai game da ƙoƙari da ake bukatar a yi kafin a yi nasara a aure. Daga baya, sai su ga cewa yin aure ya ƙunshi abubuwa da yawa fiye da yadda suke tsammani.
13. Waɗanne tambayoyi ne waɗanda suke son su yi zawarci za su yi wa kansu, kuma wane abin taimako suke da shi?
13 Saboda haka, kafin ka soma zawarci, ka tambayi kanka: ‘Me ya sa nake son na yi aure? Waɗanne abubuwa nake tsammani zan gani? Wannan mutumin ya dace da ni? Ina shirye na cika hakki na a matsayin ma’auraci?’ Don a taimake ka ka yi bincike mai kyau, “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ya wallafa talifofi da suka tattauna waɗannan batutuwan dalla-dalla.b (Mat. 24:45-47) Ka ɗauki waɗannan talifofi a matsayin shawarar da Jehobah yake ba ka. Ka bincika abubuwan da aka faɗa a ciki sosai kuma ka yi amfani da su. Kada ka bari ka zama “kamar doki ko alfadari da ba su da azanci.” (Zab. 32:8, 9) Ka fahimci bukatun aure sosai. Idan kana ganin cewa ka isa yin zawarci, ka tuna a koyaushe ka zama “gurbi . . . da tsabtar rai.”—1 Tim. 4:12.
14. Yaya manyanta a ruhaniya zai taimake ka sa’ad da ka yi aure?
14 Manyanta a ruhaniya na sa mutum ya yi nasara bayan aure. Kirista da ya manyanta a ruhaniya yana ƙoƙari ya samu “misalin tsawon cikar Kristi.” (Afis. 4:11-14) Yana ƙoƙari sosai ya koyi hali irin na Kristi. A matsayin wanda muke bin misalinsa, “Kristi kuma ba ya yi son kai ba.” (Rom. 15:3) Sa’ad da mata da miji suka biɗi abin da zai amfane kowannensu, za su sami salama da kwanciyar hankali a aurensu. (1 Kor. 10:24) Miji zai nuna ƙauna ta sadaukar da kai, kuma mata za ta kuɗiri aniya ta miƙa kai ga mijinta yadda Yesu yake miƙa kai ga Shugabansa.—1 Kor. 11:3; Afis. 5:25.
“Ka Cika Hidimarka”
15, 16. Ta yaya za ka iya nuna ci gabanka a hidimar fage?
15 Sa’ad da yake jawo hankalin Timoti ga aikinsa mai muhimmanci, Bulus ya rubuta: “Na umurce ka a gaban Allah, da Kristi Yesu, . . . ka yi wa’azin kalma; ka yi naciya.” Ya daɗa: “Ka yi aikin mai-bishara, ka cika hidimarka.” (2 Tim. 4:1, 2, 5) Don ya cika wannan aikin, Timoti yana bukatar ya zama “kiyayayye cikin zantattukan imani.”—Karanta 1 Timothawus 4:6.
16 Ta yaya za ka zama “kiyayayye cikin zantattukan imani”? Bulus ya rubuta: “Ka maida hankali ga karatu, da gargaɗi, da koyarwa. . . . Ka yi ƙwazo cikin waɗannan al’amura; ka bada kanka garesu sosai.” (1 Tim. 4:13, 15) Samun ci gaba na bukatar yin nazari na kai. Furcin nan “ba da kanka” na nufin shagala a wani aiki. Yaya kake nazari? Kana shagala sosai wajen bincika “zurfafa na Allah”? (1 Kor. 2:10) Ko kuwa kana ɗan ƙoƙartawa ne kawai? Yin bimbini a kan nazarin da ka yi zai motsa ka.—Karanta Misalai 2:1-5.
17, 18. (a) Waɗanne halaye ne ya kamata ka yi ƙoƙari ka koya? (b) Ta yaya kasancewa da irin halin Timoti zai taimake ka a hidima?
17 Wata majagaba matashiya mai suna Michelle ta ce: “Domin na ƙware a hidimar fage sosai, ina da tsari mai kyau na yin nazari, kuma ina halartan taro a kowane lokaci. A sakamakon hakan, ruhaniyata tana ci gaba da ƙaruwa.” Yin hidima na majagaba zai taimake ka ka kyautata iyawarka na yin amfani da Littafi Mai Tsarki a hidima kuma ka samu ci gaba na ruhaniya. Ka yi ƙoƙari ka zama mai karatu sosai kuma ka yi kalami mai ma’ana a taron Kirista. A matsayin matashi mai ruhaniya, ya kamata ka shirya jawabinka a Makarantar Hidima na Allah da kyau, kuma ka yi amfani da inda aka ɗauko jawabin.
18 ‘Yin aikin mai bishara’ yana nufin kyautata hidimarka da kuma taimaka wa mutane su samu ceto. Hakan na bukatar iya “koyarwa.” (2 Tim. 4:2) Fita hidimar fage da waɗanda suka ƙware a wannan aikin sosai, zai taimake ka ka koyi yadda suke koyarwa, kamar yadda Timoti ya yi koyo ta wajen yin aiki da Bulus. (1 Kor. 4:17) Sa’ad da yake magana game da waɗanda ya taimaka ma wa, Bulus ya ce ya yi musu wa’azin bishara kuma ya ba da ‘ransa,’ ko kuma ya yi amfani da ransa wajen taimakonsu, domin yana ƙaunarsu. (1 Tas. 2:8) Don ka bi misalin Bulus a hidima, kana bukatar ka kasance da irin halin Timoti, wanda ya damu da mutane sosai kuma ‘ya yi bauta zuwa yaɗuwar bishara.’ (Karanta Filibiyawa 2:19-23.) Kana nuna irin wannan halin sadaukarwar a hidimarka?
Samun Ci Gaba na Kawo Cikakken Gamsuwa
19, 20. Me ya sa samun ci gaba na ruhaniya ke kawo farin ciki?
19 Samun ci gaba na ruhaniya na bukatar ƙoƙari. Ta wajen kyautata yadda kake koyarwa, da shigewar lokaci za ka samu gatar “wadatadda mutane dayawa” ta wajen koya musu gaskiya, kuma za su zama ‘farin zuciyarka, da rawanin fahariyarka.’ (2 Kor. 6:10; 1 Tas. 2:19) “Fiye da dā, ina amfani da lokacina na taimaka wa mutane’ in ji Fred, mai hidima na cikakken lokaci. “Gaskiya ne cewa bayarwa ta fi karɓa albarka.”
20 Wata matashiya mai suna Daphne ta ce game da farin ciki da gamsuwar da take samu daga ci gaba a ruhaniya: “Na ƙulla dangantaka na kud da kud da Jehobah da na ƙara koya game da shi. Idan ka faranta wa Jehobah rai iya ƙoƙarinka, za ka sami gamsuwa sosai!” Ko da yake ba kowane lokaci ba ne mutane suke ganin ci gaba na ruhaniya, a koyaushe Jehobah yana gani kuma yana ɗaukansa da tamani. (Ibran. 4:13) Babu shakka, ku matasa Kiristoci kuna iya sa a ɗaukaka kuma yaba wa Ubanmu na samaniya. Ku ci gaba da faranta masa rai yayin da kuke ci gabanku ke bayyana a fili.—Mis. 27:11.
[Hasiya]
a An canja wasu sunaye.
b “Is This Person Right for Me?” (“Wannan Mutum ya Dace da Ni?”) a littafin nan Questions Young People Ask—Answers That Work, Littafi na biyu; “Ja-gora Daga Allah a Zaɓar Wadda Za a Aura” a fitowar Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Yuni, 2001; da kuma “How Wise Is a Teenage Marriage?” a fitowar Awake! na 22 ga Satumba, 1983.
Me Ka Koya?
• Menene samun ci gaba na ruhaniya ya ƙunsa?
• Ta yaya za ka sa mutane su ga ci gabanka . . .
sa’ad da kake fuskantar wahala?
sa’ad da kake shirin aure?
a hidimar fage?
[Hotunan da ke shafi na 15]
Addu’a za ta sa ku jimre da wahala
[Hotunan da ke shafi na 16]
Ta yaya matasa masu shela za su koyi hanyoyin koyarwa da kyau?