Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 5/15 pp. 21-25
  • Mala’iku ‘Ruhohi Ne Masu-hidima’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mala’iku ‘Ruhohi Ne Masu-hidima’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yaya Mala’iku Suke Taimakonmu?
  • Ka Yi Koyi da Yesu
  • Abin da Za Mu Koya Daga Mala’iku Masu Aminci
  • Mala’iku Suna Tallafa wa Aikin Wa’azi Sosai
  • Su Waye ne ko Kuma Mene ne Ake Nufi da Mala’iku?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Yadda Mala’iku Suke Taimaka Maka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
  • Ku Yi Koyi da Malaꞌikun Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Taimako Daga Malai’ikun Allah
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 5/15 pp. 21-25

Mala’iku ‘Ruhohi Ne Masu-hidima’

“Ba dukansu ruhohi masu-hidima ne, aikakku domin su yi hidima sabili da waɗanda za su gaji ceto?”—IBRAN. 1:14.

1. Wace ƙarfafa ce za mu samu daga Matta 18:10 da Ibraniyawa 1:14?

YESU KRISTI ya gargaɗi duk wani mutumin da zai sa mabiyansa tuntuɓe: “Ku yi hankali kada ku rena wani a cikin waɗannan ƙanƙanana; gama ina ce maku, cikin sama kullum mala’ikunsu suna duban fuskar Ubana wanda ke cikin sama.” (Mat. 18:10) Da yake maganar mala’iku masu aminci, manzo Bulus ya rubuta: “Ba dukansu ruhohi masu-hidima ne, aikakku domin su yi hidima sabili da waɗanda za su gaji ceto?” (Ibran. 1:14) Waɗannan kalaman tabbaci ne mai ban ƙarfafa cewa Allah yana amfani da waɗannan mala’iku ya taimaka wa ’yan adam. Menene Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da mala’iku? Ta yaya suke taimakonmu? Menene za mu iya koya daga misalinsu?

2, 3. Waɗanne ayyuka ne halittun ruhu na samaniya suke da shi?

2 Da akwai miliyoyin mala’iku masu aminci a sama. Dukansu ‘masu-iko ne da ke idar da saƙonsa.’ (Zab. 103:20; karanta Ru’ya ta Yohanna 5:11.) Waɗannan ruhohi ’ya’yan Allah suna da mutuntaka dabam dabam, halaye kamar na Allah, da ’yancin zaɓe. An tsara su sosai kuma suna da matsayi mai girma a tsarin Allah, Michael wato, (sunan Yesu na samaniya) ne shugaban mala’iku. (Dan. 10:13; Yahu. 9) Wannan ‘ɗan fari gaban dukan halitta’ ne “Kalman,” ko Kakaki, na Allah kuma Jehobah ya yi amfani da shi wajen halittar dukan wasu abubuwa.—Kol. 1:15-17; Yoh. 1:1-3.

3 Seraphim, waɗanda suke sanar da tsarkin Jehobah da kuma sa mutanensa su kasance da tsabta na ruhaniya suna ƙarƙashin shugaban mala’iku. Da akwai kerub, waɗanda ke hidima a matsayin masu ɗaukaka ikon mallakar Allah. (Far. 3:24; Isha. 6:1-3, 6, 7) Sauran mala’iku ko kuma manzanni suna da ayyuka dabam-dabam na cika nufin Allah.—Ibran. 12:22, 23.

4. Yaya mala’iku suka ji sa’ad da aka kafa duniya, kuma da menene ’yan adam za su samu da a ce sun yi amfani da ’yancin yin zaɓi yadda ya dace?

4 Dukan mala’iku sun yi farin ciki sa’ad da aka yi “tussan duniya” kuma sun yi farin cikin yin aikin da aka ba su a lokacin da Jehobah yake tsara wannan duniyar mai ban sha’awa don ’yan adam su zauna a cikinta. (Ayu. 38:4, 7) Jehobah ya halicce ɗan adam “ya gaza mala’iku” amma cikin ‘surarsa,’ kuma hakan ya taimaka wa ’yan adam su nuna halayen Mahalicci. (Ibran. 2:7; Far. 1:26) Da a ce Adamu da Hauwa’u sun yi amfani da ’yancinsu na yin zaɓi da kyau, da su da ’ya’yansu sun more rayuwa a cikin aljanna a matsayin waɗanda suke cikin iyalin dukan halittun Jehobah.

5, 6. Wane tawaye ne aka yi a sama, kuma menene Allah ya yi?

5 Hakika, mala’iku masu tsarki sun yi mamaki sa’ad da suka tawaye a iyalin Allah na samaniya. Ɗaya daga cikinsu ya daina yabon Jehobah amma yana son a bauta masa. Ya mai da kansa Shaiɗan (wanda ke nufin “Ɗan Hamayya”) ta wajen ƙalubalantar dacewar sarautar Jehobah kuma yana ƙoƙarin kafa sarauta ta adawa don son kai. Sa’ad da Shaiɗan ya yi ƙarya, ya zuga mutane biyu na farko su yi tawaye tare da shi ga Mahaliccinsu mai ƙauna.—Far. 3:4, 5; Yoh. 8:44.

6 Nan da nan Jehobah ya zartar da hukunci a kan Shaiɗan ta wajen yin annabci na farko a cikin Littafi Mai Tsarki: “Tsakaninka da macen kuma zan kafa magabtaka, da tsakanin zuriyarka da zuriyarta kuma: shi za ya ƙuje kanka, kai kuma za ka ƙuje duddugensa.” (Far. 3:15) Ƙiyayya za ta ci gaba tsakanin Shaiɗan da “macen” ta Allah. Hakika, Jehobah ya ɗauki ƙungiyar samaniya na halittun ruhu masu aminci a matsayin mata ƙaunatacciya da ta yi gami da shi a matsayin Miji. Wannan annabcin ya ba da tabbaci don bege, ko da yake wasu bayanai har ila ‘asiri’ ne da za a bayyana a hankali. Allah ya ce wani daga sashen ƙungiyarsa na sama zai halaka dukan ’yan tawaye kuma ta hanyarsa ce za a tara “abubuwan da ke cikin sammai, da abubuwan da ke bisa duniya.”—Afis. 1:8-10.

7. Menene wasu mala’iku suka yi a zamanin Nuhu, kuma menene sakamakon?

7 A zamanin Nuhu, mala’iku da yawa sun bar “nasu wurin zama” kuma suka canja jikinsu zuwa ta mutane domin su biɗi jin daɗi na son kai a duniya. (Yahu. 6; Far. 6:1-4) Jehobah ya jefa waɗannan ’yan tawaye cikin mugun duhu, kuma da haka suka bi Shaiɗan suka zama “mugayen ruhohi” da kuma mugayen maƙiyan bayin Allah.—Afis. 6:11-13; 2 Bit. 2:4.

Yaya Mala’iku Suke Taimakonmu?

8, 9. Ta yaya Jehobah ya yi amfani da mala’iku wajen taimakon ’yan adam?

8 Ibrahim, Yakubu, Musa, Joshua, Ishaya, Daniel, Yesu, Bitrus, Yohanna, da Bulus suna cikin waɗanda mala’iku suka yi wa hidima. Mala’iku masu adalci sun zartar da hukunci Allah kuma sun idar da annabce-annabce da umurnai, har da Dokar Musa. (2 Sar. 19:35; Dan. 10:5, 11, 14; A. M. 7:53; R. Yoh. 1:1) Tun da yake muna da cikakkiyar Kalmar Allah a yau, mala’iku ba sa bukatar su idar da saƙonnin Allah. (2 Tim. 3:16, 17) Amma, ko da yake ’yan adam ba sa ganin su, mala’iku suna aiki tuƙuru wajen yin nufin Allah da kuma tallafa wa bayinsa.

9 Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa: “Mala’ikan Ubangiji yana kafa sansani a kewaye da masu-tsoronsa, yana tseradda su kuma.” (Zab. 34:7; 91:11) Domin Shaiɗan ya ce ’yan adam ba za su kasance da aminci ga Allah ba sa’ad da suka fuskanci jaraba, Jehobah ya ƙyale Shaiɗan ya kawo kowane irin gwaji a kanmu. (Luk 21:16-19) Amma, Allah ya san daidai lokacin da zai kawar da gwajin da muke fuskanta, domin ya san cewa mun riga mun nuna amincinmu a gare shi dalla-dalla. (Karanta 1 Korinthiyawa 10:13.) Mala’iku suna shirye su ɗauki matakin da ya jitu da nufin Allah. Sun ceci Shadrach, Meshach, Abednego, Daniel da Bitrus amma ba su hana maƙiya su kashe Istafanus da Yaƙubu ba. (Dan. 3:17, 18, 28; 6:22; A. M. 7:59, 60; 12:1-3, 7, 11) Yanayin da batutuwan sun bambanta. Hakazalika, an kashe wasu cikin ’yan’uwanmu a sansanin fursuna na ’yan Nazi, amma Jehobah ya taimaki yawancinsu su tsira.

10. Ban da taimakon mala’ika, wane taimako ne za mu iya samu?

10 Nassosi bai koyar da mu ba cewa kowane mutum a duniya yana da mala’ikan da ke kāre shi. Muna addu’a tare da tabbaci cewa idan “mun roƙi komi daidai da nufinsa, [Allah] yana jinmu.” (1 Yoh. 5:14) Hakika, Jehobah yana iya turo mala’ika ya taimake mu, amma muna iya samun taimako a wata hanyar dabam. ’Yan’uwa Kiristoci suna iya ba da taimako da kuma ƙarfafa. Allah yana iya ba mu hikima da ƙarfin da muke bukata don mu jimre da ‘masuki cikin jiki’ da ke wahalar da mu kamar a ce “manzon Shaiɗan” yana marinmu.—2 Kor. 12:7-10; 1 Tas. 5:14.

Ka Yi Koyi da Yesu

11. Ta yaya mala’iku suka taimaka wa Yesu, kuma menene ya cim ma ta wajen kasancewa da aminci ga Allah?

11 Ka yi la’akari da yadda Jehobah ya yi amfani da mala’iku a batun Yesu. Sun sanar da haihuwarsa da tashinsa daga matattu kuma suka taimake shi sa’ad da yake duniya. Mala’iku suna iya hana a kama shi da kuma su hana mutuwar azaba da ya yi. Maimakon haka, an aika mala’ika ya ƙarfafa shi. (Luk 2:8-11; 22:43; 24:4-7) Daidai da nufin Jehobah, Yesu ya yi mutuwar hadaya kuma ya nuna cewa mutum kamiltacce zai iya kasancewa da aminci ga Allah duk da cewa an jaraba shi sosai. Saboda haka, Jehobah ya ta da Yesu zuwa rai marar mutuwa a sama, ya ba shi “dukan hukunci” kuma ya sa mala’iku su kasance a ƙarƙashin ikonsa. (Mat. 28:18; A. M. 2:32; 1 Bit. 3:22) Da haka, Yesu ya zama sashe na musamman na “zuriyar” “macen” Allah.—Far. 3:15; Gal. 3:16.

12. A wace hanya ce za mu yi koyi da misali mai kyau na Yesu?

12 Yesu ya san cewa bai dace ba ya gwada Jehobah ta wajen sa rai cewa mala’iku za su cece shi idan ya yi ganganci. (Karanta Matta 4:5-7.) Saboda haka, bari mu yi koyi da misalin Yesu ta wajen nuna “hankali, ba tare da yin kasadar da bai dace ba, amma mu fuskantar gwaji da gabagaɗi.—Tit. 2:12.

Abin da Za Mu Koya Daga Mala’iku Masu Aminci

13. Menene za mu iya koya daga misalin mala’iku masu aminci da aka ambata a 2 Bitrus 2:9-11?

13 Sa’ad da yake tsauta wa waɗanda suke “zagin” shafaffun bayin Jehobah, manzo Bitrus ya ambata misali mai kyau na mala’iku masu aminci. Ko da yake suna da iko sosai, cikin tawali’u mala’iku sun guji su mai da kansu alƙalai da kuma yin zargin ƙarya don suna daraja “Ubangiji.” (Karanta 2 Bitrus 2:9-11, Littafi Mai Tsarki.) Bari mu guji yanke hukuncin da bai dace ba a kan mutane, mu daraja waɗanda aka ɗanka wa hakkin kula a ikilisiya, kuma mu bar batutuwa a hannun Jehobah, Mafificin Alƙali.—Rom. 12:18, 19; Ibran. 13:17.

14. Menene za mu iya koya daga mala’iku game da kasancewa da tawali’u?

14 Mala’ikun Jehobah sun kafa mana misali mai kyau na yin hidima cikin tawali’u. Wasu mala’iku sun ƙi su gaya wa ’yan adam sunansu. (Far. 32:29; Alƙa. 13:17, 18) Ko da yake akwai miliyoyin mala’iku a sama, Littafi Mai Tsarki ya faɗi sunan Mika’ilu da Jibrailu ne kawai. Mai yiwuwa an yi hakan ne don kada mu ba mala’iku darajar da bai dace ba. (Luk 1:26; R. Yoh. 12:7) Sa’ad da manzo Yohanna ya faɗi a ƙasa don ya yi bauta a gaban wani mala’ika, mala’ikan ya gargaɗe shi: “Kada ka yarda ka yi wannan: ni abokin bauta ne tare da kai da ’yan’uwanka.” (R. Yoh. 22:8, 9) Saboda haka, za mu yi bauta da kuma addu’o’i ne ga Allah kaɗai.—Karanta Matta 4:8-10.

15. Ta yaya mala’iku suka kafa mana misalin nuna haƙuri?

15 Mala’iku sun kuma kafa misali mai kyau wajen yin haƙuri. Ko da yake suna son su san asirai na Allah, ba su san dukansu ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Su ne kuwa abubuwan da mala’iku ke ɗokin gani.” (1 Bi 1:12, LMT) Saboda haka, menene suka yi? Suna jira cikin haƙuri har sai lokacin da Allah ya ga ya dace ya sanar da “hikima iri iri” ta “wurin ikilisiya.”—Afis. 3:10, 11.

16. Ta yaya halinmu zai iya shafan mala’iku?

16 Kiristocin da ke fuskantar gwaji ‘abin kallo ne ga mala’iku.’ (1 Kor. 4:9) Cike da gamsuwa, mala’iku suna kallon ayyukanmu na aminci, kuma suna farin ciki sa’ad da mai zunubi ya tuba. (Luk 15:10) Mala’iku suna ganin halin ibada na mata Kiristoci. Littafi Mai Tsarki ya ce “mace ta rufe kanta, wato alamar ikon namiji, saboda mala’iku.” (1Ko 11:3, 10) Hakika, mala’iku suna farin ciki sa’ad da suka ga mata Kiristoci da dukan bayin Allah a duniya suna yin biyayya ga tsarin Allah da kuma shugabanci. Irin wannan biyayyar tunasarwa ce da ta dace ga waɗannan ’ya’yan Allah na samaniya.

Mala’iku Suna Tallafa wa Aikin Wa’azi Sosai

17, 18. Me ya sa za mu iya cewa mala’iku suna tallafa wa wa’azin da muke yi?

17 Mala’iku sun sa hannu cikin wasu abubuwa masu ban al’ajabi da suka faru a “ranar Ubangiji.” Wannan ya haɗa da Mulkin da aka kafa a shekara ta 1914 da kuma jefar da Shaiɗan da aljanunsa daga sama da “Mika’ilu da nasa mala’iku” suka yi. (R. Yoh. 1:10; 11:15; 12:5-9) Manzo Yohanna ya ga “wani mala’ika kuma yana firiya a tsakiyar sararin sama, yana da bishara ta har abada wadda za ya yi shelarta ga mazaunan duniya.” Mala’ikan ya ce: “Ku ji tsoron Allah, ku ba shi daraja; gama sa’ar hukuncinsa ta zo: ku yi sujjada ga wanda ya yi sama da duniya da teku da maɓulɓulan ruwaye.” (R. Yoh. 14:6, 7) Da haka, an tabbatar wa bayin Jehobah cewa mala’iku za su taimake su yayin da suke wa’azin bishara na Mulkin da aka kafa duk da cewa Iblis yana tsananta musu sosai.—R. Yoh. 12:13, 17.

18 A yau, mala’iku ba sa yi mana ja-gora zuwa ga mutane masu zuciyar kirki ta wajen yi mana magana yadda wani mala’ika ya yi wa Filibbus magana kuma yi masa ja-gora zuwa wajen Habasha bābā. (A. M. 8:26-29) Amma, labarai da yawa na zamani sun nuna cewa ko da ba ma ganinsu, mala’iku suna tallafa wa aikin wa’azi na Mulki kuma suna yi mana ja-gora zuwa ga waɗanda “aka ƙaddara su ga rai na har abada.”a (A. M. 13:48) Yana da muhimmanci mu ci gaba da yin aikin wa’azi a kai a kai don mu yi namu aikin na neman waɗanda suke son su “yi [wa Uba] sujjada cikin ruhu da cikin gaskiya kuma.”—Yoh. 4:23, 24.

19, 20. Wane aiki ne mala’iku za su yi a aukuwar da ke nuna “matuƙar zamani”?

19 Da yake maganar zamaninmu, Yesu ya ce a “cikin matuƙar zamani” mala’iku za su “rarraba miyagu daga cikin masu adalci.” (Mat. 13:37-43, 49) Mala’iku suna saka hannu a tattarawa na ƙarshe da kuma hatimce shafaffu. (Karanta Matta 24:31; R. Yoh. 7:1-3) Bugu da ƙari, mala’iku suna bin Yesu sa’ad da yake “rarraba tumaki da awaki.”—Mat. 25:31-33, 46.

20 A “bayyanuwar Ubangiji Yesu daga sama tare da mala’iku na ikonsa” za a hallaka dukan “waɗanda ba su san Allah ba, da waɗanda sun ƙi yin biyayya da bisharar Ubangijinmu Yesu.” (2 Tas. 1:6-10) Sa’ad da Yohanna ya ga wannan aukuwa a cikin wahayi, ya kwatanta cewa Yesu da rundunar mala’iku na sama suna kan fararen dawakai domin su yi yaƙi da adalci.—R. Yoh. 19:11-14.

21. Menene mala’ikan da ke “riƙe da makullin rami mara-matuƙa, yana kuwa da babbar sarƙa a hannunsa” zai yi wa Shaiɗan da aljanunsa?

21 Yohanna ya kuma ga “wani mala’ika kuma yana saukowa daga sama, yana riƙe da makullin rami mara-matuƙa, yana kuwa da babbar sarƙa a hannunsa.” Wannan ba wani ba ne sai Mika’ilu shugaban mala’iku, wanda zai ɗaure Iblis kuma ya jefa shi da aljanunsa cikin rami marar matuƙa. Za a ɗan sake su a ƙarshen Sarautar Kristi ta Shekara Dubu sa’ad da ’yan adam kamiltattu za su fuskanci gwaji na ƙarshe. Bayan hakan, za a halaka Shaiɗan da dukan sauran ’yan tawaye. (R. Yoh. 20:1-3, 7-10; 1 Yoh. 3:8) Da haka, za a kawar da dukan tawayen da aka yi wa Allah.

22. Yaya mala’iku za su sa hannu a abubuwa da za su faru nan gaba, yaya ya kamata mu ji game da aikinsu?

22 Ba da daɗewa ba za a sami ceto mai girma daga mugun tsarin Shaiɗan. Mala’iku za su yi ayyuka na musamman a waɗannan aukuwa na musamman da za su ƙunita ikon mallakar Jehobah kuma su cika dukan nufinsa ga duniya da ’yan adam. Hakika, mala’iku masu adalci “ruhohi masu-hidima ne aikakku domin su yi hidima sabili da waɗanda za su gaji ceto.” Saboda haka, bari mu yi godiya ga Jehobah Allah domin yadda yake amfani da mala’iku don ya taimaka mana mu yi nufinsa kuma mu samu rai madawwami.

[Hasiya]

a Ka duba littafin nan Jehovah’s Witnesses—Proclaimers of God’s Kingdom, shafuffuka na 549-551.

Yaya Za Ka Amsa?

• Yaya aka tsara halittun ruhu na samaniya?

• Menene wasu mala’iku suka yi a zamanin Nuhu?

• Yaya Allah ya yi amfani da mala’iku wajen taimaka mana?

• Wane aiki ne mala’iku masu adalci suke yi a zamaninmu?

[Hotunan da ke shafi na 21]

Mala’iku suna farin cikin cika nufin Allah

[Hotunan da ke shafi na 23]

Kamar yadda suka yi wa Daniel, mala’iku suna shirye su ɗauki matakin da ya jitu da nufin Allah

[Hotunan da ke shafi na 24]

Ka kasance da gabagaɗi, don mala’iku suna tallafa wa aikin wa’azin Mulki!

[Credit Line]

Globe: NASA photo

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba