Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 7/15 pp. 3-7
  • Neman Dukiya Wadda Aka ‘Ɓoye A Cikinsa’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Neman Dukiya Wadda Aka ‘Ɓoye A Cikinsa’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Neman Dukiya ta Ruhaniya
  • Dukiyoyi da Aka “Ɓoye” Cikin Kristi
  • Ku Ci Gaba da Nema
  • Ka Rika Nuna Godiya Don Abubuwan da Ba Ka Gani
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Ka Kwallafa Ranka ga Al’amuran Ibada
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Me Ya Sa Za Ka Bi “Kristi”?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • ‘Ka Zo Ka Bi Ni’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 7/15 pp. 3-7

Neman Dukiya Wadda Aka ‘Ɓoye A Cikinsa’

“Wanda an ɓoye dukan dukiya ta hikima da ta ilimi cikinsa.”—KOL. 2:3.

1, 2. (a) Waɗanne abubuwa ne aka gano a shekara ta 1922, kuma ina suke yanzu? (b) Menene Kalmar Allah ta gaya mana mu yi?

GANO dukiyoyin da aka ɓoye sau da yawa shi ne kan magana a labarai. Alal misali, a shekara ta 1922, bayan shekaru da yawa na aiki tuƙuru a yanayi mai wuya, masanin kimiyyar tona ƙasa ɗan Britaniya mai suna Howard Carter ya tono wani abu mai ban mamaki. Ya gano kabarin sarauta na Fir’auna Tutankhamen da ke cike da kayayyaki kusan 5,000.

2 Ko da yake dukiyar da Carter ya gano tana da ban sha’awa, an ajiye yawancin abubuwan a ma’adanar kayayyakin tarihi ko kuma inda mutane suke ajiye abubuwa na kansu. Ko da yake suna da amfani ga tarihi ko fasaha, ba su da amfani ga rayuwarmu ta yau da kullum. Amma, Kalmar Allah ta gaya mana mu nemi dukiyoyi da za su amfane mu da gaske. Hakan gayyata ce ga kowa, kuma ladan ya fi kowace dukiya ta zahiri.—Karanta Misalai 2:1-6.

3. A waɗanne hanyoyi ne dukiyoyin da Jehobah ya aririci masu bauta masa su nema suke da amfani?

3 Ka yi la’akari da amfanin dukiyoyi da Jehobah ya gaya wa masu bauta masa su nema. Ɗaya daga cikin irin waɗannan dukiyoyi shi ne mu ji “tsoron Ubangiji” hakan zai iya kāre mu a waɗannan miyagun zamani. (Zab. 19:9) Samun “sanin Allah” zai sa mutum ya sami ɗaukaka da ta fi wadda kowane ɗan adam zai iya samu, wato, dangantaka na kud da kud da Maɗaukaki Duka. Idan muka samu dukiyoyi na hikima, sani, da fahimi da Allah yake bayarwa, za mu iya yin nasara wajen bi da matsaloli da damuwa a rayuwarmu ta yau da kullum. (Mis. 9:10, 11) Ta yaya za mu iya samun irin waɗannan dukiyoyi masu tamani?

Neman Dukiya ta Ruhaniya

4. Yaya za mu sami dukiyoyi na ruhaniya?

4 Ba kamar masu tonan ƙasa da kuma wasu ’yan bincike da sau da yawa suke neman dukiyoyinsu a ko’ina ba, mun san ainihin inda za mu samu dukiyoyi ta ruhaniya. Kamar taswirar da ke nuna inda dukiya take, Kalmar Allah tana nuna ainihin wurin da za mu iya samun dukiyoyi da Allah ya yi mana alkawarinsu. Da yake magana game da Kristi, manzo Bulus ya rubuta: “Wanda an ɓoye dukan dukiya ta hikima da ta ilimi cikinsa.” (Kol. 2:3) Sa’ad da muka karanta waɗannan kalmomin, muna iya tambaya: ‘Me ya sa za mu nemi waɗannan dukiyoyi? Ta yaya aka “ɓoye” su cikin Kristi? Yaya za mu same su?’ Don mu samu amsoshin, bari mu bincika kalmomin manzon da kyau.

5. Me ya sa Bulus ya rubuta game da dukiyoyi na ruhaniya?

5 Bulus ya rubuta waɗannan kalmomin ga ’yan’uwansa Kiristoci da suke Kolosi. Ya gaya musu cewa yana ɗawainiya dominsu, don “zukatansu su ta’azantu, su zama haɗaɗu cikin ƙauna.” (Karanta Kolosiyawa 2:1, 2.) Me ya sa ya damu haka? Babu shakka, Bulus ya san cewa wasu da suke gabatar da ilimin falsafa na Helenanci ko kuma waɗanda suke ɗaukaka koma ga bin Dokar Musa suna rinjayar ’yan’uwan. Shi ya sa ya gargaɗi ’yan’uwan sosai: “Ku yi hankali kada kowa ya cuceku ta wurin iliminsa da ruɗinsa na banza, bisa ga ta’adar mutane, bisa ga ruknai na duniya, ba bisa ga Kristi ba.”—Kol. 2:8.

6. Me ya sa za mu so mu bi gargaɗin Bulus?

6 A yau muna fuskantar irin wannan rinjaya daga Shaiɗan da kuma mugun tsarinsa. Ilimin falsafa na duniya, har da tarbiyya na ’yan adam, da kuma ra’ayin bayyanau suna shafan ra’ayin mutane, ɗabi’unsu, makasudinsu, da salon rayuwarsu. Addinin ƙarya ne ke kawo bukukuwa masu yawa da ake yi ko’ina. An shirya masana’antun nishaɗi su gamsar da munanan sha’woyi na jiki, kuma yawancin abubuwa da ke cikin Intane suna da haɗari sosai ga matasa da manya. Ganin waɗannan abubuwa da wasu halaye na duniya a kai a kai zai iya shafan yadda muke ji da kuma halinmu game da ja-gorar da Jehobah ke tanadinsa, hakan hana mu riƙe rai wanda yake na hakika gam-gam. (Karanta 1 Timotawus 6:17-19.) A bayyane yake cewa, muna bukatar mu fahimci ma’anar kalaman Bulus zuwa ga Kolosiyawa kuma mu bi gargaɗinsa idan ba ma son mu faɗa cikin tarkunan Shaiɗan.

7. Waɗanne abubuwa biyu ne Bulus ya ce za su taimaki Kolosiyawa?

7 Idan muka sake duba kalaman Bulus zuwa ga Kolosiyawa, mun lura cewa bayan ya ambata damuwarsa, ya nuna abubuwa biyu da za su ƙarfafa su kuma su zama haɗaɗu cikin ƙauna. Na farko, ya ambata cikakken tabbaci na ‘fahiminsu.’ Suna bukatar su kasance da cikakken tabbaci cewa sun fahimci Nassosi daidai, domin bangaskiyarsu ta kasance bisa tabbataccen tushe. (Ibran. 11:1) Sa’an nan ya ambata cikakken sanin “asirin Allah.” Suna bukatar su san muhimman koyarwa ta gaskiya kuma su fahimci zurfafan al’amuran Allah sosai. (Ibran. 5:13, 14) Hakika, wannan gargaɗi ne mai kyau ga Kolosiyawa da kuma mu a yau! To, yaya za mu iya samun irin wannan tabbaci da kuma cikakken sani? Bulus ya ba da amsar a sanannen furcinsa game da Yesu Kristi: “Wanda an ɓoye dukan dukiya ta hikima da ta ilimi cikinsa.”

Dukiyoyi da Aka “Ɓoye” Cikin Kristi

8. Ka bayyana ma’anar furcin nan an “ɓoye” cikin Kristi.

8 Ko da yake an faɗi cewa an “ɓoye” dukiyoyi na hikima da ilimi cikin Kristi, hakan ba ya nufin cewa babu wanda zai iya samunsu. Maimakon haka, yana nufin cewa za mu yi ƙoƙari sosai don mu sami dukiyoyin, kuma dole ne mu mai da hankalinmu ga Yesu Kristi. Hakan ya jitu da abin da Yesu ya faɗi game da kansa: “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne rai: ba mai-zuwa wurin Uban sai ta wurina.” (Yoh. 14:6) Hakika don mu sami sanin Allah, muna bukatar taimako da ja-gorar da Yesu ke tanadinsu.

9. Waɗanne hakkoki ne aka ba Yesu?

9 Ƙari ga zama “hanya,” Yesu ya ce, “ni ne gaskiya, ni ne rai.” Wannan ya nuna cewa ban da zuwa wurin Uba ta wurinsa, yana da wani hakkin kuma. Yesu yana da hakki da yake da muhimmanci ga fahimtar koyarwar Littafi Mai Tsarki da samun rai madawwami. Hakika, a cikin Yesu an ɓoye dukiyoyi masu tamani sosai, suna jiran ɗalibai masu ƙwazo sosai su gano su. Bari mu bincika wasu cikin abubuwa masu tamani da suka shafi begenmu na nan gaba da kuma dangantakarmu da Allah.

10. Menene za mu iya koya game da Yesu daga Kolosiyawa 1:19 da 2:9?

10 “Daga cikinsa dukan cikar Allahntaka cikin jiki tana zaune.” (Kol. 1:19; 2:9) Tun da yake yana tare da Ubansa na samaniya shekaru aru-aru, Yesu ya fi kowa sanin nufin Allah da mutuntakarsa. Sa’ad da yake hidima a duniya, Yesu ya koya wa mutane abin da Ubansa ya koya masa, kuma ayyukansa sun nuna halayen da Ubansa ya koya masa. Shi ya sa Yesu ya ce: “Wanda ya gan ni ya ga Uban.” (Yoh. 14:9) Dukan hikima da sanin Allah suna ɓoye ko zaune cikin Kristi, kuma koyon dukan abin da za mu iya game da Yesu ne hanya mafi kyau da za mu iya koya game da Jehobah.

11. Wace alaƙa ke tsakanin Yesu da annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki?

11 “Shaidar Yesu ruhun annabci ne.” (R. Yoh. 19:10) Waɗannan kalaman sun nuna cewa Yesu ne yake da matsayi na musamman wajen cika annabce-annabce masu yawa da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Daga annabci na farko da Jehobah ya yi da ke rubuce a Farawa 3:15, zuwa wahayi mai girma da ke littafin Ru’ya ta Yohanna, za a fahimci annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da kyau sa’ad da aka mai da hankali ga matsayin Yesu a Mulkin Almasihu. Shi ya sa annabce-annabcen da ke cikin nassosi na Ibrananci suka yi wuyan fahimta ga waɗanda suka ƙi Yesu a matsayin Almasihu. Ya kuma bayyana abin da ya sa waɗanda ba sa daraja Nassosin Helenanci da ke ɗauke da annabce-annabcen Almasihu da yawa suke ɗaukan Yesu a matsayin babban mutum kawai. Sanin Yesu yana taimaka wa mutanen Allah su fahimci ma’anar annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da ba su cika ba tukun.—2 Kor. 1:20.

12, 13. (a) Ta yaya Yesu ya zama “hasken duniya”? (b) Da yake an ’yantar da su daga duhu na addini, dole ne mabiyan Kristi su yi menene?

12 “Ni ne hasken duniya.” (Karanta Yohanna 8:12; 9:5.) Da daɗewa kafin a haifi Yesu a duniya, annabi Ishaya ya annabta: “Mutanen da ke tafiya cikin duhu suka ga haske mai-girma: mazauna cikin ƙasa ta inuwar mutuwa, a bisansu haske ya ɓullo.” (Isha. 9:2) Manzo Matta ya bayyana cewa Yesu ya cika wannan annabci sa’ad da ya soma wa’azi kuma ya ce: “Ku tuba; gama mulkin sama ya kusa.” (Mat. 4:16, 17) Hidimar Yesu ta sa mutanen suka sami fahimi na ruhaniya da kuma ’yanci daga bauta ta koyarwar addinin ƙarya. Yesu ya ce: “Ni na zo haske cikin duniya, domin dukan wanda yana bada gaskiya gare ni kada shi zauna cikin duhu.”—Yoh. 1:3-5; 12:46.

13 Shekaru da yawa daga baya, manzo Bulus ya gaya wa ’yan’uwansa Kiristoci: “Dā ku duhu ne, amma yanzu haske ne cikin Ubangiji: ku yi tafiya kamar ’ya’yan haske.” (Afis. 5:8) Da yake an ’yantar da su daga bautar duhu na addini, dole ne Kiristoci su yi tafiya a matsayin ’ya’yan haske. Hakan ya yi daidai da abin da Yesu ya gaya wa mabiyansa a Huɗuba a kan Dutse: “Ku bari haskenku shi haskaka a gaban mutane, domin su ga ayukanku masu-kyau, su girmama Ubanku wanda ke cikin sama.” (Mat. 5:16) Kana daraja dukiyoyi na ruhaniya da ka samu a cikin Yesu sosai da har za ka gaya wa mutane su biɗe su, ta wajen kalamanka da kuma halinka mai kyau na Kirista?

14, 15. (a) Ta yaya aka yi amfani da tumaki da wasu dabbobi a bauta ta gaskiya a zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki? (b) Me ya sa Yesu ya zama dukiya da babu na biyunta a matsayinsa na “Ɗan rago na Allah”?

14 Yesu ne “Ɗan rāgo na Allah.” (Yoh. 1:29, 36) A cikin Littafi Mai Tsarki, rago yana da hakki na musamman wajen gafarta zunubi da kuma kusantar Allah. Alal misali, bayan da Ibrahim ya nuna cewa yana shirye ya miƙa ɗansa Ishaƙu, an gaya masa kada ya kashe Ishaƙu kuma aka yi masa tanadin rago a maimakonsa. (Far. 22:12, 13) Sa’ad da aka ceci Isra’ilawa daga Masar, rago ya kasance da matsayi na musamman, a wannan lokacin an yi amfani da shi a “faskar Ubangiji.” (Fit. 12:1-13) Bugu da ƙari, a Dokar Musa an yi amfani da dabbobi dabam-dabam sa’ad da ake hadaya, har da tumaki da awaki.—Fit. 29:38-42; Lev. 5:6, 7.

15 Babu wani daga cikin waɗannan hadayu, da ’yan adam suka miƙa da ya kawo ceto na dindindin daga zunubi da mutuwa. (Ibran. 10:1-4) A wani ɓangare kuma, Yesu ne ‘Ɗan rago na Allah wanda ya ɗauke zunubin duniya.’ Hakan kaɗai ma ya sa Yesu ya zama dukiya da ta fi kowace dukiya ta zahiri da aka taɓa gani. Saboda haka, yana da kyau mu ɗauki lokaci mu yi nazarin batun fansa sosai kuma mu ba da gaskiya ga wannan tanadi mai ban al’ajabi. Idan muka yi hakan, muna da begen samun albarka mai girma da lada, “ƙaramin garke” za su samu girma da ɗaukaka tare da Kristi a sama, kuma “waɗansu tumaki” za su samu rai madawwami a cikin Aljanna a duniya.—Luk 12:32; Yoh. 6:40, 47; 10:16.

16, 17. Me ya sa yake da muhimmanci mu fahimci matsayin Yesu na “shugaban bangaskiyarmu da mai-cikanta”?

16 Yesu ne “shugaban bangaskiyarmu da mai-cikanta.” (Karanta Ibraniyawa 12:1, 2.) A Ibraniyawa sura ta 11, mun ga jawabi mai daɗi da Bulus ya yi game da bangaskiya da kuma jerin maza da mata masu bangaskiya, kamar su Nuhu, Ibrahim, Saratu, da Rahab. Saboda haka, Bulus ya aririci ’yan’uwansa Kiristoci su “zuba ido ga Yesu shugaban bangaskiyarmu da mai-cikanta.” Me ya sa Bulus ya faɗi hakan?

17 Ko da yake waɗannan maza da mata masu aminci da aka ambata sunansu a Ibraniyawa sura 11 suna da bangaskiya sosai ga alkawarin Allah, ba su da cikakken bayani game da yadda Allah zai cika alkawarinsa ta wurin Almasihu da Mulkin. Da hakan, bangaskiyarsu ba cikakkiya ba ce. Hakika, har waɗanda Jehobah ya yi amfani da su su rubuta annabce-annabce da yawa game da Almasihu ba su fahimci ma’anar abin da suka rubuta sosai ba. (1 Bit. 1:10-12) Sai ta wurin Yesu ne kaɗai bangaskiya za ta zama cikakkiya. Yana da muhimmanci mu fahimci sarai kuma mu gane matsayin Yesu na “shugaban bangaskiyarmu da mai-cikanta”!

Ku Ci Gaba da Nema

18, 19. (a) Ka ambata wasu dukiyoyi na ruhaniya da ke ɓoye a cikin Kristi. (b) Me ya sa za mu ci gaba da dogara ga Yesu domin samun dukiya ta ruhaniya?

18 Mun tattauna kaɗan kawai cikin hakkokin Yesu mai tamani wajen cika nufe-nufen Allah don ceton ’yan adam. Har ila da akwai wasu abubuwa na ruhaniya masu tamani da aka ɓoye cikin Kristi. Samunsu zai sa mu farin ciki kuma za su amfane mu. Alal misali, manzo Bitrus ya kira Yesu “Sarkin rai” da “tauraro na assubahi” da ke fitowa. (A. M. 3:15; 5:31; 2 Bit. 1:19) Kuma Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da kalmar nan “Amin” ga Yesu. (R. Yoh. 3:14) Ka san ma’ana da kuma muhimmancin waɗannan hakkoki kuwa? Kamar yadda Yesu ya faɗa, ku ci gaba da “nema, za ku samu.”—Mat. 7:7.

19 Babu wani a cikin tarihi da rayuwarsa take cike da ma’ana kuma take da alaƙa sosai da madawwamin zaman lafiyarmu kamar ta Yesu. Dukiyoyi na ruhaniya suna ɓoye a cikinsa, kuma duk wanda ya nema su da dukan zuciyarsa zai iya samunsu da sauƙi. Bari ya zama abin farin ciki da albarka a gare ka ka samu dukiyoyi da aka ‘ɓoye cikinsa.’

Ka Tuna?

• An aririci Kiristoci su nemi waɗanne dukiyoyi?

• Me ya sa gargaɗin Bulus ga Kolosiyawa har ila ya dace a gare mu a yau?

• Ka faɗa kuma ka bayyana wasu cikin dukiyoyi na ruhaniya da aka “ɓoye” cikin Kristi.

[Hotunan da ke shafi na 5]

Littafi Mai Tsarki yana kama da taswira na dukiya da ke yi mana ja-gorar zuwa wajen dukiyoyi da aka ‘ɓoye cikin’ Kristi

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba