Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 10/1 pp. 13-15
  • “Menene Za Mu Ci?”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Menene Za Mu Ci?”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Ba Mu “Abincin Yini”
  • “Ku Zo, Ku Karya; ga Abincin Safiya”
  • “In Za Ka Kira Biki”
  • “Kada Ku Yi Alhini”
  • Kana Cin Gurasa Mai Ba da Rai?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • “Ku Yi Wannan Abin Tunawa da Ni”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Me Muka Koya Daga Yadda Yesu Ya Ciyar da Mutane da Burodi?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Me Za Ka Yi don Ka Sami Rai na har Abada?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 10/1 pp. 13-15

“Menene Za Mu Ci?”

ABINCI da abin sha, sune abubuwan da mutane suke yawan maganarsu a lokacin hidimar Yesu. Mu’ujizansa na farko shi ne mai da ruwa zuwa anab, kuma sau biyu ya ciyar da mutane masu yawa da gurasa da kuma kifi kaɗan. (Matta 16:7-10; Yohanna 2:3-11) An san Yesu da cin abinci tare da matalauta da kuma mawadata. Hakika, maƙiyan Yesu sun zarge shi da zarin ci kuma sun ce mashayi ne. (Matta 11:18, 19) Gaskiyar ita ce, Yesu ba ya hakan. Amma dai, ya san cewa abinci da abin sha suna da muhimmanci ga mutane, kuma ya yi amfani da waɗannan abubuwa don ya koyar da darussa na ruhaniya masu muhimmanci.—Luka 22:14-20; Yohanna 6:35-40.

Waɗanne irin abinci da abin sha ne aka fi sani a zamanin Yesu? Ta yaya ake yin abinci a lokacin? Kuma wane ƙoƙari ne ake yi don a shirya shi? Amsoshin waɗannan tambayoyin za su taimaka maka ka fahimci wasu aukuwa da furci da aka ambata a Linjila.

Ka Ba Mu “Abincin Yini”

Sa’ad da Yesu ya koya wa almajiransa yadda za su yi addu’a, ya bayyana cewa ya dace a roƙi Allah ya yi tanadin ainihin abubuwan da ake bukata a rayuwa, wato, “abincin yini.” (Matta 6:11) Burodi abinci ne da ake yawan ci shi ya sa a yaren Ibrananci da Helenanci, furcin nan “ci abinci” yana nufin “ci burodi.” Hatsin da ake yin burodi da shi, kamar su, alkama da sha’ir, da kuma maiwa da gero su ne yawancin abincin da Yahudawa na ƙarni na farko suke ci. Masu bincike sun kimanta cewa mutum ɗaya yakan ci kusan kilo ɗari biyu na hatsi a shekara, kuma zai samu kusan rabin kalori da ya ke bukata don gina jikinsa.

Za a iya sayan burodi a kasuwa. Amma yawancin iyalai sukan gasa nasu ne, kuma hakan ba ƙaramin aiki ba ne. Littafin nan mai suna Bread, Wine, Walls and Scrolls ya bayyana: “Tun da yake ajiye fulawa har lokaci mai tsawo yana da wuya, uwargida tana niƙa fulawar a kullum.” Menene yawancin lokacin da wannan aikin zai ɗauka? In ji mawallafin, “yin niƙa da hannu har tsawon awa ɗaya aiki ne mai wuyan gaske, kuma abin da za a samu bai kai kilo guda na fulawa ba daga kilo ɗaya na alkama. Tun da alkamar da mutum ɗaya yake ci a rana ya kusa rabin kilo, domin ayi burodin da mutane biyar ko shida za su ci, uwargidan tana bukatan ta yi ta niƙa har tsawon awoyi uku.”

Yanzu ka yi la’akari da Maryamu, mahaifiyar Yesu. Ƙari ga sauran ayyukanta na gida, za ta gasa burodin da zai ishe mijinta, yaranta maza biyar, da aƙalla ’ya’ya mata biyu. (Matta 13:55, 56) Babu shakka, Maryamu kamar sauran matan Yahudawa, takan yi aiki tuƙuru don ta ba da “abincin yini.”

“Ku Zo, Ku Karya; ga Abincin Safiya”

Bayan da aka ta da Yesu daga matattu, ya bayyana ga wasu cikin almajiransa da asuba. Almajiran sun fita kamun kifi tun daddare, amma ba su yi nasara ba. Yesu ya ce wa almajiransa da sun riga sun gaji, “Ku zo, ku karya; ga abincin safiya.” Sai ya ba su gasashen kifi da burodi. (Yohanna 21:9-13) Ko da yake a nan kaɗai ne Linjila ta ambata abincin safiya, amma mutanen sun saba karyawa da abinci kamar su burodi ’ya’yan itace da zaitun.

Abincin rana fa? Menene waɗanda suke yin aiki za su ci? Littafin nan Life in Biblical Israel ya ce: Abincin da ake ci da rana ba mai nauyi ba ne, ya haɗa da burodi, hatsi, zaitun, da ’ya’yan ɓaure.” Wataƙila abubuwan da almajiran suke riƙe da su ke nan sa’ad da suka tarar da Yesu yana yin magana da matar nan ’yar Samariya a bakin rijiya kusa da Sukar. Lokacin “wajen sa’a ta shidda ne,” ko tsakar rana, kuma almajiran sun riga sun “tafi cikin gari garin sayen abinci.”—Yohanna 4:5-8.

Da yamma, iyalai suna taruwa don su ci ainihin abincin ranar tare. Sa’ad yake kwatanta wannan abincin, littafin nan Poverty and Charity in Roman Palestine, First Three Centuries C.E. ya ce: “Yawancin mutane suna cin burodi ko fate-fate da aka yi da sha’ir, hatsi iri-iri, a wani lokaci kuma alkama. A yawancin lokaci suna haɗa abincin da gishiri da mai ko kuma zaitun, a wani lokaci kuma da romo mai ƙamshi, zuma, ko kuwa ruwan ’ya’yan itace.” Wataƙila suna kuma haɗa abincinsu da madara, cuku, ganyaye, da kuma ɗanye ko busashen ’ya’yan itace. Kusan ganyaye talatin dabam-dabam ne suke da su a lokacin, kamar su albasa, tafarnuwa, karas, da kabeji, da sauran su, suna kuma shuka ’ya’yan itace iri-iri fiye da ashirin da biyar a wannan yankin, kamar su (1) ɓaure, (2) dabino, da (3) ruman.

A zuciyarka, kana ganin waɗannan kayan haɗa abinci a kan teburi sa’ad da Yesu ya ci abincin dare tare Li’azaru da yayyensa mata, Martha da Maryamu? Yanzu ka yi tunanin irin ƙamshin da ya cika ɗakin sa’ad da Maryamu ta shafe ƙafafun Yesu da “nard,” ƙamshin abincin ya haɗu da na man mai tsada.—Yohanna 12:1-3.

“In Za Ka Kira Biki”

A wani lokacin kuma, sa’ad da yake cikin abinci a “gidan wani daga cikin hakiman Farisawa,” Yesu ya koya wa waɗanda suke wurin darasi mai kyau. Ya ce: “In za ka kira biki, sai ka gayyato gajiyayyu, da musakai, da guragu, da makafi. Za ka kuwa sami albarka, da ya ke ba su da hanyar sāka maka. Sai kuwa a sāka maka ranar tashin masu adalci.” (Luka 14:1-14; Littafi Mai Tsarki) Da a ce Bafarisin ya bi shawarar Yesu, da wane irin abinci ne zai ba da a wannan bikin?

Wataƙila mai wadata zai iya ba da burodi mai kyau kala-kala, waɗanda aka haɗa da anab, zuma, madara da kayan ƙamshi. Wataƙila, za a samu man shanu da cuku a teburin. Babu shakka, za a samu ɗanyen zaitun, zaitun da ya daɗe a ajiye, ko man zaitun a kan teburin. In ji littafin nan Food in Antiquity, “kowanne mutum yana cin kilo ashirin na man zaitun a kowace shekara a cikin abinci, sukan kuma yi amfani da shi don kwalliya da kuma ƙarin haske.”

Idan Bafarisin yana zaune ne kusa da teku, wataƙila shi da baƙinsa za su ci kifin da ba a daɗe da kamawa ba. Waɗanda suke zama nesa da teku sukan ci kifin da aka adana da gishiri maganin lalacewa. Maigidan wataƙila zai ba da nama, abin da ba a yawan ba baƙo talaka. Wani abinci kuma da wataƙila za a ba da shi ne abincin da aka yi da ƙwai. (Luka 11:12) Wataƙila za a haɗa abincin nan ne da kayan ƙamshi, kamar su minti, ɗanɗoya, lafsur, da mastad. (Matta 13:31; 23:23; Luka 11:42) Bayan an gama cikin ainihin abincin, wataƙila baƙin sun more kayan zaki da aka yi da gasashen alkama kuma aka haɗa da durumi, zuma da kayan ƙamshi.

Wataƙila akan ba waɗanda suke wajen biki inabi, ɗanye ko busashe, ko kuma wanda aka mai da ruwan anab. An gano dubban abubuwan yin anab a ƙasar Falasɗinu, hakan tabbaci ne cewa mutanen suna jin daɗin shan ruwan anab. A wani ɓangare a Gibeyon, masu tona ƙasa sun gano inda ake zuba anab guda sittin da uku da ke rufe cikin dutse wanda zai iya ɗaukan kusan galan dubu ashirin da biyar na anab.

“Kada Ku Yi Alhini”

Yayin da kake karanta Linjila, ka lura da yawan lokaci da Yesu ya ambata abinci ko abin sha a kwatancinsa ko kuwa yadda yake koyar da darasi mai muhimmanci sa’ad da yake cin abinci. Babu shakka, Yesu da almajiransa sun more cin abinci da abin sha, musamman ma sa’ad da suke tare da abokai, amma ba su saka waɗannan farko a rayuwarsu ba.

Yesu ya taimaka wa almajiransa su kasance da ra’ayin da ya dace game da abinci da abin sha sa’ad da ya ce: “Kada ku yi alhini fa, kuna cewa, Me za mu ci? ko kuwa, Me za mu sha? ko kuwa, Da minene za mu yi sutura? Gama waɗannan abubuwa duka Al’ummai suna ta biɗa; gama Ubanku na sama ya sani kuna bukatar waɗannan abubuwa duka.” (Matta 6:31, 32) Almajiran sun saka wannan cikin zuciya, kuma Allah ya kula da bukatunsu. (2 Korintiyawa 9:8) Ko da yake, irin abincinka wataƙila zai iya bambanta da na waɗanda ke ƙarni na farko. Amma za ka iya tabbata cewa Allah zai kula da kai idan ka saka bautarsa farko a rayuwarka.—Matta 6:33, 34.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba