Abin Da Muka Koya Daga Wurin Yesu
Game da Rayuwar ’Yan adam a Nan Gaba
Yesu ya yi alkawarin yin rayuwa a sama ne?
E, ya yi! An ta da Yesu da kansa daga matattu, kuma ya koma sama ya kasance tare da Ubansa. Amma kafin mutuwarsa da kuma tashinsa daga matattu, ya gaya wa amintattun manzaninsa sha ɗaya: “A cikin gidan Ubana akwai wurin zama dayawa. . . . Zan tafi garin in shirya muku wuri.” (Yohanna 14:2) Amma, mutane ƙalilan ne za su samu wannan gatan. Yesu ya bayyana wannan gaskiyar dalla-dalla sa’ad da ya gaya wa almajiransa cewa: “Ku ƙaramin garke, kada ku ji tsoro; gama Ubanku yana jin daɗi shi ba ku mulkin.”—Luka 12:32.
Menene ‘ƙaramin garken’ za su yi a sama?
Uban yana son wannan ƙaramin rukuni su kasance cikin gwamnatin da ke sama tare da Yesu. Yaya muka san hakan? Bayan da aka ta da shi daga matattu, Yesu ya bayyana wa manzo Yohanna cewa wasu amintattun mutane za su yi “mulki bisa duniya.” (Ru’ya ta Yohanna 1:1; 5:9, 10) Wannan albishiri ne. Abin da ’yan adam suka fi so shi ne gwamnati mai kyau. Menene wannan gwamnatin da Yesu zai yi sarautarsa zai cim ma? Yesu ya ce: ‘Ku da kuka biyo ni, cikin sabonta sa’anda Ɗan mutum za ya zauna bisa kursiyin darajassa, ku kuma za ku zauna bisa kursiyi goma sha biyu.’ (Matta 19:28) Wannan sarautar da Yesu da mabiyansa za su yi, za ta kawo “sabonta,” na kamiltaccen yanayin da ma’aurata na farko suka more a duniya kafin su yi zunubi.
Wane bege ne Yesu ya ba sauran ’yan Adam?
An halicci ’yan adam ne don su yi rayuwa a duniya, ba kamar Yesu ba, wanda aka halicce shi don ya yi rayuwa a sama. (Zabura 115:16) Saboda haka, Yesu ya ce: “Ku na ƙasa ne; ni na bisa ne.” (Yohanna 8:23) Yesu ya yi magana game da rayuwa mai kyau a nan gaba da ’yan adam za su more a duniya. Akwai lokacin da ya ce: “Masu-albarka ne masu-tawali’u: gama su za su gāji duniya.” (Matta 5:5) Ya yi ƙaulin hurarriyar zabura da ta ce: “Masu-tawali’u za su gāji ƙasan; za su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama. Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.”—Zabura 37:11, 29.
Saboda haka, ba “ƙaramin garken” da za su je sama ba ne kawai za su samu rai na har abada. Yesu ya kuma yi magana game da bege da dukan miliyoyin ’yan adam suke da shi. Ya ce: ‘Allah ya yi ƙaunar duniya har ya bada Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana bada gaskiya gareshi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.’—Yohanna 3:16.
Ta yaya Allah zai cire wahalar da ’yan adam suke sha?
Yesu ya yi maganar samun sauƙi daga ɓangarori biyu da ake shan wahala sa’ad da ya ce: “Shari’ar wannan duniya yanzu ta ke; yanzu za a fitar da mai-mulkin wannan duniya.” (Yohanna 12:31) Na farko, za a hukunta da kuma halaka mutanen da ba sa bauta wa Allah da suke haddasa shan wahala. Na biyu, za a halaka Shaiɗan kuma ba za ya sake samun damar yaudarar ’yan adam ba.
Menene zai faru da mutanen da suka yi rayuwa kuma suka mutu tun fil azal ba tare da samun damar koya game da Allah da Kristi ba kuma su yi imani da su? Yesu ya gaya wa mai zunubin da ya mutu kusa da Shi: ‘Za ka kasance tare da ni cikin Al’janna.’ (Luka 23:43) Wannan mutumin, tare da wasu miliyoyin mutane, za su samu zarafin koya game da Allah sa’ad da Yesu zai ta da su daga matattu a al’janna a duniya. A lokacin za su samu damar kasancewa cikin masu adalcin da za su more rai na har abada a duniya.—Ayyukan Manzanni 24:15
Don samun ƙarin bayani, ka duba babi na 3 da na 7 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?a
[Hasiya]
a Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
[Hotunan da ke shafi na 19]
“Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.”—Zabura 37:29