Ku Koyar Da Yaranku
Rahab ta Saurari Labarin
BARI a ce muna shekaru 3,500 da suka wuce. Muna zaune a birnin Jericho, a ƙasar Ka’anan. Wata yarinya mai suna Rahab tana zaune a wannan birnin. An haife ta ne bayan da Musa ya fitar da Isra’ilawa daga bauta a ƙasar Masar kuma ya yi musu ja-gora a kan busasshiyar ƙasa a Jan Teku! A lokacin babu rediyo, telibijin, ko kuma intane, amma Rahab ta samu labarin wannan mu’ujizar, duk da cewa ta faru ne a ƙasa mai nisa sosai daga inda take zaune. Ka san yadda ta samu wannan labarin?—a
Babu shakka matafiya ne suka ba da labarin wannan mu’ujizar. Sa’ad da ta yi girma, Rahab ta tuna abin da Jehobah ya yi wa mutanensa. Ta kuma ji waɗansu abubuwa masu ban al’ajabi game da Isra’ilawa. Bayan shekaru 40 a Jeji, sun shiga ƙasar Ka’anan, kuma Allah ya taimaka musu su halaka dukan waɗanda suke hamayya da su. A yanzu Rahab ta samu labari cewa Isra’ilawa suna dab da ketare Kogin Urdun zuwa Jericho!
Wata yamma, baƙi biyu suka zo gidan Rahab domin sun san cewa tana aiki ne a wurin da baƙi za su iya zama. Sai ta marabce su. Daddare, sarkin Jericho ya samu labarin cewa ’yan Isra’ila ’yan leƙen asiri sun shigo cikin ƙasar Jericho kuma suna gidan da Rahab take yin aiki. Sai sarkin ya aika ’yan saƙo ga Rahab, waɗanda suka gaya mata cewa ta fito da mutanen da suka shigo gidanta. Ka san abin da Rahab ta riga ta ji, da kuma matakin da ta ɗauka?—
Tun kafin ’yan aiken sarkin su isa wurin Rahab, ta riga ta ji labarin cewa Isra’ilawan ’yan leƙen asiri ne. Sai ta ɓoye su a kan rufin ɗakin kuma ta gaya wa ’yan aiken sarkin cewa: “I, mazajen suka zo wurina . . . Ya zama kuwa a [lokacin] rufin ƙofa, sa’anda ana duhu, sai mazajen suka fita.” Rahab ta umurce su: “Ku bi su.”
Me ya sa Rahab ta kāre ’yan leƙen asirin?— Ta bayyana dalilin, sa’ad da take gaya musu cewa: “Na sani Ubangiji ya rigaya ya ba ku ƙasar . . . Gama mun ji yadda Ubangiji ya shanyar da ruwan Jan Teku a gabanku, lokacinda kuka fito Masar.” Ta kuma ji yadda Allah ya sa Isra’ila suka halaka maƙiyinsu.
Babu shakka, Jehobah ya yi farin ciki sosai cewa Rahab ta kāre waɗannan ’yan leƙen asirin, kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya gaya mana a Ibraniyawa 11:31. Ya kuma yi farin ciki sa’ad da ta roƙi ’yan leƙen asirin cewa: ‘Na yi maku alheri, ku kuma ku yi ma gidan ubana alheri, ku ba ni alama mai-gaskiya: ku ceci ubana da rai, da uwata, da ’yan’uwana maza da mata.’ ’Yan leƙen asirin sun yi wa Rahab alkawari cewa za su yi hakan idan ta bi waɗannan umurnin. Ka san umurnin kuwa?—
‘Za ki ɗaura wannan igiya ta jan zare a cikin taga,’ in ji ’yan leƙen asirin, ‘kuma za ki tattara dukan iyalin ubanki cikin gidanki. Idan kin yi hakkan, kowa a gidanki za su tsira.’ Rahab ta yi daidai abin da ’yan leƙen asirin suka gaya mata. Ka san abin da ya faru a lokacin?—
Isra’ilawa suka isa bayan ganuwar Jericho. A kullum suna zagaya birnin sau ɗaya har tsawon kwanaki shida ba tare da kururruwa ba. A rana ta bakwai, suka zagaya birnin sau bakwai sai suka yi ihu. Sai duk ganuwar ta faɗi, amma ban da wurin da aka ɗaura jan igiya a taga! Rahab da iyalinta sun tsira.—Joshua 2:1-24; 6:1-5, 14, 15, 20-25.
Menene za mu iya koya daga abin da Rahab ta yi?— Ta saurari labarin yadda Allah yake kāre mutanensa kuma ta taimaka musu sa’ad da ta samu zarafin yin hakan. Hakika, Rahab ta zaɓi ta bauta wa Jehobah tare da mutanensa! Kai ma za ka yi hakan?— Muna yin addu’a cewa za ka yi hakan.
[Hasiya]
a Idan kana karanta wa yara, wannan alamar fid da ma’ana tana nufin ka dakata, ka yi masu tambayar.
Tambayoyi:
○ Wane labari mai muhimmanci ne Rahab ta ji sa’ad da take ƙarama?
○ Yaya ta bi da Isra’ilawa ’yan leƙen asiri, kuma me ya sa?
○ Wane alkawari ne Rahab ta sa ’yan leƙen asirin suka yi mata?
○ Me ya sa muka san cewa Rahab ta faranta wa Jehobah rai, kuma yaya za ka iya yin koyi da ita?