Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 8/15 pp. 3-7
  • Allah Ne Ya Ba Da Begen Rai Na Har Abada A Duniya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Allah Ne Ya Ba Da Begen Rai Na Har Abada A Duniya
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ‘Sarayar da Halitta ta Zama Banza . . . Domin Sa Zuciya’
  • ‘Ruhun Yana I Mani’
  • “A Cece Shi Daga Gangarawa Cikin Rami”
  • An Haɗiye Mutuwa Daga Duniya
  • Jehobah Ya Warkar da Shi
    Ka Yi Koyi da Bangaskiyarsu
  • Tashin Matattu —Koyarwa Da Ta Shafe Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Abokan Kirki Suna Ba da Shawara Mai Kyau
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
  • Kiristoci Suna Da Begen Rai Na Har Abada A Duniya ne?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 8/15 pp. 3-7

Allah Ne Ya Ba Da Begen Rai Na Har Abada A Duniya

“An sarayar da halitta ta zama banza. . . . Duk da haka akwai sa zuciya.”—ROM. 8:20, Littafi Mai Tsarki.

1, 2. (a) Me ya sa begen rai na har abada a duniya yake da muhimmanci a gare mu? (b) Me ya sa mutane da yawa suke shakkar yin rayuwa na har abada a duniya?

WATAƘILA ka tuna farin cikin da ka yi sa’ad da ka koya da farko cewa a nan gaba, mutane ba za su ƙara tsufa ba kuma ba za su mutu ba, amma za su rayu har abada a duniya. (Yoh. 17:3; R. Yoh. 21:3, 4) Mai yiwuwa ka yi farin cikin gaya wa mutane game da wannan begen da ke cikin Nassosi. Ballantana ma, begen rai madawwami sashe ne mai muhimmanci na bisharar da muke wa’azinta. Yana shafan halinmu game da rayuwa.

2 Amma, yawancin addinai na Kiristendam sun yi watsi da begen rai madawwami a duniya. Ko da yake Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa kurwa tana mutuwa, yawancin coci suna koyar da batun nan da ya saɓa da Nassosi cewa ’yan adam suna da kurwa da ba ta mutuwa da ke rayuwa a duniya ta ruhu. (Ezek. 18:20) Saboda haka, mutane da yawa suna shakkar yin rayuwa a duniya har abada. Muna iya yin wannan tambayar: “Littafi Mai Tsarki ya goyi bayan wannan begen kuwa? Idan haka ne, a wane lokaci ne Allah ya bayyana wa ’yan adam wannan begen da farko?

‘Sarayar da Halitta ta Zama Banza . . . Domin Sa Zuciya’

3. Ta yaya nufin Allah game da mutane ya bayyana tun daga somawar tarihin ’yan adam?

3 Jehobah ya bayyana nufinsa ga mutane a farkon tarihin ’yan adam. Allah ya nuna sarai cewa Adamu zai rayu har abada idan ya yi biyayya. (Far. 2:9, 17; 3:22) Babu shakka, zuriyar farko ta Adamu ta koyi yadda ’yan adam suka zama ajizai, kuma abubuwan da muke gani sun tabbatar da hakan. An rufe hanyar shiga lambun Adnin, kuma mutane suka tsufa suka mutu. (Far. 3:23, 24) Da shigewar lokaci, tsawon rayuwar ’yan adam ta ragu. Adamu ya mutu yana da shekaru 930. Shem wanda ya tsira daga Rigyawa ya mutu yana da shekaru 600, kuma ɗansa Arpachshad ya mutu yana da shekaru 438. Terah, mahaifin Ibrahim ya mutu yana da shekaru 205. Ibrahim ya mutu yana da shekaru 175 kuma ɗansa Ishaku ya mutu yana da shekaru 180, Yakubu kuma ya mutu yana da shekaru 147. (Far. 5:5; 11:10-13, 32; 25:7; 35:28; 47:28) Wataƙila mutane da yawa za su ɗauka cewa wannan raguwa ta tsawon shekaru tana nufin cewa an yi hasarar begen rai na har abada! Amma, suna da dalilin kasancewa da begen cewa za a iya sake samun rai na har abada?

4. Menene ya sa mutane masu aminci na zamanin dā suka gaskata cewa Allah zai dawo da albarkar da Adamu ya rasa?

4 Kalmar Allah ta ce: “An sarayar da halitta [ta ’yan adam] ta zama banza . . . [domin] akwai sa zuciya.” (Rom. 8:20) Wane sa zuciya [ko bege] ke nan? Annabci na farko a cikin Littafi Mai Tsarki ya yi nuni ga “zuriya” da za ta ‘ƙuje kan macijin.’ (Karanta Farawa 3:1-5, 15.) Ga mutane masu aminci, alkawarin da aka yi na wannan Zuriyar ya ba su begen cewa Allah ba zai yasar da nufinsa ba game da ’yan adam. Ya ba mutane kamar Habila da Nuhu dalilin gaskata cewa Allah zai dawo da albarkar da Adamu ya rasa. Wataƙila waɗannan mutanen sun fahimci cewa ‘ƙuje duddugen zuriyar’ zai ƙunshi zubar da jini.—Far. 4:4; 8:20; Ibran. 11:4.

5. Menene ya nuna cewa Ibrahim yana da begen tashin matattu?

5 Ka yi la’akari da Ibrahim. Sa’ad da aka jarraba shi, Ibrahim “ya miƙa Ishaƙu . . . ɗansa haifaffensa kaɗai.” (Ibran. 11:17) Me ya sa yake son ya yi hakan? (Karanta Ibraniyawa 11:19.) Domin ya gaskata da tashin matattu! Ibrahim yana da dalilin gaskata da tashin matattu. Balle ma, Jehobah ya mai da wa Ibrahim ikon haihuwa kuma ya sa ya yiwu shi da matarsa Saratu su haifi ɗa duk da yake sun tsufa. (Far. 18:10-14; 21:1-3; Rom. 4:19-21) Ibrahim ya gaskata da maganar Jehobah. Allah ya gaya masa: “Daga cikin Ishaƙu za a ƙira zuriyarka.” (Far. 21:12) Saboda haka, Ibrahim yana da dalili mai kyau na sa rai cewa Allah zai ta da Ishaƙu daga matattu.

6, 7. (a) Wane alkawari ne Jehobah ya yi wa Ibrahim? (b) Ta yaya alkawarin da Jehobah ya yi wa Ibrahim ya ba da bege ga ’yan adam?

6 Domin bangaskiya na musamman da Ibrahim yake da ita, Jehobah ya yi masa alkawari game da ɗansa, ko kuma ‘zuriya.’ (Karanta Farawa 22:18.) Yesu Kristi ne ainihin sashe na musamman na wannan ‘zuriya.’ (Gal. 3:16) Jehobah ya gaya wa Ibrahim cewa za a riɓanya ‘tsatsonsa [“zuriya,” NW]’ “kamar taurarin sama, kamar yashi kuma wanda ke a bakin teku” wato, adadin da Ibrahim bai sani ba. (Far. 22:17) Amma, daga baya aka bayyana wannan adadin. Yesu Kristi da mutane 144,000, da za su yi sarauta da shi a Mulkinsa, su ne wannan “zuriyar.” (Gal. 3:29; R. Yoh. 7:4; 14:1) Ta wurin Mulkin Almasihu ne “dukan al’umman duniya za su sami albarka.”

7 Mai yiwuwa Ibrahim bai fahimci cikakkiyar ma’anar alkawarin da Jehobah ya yi masa ba. Duk da haka, yana jiran “birnin da ke da tussa,” in ji Littafi Mai Tsarki. (Ibran. 11:10) Mulkin Allah ne wannan birnin. Dole ne Ibrahim ya sake rayuwa idan zai samu albarka a wannan Mulkin. Zai yi rayuwa har abada a duniya sa’ad da aka ta da shi daga matattu. Waɗanda suka tsira daga Armageddon ko waɗanda aka ta da su daga mutuwa za su rayu har abada.—R. Yoh. 7:9, 14; 20:12-14.

‘Ruhun Yana I Mani’

8, 9. Me ya sa littafin Ayuba ba labarin jarraba mutum ɗaya kawai ba ne?

8 A zamanin annabi Musa da kuma Yusufu, tattaba kunnen Ibrahim, an yi wani mutumi mai suna Ayuba. Littafin Ayuba da ke cikin Littafi Mai Tsarki da wataƙila Musa ne ya rubuta shi, ya bayyana abin da ya sa Jehobah ya ƙyale Ayuba ya sha wahala da kuma sakamakon da ya samu. Amma, littafin Ayuba ba labari ba ne ba kawai na jarraba mutum ɗaya, ya tattauna batutuwan da suka shafi dukan ’yan adam da halittu na ruhu. Littafin ya sa mun fahimci yadda Jehobah yake sarauta a hanya mai kyau, kuma ya nuna cewa aminci da kuma begen rai na dukan bayin Allah a duniya suna cikin batun da aka ta da a Adnin. Ko da yake Ayuba bai fahimci wannan batun ba, bai ƙyale abokansa uku su sa ya yi tunanin cewa bai riƙe amincinsa ba. (Ayu. 27:5) Ya kamata wannan ya ƙarfafa bangaskiyarmu kuma ya taimaka mana mu fahimci cewa za mu iya riƙe amincinmu kuma mu ɗaukaka ikon mallaka na Jehobah.

9 Bayan mutane uku da suka ce wai sun zo yi wa Ayuba ta’aziyya sun gama magana, “Elihu fa ɗan Barachel Ba-buzi ya amsa.” Menene ya motsa shi ya yi magana? Ya ce, “cike na ke da magana: Ruhun da ke cikina yana i mani.” (Ayu. 32:5, 6, 18) Ko da yake abin da aka hure Elihu ya faɗa ya cika sa’ad da gwajin Ayuba ya ƙare, kalmominsa suna da ma’ana ga mutane. Sun sa dukan waɗanda suke da aminci ga Allah su kasance da bege.

10. Menene ya nuna cewa saƙon Jehobah ga mutum ɗaya a wani lokaci yana da ma’ana ga dukan ’yan adam?

10 A wani lokaci Jehobah yana ba da saƙo ga mutum ɗaya kuma saƙon ya shafi dukan ’yan adam. Za mu iya ganin hakan daga annabcin Daniyel da ya shafi mafarkin Sarki Nebuchadnezzar na Babila game da sare itace mai girma. (Dan. 4:10-27) Ko da yake wannan mafarkin ya cika a kan Nebuchadnezzar, ya yi nuni ga wani abu mafi girma. Ya nuna cewa bayan shekaru 2,520, wadda za ta soma a shekara ta 607 K.Z,a Allah zai yi sarauta bisa duniya ta hanyar zuriyar Sarki Dauda. Allah ya soma sabuwar sarauta bisa duniyarmu ta hanyar naɗa Yesu Kristi Sarkin samaniya a shekara ta 1914. Ka yi tunanin yadda sarautar Mulkin za ta cika begen ’yan adam masu biyayya nan ba da daɗewa ba!

“A Cece Shi Daga Gangarawa Cikin Rami”

11. Menene kalaman Elihu suka nuna game da Allah?

11 Sa’ad da yake mai da martani ga Ayuba, Elihu ya yi maganar “mala’ika, matsakanci, ɗaya cikin dubu, domin shi nuna ma mutum abin da ke daidai gareshi.” Idan wannan mala’ikan ya yi “addu’a ga Allah, . . . [don] ya . . . karɓe shi da alheri” kuma fa? Elihu ya ce: “Sai shi [Allah ya] yi masa nasiha, shi ce masa, a cece shi daga gangarawa cikin rami, na sami fansa. Namansa za ya komo ya fi na yaro sabontaka; ya komo kwanakin ƙuruciyarsa ke nan.” (Ayu. 33:23-26) Waɗannan kalmomin sun nuna cewa Allah yana shirye ya karɓi “fansa” domin ’yan adam da suka tuba.—Ayu. 33:24.

12. Wane bege ne kalaman Elihu suka ba ’yan adam gabaki ɗaya?

12 Shekaru da yawa bayan haka, kamar annabi Daniyel, wataƙila Elihu bai fahimci cikakkiyar ma’anar fansa ba. (Dan. 12:8; 1 Bit. 1:10-12) Duk da haka, kalaman Elihu sun ba da bege cewa wata rana Allah zai karɓi fansa kuma ya ’yantar da ’yan adam daga mugun sakamakon tsufa da kuma mutuwa. Kalaman Elihu sun ba da bege mai ban al’ajabi na rai madawwami. Littafin Ayuba ya kuma nuna cewa za a yi tashin matattu.—Ayu. 14:14, 15.

13. Yaya Kiristoci suka fahimci kalaman Elihu?

13 A yau, kalaman Elihu sun ci gaba da kasancewa da ma’ana ga miliyoyin Kiristocin da ke da begen tsira daga halakar wannan zamani. Tsofaffin da ke cikin waɗanda suka tsira za su koma kwanakin ƙuruciyarsu. (R. Yoh. 7:9, 10, 14-17) Bugu da ƙari, begen ganin waɗanda aka ta da daga matattu da za su koma zuwa kwanakin ƙuruciyarsu ya ci gaba da sa mutane masu aminci farin ciki. Hakika, rayuwa ba tare da mutuwa ba a sama ga Kiristoci shafaffu da kuma rai madawwami a duniya don “waɗansu tumaki” na Yesu, ya dangana ne bisa ba da gaskiya ga hadayar fansa ta Kristi.—Yoh. 10:16; Rom. 6:23.

An Haɗiye Mutuwa Daga Duniya

14. Menene ya nuna cewa ana bukatar wani abu fiye da Dokar Musa domin Isra’ilawa su samu begen rai madawwami?

14 Zuriyar Ibrahim ta zama al’umma na kanta sa’ad da ta ɗauki alkawarin yin dangantaka da Allah. Sa’ad da yake ba su Dokar, Jehobah ya ce: ‘Za ku fa kiyaye farillaina, da shari’una: waɗanda idan mutum ya yi su, za ya rayu ta wurinsu: Ni ne Ubangiji.’ (Lev. 18:5) Amma, sun ƙi yin rayuwar da ta jitu da cikakken mizanan Dokar, Dokar ta hukunta Isra’ilawa kuma suna bukatan a fanshe su daga wannan hukuncin.—Gal. 3:13.

15. Wace albarka ta nan gaba ce aka hure Dauda ya rubuta?

15 Bayan Musa, Jehobah ya hure sauran marubutan Littafi Mai Tsarki su ambata begen rai madawwami. (Zab. 21:4; 37:29) Alal misali, mai zabura Dauda ya kammala wata waƙa game da haɗin kan masu bauta ta gaskiya a Sihiyona da waɗannan kalaman: “Daga can Ubangiji ya umurta albarka, rai ke nan na har abada.”—Zab. 133:3.

16. Ta bakin Ishaya, wane alkawari ne Jehobah ya yi game da “dukan duniya” nan gaba?

16 Jehobah ya hure Ishaya ya yi annabci game da rai na har abada a duniya. (Karanta Ishaya 25:7, 8.) Kamar bargo da ke ‘rufewa,’ zunubi da mutuwa sun zama kamar kaya mai nauyi ga ’yan adam. Jehobah ya tabbatar wa mutanensa cewa za a haɗiye ko kuma za a cire mutuwa “daga dukan duniya.”

17. Wane annabci game da matsayin da Almasihu zai cika ne ya buɗe hanyar rai na har abada?

17 Ka yi la’akari da ƙa’idar da ake bi a Dokar Musa game da bunsurun Azazel. Sau ɗaya a shekara, a Ranar Kafara, babban firist ‘zai ɗibiya hannunsa duka biyu a bisa kan bunsuru mai-rai, ya furta dukan muguntar ’ya’yan Isra’ila a bisan kan bunsurun, bunsurun kuma za ya ɗauka wa kansa dukan muguntarsu zuwa cikin ƙasa inda babu kowa.’ (Lev. 16:7-10, 21, 22) Ishaya ya annabta zuwan Almasihu, wanda zai cika irin wannan matsayin na ɗaukan “cutarmu,” “baƙincikinmu” da kuma “zunubi na mutane da yawa,” ta hakan ya buɗe hanyar rai na har abada.—Karanta Ishaya 53:4-6, 12.

18, 19. Wane bege ne aka nanata a Ishaya 26:19 da kuma Daniyel 12:13?

18 Ta bakin Ishaya, Jehobah ya gaya wa mutanensa Isra’ila: “Matattunka za su yi rai: gawayena za su tashi. Ku farka, ku raira waƙa, ku da ke zaune cikin turɓaya: gama rāɓarka rābar haske ce, ƙasa kuwa za ta fitar da matattu.” (Isha. 26:19) Nassosin Ibrananci sun nuna sarai cewa akwai begen tashin matattu da kuma rayuwa a duniya. Alal misali, sa’ad da Daniyel ya kai kusan shekara 100, Jehobah ya ba shi wannan tabbacin: “Za ka huta, ka tsaya a cikin rabonka, a ƙarshen kwanaki.”—Dan. 12:13.

19 Domin begen tashin matattu, Martha ta gaya wa Yesu game da ɗan’uwanta da ya rasu: “Na sani zai tashi kuma a cikin tashin matattu a kan rana ta ƙarshe.” (Yoh. 11:24) Koyarwar Yesu da hurarrun rubuce-rubuce na almajiransa sun canja wannan begen ne? Har ila, Jehobah yana miƙa wa ’yan adam begen rai na har abada a duniya kuwa? Za mu tattauna amsoshin waɗannan tambayoyin a talifi na gaba.

[Hasiya]

a Ka duba babi na 6 na littafin nan Pay Attention to Daniel’s Prophecy!

Za Ka Iya Ba da Bayani?

• An ƙasƙantar da talikan ’yan adam ta “zama banza” domin wane bege?

• Menene ya nuna cewa Ibrahim yana da bangaskiya a tashin matattu?

• Wane bege ne kalaman Elihu ga Ayuba ya ba ’yan adam?

• Yaya Nassosin Ibrananci suka nanata begen tashin matattu da kuma rai na har abada a duniya?

[Hotunan da ke shafi na 5]

Kalaman Elihu ga Ayuba sun ba da bege cewa za a ’yantar da ’yan adam daga tsufa da mutuwa

[Hotunan da ke shafi na 6]

An tabbatar wa Daniyel cewa ‘zai tsaya a cikin rabonsa a ƙarshen kwanaki’

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba