Domin Matasanmu
Mu’ujiza a Ranar Fentakos!
Umurni: Ka yi wannan aikin a inda za ka iya mai da hankalinka wuri ɗaya. Sa’ad da ka ke karanta Nassosi ka sa kanka cikin yanayin. Ka yi tunanin yanayin a zuciyarka. Ka ji muryoyin mutanen. Ka ji yadda ainihin mutanen da ke ciki suke ji. Ka sa labarin ya kasance kamar yanzu yake faruwa!
KA YI TUNANI A KAN YANAYIN NAN.—KARANTA AYYUKAN MANZANNI 2:1-21; 38-41.
Menene ka tuna sa’ad da kake karanta labarin nan game da “iska mai-ƙarfi” da kuma ‘harsuna kamar na wuta’?
․․․․․
Kana ganin menene mutanen suke cewa sa’ad da suka yi mamakin jin almajiran suna furta kalamai a harsuna dabam-dabam?
․․․․․
Yaya fuskokin waɗanda aka kwatanta a aya ta 13 kamar waɗanda suke ba’a yake?
․․․․․
KA YI BINCIKE SOSAI.
Wane irin idi ne Fentakos, kuma yaya wannan bikin ya shafi yanayin waɗanda suka taru a Urushalima? (Kubawar Shari’a 16:10-12)
․․․․․
Ta yaya Bitrus ya daraja waɗanda ya yi wa magana, kuma ta yaya ya yi magana a kan abin da suke so? (Ayyukan Manzanni 2:29)
․․․․․
Ta yaya gaba gaɗin Bitrus a ranar Fentakos ya bambanta da sa’ad da yake farfajiyar babban firist? (Matta 26:69-75)
․․․․․
KA YI AMFANI DA ABIN DA KA KOYA. KA RUBUTA ABIN DA KA KOYA GAME DA . . .
Muhimmancin faɗin abin da masu sauraronmu suke marmari da kuma girmama su sa’ad da muke koya musu imaninmu daga Littafi Mai Tsarki.
․․․․․
Damarka ta zama mashaidin Jehobah mai gaba gaɗi, ko da kana ɗan jin tsoro a yanzu.
․․․․․
WANE ƁANGAREN WANNAN LABARIN NE YA FI MA’ANA A GARE KA, KUMA ME YA SA?
Don ƙarin bincike, ka duba Hasumiyar Tsaro na 15 ga Satumba, 1996, shafofi na 8-9.
․․․․․