Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 1/1 pp. 29-32
  • Ya Yaƙi Tsoro da Kuma Shakka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ya Yaƙi Tsoro da Kuma Shakka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “Mun Sami Almasihu”!
  • “Kada Ka Ji Tsoro”
  • “Don Me Ka Yi Shakka?”
  • Ya Shawo Kan Tsoro da Kuma Shakka
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Ya Koyi Gafartawa Daga Wurin Ubangijinsa
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Ya Koyi Gafartawa Daga Wurin Ubangijinsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ya Kasance da Aminci a Lokacin Gwaji
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 1/1 pp. 29-32

Ka Yi Koyi Da Imaninsu

Ya Yaƙi Tsoro da Kuma Shakka

BITRUS ya yi dare yana tuka jirgin ruwa. Shin hasken da ya hango a yamma, alamar wayewar gari ne? Ya riga ya gaji da tuka jirgin. Iskar da ke kaɗa sumansa tana ta ta da Tekun Galili. Rakumin ruwa yana ta kaɗa jirgin kamun kifin, yana ta fesa wa Bitrus ruwa. Duk da haka, ya ci gaba da tuka jirgin.

Bitrus da abokansa sun bar Yesu shi kaɗai a bakin tekun. A ranar, sun ga yadda Yesu ya ciyar da taron mutane masu jin yunwa da ɗan ƙaramin gurasa da kifi. Mutanen sun nemi su naɗa Yesu sarki, amma ba ya son ya saka hannu a siyasa. Ya kuma ƙudurta ya kāre mabiyansa daga biɗar irin waɗannan muraɗin. Sa’ad da ya sallami taron jama’ar, sai ya gaya wa almajiransa su shiga jirgin su haye zuwa can ɓangaren kogin shi kuma ya hau kan dutsen don ya yi addu’a shi kaɗai.—Markus 6:35-45; Yohanna 6:14, 15.

Wata ya riga ya fito sa’ad da almajiran suka shiga cikin jirgin, kuma a yanzu watan ya soma faɗuwa zuwa ɓangaren yamma. Duk da haka, sun ƙoƙarta su yi tafiya ta mil kaɗan. Ƙarfin raƙumin ruwan da kuma iskar da ke kaɗawa ta sa tattaunawa da juna ya yi wuya. Wataƙila Bitrus bai yi magana da kowa ba, kuma ya yi zurfi cikin tunani.

Yana da abubuwa da yawa da zai yi tunani a kai! A yanzu ya yi wajen shekara biyu yana bin Yesu Banazarat. Ya koyi abubuwa da yawa, amma yana da ƙarin abubuwan da zai koya. Ƙudurin da ya yi na yaƙar matsaloli kamar su yin shakka da kuma jin tsoro ya sa ya zama misali mai kyau da za mu yi koyi da shi. Bari mu ga yadda ya faru.

“Mun Sami Almasihu”!

Bitrus ba zai taɓa mance ranar da ya sadu da Yesu Banazarat ba. Ɗan’uwansa, Andarawus ne ya soma gaya masa labarin mai ban mamaki: “Mun sami Almasihu.” Da jin waɗannan kalaman, sai rayuwar Bitrus ta soma canjawa. Ba za ta taɓa zama kamar yadda take a dā ba.—Yohanna 1:41.

Bitrus yana da zama ne a Kafarnahum, birnin da ke kusa da tafki mai suna Tekun Galili. Shi da Andarawus suna sana’ar kamun kifi ne tare da Yaƙub da Yohanna, yaran Zebedee. Waɗanda suke zama tare da Bitrus su ne matarsa, surukarsa da kuma ɗan’uwansa, Andarawus. Biyan bukatun waɗannan mutanen da sana’ar kamun kifi yana bukatar yin aiki tuƙuru, nuna kuzari, da gwaninta. Ka yi tunanin daren da suke yi suna aiki mai wuya, suna jefa tarun tsakanin jiragen biyu a cikin kogin kuma su kwashi duk irin kifin da suka kama zuwa bakin teku. Za mu kuma iya yin tunanin kwanakin da suke yi suna aiki tuƙuru, suna ware kifayen su sayar, kuma su gyara tarun.

Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa, Andarawus almajirin Yohanna Mai baftisma ne. Babu shakka, da kunnuwansa biyu, Bitrus ya saurari labaran da ɗan’uwansa ya gaya masa game da Yohanna. Wata rana, Andarawus ya ga Yohanna yana nuna Yesu Banazarat yana cewa: “Duba, ga Ɗan rago na Allah!” Nan take Andarawus ya zama mabiyin Yesu kuma ya gaya wa Bitrus wannan labarin mai motsawa: Almasihun ya bayyana! (Yohanna 1:35-40) Bayan tawayen da aka yi a gonar Adnin shekaru dubu huɗu kafin lokacin, Jehobah Allah ya yi alkawarin cewa wani mutumi na musamman zai zo don ya yi tanadin bege na gaske ga ’yan Adam. (Farawa 3:15) Andarawus ya sadu da wannan Mai Ceton, wato, Almasihu da kansa! Bitrus ma ya gaggauta don ya sadu da Yesu.

Har wannan ranar, ana kiran Bitrus da sunan nan Siman, ko Saminu. Amma Yesu ya kalle shi ya ce: “Kai ne Saminu ɗan Yahaya? Za a kira ka Kefas,” wato Bitrus. (Yohanna 1:42) “Kefas” sunan gama-gari ne wanda ke nufin “dutse.” Babu shakka, kalaman Yesu annabci ne. Ya ga cewa Bitrus zai zama kamar dutse, wanda zai kasance da tasiri a tsakanin mabiyan Kristi. Bitrus ya ga kansa hakan kuwa? Da kyar. Wasu a cikin waɗanda suke karanta labaran da ke cikin Linjila a yau ba sa ganin Bitrus a matsayin mutum mai tsayin daka, wanda za a dogara da shi. Wasu sun ce ba shi da ƙarfi, kuma bai iya tsai da shawara ba.

Bitrus yana da kurakurensa. Kuma Yesu ya san da hakan. Amma Yesu, kamar Ubansa, Jehobah, yana mai da hankali ne ga hali mai kyau na mutane. Yesu ya ga halaye masu kyau a Bitrus, kuma ya nemi ya taimaka masa ya ci gaba da nuna waɗannan halayen masu kyau. Jehobah da Ɗansa suna mai da hankali ne ga halayenmu masu kyau a yau. Muna iya yin shakkar cewa muna da halaye masu kyau da za su iya gani a cikinmu. Amma, muna bukatan mu gaskata da ra’ayinsu kuma mu yarda su koyar da mu kuma su daidaita mu kamar yadda suka yi wa Bitrus.—1 Yohanna 3:19, 20.

“Kada Ka Ji Tsoro”

Wataƙila Bitrus ya bi Yesu sa’ad da ya soma aikin wa’azi. Mai yiwuwa ya ga sa’ad da Yesu ya yi mu’ujizansa na farko, wato, juya ruwa zuwa inabi a bikin auren da aka yi a Kana. Mafi muhimmanci, ya ji saƙon Yesu mai cike da bege game da Mulkin Allah. Duk da haka, ya bar Yesu kuma ya koma bakin sana’arsa ta kamun kifi. Watanni kaɗan bayan hakan, Bitrus ya sake haɗuwa da Yesu, kuma a wannan lokacin Yesu ya gayyaci Bitrus ya ci gaba da binsa a dukan rayuwarsa.

Bitrus bai daɗe da kammala aiki mai ban haushi da ya yi daddare ba. Sau da yawa sun jefa tarunsu cikin kogi, amma ba su kama komi ba. Babu shakka, Bitrus ya yi amfani da dukan gwanintar da yake da ita don ya tabbata cewa sun kama kifaye, sun gwada wurare dabam-dabam don su ga inda kifayen suke cin abinci. Kamar sauran masu kama kifi, babu shakka da akwai lokacin da ya ji kamar ya shiga cikin kogin ya kakkamo kifayen ya saka su cikin tarunsa. Amma, irin wannan tunanin zai daɗa takaicinsa ne kawai. Ba wai Bitrus ya fito yin wasa ba ne; yana ciyar da mutane da wannan sana’ar ce ta kamun kifi. A ƙarshe, ya dawo bakin kogin ba tare da komi ba. Duk da haka, yana bukatan ya wanke tarun. Yana cikin yin hakan ne Yesu ya isa wurinsa.

Taron jama’a sun kewaye Yesu suna sauraron abin da yake cewa. Tun da yake sun kewaye shi, Yesu ya shiga cikin jirgin Bitrus kuma ya gaya masa ya ɗan ja jirgin kaɗan daga kan ƙasa. Da babbar murya, Yesu ya koyar da taron. Bitrus da mutanen da ke bakin kogin sun saurara sosai. Bai taɓa nuna cewa ya gaji da jin yadda Yesu yake tattauna ainihin jigon wa’azinsa ba, wato, Mulkin Allah. Zai kasance gata ya taimaka wa Kristi wajen yaɗa wannan saƙo na bege a ƙasar gaba ɗaya! Amma hakan zai kasance da sauƙi kuwa? Da me za su ciyar da kansu? Wataƙila Bitrus ya sake yin tunani a kan dukan wahalar da ya sha da daddare yana neman kifi.—Luka 5:1-3.

Sa’ad da Yesu ya kammala yin magana, sai ya gaya wa Bitrus: “A zakuɗa zuwa wuri mai-zurfi, ku jefa tarorinku, domin sū.” Bitrus yana cike da shakka. Ya ce: “Ubangiji, dukan dare muka yi wahala, ba mu sami kome ba: amma bisa maganarka sai in jefa tarori.” Babu shakka, Bitrus bai so ya sake jefa tarunsa ba, musamman ma a lokacin da kifayen ba za su fito cin abinci ba! Duk da haka, ya yi biyayya, wataƙila ya gaya wa abokan aikinsa da suke ɗayan jirgin su bi shi.—Luka 5:4, 5.

Bitrus ya ji wani irin nauyi sa’ad da ya soma jan tarun. Abin mamaki, ya sake ja da ƙarfi, kuma nan da nan, ya ga kifaye da yawa a cikin tarun! A razane, ya kira mutanen da ke jirgin na biyu su zo su taimaka masa. Sa’ad da suka zo, suka gane cewa jirgi guda ba zai iya ɗaukan kifayen ba. Sai suka cika jiragen biyu, amma duk da haka, da akwai saura da yawa, sai jiragen suka soma nitsewa saboda nauyin. Bitrus ya cika da mamaki. Ya ga yadda Kristi ya yi amfani da ikonsa a dā, amma wannan karon abin ya shafi shi da iyalinsa! Yesu mutumi ne da yake da ikon saka kifi cikin taruna! Bitrus ya cika da tsoro. Ya ɗurkusa kuma ya ce: “Ka rabu da ni, ya Ubangiji, gama ni mutum mai-zunubi ne.” Ta yaya zai taɓa iya yin tarayya da Wanda yake yin amfani da ikon Allah a waɗannan hanyoyin?—Luka 5:6-9.

Yesu ya ce: “Kada ka ji tsoro; daga nan gaba za ka kama mutane.” (Luka 5:10, 11) Wannan ba lokaci ba ne na yin shakka ko tsoro. Shakkar da Bitrus ya yi game da batutuwan nan kamar kamun kifi ba daidai ba ne, tsoronsa game da kurakurensa da laifofinsa ba su da amfani. Yesu yana da aiki mai girma da zai yi, hidimar da za ta canja tarihi. Yana bauta wa Allahn da ke “gafara a yalwace.” (Ishaya 55:7) Jehobah zai kula da bukatunsu, na zahiri da na ruhaniya.—Matta 6:33.

Bitrus ya ɗauki mataki nan da nan, kamar yadda Yaƙub da Yohanna suka yi. “Suka zo da jiragensu a wajen gaɓa, suka rabu da abubuwa duka, suka bi shi.” (Luka 5:11) Bitrus ya ba da gaskiya ga Yesu da kuma Wanda ya aiko shi. Wannan shawarar da ya yanke ita ce mafi kyau. Kiristoci a yau da suka sha kan shakka da tsoron da suke ji na yin hidimar Allah suna nuna bangaskiya kamar Bitrus. Irin wannan bangaskiyar ga Jehobah daidai ne.—Zabura 22:4, 5.

“Don Me Ka Yi Shakka?”

Shekaru biyu bayan ya saɗu da Yesu, Bitrus ya tuka jirginsa a Tekun Galili yadda aka ambata da farko. Ko da yake ba mu san tunanin da yake yi a lokacin ba. Amma, da akwai abubuwa da yawa da za a iya ambata! Yesu ya warkar da surukar Bitrus. Ya ba da Huɗuba a kan Dutse. Sau da yawa, ta hanyar koyarwarsa da ayyukansa masu ban al’ajabi, ya nuna cewa shi ne Almasihu, Zaɓaɓɓe na Jehobah. Bayan watanni sun wuce, laifuffukan Bitrus, kamar su jin tsoro da yin shakka, sun ɗan ragu. Yesu ya zaɓi Bitrus ya zama ɗaya daga cikin manzanni 12! Duk da haka, Bitrus bai kawar da jin tsoro da yin shakka ba gabaki ɗaya, kamar yadda za mu gani a gaba.

Wajen ƙarfe uku na dare, Bitrus ya daina tuka jirgin sai ya zauna tsaye. Can gaba da rakumin ruwa, ya ga wani abu yana tafe! Shin rakumin ruwan ne ke haskaka watan? A’a, wannan a tsaye yake. Mutum ne! E, mutum ne, kuma yana tafiya ne a kan tekun! Sa’ad da mutumin ya kusance su, ya yi kamar zai shiga tsakiyarsu. Cike da tsoro, almajiran suka yi tsammanin cewa mafarki suke yi. Sai mutumin ya ce: “Kwantadda hankalinku ni ne; kada ku ji tsoro.” Yesu ne!—Matta 14:25-28.

Bitrus ya amsa: “Ubangiji, idan kai ne, ka umurce ni in zo wurinka a bisa ruwaye.” Ya nuna gaba gaɗi a matakin da ya fara ɗauka. Cike da sha’awa don wannan mu’ujiza na musamman, Bitrus ya so ya daɗa nuna zurfin bangaskiyarsa. Yana son ya yi rabo a aukuwan. Da tawali’u, Yesu ya ce masa ya taho. Bitrus ya hau bakin jirgin sai ya dira cikin tekun. Ka yi tunani yadda Bitrus ya ji sa’ad da ya ga yana tafiya a kan ruwa. Babu shakka ya cika da mamaki sa’ad da ya soma tafiya zuwa inda Yesu yake. Amma, sai wani abu ya soma damunsa.—Matta 14:29.

Bitrus yana bukatan ya dogara ga Yesu. Yesu ne yake yin amfani da ikon Jehobah, don Bitrus ya yi tafiya a kan rakumin ruwan. Kuma Yesu yana yin hakan ne don bangaskiyar da Bitrus yake da ita a gare shi. Amma sai hankalin Bitrus ya rabu. Mun karanta: “Sa’anda ya ga iska, ya ji tsoro.” Bitrus ya ga yadda rakumin ruwan yake tura jirgin, yana ta da ruwan, sai ya ji tsoro. Wataƙila ya yi tsammanin cewa yana nutsewa cikin ruwan. Sa’ad da tsoronsa ya daɗu, sai bangaskiyarsa ta ragu. Mutumin da ake kira Dutse saboda ƙwazonsa na gaba gaɗi ya soma nutsewa kamar dutse saboda rashin bangaskiyarsa. Bitrus ya iya iyo sosai, amma bai dogara da wannan iyawar ba a yanzu. Sai ya ta da muryarsa: “Ubangiji, ka cece ni.” Sai Yesu ya kama hannunsa ya jawo shi. Sa’ad da suke kan tekun, Yesu ya koya wa Bitrus wannan darassi mai muhimmanci: “Kai mai-ƙanƙantar bangaskiya, don me ka yi shakka?”—Matta 14:30, 31.

“Yi shakka,” wannan furci ne mai muhimmanci! Yin shakka zai iya kai ga halaka. Idan muka bari ya rinjaye mu, zai iya raunana bangaskiyarmu kuma mu nutse a ruhaniyance. Muna bukatan mu yaƙi hakan sosai! Ta yaya? Ta wajen mai da hankalinmu inda ya kamata. Idan muka mai da hankali ga abubuwan da ke tsorata mu, abubuwan da ke sa mu sanyin gwiwa, abubuwan da za su iya raba hankalinmu daga Jehobah da Ɗansa, shakkarmu za ta ƙaru. Idan muka mai da hankalinmu ga Jehobah da Ɗansa, a kan abubuwan da suka yi, abubuwan da suke yi, da kuma waɗanda za su yi wa mutanen da ke ƙaunarsu, za mu kasance da bangaskiya mai ƙarfi.

Sa’ad da Bitrus ya bi Yesu zuwa cikin jirgin, ya ga rakumin ruwan na kwantawa. Tekun Galili ya kwanta. Bitrus tare da sauran almajiransa suka ce, “Hakika kai Ɗan Allah ne.” (Matta 14:33) Sa’ad da safiya ta soma yi, babu shakka zuciyar Bitrus ta cika da farin ciki. Ya kawar da shakka da kuma tsoro. Hakika, yana da ayyuka masu yawa da zai yi kafin ya zama Kirista mai kama da dutse da Yesu ya annabta. Amma ya ƙudurta ya ci gaba da yin ƙoƙari, da kuma samun ci gaba. Kai ma kana da irin wannan ƙudurin? Babu shakka, za ka ga cewa bangaskiyar Bitrus abin koyi ne.

[Hoton da ke shafi na 30, 31]

Yesu ya ga abubuwa masu kyau da yawa a cikin wannan ɗan sū mai tawali’u

[Hoton da ke shafi na 31]

‘Ubangiji, ni mutum mai zunubi ne’

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba