Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 10/15 pp. 17-21
  • Yadda Za A Ci Gaba Da Abuta A Duniya Marar Ƙauna

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za A Ci Gaba Da Abuta A Duniya Marar Ƙauna
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Menene Tushen Abota Mai Kyau?
  • Yadda Za Mu Samu Abokan Kirki
  • Sa’ad da Ake Bukatar a Daina Abokantaka
  • Yadda Za a Ci Gaba da Abuta Mai Kyau
  • Mene ne Baibul Ya Ce Game da Yin Abokantaka?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ka Zabi Abokan Kirki
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ka Yi Abokantaka da Masu Kaunar Allah
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 10/15 pp. 17-21

Yadda Za A Ci Gaba Da Abuta A Duniya Marar Ƙauna

“Waɗannan abubuwa na ke umurtanku, domin ku yi ƙaunar juna.”—YOH. 15:17.

1. Me ya sa Kiristoci na ƙarni na farko suke bukatar su zama abokai na kud da kud?

ADARENSA na ƙarshe a duniya, Yesu ya ƙarfafa almajiransa masu aminci su zama abokai ga juna. Da yamma, ya faɗa cewa ƙauna da suka nuna wa juna za ta nuna cewa su mabiyansa ne. (Yoh. 13:35) Manzannin suna bukatar su zama aminai idan za su jimre wa gwaji da za su fuskanta a gaba kuma su cim ma aikin da Yesu zai ba su ba da daɗewa ba. Hakika, an san Kiristoci na ƙarni na farko don ibadarsu ga Allah da kuma juna.

2. (a) Menene muka ƙuduri aniyar yi, kuma me ya sa? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika?

2 A yau, abin farin ciki ne da yake muna tarayya da ƙungiya na dukan duniya da waɗanda suke ciki suke bin gurbin da Kiristoci na ƙarni na farko suka kafa! Mun ƙuduri aniya mu yi biyayya da umurnin Yesu na nuna tabbataciyar ƙauna ga juna. Amma, a wannan kwanaki na ƙarshe, yawancin mutane marasa aminci ne da kuma marasa ƙauna irin na tabi’a. (2 Tim. 3:1-3) Sau da yawa ba sa ƙulla abota na ƙwarai kuma suna son kai. Don mu ci gaba da kasancewa Kiristoci na gaskiya, dole ne mu guji irin waɗannan halayen. Bari mu bincika tambayoyi na gaba: Menene tushen abota mai kyau? Ta yaya za mu samu abokai na ƙwarai? A wane lokaci ne za mu iya daina dangantaka da wani aboki? Kuma yaya za mu ci gaba da yin abota mai ƙarfafawa?

Menene Tushen Abota Mai Kyau?

3, 4. Menene tushen abuta na ƙwarai, kuma me ya sa?

3 Ana ƙulla abota mai ƙarfi bisa ƙauna ga Jehobah. Sarki Sulemanu ya rubuta: “Idan mutum ya rinjayi wanda shi ke shi kaɗai, biyu za su iya tsaya masa; igiya riɓi uku kuma ba shi tsunkuwa da sauri ba.” (M. Wa. 4:12) Idan Jehobah ne igiya ta uku a abota, wannan abota za ta daɗe.

4 Hakika, waɗanda ba sa ƙaunar Jehobah su ma suna iya ƙulla abota mai gamsarwa. Amma, idan ƙauna ga Allah ne ta sa mutane suka zama abokai, dangantakarsu za ta kasance da ƙarfi. Idan jayayya ta taso, abokan kirki za su bi da juna a hanya da ke faranta wa Jehobah rai. Idan masu hamayya da Allah suka yi ƙoƙari su jawo rabuwa, waɗannan abokan gaba suna fahimtar cewa ba a raba abuta tsakanin Kiristoci na gaskiya. A cikin tarihi, bayin Jehobah sun nuna cewa suna shirye su mutu maimakon su ci amanar juna.—Karanta 1 Yohanna 3:16.

5. Me ya sa abota tsakanin Ruth da Naomi ta daɗe sosai?

5 Babu shakka, abuta mafi gamsarwa ita ce wadda aka ƙulla da waɗanda suke ƙaunar Jehobah. Ka yi la’akari da misalin Ruth da Naomi. Waɗannan mata sun ƙulla abota wadda take cikin abota mafi kyau da aka rubuta cikin Littafi Mai Tsarki. Menene ya sa abotarsu ta daɗe? Ruth ta bayyana dalilin sa’ad da ta gaya wa Naomi: “Danginki za su zama dangina, Allahnki kuma Allahna . . . Ubangiji ya yi mani hukunci mai zafi, idan ba mutuwa kaɗai ta raba ni da ke.” (Ruth 1:16, 17) Babu shakka, Ruth da Naomi suna ƙaunar Allah sosai, kuma sun ƙyale wannan ƙaunar ta shafi yadda suke bi da juna. Saboda haka, Jehobah ya albarkaci waɗannan matan.

Yadda Za Mu Samu Abokan Kirki

6-8. (a) Menene ke sa abota ta daɗe? (b) Ta yaya za ka ɗauki matakin samun abokai?

6 Misalin Ruth da Naomi ya nuna cewa ba a samun abokan kirki haka kawai. Ƙauna ga Jehobah ne tushen ta. Amma, abuta da take daɗewa tana bukatar aiki tuƙuru da sadaukar da kai. ’Yan’uwa a cikin iyalan Kirista da suke bauta wa Jehobah suna bukatar su yi aiki tuƙuru don su ƙulla abota na kud da kud. To, ta yaya za ka iya samun abokan kirki?

7 Ka ɗauki mataki. Manzo Bulus ya ƙarfafa abokansa a cikin ikilisiyar Roma su “himmantu ga yi wa baƙi alheri.” (Rom. 12:13; Littafi Mai Tsarki) Don mu samu abokan kirki muna bukatar mu yi amfani da kowane zarafi don mu yi alheri. Babu wanda zai yi alheri dominka. (Karanta Misalai 3:27.) Hanya ɗaya da za ka samu abokai ita ce ta gayyatar mutane dabam dabam a cikin ikilisiya su ci abinci tare da kai. Za ka sa yin alheri a kai a kai ga waɗanda suke cikin ikilisiyarku ya zama halinka?

8 Wata hanya da za ka ɗauki matakin samun abokai ita ce ta wajen gayyatar mutane dabam dabam su fita aikin wa’azi tare da kai. Sa’ad da ka tsaya a ƙofar mai gida kuma ka ji abokin hidimarka yana magana da dukan zuciyarsa game da ƙaunarsa ko nata ga Jehobah, za ka kusaci wannan abokin hidimarka.

9, 10. Wane misali ne Bulus ya kafa, kuma yaya za mu iya yin koyi da shi?

9 Ka nuna ƙauna ga dukan mutane. (Karanta 2 Korintiyawa 6:12, 13.) Ka taɓa ji kamar babu kowa a cikin ikilisiyarku da zai iya zama abokinka? Idan haka ne, kana sa iyaka ne game da wanda kake tunani zai iya zama abokinka? Manzo Bulus ya kafa misali mai kyau na nuna ƙauna ga mutane. A wani lokaci, bai taɓa tunani cewa zai ƙulla abota da waɗanda ba Yahudawa ba. Amma, ya zama “manzon Al’ummai.”—Rom. 11:13.

10 Ƙari ga haka, Bulus bai yi abota da tsaransa ba kawai. Alal misali, shi da Timotawus sun zama aminai duk da bambancin shekara da kuma yanayinsu a rayuwa. A yau, matasa da yawa suna ɗaukan abota da suka ƙulla da tsofaffi da suke cikin ikilisiya da tamani. “Ina da wata ƙawa da take cikin shekarunta na hamsin zuwa sattin” in ji Venessa, wata matashiya. “Zan iya gaya mata kome da zan iya gaya wa abokai da ke tsarata. Kuma tana ƙauna ta sosai.” Ta yaya ake ƙulla irin wannan abuta? Vanessa ta ce: “Na yi ƙoƙari ne na ƙulla wannan abota, ban jira ba wani ya zo ya same ni.” Kana shirye ka ƙulla abota da waɗanda ba tsaranka ba ne? Babu shakka Jehobah zai albarkace ka saboda ƙoƙarce-ƙoƙarcenka.

11. Menene za mu iya koya daga misalin Jonathan da Dauda?

11 Ka kasance mai aminci. Sulemanu ya rubuta: “Aboki kullayaumi ƙauna ya ke yi, kuma an haifi ɗan’uwa domin kwanakin shan wuya.” (Mis. 17:17) Sa’ad da yake rubuta waɗannan kalmomin, mai yiwuwa Sulemanu yana maganar abota da babansa Dauda ya more da Jonathan. (1 Sam. 18:1) Sarki Saul ya so ɗansa Jonathan ya gāji karagar Isra’ila. Amma Jonathan ya amince cewa Jehobah ya zaɓi Dauda ya zama sarki. Ba kamar Saul ba, Jonathan bai yi kishin Dauda ba. Bai yi fushi ba don an yabi Dauda, kuma bai gaskata da tsegumi da Saul yake yaɗawa game da Dauda ba. (1 Sam. 20:24-34) Muna aikatawa kamar Jonathan kuwa? Sa’ad da abokanmu suka sami gata, muna farin ciki da su kuwa? Sa’ad da suke shan wahala, muna ƙarfafa da kuma tallafa musu kuwa? Idan mun ji gulma game da wani aboki, muna saurin yarda da hakan? Ko kuwa kamar Jonathan, muna kāre abokinmu cikin aminci?

Sa’ad da Ake Bukatar a Daina Abokantaka

12-14. Wane kaluɓale ne wasu ɗaliban Littafi Mai Tsarki suke fuskanta, kuma ta yaya za mu iya taimaka musu?

12 Sa’ad da ɗalibin Littafi Mai Tsarki ya soma yin canje-canje a salon rayuwarsa, yana iya fuskantar kaluɓale sosai game da yin abota. Mai yiwuwa yana da abokai da yake jin daɗin yin tarayya da su amma ba sa bin mizanan Littafi Mai Tsarki game da ɗabi’a. A dā, wataƙila yakan kasancewa da su a kai a kai yana cuɗanya da su. Amma yanzu, ya ga cewa ayyukansu zai iya zama mugun tasiri a gare shi, kuma ya ga cewa yana bukatan ya rage tarayya da irin waɗannan abokai. (1 Kor. 15:33) Duk da haka, yana iya jin cewa idan bai yi tarayya da su ba, yana rashin aminci.

13 Idan kai ɗalibin Littafi Mai Tsarki ne da yake cikin wannan yanayin, ka tuna cewa abokin kirki zai yi farin ciki cewa kana ƙoƙari ka kyautata rayuwarka. Shi ko ita zai so ya bi ka wajen koyo game da Jehobah. A wata sassa, abokan ƙarya za su yi ‘aibatanka’ domin ba ka bi su “zuwa cikin haukar lalata” ba. (1 Bit. 4:3, 4) Hakika, waɗannan abokan ne suke maka rashin aminci, ba kai ba.

14 Sa’ad da abokansu na dā da ba sa ƙaunar Allah suka yi watsi da ɗaliban Littafi Mai Tsarki, waɗanda suke cikin ikilisiya za su zama abokansu. (Gal. 6:10) Ka san waɗanda suke halartan taronku da suke nazarin Littafi Mai Tsarki? A wani lokaci kana tarayya mai ƙarfafawa da su kuwa?

15, 16. (a) Yaya ya kamata mu aikata idan abokinmu ya daina bauta wa Jehobah? (b) Ta yaya za mu nuna ƙaunarmu ga Allah?

15 Idan wani abokinka da ke cikin ikilisiya ya tsai da shawara ya ko kuma ta juya wa Jehobah baya kuma fa, wataƙila yana bukatan a yi masa yankan zumunci? Irin wannan yanayin yana iya kawo baƙin ciki. Da take faɗan yadda ta ji sa’ad da wata ƙawarta ta daina bauta wa Jehobah, wata ’yar’uwa ta ce: “Na ji kamar wani abu a cikin jikina ya mutu. Ca nake ƙawata ta kafu sosai a cikin gaskiya, amma ba hakan ba. Na yi tunani ko dama tana bauta wa Jehobah ne don kawai ta faranta iyalinta. Sai na soma sake bincika muradina. Ina bauta wa Jehobah don dalilai da suka dace ne? Ta yaya wannan ’yar’uwar ta jimre? Ta ce: “Na tura nawayata ga Jehobah. Na ƙuduri aniya na nuna wa Jehobah cewa ina ƙaunarsa ba don kawai ya ba ni abokai cikin ƙungiyarsa ba.”

16 Kada mu yi tsammanin za mu ci gaba da zaman abokin Allah idan mun bi waɗanda suka zaɓa su zama abokan duniya. Almajiri Yaƙub ya rubuta: “Ba ku sani ba abutar duniya magabtaka ce da Allah? Dukan wanda ya ko so shi zama abokin duniya fa yana maida kansa magabcin Allah.” (Yaƙ. 4:4) Muna iya nuna muna ƙaunar Allah ta wajen kasancewa da aminci cewa zai taimaka mana mu jimre da rashin abokinmu idan muka kasance da aminci a gare shi. (Karanta Zabura 18:25.) ’Yar’uwa da aka ambata ɗazu ta kammala hakan: “Na koya cewa ba za mu iya sa wani ya ƙaunaci Jehobah ba ko kuma ya ƙaunace mu. Mutumin ne zai yi zaɓin da kansa.” Amma, menene za mu iya yi don mu ci gaba da abuta mai ƙarfafawa da waɗanda suke cikin ikilisiya?

Yadda Za a Ci Gaba da Abuta Mai Kyau

17. Ta yaya abokan kirki suke magana ga juna?

17 Tattaunawa tare na sa abokai su kusaci juna. Sa’ad da ka karanta labaran Littafi Mai Tsarki game da Ruth da Naomi, Dauda da Jonathan, da kuma Bulus da Timotawus, za ka lura cewa abokai suna magana a sake amma suna daraja juna. Game da yadda za mu tattauna da wasu, Bulus ya rubuta: “Bari zancenku kullum ya kasance tare da alheri, gyartace da gishiri.” A nan Bulus ainihi yana magana game da yadda za mu yi magana ga waɗanda “ke waje” wato, waɗanda ba ’yan’uwanmu Kirista ba. (Kol. 4:5, 6) Hakika, idan waɗanda ba masu bi ba suna bukatan mu daraja su sa’ad da muke musu magana, abokanmu da ke cikin ikilisiya sun fi cancanta mu yi musu hakan!

18, 19. Yaya ya kamata mu ɗauki kowane gargaɗi da wani aboki Kirista ya ba mu, wane misali ne dattawa da suke Afisa suka kafa mana?

18 Abokan kirki suna daraja ra’ayin juna, saboda haka tattaunawa tsakaninsu ya kamata ya kasance da alheri da kuma kai tsaye. Sarki Sulemanu mai hikima ya rubuta: “Mai na shafawa da turare su kan faranta zuciya: Haka nan ne kuma daɗin abokin mutum, wanda ya fito daga wurin shawarar kirki.” (Mis. 27:9) Haka ne kake ɗaukan kowace shawara da wani aboki ya ba ka? (Karanta Zabura 141:5.) Idan abokinka ya nuna damuwa game da wani tafarkin da kake bi, yaya kake aikatawa? Kana ɗaukan irin wannan kalaman a matsayin ƙauna ta alheri, ko kuwa kana fushi?

19 Manzo Bulus ya more dangantaka na kud da kud da dattawan da ke ikilisiyar Afisa. Wataƙila ya san wasu cikin waɗannan maza sa’ad da suka zama masu bi. Amma, a taronsa na ƙarshe da su, ya ba su gargaɗi kai tsaye. Yaya suka aikata? Abokan Bulus ba su yi fushi ba. Maimakon haka, sun yi godiya da yadda ya damu da su, har ma sun yi kuka don ba za su sake ganinsa ba.—A. M. 20:17, 29, 30, 36-38.

20. Menene abokin kirki zai yi?

20 Abokan kirki suna karɓan gargaɗi mai kyau kuma suna ba da gargaɗi ga wasu. Hakika, muna bukatan mu fahimci sa’ad da za mu yi namu “sha’ani.” (1 Tas. 4:11) Kuma dole ne mu fahimci cewa kowanenmu “za ya kawo lissafin kansa ga Allah.” (Rom. 14:12) Amma idan bukata ta kama, abokin kirki zai tuna wa abokinsa game da mizanan Jehobah. (1 Kor. 7:39) Alal misali, menene za ka yi idan ka lura cewa abokinka da bai yi aure ba yana ƙulla dangantaka na soyayya da wadda ba mai bi ba ce? Don kana tsoron ɓata wa abokinka rai, za ka guji gaya wa abokinka damuwarka? Ko kuma idan abokinka ya yi banza da gargaɗinka, menene za ka yi? Abokin kirki zai nemi taimakon makiyaya masu ƙauna su taimaka wa abokinsa da ya yi laifi. Ɗaukan irin wannan mataki yana bukatar gaba gaɗi. Duk da haka, abuta da ke bisa ƙauna ga Jehobah ba zai ɓace dindindin ba.

21. Menene dukanmu za mu yi a wani lokaci, amma me ya sa yake da muhimmanci mu ƙulla abuta da za ta daɗe a cikin ikilisiya?

21 Karanta Kolosiyawa 3:13, 14. A wani lokaci, za mu ba abokanmu dalilin “ƙara” game da mu, su kuma za su yi ko kuma su faɗa abubuwa da za su ɓata mana rai. Yaƙub ya rubuta, “a cikin abu dayawa dukanmu mu kan yi tuntuɓe.” (Yaƙ. 3:2) Amma, abin da ke nuna abuta ba yawan lokaci da muka yi wa juna laifi ba amma yadda muke gafarta waɗannan laifuffuka gabaki ɗaya. Yana da muhimmanci mu ƙulla abuta da za ta daɗe ta wajen faɗan zuciyarmu sa’ad da muke tattaunawa da kuma gafarta wa juna! Idan mun nuna irin wannan ƙaunar, za ta zama “magamin kamalta.”

Yaya Za Ka Amsa?

• Ta yaya za mu samu abokan kirki?

• A wane lokaci ne ya kamata mu daina abuta da wani?

• Menene za mu yi don mu ƙulla abuta da za ta daɗe?

[Hotunan da ke shafi na 18]

Menene tushen abuta da ta daɗe tsakanin Ruth da Naomi?

[Hotunan da ke shafi na 19]

Kana nuna karimci a kai a kai?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba